Showing 90001 words to 93000 words out of 131659 words

Chapter 31 - Mazan Ko Matan Complete Hausa by M Shakur.pdf

M Shakur   

13 Nov 2025

362

hakuri, duba da baida wani bad record
kotu ta yanke hukuncin rike Nura harsai yabiya fine na naira dubu dari uku, 300,000!” Dasauri
Alhaji Musa yace “Alhamdulillah” Alkali yace “idan akwai wanda keda wani magana cikin
parties din zasu iyayi” hannu Nura yadaga hakan yasa Alkali yace “ina jinka” tashi Nura yayi ya
kalli Alkali anatse yace “inason kotu ta shaida ni Nura na saki matata Hadiza SAKI DAYA!” Wani
kalan dum! Dummmm! Hadiza taji azuciyanta yayi dawani kalan sauri tadaga kanta takalli Nura

hannunta na rawa rawa, Nura na kallon Alkali yace “inason kotun nan tazama shamaki
tsakanina da ita, kada Hadiza tasake daga kafa ta taka gidana! Duka wani abu nata na cikin
gidana daidai da cokali zan tattara nasa a mota yau ba gobe ba na aika gidan iyayenta inda na
aurota, sannan kada ta daukan mini yarana! Alkali inaso kamin katanga da ita!” Hawaye Hadiza
taji zasu zubo daga idanunta tarikesu gam tana fuzgar da iska da baki kirjinta kaman ana barza
masara dasauri Zeenah tazo ta bayanta tana mata whispering “kada ki kuskura ki nuna kinji
wani abu dan dadi zaiji, abinda yakeso yagani kenan” daurewa Hadiza tayi ta rike hawayen
Alkali yagama rubuce rubuce yace “you can sit” yakalli Hadiza yace “kaman yanda kikaji mijinki
ya sakeki kuma yamiki shamaki da gida wanda yake nashi, dan haka kada ki kara sa kafa
agidan shi kikai haka zai iya daukaka kara akanki, zancen yara kuma dake da shi zaku iya
daukaka kara kuyi case na custody yara” cikeda karfin hali Hadiza tace “no need yara nawa ne
ko suna hannunshi ko suna hannun uban idan inason ganinsu zan kirashi shiya kawominsu,
kuma dama koda bai sakeni ba ni zancemai ya sakeni, me akeyi da namiji mai dukan mata”
wani dadi Zeenah taji hardama Hadiza tafi kasa kasa Alkali yace “kotu tazo karshe” yatashi
yafice police sukazo aka wuce da Nura lawyer shi da Alhaji Musa suka bisu, court room din
yarage saura su Hadiza, hawayen da Hadiza ke rikewa ne suka zubomata wlh bazamata iya
describing in words how she’s feeling right now ba, bata taba expecting Nura zai saketa ba
sabida ta makashi a kotu, tunanin baimazo ranta ba yanzu Nura yamata saki biyu kenan, Mrs
Oyenyi da bata wani san komiba ita she’s just a lawyer tace “why are you crying? You should be
happy a man like this dayayi inflicting so much pain in you yasake ki infact this calls for
celebration ma” Zeenah tace “owooo tell her oo Mrs Oyenyi, I don’t know why Hadiza base her
whole life on this guy not knowing yanzu ne zaki fara cin rayuwanki da kyau dakuma tsinke, ni
dayama miki biyu yacikashe” dasauri Hadiza tadago jajayen idanunta takalleta Zeenah tace
“yes you should be free of this Nura for good haba yanzu kuma abin takaici kina wani zubar da
precious hawayenki sabida namiji wlh tir Hadiza kinji kunya, you are a disgrace to mata
damukasan ciwon kanmu, you are a disgrace to all feminist out there” hannu Hadiza tasa ta
share fuskanta tass tai murmushi tace “ba ina kuka sabida Nura yasakeni bane Zeenah, kuka
nayi sabida kalman saki feels somehow ajikin mata, but danya sakeni sai mene harda wani
amini katanga da gidanshi tunda gidan dirhami gareshi ko gidan sarkin dubai ne dashi ko prince
of Saudi useless Man gidan da I can buy like 10 of it” Zeenah tace “owooo, tashi mutafi jor let’s
go and celebrate book hotel and sleep today kafin gobe muje house hunting” dasauri Hadiza
tace “gidan ki fa? I thought anan zan kwana”? Dan murmushin yake Zeenah tayi tace “ohh my
bad ni nama manta ba matsala saiki kwana agidana, muje let’s call Baraka and pick her up a
hanya” tashi Mrs Oyenyi tayi sukai sallama daman sun gama biyanta suka wuce ahanya suka
dauki Baraka wacce Sam bataji dadin labarin ba amman ina ruwanta, deep down Hadiza is so
worried amman Zeenah taki bata room to show how worried she is kuma itama din batason
suce tacika depending on a man ko she’s a disgrace to feminist.
Sai bayan magrib suka tafi gidan Zeenah, babban gidane mai kyau but baimakai gidan Hadiza
girma da kyau dinba dudda matar minister ce, shiga sukayi ciki, Zeenah na murmushi tace “ai
you are full ko kina bukatan abinci naga munci mun koshi a inda mukaje bari nabaki ruwa
kinsan ni yan aiki na basa kwana da yamma suke tafiya saisa kikaga zan baki ruwa da kaina”
Gyadamata kai Hadiza tayi Zeenah tadauko ruwa taba Hadiza tace “muje na kaiki dakinki” dan
kallonta Hadiza tayi saitaga kaman she’s rushing ko ruwan fa bata budeba amman bata

damuba ta tashi tabita sukaje sama takaita wani daki tace “to saida safe”gyadamata kai Hadiza
tayi dudda she wanted su danyi hira har zuwa irin 12 din nan nadare but she guess tagaji tunda
tun safe suna tare wucewa Zeena tayi agurguje ta sauko kasa ta kwashi takalmin Hadiza dake
gaban kofa tashigo dasu da sauri ta wuce kitchen dinta taboye takalmin abaya shi kofa sannan
tashiga kitchen agurguje fa tashiga hada girki.

Hadiza datagaji dan bayan tayi sallan isha’i bacci yayi awon gaba da ita cikin bacci mai nauyin
gaske taji hayaniya da kaman karan fashewan abu hakan yasa ta bude idanunta ahankali
baccin na fita daga idanunta muryan namiji taji yana cewa “takalmin waye wannan Zeenatu?
Wakika kawo gidan nan bayan nagaya miki banason ana zuwa mini gidana?” muryan Zeenah
taji kasa kasa bataji metake cewaba saikuma chan takarajin karan fashewa abu kaman plate
haka ko glass cup yayi ihu yace “ubanwa yace ki kawo mini wata kawarki gidana I don’t care if
she’s squatting here sabida mijinta yasaketa, are you deaf? Are you stupid, gidan ki ne? Is this
house yours? Who do you think you are Zeenatu dazaki dinga shigo da mutane ba tareda kin
sanar da ni ba? Oya go and call her ta tattara yinata yinata tabarmin gidana inba hakaba wlh
kema koranki zanyi yanzun nan” zaro idanu Hadiza tayi saikuma ta dafa kirjinta Zeenah ne da
mijinta ke fada haka akanta ake magana ko wata kawan daban? Tashi tayi ahankali tabude
kofan dakinta tafito tayi tafiya tadan leka downstairs ta yanda basa ganinta Zeenah tagani tayi
kneeling awajen dinning da duk an faffasa plates tahada hannunta biyu harda kuka tana rokon
wani attajirin mutum dabai wani tsufa ba kaman Nurin ta yake, murya kasa kasa tana cewa “dan
Allah karufamin asiri kada ka tozar ta ni kabarta ta kwana gobe zata tafi i promise” kana
ganinshi kaga masifaffe har zufa ke keto mai a hanci da goshi, ga takalman ta dataga an
wawwatsar a falo mutuwan tsaye Hadiza tayi dataga yadauki cup yakara bugawa a katsa ita
kanta Hadizan saida ta firgita kaman glass zaizo nan sama inda take ya shiga jikinta cikin fushi
yace “stop begging me useless woman who are you dazaki dingayi yanda kikaga dama
agidana, jeki kira kawar naki kubar gidana dagake har ita” hannu Hadiza tasa ta taushe bakinta
mamaki sai kawai ta juya fuuu cikeda zuciya dan tafi karfin wulakanci akan wannan kurkukun
gidan tawuce dakin datake tadauki handbag nata kawai tashiga saukowa jin tafiya yasa
dukansu suka juyo dasauri Zeenah ta mike tana goge fuskanta ta kakalo murmushi cike da
duniyanci tace “Hadiza zoki gaisa da Baby hala karan plate ya tadaki daga bacci ko dan dazu
na leko naga kinyi bacci, wlh bari mukayi yanzun nan” wani kallo Hadiza kema Zeenah yanda
tayi just now kaman hawainiya sai kawai ta tsinke da lamarinta batace komiba tace “ina key
motata”? Center table Zeenah ta nuna mata Hadiza na tsallake tsallake kwallaben dakenan har
falon tawuce tadauki key motanta ta kwashi takalmanta tai wajen kofa cikeda zuciya Mijin
Zeenah ya nuna Hadiza da hannu yace “jibi mara kunyan da kike cewa ta kwana agidana
taganni bata iya gaidani ba” azuciye Hadiza ta juyo tace “anki agaidakan mata mutuncin
mahaukac…….” “Hadizaaaaaaa!!!!!!” Zeenah tama Hadiza wani kalan ihu kaman zata tsaga
gidan tace “karki kuskura ki zagin mijina wallahi cus zakiga other side of me” baki Hadiza
tabude completely flabbergasted tana kallon Zeenah, saikuma chan ta nuna kanta tace “Zeenah
you, me!” For the first time in history the chatterbox Hadiza was speechless tama kasa
constructing sentence tsabagen shock tana kallon camellion Zeenah, Zeenah tace “yes zaki
shigo har gidana ki zagi mijina are you okay an gayamiki irin ex mijinki ne shi Nura”? Shiru
Hadiza tayi tana kallon Zeenah, zata sake maganan mijin Zeenah yace “kneel down ki gayamin

wace jakace wannan mara tarbiya kika kawomin gida, and you leave my house kafin nakira
bodyguards dina a kulleki” ya nuna Hadiza da yatsa cike da wulakanci kaman kashi yakema
magana, Hadiza ga mamakinta kneeling taga Zeenah tayi agabanshi kaman baiwa sai kawai
tajuya da gudu sosai fa tawuce motanta da dazu Zeenah tayi parking achan bayan gida sai
yanzu tagane mesa tai parking awajen ashe batason mijin yasan takawo wata gida ne tashiga
motan da sauri ta tuki tafito around 12:15Am nadare kawai tahau kuka cus from just little abinda
tagani dudda mijin Zeenah is a minister tafi Zeenah enjoying rayuwa in every aspect starting
from gidama, maybe halan ya ijiye Zeenah a wannan gidan sabida itane Amarya kuma batada
yara but still she expect gidan minister yafi gidan mijinta that is into real estate girma da komi
amman gidan ta yafi gidan nan da girma da komu har interiors na gidan ta yafi na Zeenah kyau,
not to talk of babban gidan da Nura ke gina mata da ba’a gamaba lokacin daya kaita gidan ita
kanta saida tai ihu wani kalan design na gini yake da bata taba ganin kalanshi a abujan nan ba,
look at yanda Zeenah ke living in fear tun a kotu data cemata zata kwana agidan ta ta lura da
wani abu, look at yanda take baiwa in her own house kneeling agaban miji yana fashe fasten
utensils agabanki what if tasami injury, sannan bataga yar aiki ko guda daya ba halama batada
yan aiki, jibi yanda mijin keta ihu akan me zata kawo wata gidanshi batare data fadamai ba ita
look at yanda take kawo kowa gidanta ba ruwan Nura itanema Nura bai isa yakawo kowa bai
fadamata ba, Zeenah has been lying to them all this while tana zuga ita da Baraka suci uban
mijinsu yanda takeyi so dama karya take, imagine Zeenah data gama zugata dazu harda
cemata she’s a disgrace to all feminist out there, look at Zeenah miji ke bossing around yana
sata kneeling kaman student, Zeenah dake gayamata taji kunya tana kuka kan namiji look at
Zeenah da life datakeyi! Ya Allah! Daidai Hadiza na parking acikin Hilton hotel tadade a mota tai
kuka harta godema Allah gash Anty Jams sun kirata bata dauka ba, bawai tana nadaman
abinda tayi bane for slapping her da Nura yayi he deserves to be thought a lesson but she’s just
hurt yanda Zeenah made her look so stupid and a fool bayan tafita more gidan miji in every
aspect dudda tana auren minister, but Zeenah made her look kaman itace the unluckiest wife in
history, koda yaushe ji take she wants to be rulling her house kaman yanda Zeenah ke gaya
musu tanayi, and abinda ke faruwa is bata cika zuwa gidansu ba cus kullum tana shago
kawancen su is suzo shagonta ayi hira a fita, sudanje occasion ko outing that is it, Hadiza
batada yawon zuwa gidan kawaye business nata baya barinta saisa batasan actual condition na
gidan Zeenah ba, mesa Zeenah zata zugata bayan itane ke facing abuse ma agidanta not she
dan Nura bai taba fasa plates a inda take ba, Zeenah lied to her and betray her, tazugata and
made her look so stupid, fool, and immature.
Hadiza taci kuka ta koshi sannan tafito taje tai booking daki jin kanta na sarawa ta tsani karya
da yaudara dan ita kozata mutu bata karya, bata yaudara, bata pretending to be who she’s not,
she’s just herself aduk inda zataje a duniya be it to mijinta, relatives nata ko friends natama,
ganin kanta zai tsage yasa taje ta kwanta.
BECAREFUL WITH FRIENDS MATAN AURE!!!!
SOME FRIENDS ARE EVIL!! SNITCH!! ENVIOUS!! WISE!! AND CROOKS!!!
Zeenah is just one!!! Now ku fadamin mesa Zeenah tama Hadiza what she did to her??? Please
kubani amsan nan!

MATAN AURE KUDENA FADAMA KAWAYEN KU MATSALOLIN KU wani zubin daka fadama
friends your issues gwara stranger na rantse, bawai ina cewa all friends are bad bane no! But
some friends basason suga progress arayuwanki ko cigaba.

Dan Allah kubarni nayi this book yanda na tsara nace zan muku magana akan major abubuwan
dake kashe aure ayau which the most common one is FEMINISM wanda shine nake nuna
muku abubuwan dayake causing arayuwan mu na yau, look at inda Feminism yayi landing
Hadiza, this book is not for enjoyment or catching fun novel nope! Idan irin wannan kukeso I
have them very tantalizing ma ga dadi check my wattpad page Mshakurworld. This novel is an
educating novel dayake nuna illolin of some actions na both side, look at how nake rubuta this
book any action na mutum ina nuna how that person thinks and see things, still ina nuna muku
idan kina kaza it can leads to this and this and this, this novel is about auren mutum biyu Nura
and Hadiza, life nasu, origin na problem din, kaza kaza kaza, I break everything down for you,
and I can tell you for free Nura is the origin na this issues for not teaching Hadiza and guiding
her as her leader, ya saki Hadiza dayawa, yabata freedom da yawa, saisa hakuri ma da shiru
shiru idan yayi yawa is a disease, lokacin dazakace okay bari nafara gyara karfen yariga
yanuna harma ya nika, please masu cewa am bias am this and that look at this book from
different perspectives and you will see abinda nake kokarin yi.
This is a wake up call to all of us mata cewa mu gyara, and this is a wake up call to maza na
idan matanku nayi ba daidai ba correct them dan ba soyayya bane dan kayi letting go of
mistake na mata infact cutar da ita ma kakeyi indirectly.

Anata cewa shi mutum baya chanza wa menene menene, kowa aduniya na da tendency
chanza wa either from good to bad or from bad to good, wasu they just have to experience life
outside the box kafin suyi tunani, look at Hadiza yanzu just few minutes datayi agidan Zeenah
she saw rayuwan wasu couples and tafara tunani this that and this, Hadiza will change guys I
know abinda nakeyi but mubarta tayi rayuwan da babu Nura aciki muga how things goes and I
sincerely hope you will understand cewa littafin nan nayi shi ne for the betterment of our society
in general both daga bangaren mata da bangaren maza Thank you.
Allah yamana albarka gabaki daya, yau nabude layina you can either call me or drop a
message kota whatsapp kota text 07012181461.

Zaku shiga shiga group na matan aure na with just 2k. Chat me up idan kinaso.
THANK YOU ❤️
MATAN?? Ko MAZAN??


✍M SHAKUR

EPISODE 2️⃣7️⃣
KUJE AGUJE‍♀️‍♀️ KU KOYI HARKAN KITCHEN‍♂️‍♂️

Great news for the people outside jos who are eagerly want to become pastry chefs and bakers.

BAKE N’ FROST
is bringing you it’s first online class and the class will come with alot of benefits.
Make sure you join us today.
Believe me, you won’t regret it because we will be teaching you everything from scratch
‎Open this link to join my WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/Hs8bU0RnXpLA5Lvr1o4qDe

Hadiza tajuya nan tajuya chan takasa bacci hakan yasa ta mike tawuce bayi ta tsaya gaban
mirror ta wanke fuskanta tana kallon kanta idanunta sunyi jazur, takasa wrapping head nata
around abinda Zeenah ta mata, wani kalan daura hannayen ta biyu tayi akan bakinta tafashe da
kuka da kyar ta lallashi kanta tafito tadawo daki, wayanta tadauka takira Barakah amman harya
katse bata dauka ba hakura tayi ta ijiye wayan ta lumshe idanunta, da ace Zeenah bata ambato
zancen court ba da batasa Nuri a kotu ba wlh dudda tasan saitayi bura’uba dashi dan bai isa ya
mareta bane ta hakura ba but bazata taba tunanin kotu ba. Zama tayi ta gaban gado tayi shiruu
tanaji kaman an daura mata dutse akirji saikuma ta mike tsaye taje gaban wardobe tabude
she’s feeling so angry da kanta, duk wacce tace zata iya maka bayanın the feeling after been
divorce daga mijinka is just lying dan the feeling is just unexplainable, she’s having different
emotions, She’s angry da abu biyu yanda Nura yasaketa yakuma mata iyaka da gidanshi and
his life gabaki daya, yanzu fa idan tashiga rayuwanshi yanada hujjan yimata kome yaga dama
dakuma abinda Zeenah tamata, takasa gathering courage na kiran gidansu dudda taga kiran
Anty Jams takasa dauka takasa kiranta she don’t even know what she’s doing, all abinda tasani
is zataci durun uban da uwar Zeenah gobe before she even think of anything dan idan bataci
uban Zeena ba bazata sami kwanciyan hankali ba.

Komawa gado tayi ta kwanta tasake daga wayanta batasan metake ba but kawai samin kanta
tayi da shiga gallery taciro hoton Nura yana sanye da suit da cake agabanshi ranan dayay
lunching real esatate company nashi na a Abuja tamai hoton yana murmushi sosai yayi kyau da
fararen hakoranshi, Nura is very very handsome, dudda shekaru sun ja but few furfura gareshi
kodan yanada kudi ne kuma yana kula da kanshi ga yawan shan fruits but he’s super cute,
kuma he’s still very fit bai ijiye wannan pot belly ba. Kuka Hadiza takejinyi tana kallon hoton but
tahana kanta yi takasa yardanma kanta tayi kuka sabida wani yasaketa da sauri cikin karfin hali
tana kallon hoton nashi cikin wani kalan murya da kasan she’s so hurt tace “ni zaka saka Nuri

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login