Showing 36001 words to 39000 words out of 131659 words

Chapter 13 - Mazan Ko Matan Complete Hausa by M Shakur.pdf

M Shakur   

13 Nov 2025

372

Anty Jams Nuri yataba gayamiki yadawo daga
office babu abinci agidan nan? Ba abinci about kala biyu akan dinning cikin warmers?? Ko
yadawo yaga dakinshi ko bayinshi da datti ko singlets da boxers nashi ba’a wanke ba? Bazaki
taba shigowa gidana ki ga datti ko daya ba akasa ko ki taka kasa, ko issues damuka samu this
time kan Mamanshi sabida rainin dayamin ne sai bayan yace suzo zai sanar dani amman tunda
mukai aure nataba samin matsala da uwarsa? No, mukaje kano mu sauka agidan nadan wuni
daganan na gudo gidanmu so menayi? Police dana dauko is because Shegiyar kanwarsu had
the audacity tashigo har gidana ta nemeni da fada tana zagina takuma yakusheni da kumbunan
vampires nata, I need to show them no one can bully Hadiza in her house, so Anty Jams
menene kike fadamin? Inada damuwa which kinsan bazan iya fadama friends dinaba sumin
dariya bayan cika bakin danagama yi na inada karfi da iko agida suga abinda mijina kemin, I
called u cus kene sister na and look at wat u are telling me eh, nayi deserving abinda Nuri
kemini? Ya dannamini saki daya yanzu kuma ya maidani thrash ya kwashe yarana, shima yabar
gidan yabarni ni kadai inata kwana agidan nan kaman mayya, sannan ina kiranshi yana kashe
waya kuma nasan yana kunna wayanshi dan nasan dole yakira mamanshi kuma yaga
messeges dina yayi ignoring, ina gayamiki kina mini masifa that i failed as a mom and a wife

what have I done? Menayi? Eh”? Duk yanda taso ta daure ta rike zuciyanta kartai kuka takasa
sai kawai tafashe da kuka awayan ita karan kanta bazata iya misilta kalan zafin datakeji ba na
yanda Nuri ke soyata a pan dinan, ance dama blood is thicker that water wani iri Anty Jamila taji
hakan yasa cikeda lallashi tace “Hadiza kinfi kowa sanin yanda nake sonki, tun kina yar karama
you’ve always being my DiDi, Hadiza mun taso cikin tarbiya mai kyau muke aikin gida I
remember lokacin idan yau nine da shara to kene da wanke wanke, the next day nine da wanke
wanke kene da shara same goes for girki, Hadiza Baba da Mama nada rufin asiri mun taso
bamu rasa komiba but we were trained muma kanmu komi muke wanki, muje aike bamu da yar
aiki Hadiza, mun taso munga yanda Mama kema Baban mu girki tabashi, tamishi komi, Nura ya
nuna shi girkin ki yakeso yaci how many minutes zai daukeki kimai? Is just breakfast and dinner
da rana yana office, Hadiza Nura ba dan Abuja bane that’s wat nakeso ki gane bazamfare ne
girman kano, ya nunamiki he doesn’t want the Abuja lifestyle dole ne saikinyi lifestyle din to
please your friends and co? This is peer pressure Hadiza, must u do abinda kikaga anayi
agarinku? Anyi magana kice feminism you know your rights Nura yafiki sanin rights naki tunda
har mutumin nan zai bude miki kasuwanci ya daukeki kuje garuruwa ki samo contact na
suppliers ki saro kaya, Hadiza Nura na mugun sonki how many men zasu iya ma matansu
abinda Nura yamiki yet baki da wanda zaki cima mutunci sai shi sabida kinganshi shiru shiru
baida hayaniya kuma yana sonki saikikai abusing simplicity nashi” hawaye Hadiza ta share cikin
muryan kuka tace “Anty idan baka rikema maza wuta ba cin ubanka suke, ga Baraka nan
mijinta juyata yake kaman lagwani, yahanata business kudi sai wanda yaga dama zai dan
yammata, gashi da mata ihu agaban kowa haka kikeso Nura yamaidani? Ya takani duk sanda
yaso? Noo bazan yarda ba wlh, fire for fire yanzu shine new system na zaman lafiya tsakanin
mata da miji agidan aure” Anty Jamila tace “Noo fire for fire is never option, look at you yanzu
jibi yanda kike kuka kina bala’in son mijinki but girman kai da al’adan yahudu da nasara yasa
you are gradually loosing him” dasauri Hadiza tace “I reject it Anty Jams, bazan taba loosing
Nuri na ba, yana bala’in sona, duk yan uwanshi ne da Mamanshi suka gama zugashi, Nuri
baitabamin hakaba, Nuri kome zanmai baya fushi dani, baida riko ko ijiye mutum azuciya, he
will still come back to me and talk to me and call me, Nuri na baitaba shareni ba, wlh all this
aikin Maman shi ne da kanwarsa kuma muzuba da ni da su” girgiza kai Anty Jamila tayi zatai
magana Hadiza ta tareta tace “karki damu you’ve said enough Anty Jams ko’ina Nuri yaje zaizo
har nan har gidan nan yasameni bawai ina kukane sabida abin yawani dameni ba, kukan
danakeyi na bakin ciki ne cus nine yakamata na dinga cusama namiji kalan bakincikin nan ba
namiji ya dinga cusamin ba ninefa Anty Jams is still me Hadiza bakatakani bama nabaka
hot-hot balle kuma katakani, wlh Nuri zai gane ni yagasama aya a heart, saida safe” bama ta
jira amsan Anty jams ba ta katse wayan ta ijiye wayan tanabin dakinta da kallo gidan gabaki
daya bayamata dadi sabida yanda ba kowa ciki, mutum rahama ne hayaniyan yaranta is
something, kawai she’s not enjoying komi, mamaki take take kuma karayi itane Nuri bazai
returning call nataba, lallai Nuri don get liver, tasaba saidai ita ta katsemai waya amman wai
itane ya katsema waya tun ranan yaki kiranta back, yaki replying messege nata, hmmm takasa
yarda ita Nuri zaima haka cus baitaba mata iskancin maza haka ba tunda sukai aure sai yau, da
wannan abin har gwara ya mareta ma eh tasan mari ne bakaramin shiganta wannan silent da
ignoring attitude din da Nura yamata ke damun zuciyanta ba.
****

Bayan 2weeks
Cur Nura yabuga two weeks yana gogan lafiyayyen amarci shida Ummi, yaki kiran Hadiza ko
returning calls nata but yana kiran mai gadinshi everyweek yaturamai kudi ayi cefene wanda
dama haka yakeyi dudda yasan ba girkawa zatayiba Mamanshi da yaranshi kusan kullum sai
sunyi waya daman. Lafiyayyen soyayya yake bugawa shida Ummi jinshi yake kaman wani sarki ko shugaban kasa
ne ma zai fadi, baitaba sanin yar kauye can give him this much respect, affection, peace and
love ba saida ya aureta, wlh ayanda Ummi kemai da ace an halasta a addini cewa mata ta
bautama mijinta da Ummi zata bautamai ba tantama that girl is just an Angel, saisa shima he
became like a fool kome takeso koda batace tanamaso ba zai mata.
Yau zasu koma Abuja jirginsu is by 1, yadan fita haka yabarta tana yima su Amal wasu kayan
zaki a kitchen, dudda she’s hiding it but he could see fear a idanunta.
Tana zaune a kitchen tana kallon wasu cute robobi data jera su Iloka, kwakumeti, tuwon
madara, tsami gaye, gullisuwa data musu tayi shiru tana tunani, bini bini gabanta na fadi
batasan yaya zata kalli Anty ba, ita tunanin ta kenan danta dauka Nura ya sanar da Hadiza,
baitaba mata maganan Hadiza ba ko yace any bad thing about her kullum abunsu suke baya
kawo sunan matarshi aciki. Tana zaune taji an manna mata kiss dasauri ta dago kanta Nura ne,
robobin ya kwasa dagakan kujeran yazauna yana facing nata yace “ya akayi Hajiya Ummi
tunanin me kike”? Murmushi tamai cikeda wayincewa tace “bakomi kawo naje nayi parking a
akwati” tai maganan tana mikewa dasauri tajuyar da kanta zata tafi karaf Nura ya kamo
hannunta tsayawa tayi batare daya juyoba robobin ya kalla yace “baki amsaba zaki tafi kuma
gashi” dasauri takai hannunta tashare hawayen daya zubomata sannan tajuyo Nura yabi
kwayan idanunta da kallo hannu tamikamai ahankali tace “kawo” kin bata yayi ya ijiye robobin a
gefe ya mike yakai hannunshi kan fuskanta yace “menene? Meke damunki? Talk to me menene
damuwanki Ummi”? Girgizamai kai tayi dasauri tana kokarin kauda kanta tanaso ta ture
hannunshi saikuma kuka ya kufce mata dasauri ta fizge kanta ta juya tareda kifa kanta a
bangon kitchen din yanda yara keyi tafashe da kuka sosai tace “ni banso nakoma Abuja kabarni
anan naci amanar Anty bazan iya kallonta ba, nasan tunda ka sanar da ita zancen Auren nan
zuciyanta bazai mata dadi ba babu wacce keson kishiya barinma yar aikin ka, wlh wlh Allah ma
yaga zuciyana bantaba so na aurema Anty Miji ba Auren kaman amafarki haka nima naga
yafaru, banda kirki My Noor, ban kyautama Anty ba” Nura yadade yana kallonta all he sees is
tsantsan childishness da rashin wayau, tahowa yayi ahankali wajen yajuyo da ita hannunshi
yakai kan fuskanta yana sharemata yace “jibi yanda kika bata kwalliyan dakikamin eh” ahankali
tace “kayakuri” murmushi yayi this is one reason dayasa yake kara sonta she apologize to him
ko bataimai laifi ba, ahankali tana jikinshi yace “bazan taba iya barin matata awani gari ba ni ina
wani gari, maza dayawa na haka but ni baya cikin tsarina Inason duk inda nake iyalina na wajen
kinajina” gyadamai kai tayi ahankali, anatse yace “bakici amanan Hadiza ba ni mijin mata hudu
ne, nan gaba still idan naji inada bukatan kara aure still zanyi Ummi, so bakiyi laifiba” yayi
maganan kai tsaye yace “dake da Hadiza dukanku matayena ne daya kuke awajena babu
wacce tafi wata and dukanku kuna karkashina ne, nina aureki bake kika aure ni ba, inma laifine
aure kinga kenan nine nai laaifin bakeba dan nine na aureki, idan mun koma gida ki bata
girmanta amatsayinta na wacce ta girmeki sannan mahaifiyar su Aman da Amal ban yarda ki

mata rashin kunya or anything ba dudda nasan ba halinki bane kada ki shiga harkanta kome
zatace idan kinga bazaki iyaba ki shiga daki ki kulle kofa ki kirani muyi waya idan bananan but
kada kiyi fada da ita okay” gyadamai kai tayi, ahankali ya manna mata kiss a goshi yace “Ummi
ina sonki sabida kina bani kwanciyan hankali kada ki chanza daga hakan okay” gyadamai kai
tayi, idanunta dasuka cika da hawaye ya kalla yanda fuskanta ya kwabe sai kawai yaji
sha’awanta yakamashi hannunshi yadaga yakalli Rolex dake daure a writs nashi yace “akwai
sauran time zoki bani hakkina daman jiya da daddare sau biyu kawai nayi kikahau bacci
raguwa” murmushi tayi tana turamai baki kaman yar yarinya cikeda so tace “nan fa kitchen ne”
yana daga riganta sama yace “eh nima ilokan wajen zan dafa a kitchen inci tunda ni bancin na
roba ba” dariya Ummi tayi tace “saina cinye bakinka yau” kawomata bakin yayi yace “ai nace
nabaki tunda ke kinfi son kiss kan komi kin sa lips dina sun kara pink tsabagen tsotsa oya
sumbaceni” kaman jira take dasauri tayi grabbing lips nashi tashiga kissing nashi ya mannata
abango yana kissing nata back yana warware wando yana ja kasa……


Saura kadan suyi missing flight nasu amman Alhamdulillah sunkai on time daman business
class yabiya nan da nan sukai boarding, ashe ranan nan data daure sabida mutane ne yau
harsuka sauka Abuja tana rungume ajikinshi sunyi kyau daga ita harshi ruwan amarci yasa
Nura yakara haske yana sheki yadan kara kiba sabida abincin dayake samu akai akai itakuma
Ummi kaman ba itaba fatanta ya goge tana sheki hannunta rikeda Samsung Z-flip dan kaita
shago yayi yace ta zaba shita zaba wai sabida yanda yake budewa yana rufewa ya saya mata
shikuma yana rike da hannunta suka fito suka shiga jeep dake jiransu wanda yaron Nura ne na
office ya gaida Ummi akunyace ya amsa dudda tana shakkan zuwa su gida amman daurewa
tayi ga mamakinta wani gida daban sukaje Nura yace “muje Muga Hajiya ko sai mu dauko
yaran mu anjima saimu tafi gida” gyadamai kai tayi parking sukayi gidane babba mai kyau suka
shiga suna sallama a babban falon inda su Aman da Amal ke wasa da guje guja dawata
karaman yarinya dasu Hajiya da Meena da Matar Baffan shi yaran suka juyo wani irin ihu da
Amal da Aman sukayi suka taho dagudu bude hannu Nura dake gabansu yayi suka taho aguje
ga mamakinshi wucewa sukayi suka rungume Ummi Amal sai kawai tafashe da kuka shima
Aman haka Ummi kawai ta yarda handbag da wayanta ta rungume yaran itama saiga hawaye
shiru daga Nura har duka yan dakin sukayi suna kallonsu Nura saiyaji yakara jin dadi da
natsuwa dakuma hamdala da auren Ummi dayayi da kyar Ummi ta iya sakinsu cikeda dabara
tace “ga Dadyn ku bakumai oyoyo ba” sakin Ummi sukayi da sauri sukai wajen Dadyn su Ummi
kuma tazo wajensu Hajiya ta duka ta gaishesu bayan anyi gaishe gaishe aka kawo abinci sukai
nak Nura yafita sallan la’asar itama Hajiya tace bari nayi, Ummi taje ta cewa Meena pls Meena
je mota ki bude akwatina akwai wani leda shine a saman kayana ki kawomini abin Hajiyane”
murmushi Meena tayi tace “nifa” dasauri tace “naki na handbag dina” wucewa Meena tayi tafita
bata wani jimaba takawoma Ummi ummi ta karba Meena tace “je daki ki kaimata mana kina
kuma jin kunya ni natafi kitchen” wucewa Meena kitchen tayi Ummi tawuce dakin, Hajiya na
zaune kan dadduma Ummi tayi sallama Hajiya tace “shigo mana Ummi aiba saikin jira nace ki
shigo ba shigo shigo maza” dakin Ummi tashiga har gaban Hajiya ta duka akunyace tabama
Hajiya ledan tace “Hajiya ga tsaraban dana yo miki ba yawa” dasauri Hajiya tazaro idanu tace
“laaaaaa Ummi harda wani yimini tsaraba ikon Allah, toooo Allah yayi Albarka Ummi, Allah

yakawo kazantar daki” bude ledan tayi wasu manyan atampopi ne guda biyu akwatin nan da
Nura yakawo gida ranan kayanta ne daya sayomata su kafin yamata proper akwati, an dinka
wasu some baa dinka ba amman tadauko atampopi wayanda sukafi kyau aciki guda biyu,
tasama Hajiya wani soft silipas dan madina blue da ake saidawa akauyensu tasayo, da irin
dankwalayen nan na tsofaffi kallabi masu kyau guda uku daban daban, ga mamakin Ummi sai
kawai Hajiya tafashe da kuka sosai tana kallon kayan tace “Ummi ni kikasiyoma duka
abubuwan nan”? Adan tsorace Ummi ta kalleta danta tsorata kartaga kaman ta rainata tanada
yara masu kudi yarta na Egypt amman tazo tana mata kyautan danmadina, sai kawai taga
Hajiya tahau kwalama Meena da matan baffansu kira dasauri suka shigo cikeda kukan farin ciki
tace “Karime, Meena ku kalli abinda yarinyar nan tasayo mini, babu wanda yataba siyamini
tsaraba irin wannan daya faranta mini rai haka, nadade ina neman dan madina sabida ciwon
kafana kinsan takalmin da laushi duk silipas da ake sayomini saidai nasa ba yanda zanyi, jibi
kalluba ku kalli atampopi na, Allah miki albarka Ummi, yanda kika faranta mini ubangiji Allah ya
fara tamiki” sai kawai sukahau yima Ummi godiya akunyace ta tashi tafita Meena tabiyota
sukaje dakin da Meena ke kwana sai Meena taji takara sonta sabida yanda tasaka Hajiya farin
ciki kuma tai alkawari zata kira su Ya Aisha dukta fadi musu dudda tasan ma Hajiya zata fadi,
dan babu wanda bazaiji labarin kyautan nan ba yau haka Hajiya taje bata boye abin arziki.

Nura na shigowa gidan Hajiya tace “Nura kalli tsaraban da matanka tayomini ohhh Nura
yarinyar nan Ummi saidai Allah ya yimata albarka kawai, kasan yanda silipas din nan da
kalluban nan sukamin dadi kuwa, gashi yamin chass akafa, achan achan Masha Allah kaga
kiramini kanwarka Aishaa nagaya mata abinda matarka tamin” yana xaune nan yana taya
Hajiya dialing numbers saida takira yaranta uku mata ta gayamusu sukace asa Meena ta tura
musu lomban amaryan Ya Nura duk zasu kira sunata godiya.
Yanda Hajiya ke murna tana fadama kowa kyautan nan sai shiwa Ummi albarka take bakaramin
dadi Nura yaji aranshi ba yana kallon atampopin, shine yasayo su anan Adamawa abinda yafi
bashi mamaki yanda sunfi kowani atampa kyau cikin kayan daya sayo mata, design nasu is so
beautiful but suta dauka tabawa Hajiya kuma wlh bata fadamai ba, baimasan tana tareda
takalman nan ko kallbin nan ba that means tun akuayensu tasayo, kawai saiyaji yakara
respecting yarinyar imagine ko shi baisayo musu tsaraba ba shi dama ansanshi baya tsaraba
bai iya riko tsarababa amman yatashi sayo abu zai shiga super market ya jido kaya, abin really
touched him bazaima iya misilta dadin dayaji ba, duk wanda zai tayashi da Hajiyan shi farin ciki
babu abinda bazaima mutumin ba cus Hajiya number 1 ce arayuwanshi.
Zama yayi abinshi tareda Hajiya anan dakin nata sunata hira bini bini ta shiwa Ummi albarka
har abin yasa yasomajin kishi maisa shima bai kawo tsaraba ba yasami kalan addu’an nan da
Hajiya kema Ummi haka? Kawai abin saiya zama kaman eye opener dagayau duk yayi tafiya
kobaiso saiya sayo tsaraba yakawo shima In sha Allah Ummi takoyamai something in this his
old age.
“Ka sanarda Hadiza kayi aure Nura?” Dasauri yadago kanshi daga katifa yakalli Hajiya jin
tambayanta ganin yayi shiru yasa tace “baka kyautaba Nura ai kome Hadiza tamaka ba’a haka,
bai dace kawai taga mata daga sama ba dan haka ka sanar da ita yau, sannan ka kira
kanwarka Aisha ko ita ko Maimuna ko Matar Baffan ka Karemi kabasu kudi ahadoma Ummi da
Hadiza akwati, sannan kaji tsoron Allah kayi adalci atsakanin su dan rashin yinsa zai kaika

wuta, ka manta duka halin Hadiza na baya ka bude sabon chapter yanzu and treat them equally
kada ka cutar da Hadiza sannan kada ka bari ta cutar da Ummi dubada tafita wayewa dakuma
shekaru, sannan kada kabari Ummi ta raina Hadiza ganin itace amarya ko ka nuna mata
kafifitata kan Hadiza, kada ka kuskura ka rike matanka ahaka kowacce ka rike sirrinta
azuciyanka kada ka sanar da Hadiza kanada matsala da Ummi haka kada kasanar da Ummi
kanada matsala da Hadiza, ka kama girmanka kayi tsayin daka akansu, ka tsare hakki dakuma
mutuncin kowa kanajina Nura” Gyadamata kai yayi ahankali yace “naji Hajiya” kanshi ta shafa
tace “kayafema Hadiza kome tamaka kada ka riketa da laifinta please sannan yau karaba musu
kwana, tunda baka gari kuma duk kana tareda Ummi ne lokacin yau kashiga dakin Hadiza
kajini”? Gyadamata kai yayi yace “naji” ahankali tace “Allah yamaka Albarka Nura, yanda kake
kulawa dani dinnan ka tsaya akan lamarina, kabani ci kabani sha kamin duk abinda nakeso
sannan kaji magana ta Nura ubangiji Allah ya saka mata da aljanna” murmushi yamata yace
“Ameen Hajiya nagode” murmushi tamai tace “idan naji sauki komi ya tabbata saika gana da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login