Showing 45001 words to 48000 words out of 131659 words
yadauketa yakaita bayi yamata
brush da wanka yafito da ita da towel yakoma dakin Aman yamai wanka shima wlh aikin yara is
not easy yafito dashi da towel ya kwashi kayanshi sukazo dakin Amal anan yashiga shiryasu
sunamai hira yana wasa dasu.
My people wai kunji labarin BUKKISH FABRICS N MORE??
Ku saurara kunji bantaba ganin masu harkan Atampas, laces dakuma lafiyayyun gangariyan
ready to wear kaya ba dake badawa akan sari kwashakwasha kaman BUKKISH FABRICS N
MORE ba, both
wholesales n retails sunayi, sunefa akama taken PAY LESS STAY IN FASHION, wato ki biya
kudi kadan amman ki saka kayan yayi adama dake, ku tura musu message now ku kwashi kaya
with little kudi, danna link din nan kimusu maganaí ˝í±‡í ĽíżĽ
wa.me/+2349034368170
Zaku iya duba shagonsu a TikTok- Bukkish fabrics n more
Nan da nan Ummi tagama abincin Hajiya tahada breakfast tasoya chips ta sossoya eggs da
sausage ta hadama su Amal abinci a lunch bag tadauko tafito zata ijiye a dinning tahada ido da
Hadiza dake tsaye a dinning din tana sanye da riga da wani palazzo trouser mai shegen kyau
na material pink tayi folding hannunta a kirji tana kallon Ummi da jajayen idanunta dasuka
kumbura sukai jazur kaman mai ciwon ido abinku da faran fata, chak Ummi ta tsaya anan
gaban kitchen din takasa karasowa dinning din ayanda zuciya ke diban Hadiza jitake kaman
tazo ta shake Ummi tamutu gabaki daya, daga kafanta tayi tafara tafiya ahankali akuma zuciye
tace “how dare you Ummi kika aure mini miji? Ni Hadiza kika aurama miji? Kin manta lokacin
dana taimaka miki kina neman aiki ido rufe wayanda kikema aiki ada sunyi japa sun koma
Canada anata gantali dake a Abuja ana nema miki gidan aiki baki samuba, na taimaki
rayuwanki nabaki aiki nakuma biyaki da kyau, yan aiki da ake biya duba ashirin, dubu shabiya
but ni nace zani dinga biyan ki dubu hamsin sabida duka gidana zaki kula dashi da yarana
sabida bani zama ina fita aiki, sakkayan dazaki mini kenan ki aure mini miji, mijina Ummi? Nura
na?” Ihu Hadiza tayi tana tafiya tace “ki daga fuska ki kalli kwayar idanuna bakar munafuka,
algunguma, makira bakar mayya, butulu, shedaniya watsassiya, sai bayan kin aureshi zakizo ki
kasa kallona kina sunnar da kanki kasa kaman baiwar Allah, dagakai ki kalleni Ummi, nace ki
kalleni!” Hadiza tai maganan tana ihu daidai tana kaiwa gaban Ummi ta finciko gaban riganta
gamgam tawani kalan jijjiga Ummi ta mugun makureta tana kallon fuskanta tace
“wulakantacciyan yarinyar irinki harta isa ta aure mini miji, ni Ummi kina yar aiki na, sabida ina
fita na barmiki gida kikai using opportunity nan kika auri miji na eh”? Hadiza tai maganan tana
buga Ummi abango saida Ummi tasaki lunchbag din kasa tai kara Hadiza ta makure mata wuya
tace “wlh, wlh, yau saidai afutar da gawanki ki daga gidan nan, ke! Dakikiyar yarinyar irinki tayi
kadan tace inyi kishi da ita, bazan taba iya raba Nuri dakowa ba balle ke jinjiran yar iska
kinajina? I will kill duk wacce tace zata auri Nuri na, dagani sai shi har lahira” “Hadiza!” Nura
daya sauko tareda yaran suna surutu ya hangosu da gudu gudu ya sauko daga bene yazo
wajen da sauri ya bambare hannun Hadiza daga wuyan Ummi yace “are u mad kasheta zakiyi”?
Tari Ummi tahauyi sosai tana nishi idanunta sunyi ja, cikeda fada Hadiza tasake yowa kan
Ummi tace “Nuri ba ruwanka awannan fadan is between me and this this munafukar makiran
yarinyar” dasauri Nura yatura Ummi bayanshi daidai su Aman suna zuwa wajen da gudu zasuyi
wajen Ummi suna “Anty Ummi sorry” rikesu Hadiza tayi dasauri tana tafarfasa tace “ku zonan
ina zaku?” Dasauri Aman yace “wurin Anty Ummi, u hurt her Mom” cikin ihu Hadiza kaman zata
make Aman tace “waye Ummi? Me kuka hada da ita? Who is that girl to you? Dagayau baku ba
ita Aman kaida sister ka, Ummi is a bad evil person, babu wanda yataba cutata arayuwan nan
kaman ita, bantaba nadaman abu arayuwana kaman nai nadaman ranan dana dauketa aiki ba,
kar wanda yasake kiran sunanta cikinku agidan nan, Ummi is the worst evi…….” “Hadiza!” Nura
yasake kiranta ranshi abace dasauri Hadiza takalli Nura tace “what!? Nura I said what kake
kirana? Don’t tell me ka yarda cewa yar aikin nan son yarana take? Okay bakaso nagayama
yarana she’s evil, Lemme tell you something today Yarinyar nan bata taba son yarana ba, she
just use them tayi winning heart naka da nawa damuka yarda ta zauna gidanmu, bata taba son
yarana ba, she use them taja ra’ayinka kasota, tunda ta kyallara ido taga muna biyanta 50k
instead of 20-15k da ake biyanta a inda tabasa aiki ta kudurci aniyan saita aureka, saita zama
matarka, saisa taja yaran jikinta sabida tasan you love yarannan morethan ur life sune the way
to your heart, your weakest point Nura, open your eyes and see Ummi played you and me, Nuri
Mezakayi da this village evil girl yar aiki fa eh Allah kadai yasan mazan mutane nawa taci, I will
post her pictures on social media to makesure babu wanda yakara daukanta aiki a abujan nan
tunda she’s a witch, ka barni naci bura’uban yarinyar nan Nuri tasan cewa Allah dayane” Hadiza
takaima Ummi nushi Nuri yatare hannu ta hanyar rike hannunta gam cikin kakkausan murya
yace “karkiyi kuskuren tabamin mata Hadiza stop all this thing!” Nura yayi ihu saikuma cikin
turenci yace “I’ve given this respect leave this girl alone before I disrespect you in front of her”
tafi Hadiza tayi tace “akwai disrespect daya wuce na kariga ka aurota ka kwanta da yar aikina
taga kalan buranka dani uwar dakinta keci akwai Eh Nura talk!” Hadiza tai ihuu dayasa Nura ya
runtse idanu yabude su ahankali yakalli Aman da Amal daduk ke kallon Maman nasu sunyi
tsuru tsuru, dan juyowa kadan Nura yayi yakalli Ummi dake labe abayanshi yace “tafi dakinki”
gyadamai kai tayi tawuce Hadiza zatayi kanta Nura yariketa gam, Hadiza tabita da kallo tana
duramata ashar tace “munafuka, jibeta kaman bushashen kifin dayay kwantar a kasuwa
oporoko, banda ma namiji kanshi kaman kan jarirai ne mezakayi da yarinyar nan mai kama da
fiffiken kunkurun dayay shekara dari da uku aduniya eh, makira zuciyanta yafi fatar jikinta baki,
tanaji da lebe kaman wacce ke aiki agidan giy……” “Hadiza!” Nura yayi maganan yana fizgota
su Aman suka fashe da kuka Nura yakalli yaran saikuma yasaketa yace “look at yaranki ko
breakfast basuyi ba zasuje school kina haukan nan bakisan zaiyi affecting mental health da
cognitive development nasu ba” cikin fushi tace “eh bazasuyi breakfast dinba ka gayama
yarinyar chan bata ba yarana, kada ta kara dafa musu abinci kota musu wani abu, wlh ko
hannunta nagani akan jikin yarana kome namata ita taja and kada ka ta kara shigan mini
kitchen” Nura yana wani kallonta yace “kitchen banaki bane, duk wani abu naki na kitchen din
nabaki dama ki kwashe ki ciresu daga kitchen din zan sayo wasu nasa cus Ummi will enter this
kitchen and cook for me” Nura yakallesu yace “zo kuyi breakfast” rike hannun yaran tayi tace
“Nura bari kaji yesterday you took advantage of my fragile state kayi yanda kaga dama dani not
anymore, billahillazi Nura zan nuna maka cewa yimini kishiya was the worst mistake daka tabayi
arayuwan ka, bakana fadin bakada kwanciyan hankali ba yanzu kafara ganin asalin rashin
kwanciyan hankali, muzuba nidakai I will deal with you and deal with that thing daka kawomin
gidan nan as matan ka, bakasan ba’a wasa da fire ba because u will get burn, Nura I will treat
you f*ck up wallahi kuwa” sosai Nura ke kallon Hadiza but sabida yaran saiyayi shiru yatako har
gabanta yaduka yakama Aman da Amal dake kuka looking terrified ya karbe su daga hannunta
yace “bani yarana” yajuya zaiyi dinning dasu kafin yaje Hadiza tarigashi zuwa dinning din duka
abincin da Ummi takai dinning dan breakfast Hadiza ta kabar, dasauri Nura yaja Aman baya
dan yadauki Amal gudun karya kone da ruwan zafi yana kallon Hadiza, ahaukace ta duka ta
kwashi lunchbox na yaran da Ummi ta watsar akasa dataji shaka dazu ta bude tana ciro komi
tana zZzagewa akasa tace “baza’a aci abincin yar aikin ba, yarana bazasu karacin abincinta ba,
nace baza’a ciba, angama cin abinci again, Nura that peace dakace bakasamu dani ba ajikin
yar aikina zaka samu wlh, wlh, wlh bazaka sameshi ba, Nura u will never know peace now
dakamin kishiya I swear by Allah” sosai Nura ke kallon Hadiza kaman ba itane tagama kuka jiya
kaman wacce ke shirin mutuwa ba, baice mata komiba yajuya yakoma falo yazauna yaciro
wayanshi yakira school din yaran yace abasu breakfsat da lunch yau daidai motan school din
zuwa, lallashin yaran yayi yadauko juice a fridge yabasu sannan yafita yasasu a school bus
sannan yadawo cikin gida Hadiza na tsaye a tsakar falon tarike waist nata tan kallon Nuran.
Baiko kalleta ba yawuce zaiyi stairs tabishi da sauri tana ihu tana surfafa masifa tace “bakaji
kunya na ba sabida kaine babban munafukan mazan duniya, Nura the president of MMA!
Mugayen Maza Association, zaka kama ka auremini yar aikin dana samo nakawo gidan nan,
kabita har kauyensu ka aureta kaje kayi honeymoon da ita batare daka dauki wayana ba for that
2weeks, shine kanada audacity kazo da daddare ka lallabani kana samin jikinka ajikina jikinka
daya hadu dana yar aikina eh Nura? I looked up to you kullum as a role model cus Nadade
banga namiji mai hankalin kaba, but I was wrong gaskiyan bature ne dayace a fool at 40 is a
fool forever dan tell me why will a sensible, educated wise old man zai kama ya aurowa
matarshi yar aikinta? Nura yar aikina ka auromini sabida daidaicewa da wawatsula” uppan Nura
baice mataba wardobe nata yabude yadauko kayanshi yawuce yafito daga dakin duk tana
binshi yaje dakin Aman ya ijiye komi kan gado yafada bayin yayo wanka yafito yadauki cream
din Aman yashafa still surfafa bala’i Hadiza take tsaf yagama yafito yasauka kitchen yaje
yadauki babban kulan dake kan Island Hadiza takawo hannunta anan ne Nura yace “idan kikai
kuskuren ko gigin taba abincin mahaifiyata Hadiza I will show inda haukanki ya tsaya anan
nawa yafara” yana maganan yawuce ta yafita tabiyoshi tace “ai dama nasan kai mahaukaci ne
dan mahaukaci kadai zai auroma matarshi yar aiki” fita yayi anan gaban kofa ta tsaya tana
kallonshi dan bataso tafita tana fada, estate dinsu da ake ganinta as don aga tana fada, abincin
ya ijiye a bayan mota ya kulle motan yadawo cikin gida Hadiza tasake binshi kitchen din
yashiga ragowan friend Irish daya gani a pkate da egg yadauka, spoon yadauka yafito Hadiza
nabiye dashi tace “ina zaka da abincin nan eh, Nuri ina zaka da abincin nan”? Dakin Ummi
yabude yashiga biyoshi Hadiza tayi ciki ga mamakinta Nura just pushed her outside yamaida
kofan yarufe yasa key tahau buga kofan da gudu tana ihu. “Nura ni kai pushing outside like that
eh? Wlh wlh sainayi maganinka dakai da karuwan nan daka ijiye adaki” kallon Ummi yayi
dayagani kwance kan gado kaman marainiya idanunta sunyi ja amman ba kuka takeba zama
kusada ita yayi kan gadon yana ijiye abincin agefe murmushi Ummi tamai tace “shine saika
kawomin abinci maisa kakemin aik…..” hannu yadaura akan bakinshi alamun tamai shiru
hakan yasa tai shiru yakai hannunshi yadagata wajen window dakin yayi da ita ya yaye window
yadaga wuyanta yana dubawa yana tattabawa ganin yadanyi ja yace “dazafi” dasauri ta
girgizamai kai tace “ba zafi” yana kallon kwayan idanunta ahankali yace “mesa baki gudu ba
dakikaga zata miki wani abu ko kiyi ihu ki kira sunana what it tamiki wani illan?” Murmushi tamai
tacire hannunshi daga wuyanta tace “Anty bazata min wani illa ba ba muguwa bace, kawai fushi
take sabida mun mata laifi” dan shiru Nura yayi yana kallonta saikuma ahankali yace “Ummi
aure ba laifi bane like I said ranan nan ko nan gaba naji ina bukatan wata matan zan iya nakara
aure, mata hudu zan iya aura” Ummi na kallonshi tace “Anty na sonka sosai, kuma soyayyan
yasa take fushi haka” yana kallon kwayan idanunta yace “kefa?” Murmushi tamai tace “nima ina
sonka sosan bala’i, tafashashen so ma nake maka my Noor bai huce ba” yana kallon bakinta
yace “Allah yar matata”? Dan dariya tamai tace “da gaske, ba Hajiya zakakai asibiti ba lokacin
na tafiya kazo kaje” dan ijiyan zuciya yasauke yace “banso na bar gidan nan ahaka” dasauri
Ummi tace “babu abinda zai faru kaje ka kai Hajiya asibiti abincinta na kitchen a flask kadauka”
ahankali yana kallonta yace “nadauka” ganin ya tsaya yana kallonta yasa tace “menene?” Yana
kallon kwayan idanunta yace “Aman da Amal yaranki ne kada ki rabu dasu sabida Maman su
kinji” murmushi tamai tace “tom Baban Aman da Amal” rungumeta yayi ahankali yace “kiyakuri
da abubuwan da Hadiza tafada miki kinji, kada ki riketa azuciyanki, kiyakuri Hajiya Ummi” dudda
taji wani iri amman tadaure tafita daga jikinshi dasauri tace “komi yawuce katafi” Gyadamata kai
yayi yace “biyoni ki rufe kofan da key” biyoshi tayi yace “kiyi breakfast zan dawo yanzun nan”
gyadamai kai tayi yabude kofa yafice tasa key dasauri ganin Hadizan na tsaye awajen yawuce
Hadiza tasakebin Nuri tana masifa tace “tell this girl ko dakin yarana takara shiga wlh saina
watsar da ita, karta kara taba wani abu that belongs to me in this house wucewa Nuri yayi
yawuce yashiga motanshi yabar gidan Hadiza ta dawo sama tashiga surfafa zagi na uwa da
uba ma Ummi, Ummi tayi shiru.
Tashi Hadiza tayi ganin taki kulata tazo gaban dakin ta bubbuga tace “kifito mana idan ke diyar
halas ce yadade da tsufa a inda yatafi yanzu, dagani saike agidan, kifito muyi magana woman
to woman mace to mace, cus inada wasu abubuwa dazan fada miki kifito Ummi kibude kofan
nan kifito” Hadiza tai dariyan keta tana tafiya tace “dan kauye dan kauye ne, ni wlh at this point
ma tausayi kike bani Ummi, bari nafada miki wani sirri dabaki sani ba for free” tasake shiru tace
“kinga Uwargidan miji itace kokon rayuwanshi, Ummi bar ganin kin zauna agidan nan kinga nida
mijina munada yan matsaloli sai kikai yan dabarun ki na gidahuman kauye kikaja ra’ayinshi ya
aureki to tsaya kiji wani abu dabaki sani ba game da mijina Nura” Hadiza takara murmushi tace
“Nura kwata kwata dakikan mata dabasuyi boko ba basa burgeshi kije ki tambaya kiji, Baban
Nura professor ne a BUK abinda yadawo dasu kano kenan daga zamfara, Hajiya wannan
dakike gani tsohuwan secondary school English teacher ce, kannen Nura kap dukansu
graduate ne dasuka gama jami’a har Meena Kwanan nan tagama bautan kasama, kinganni nan
Nura bai yarda ya aureni ba saida nagama jami’a gabaki daya muna dawowa garin nan yasa
nacigaba da karatun wuce jami’a wato masters sabida dan boko ne shi, yanason yaga matarshi
yar gayu yar boko tanuna ma business partners nashi, kinsan mesa nake gayamiki
maganganun nan”? Hadiza tasake dariya tace “sabida ke dakikiyace jaka kuma, Nuran dakike
gani kin aura yau Nuran daya sami yar karaman matsala da Hadizan shice, kije kano ki
tambaya abaki labarin kalan soyayyan damukayi, ban bashi jikina ba damuwa da sha’awa
kinsan mutum shiru shiru mara magana yasa yaga kaman yana sonki wlh Ummi kindaiji na
rantse miki Nura baya sonki sabida baki cikin kalan ko siffofin matan dayakeso” wani abu Ummi
taji ya tsayamata awuya chak yaki wucewa takasa hadiyewa, Hadiza tace “bansan ko kinji
magananmu jiyaba, jiya nace yasakeki zan chanza Ummi kinsan meyace mini”? Hadiza tai
maganan cikeda tsantsan tunzura mutum saikuma ta kyalkyace da dariya tana tafi tace
“wohoho ta yanda zaki gane kin tafka shirme Ummi kin auri mijina kin dauka kin sami gidan
mijin cemin yayi nafara chanzawa tukunna yagani, idan na chanza nakoma Hadizata nada zai
sakeki ki tafi mucigaba da rayuwanmu mukadai hankali kwance” dasauri Ummi ta tashi daga
gadon zuciyanta na rawa tanajin wani iri, Hadiza tace “haka yadinga lallabani har saida ya samu
nabashi hakkinshi that means keba komi bace awajenshi ba sati biyu dakukai kuna amarci
kaman yanacin kashi haka yaji saida ya kwanta dani jiya yajishi daidai, yajishi damdam yajishi
yakoshi, kuma kada ki manta rashin jituwan damuka samu dani da dashi yasa yaje yama
nemeki” hawaye Ummi taji sun sauko daga idanunta, Hadiza tace “Ummi ki rubuta ki ijiye
kwanan nan Nura zai sake ki kibar gidan nan dan bazai taba hada jini da jakan kauye ba da
turenci nan nan bata iyaba wlh saiya sake k…….” Bude kofan Ummi tayi dasauri tafito idanunta
sunyi jazur tahada idanu da Hadiza for the first time tunda tadawo gidan tace “Hadiza kinyi
kadan ki rabani da Nura” sosai Hadiza ke kallonta ganin idanunta sunyi ja maganan ta shigeta
kenan yasa ta taka zuwa gaban Ummi Ummi ta tsaya chak tana kallonta ba gudu ba jada baya,
Hadiza namata wani kalan kallo tace “nabaki daganan zuwa sati biyu saikinbar gidan nan dan
baki da waje awajen mijina” Ummi na kallonta tace “Hadiza ban auri Nura dan na kuntata miki
ba, shiya nemeni da aure na aureshi kuma magana daya zuwa biyu zan fadamiki, nifa nayi miji
kuma naga wajen zama, zama kuma daram! Wallahi ko ana hamaza hamata bazan rabu da
mijina ba, barima kiji mutuwa kadaice zata iya fitar dani daga rayuwan Nura!” Hannu Hadiza ta
daga zata kaima Ummi mari Ummi tarike hannun gam idanunta sunyi masifan ja kirjinta na
tafarfasa itama jin ance Nura zai saketa tace “Hadiza kul!” Ummi tazare mata idanu kaman yar
daba tace “dazu nariga nabarki kinmin hukunci sabida nasan ban kyautamiki ba na auri mijinki
daya nemeni amman yanzu kikai kuskuren dukana Hadiza kin tuna kalan dukan da Meena
tamiki”? Ummi tayi maganan tana kallon kwayan idanun Hadiza kaman yanda Hadiza ke
kallonta mamaki yagama kasheta, Ummi tace “wlh saina miki dukan dayafi wanda Meena tamiki
domin shiru shiru ba hauka bane, dan hakin daka raina shine yafi tsole ido, kul Hadiza! Wallahi
kul! Duk abinda zakiyi kiyi but