Showing 69001 words to 72000 words out of 131659 words
gadon dan tasan ba lafiya
ta nemi hijabinta har kasa tasaka dan ba kaya ajikinta tafito da sauri daidai Nura nafitowa daga
dakin Hadiza da jallabiyanshi ajike dauke da Hadiza da kayan bacci ne kawai ajikinta komi na
jikinta diddiga yake da ruwa a sheme hannuwanta na lilo daidai lokacin Meena itama na
haurowa saman Aman da Amal duk sun bude kofa sun fito, mugun faduwa gaban Ummi yayi
daga ita har Meena atare sukace “meya faru”? Nura baimabi takansu ba yashiga sauka kasa
Amal tafashe da kuka cikin magagin bacci tana sosa ido dasauri Ummi ta dauketa tana kama
hannun Aman dayace “what happen to Mom”? Bata iya bashi amsa ba takamashi sukai kasa da
Hajiya Nura yaci karo dake tsaye gaban bene ganin Hadiza a hannun Nura kaman jaririn da aka
haifo daga ciki yasa tace “Subhanallahi meke faruwa”? Arude Nura yace “Hajiya bansaniba
abayi na sameta ahaka, dubamin ita Hajiya bata numfashi, Hajiya dubamin ita” dukawa Nura
yayi rikeda Hadiza awajen dasauri Hajiya ta duka takai yatsanta kasan hancin Hadiza but shiru,
saikuma dasauri tasaka karamin yatsanta cikin kunnenta takai babban yatsanta wajen sajenta
tayi shiru saikuma tacire dasauri takai hannunta damanta idanunta tabude duk Nura nabin
mamanshi da kallo dan Hajiya ita kewa mata dasuka rasu wanka a unguwansu akano.
Ganin yanayin idanunta yasa Hajiya tace “Innalillahi Wa Innailaihi Raji’un!” Dawani kalan sauri
Nura daya gama rudewa yace “noooooo! Hadiza this is not our promise Hadiza, Hadiza” dasauri
Ummi tajuya dasu Aman da Amal dake kuka sukai sama baikamata yara na ganin irin wannan
abunba, Meena ta taushe bakinta jikinta na rawa, hannunshi Nura yakai yana bubbuga kuncinta
yace “Hadiza wake up, wake up don’t do this to me Hadiza, don’t do this to me!” Yayi ihu yana
jijjigata ajikinshi yace “tayaya kikeso na raini Aman and Amal ni kadai on my own without you?
Don’t betray me this way, I want to spend all my life dake Hadiza kitashi ban yarda ba, wake up”
ya dinga jijjigata kaman zai karya mata wuya dasauri Hajiya takama hannunshi tareda
girgizamai kai tace “Nura!” Ihu yayi yace “Hajiya nooooo, tasan alkawarin mu, she can’t leave
me so soon, a……..asibiti…” kaman wanda yatuna wani abu tashi yayi da sauri ya dauketa
yafice da ita bayan yadauki key anan tray dasuke ijiye keys, bude bayan mota yayi yasata
yashiga gaba yaja motan da mugun gudu bini bini yana tuki yana kallonta da kyar cikin ikon
Allah yakai asibitin su babban private clinic ne.
Yana parking yawani fito ya fanfala da gudu cikin hospital din. “Doctor help me” yayi wani ihu
dayasa some few nurses da Doctors suka fito, ganin Alhaji Nura dan nanne hospital nasu yasa
duk sukayi wajenshi yama kasa magana waje kawai yake nuna musu yace “my…..my” sai
kawai yayi waje da sauri Doctors suka bishi daya daga cikin likitocin yana sa Nurses afito da
gado suna zuwa wajen motan kaman Nura zai fashe da kuka yace “she’s not breathing namata
CPR still batai responding ba” dasauri Dr yashiga saka stethoscope yace “minti nawa kenan
yanzu da daina nunfashinta”? Cikin mugun damuwa Nura yace “I don’t know I just met her abayi
haka, Dr please do something please, I don’t care do whatever u have to do, she can’t go like
this, tanada yara biyu yan kanana, please karufamin asiri and do something” daukan Hadiza
akayi aka daura agado idan kaga yanda ake gudu da ita akan gadon idan kanada hawan jini zai
iya tashi Nura zai bisu cikin dakin aka hanashi aka rufo kofa, tadan karamin window kofan yake
lekawa ganin ansa almakashi ana yaga rigan jikinta ana mammakala mata wasu mashina akirji
gabaki daya doctors biyu da nurses hudu sun haukace ana hada defibrillator dan ayi shocking
zuciyanta, hade hannu Nura yayi yakai yashafa kanshi yana juyi saikuma yasake hada
hannayen duka hankalinshi atashe yace “Ya Allah karka dauki ran Hadiza yanzu please Ya
Allah, nayi alkawari zanyi azumi uku kadawo min da ita, I need to tell her how much she means
to me, nagayamata ina sonta haryau har gobe, and I never intend on hurting her in anyway,
Hadiza is my soulmate, Maman yarana guda biyu, my life partner, Ya Allah nasan tayi kuskure
da dama but please give her a second chance please give her a second chance to amend all
her mistakes ya Allah ka taimakamin” wayanshi ne yashiga ringing hakan yasa ya tattaba
Aljihunshi yaciro ganin Ummi ne yasa arude yadauki wayan yakai kunne cikeda tashin hankali
yace “Ummi” cikeda damuwa Ummi tace “Ya jikin Anty naga ayanda kafita saisa nakira naji ko
kunkai lpy, su Amal nata kuka meya sami, Mommy su bansan mezan gayamusu ba” arude Nura
yace “Ummi kutaya Hadiza addu’a ki gayama su Aman suma Maman su addu’a, Ummi banson
Hadiza tamutu, she means a lot to me, Maman yarana, nariga nafaro rayuwana da ita, tayaya
zan cigaba da rayuwa babu ita eh Ummi?” Yanda Nura ke magana zakasan bemasan meyake
fadiba cikeda so dakuma tausayin mijinta tace “in sha Allah babu abinda zai sami Anty kaji
Baban Amali, Allah ubangiji yatada kafadanta, ka koma wajensu kada anemeka, kada kadamu
zan kula da kowa na gida kaji Mijina” cikeda so yace “nagode Ummi ki tayani bawa Hajiya
kulawa kar jininta yahau” gyadamai kai tayi tace “to Mijina zanyi, ka manta damu anan ka maida
hankalinka wajen Anty tafi bukatarka, Allah yabawa Anty Lpy” ta katse wayan, komawa gaban
kofan yayi daidai ana bude kofan Dr daya yafito dasauri Nura yace “doc…..” anatse Doctor yace
“she’s alive!”.
Wani kalan rungume Dr Nura yayi saikuma yasake shi da sauri yaxube awajen yayi sujjada
yatashi sauran likitocin duk suka fito da Nurses sai godiya yake musu head Dr yace “zaka iya
shiga ka dubata but kada ka tadata kafin ka sameni a office” dasauri cikeda farin ciki yace “to,
to, nagode Dr” dasauri yashiga ciro wayanshi yayi dialing number Ummi dasauri ringing daya
tadaga cikeda farin ciki yace “Ummi Hadiza na raye! Tafarfado” dasauri Ummi tace
“Alhamdulillah Alhamdulilah!” tahau fadama su Hajiya akan wayan duk sai hamdalasuke,
ahankali Nura yana jinsu yace “ina Amal da Aman”? Ita tama dauka ya katse wayan da sauri
tace “Amal na kuka gatanan na goyata tayi bacci, shikuma Aman gashinan kan cinyana
idanunshi biyu yayi shiru kanason kaga Mommy ka ko”? Tai maganan a tana shafakan Aman,
Gyadamata kai Aman yayi ahankali, “bashi wayan” Dasauri Ummi tabama Aman wayan cikin
sanyin murya yaron yace “what happen to my Mom Dady?” Murmushi sosai Nura yayi yanzu
yakara tabbatar yes Allah ne yabama Hadiza second chance tunda gashi yau Aman ne ke
wannan damuwan kan mamanshi yaron da is always angry with her, cikeda so da lallashi yace
“Momy was a bit sick but yanzu she’s fine, tana bacci anjima zanzo gida na kwaso ku kuzo ku
ganta kaji” gyadamai kai Aman yayi Nura yace “you are the only man in the house, bana nan
kaine incharge so promise me you will take care of your Grandma, Aunt, Anty Ummi and little
Amali, promise me zaka kula da kowa” ahankali Aman yace “I promise Dad, take care of my
Mom” murmushi Nura yayi yace “to zanyi, Daddy loves you and Amali a lot ko kada kadamu
anjima zanzo gida ok” “okay Dady” katse wayan Nura yayi yawuce yabude dakin ahankali ya
shiga, Hadiza na kwance kan gado da kayan patient an saka mata oxygen mask a hancı har
lokacin she’s still connected to some machines zuwa yayi gaban gadon ya zaune tareda kama
hannunta da sauri yakai bakinshi yayi kissing yana kallonta yayi shiru, she looks so peaceful
tana baccin nan babu wanda zai ganta yace fitinanniyan mata ce, sake kissing hannunta Nura
yayi murya chan kasa yace “thanks for pulling through, you scare the hell out of me today
Hadiza” yayi shiru yana kallonta saikuma ya rungume hannunta akirjinshi yace “I love you very
very much Hadiza despite all your crazy and annoying attitude but still ina sonki that’s why I’ve
been putting up with your shit all this years, ni kaina I wonder why nakeson stubborn mata irin
ki, but yazanyi the love is just unconditional kada ki karamin abinda kikamin yau okay! Kin
tsorata Nurin ki sosai Hadiza” yayi shiru saikuma yasake kai hannunta kan bakinshi ya manna
mata kiss yana kallon fuskanta yace “bantaba tsanan kiba for once duk kalan abinda zakimini,
infact sometime nakan gayama kaina ma I should be grateful inada matan da will always say
what’s on her mind the way it is, babu kwana kwana that’s you Hadiza, you are so real ba
kaman sauran mata ba that use to be cunny and sly, nasan halinki tsaf ciki da waje saidai na
gayama mutane who u are, you are just stubborn, gaki da anger issue but u are not wicked
Hadiza, and u are not evil, u don’t even have that time, baki cikin sahun matan dake bin
malamai ko bokaye so sometimes I feel kome zakiyi I can put you with it because bakida mugun
nufi azuciyanki kuma baki shirka and idan akwai soyayya kome zakimin zan iya hadiyewa and
be the man saisa ake ganin kaman nina bataki” yayi shiru yana kallon fuskanta yace “I just want
you happy, I want you to enjoy your self saisa I gave you all that u desire, Hadiza banyi aure
dan to hurt you ba infact I did it for you, I did it for my children and for myself, you were not
willing to change and I don’t wanna force you, danaga kin aminta da Ummi, keda baki yabon
kowa but kika yabama Ummi not once, not twice yasa I looked at the girl to see menene in this
girl da matane the whole Hadiza ke yaba” yadanyi shiru ahankali yace “ke kikamin auren nan
Hadiza and I was still considerate to marry the girl wacce keda yaranmu kukai approving sabida
karna saba miki, I don’t think akwai a man that can love his wife this much kaman ni” yayi shiru
yace “I thought bana gabanki cus u don’t value me Hadiza, u don’t look at me with love and
affection dakikemin kafin muyi aure, rather koda yaushe kallona kike like your mate, bantaba
sanin u will react this way da auren nan ba cus banga soyayyan dakikemin ba is as if yayi
disappearing, to my biggest suprise naga auren yasa kin dawo dumu dumu kinasona saisa
danaga haka I always give you my attention, and my love cus I don’t wanna hurt you, I took care
of you, pamper you, always showing you how much u mean to me that babu abinda ya chanza
a soyayyan danake miki eh Hadiza. I want you ki tashi mu rufe wannan chapter na fada kullum,
mudawo kaman yanda muke da and forget everything and live as one okay happily ever after”
yayi maganan yana tashi ya manna mata kiss a goshi sannan yakara gyaramata bargo yafito
yawuce office na doctor.
Zama Nura yayi kan kujeran dake facing Doctor su dake duba file na Hadiza da glasses a
idanu, saida yagama yadago yakalli Nura dake kallonshi yace “Alhaji what your wife had today
was SCA, watto sudden cardiac arrest!” Sosai Nura ke kallonshi Dr yace “well all I can say
miracle kawai yadawo da ita duba da lokacin daya daukeka da ganinta da bata CPR, dakuma
kawota nan hospital still ta farfado is just God!” Ahankali Nura yace “Alhamdulillah Ya Allah,
Hamdan Kaseeran Dayyiban Mubarakan fii” Dr yadan sauke ijiyan zuciya yace “zanyi managing
nata a hospital for 7days dan I need to rule out daga ina wannan matsalan yafara cus this is her
hospital bamu santa dawani matsalan zuciya ba nor hawan jini so inaso zan mata some test
dazamu duba complete lafiyan zuciyanta tundaga kan arteries da veins da komi na zuciyan,
zatayi EKG, MUGA, MRI, Exercise stress echocardiogram test, gashi u need to make payment”
yabama Nura takarda ya karba dasauri yana dubawa Dr yace “Alhaji Nura” anatse Nura yace
“na’am Dr” Doctor yace “so far so good we don’t know meya jawoma this issue and banso nayi
digging into personal life dinku but ina ganin bayan munyi ruling out the heart issue I will refer
her to a psychologist cus I think matanka is suicidal!” Dasauri Nura yace “no, no Dr, Hadiza
musulma ce nasan we are having one or two issues but nasan bazata taba tunanin kashe kanta
ba” Dr yace “yet kasameta abayi akasa ta kunnama kanta ruwa she knows the dangers of that,
banda she’s risking jikinta ma cold that could result to pneumonia, she’s also an adult 32yrs da
2kids more of the reason why dole nayi referring nata to psychologist cus I believe batama san
metakeyi ba duba da what’s at stake, what life nata means to you, to her kids and to her family”
Shiru Nura yayi yakasa magana kana ganin fuskanshi kasan he’s feeling guilty he’s not just
happy, ahankali Dr yace “it’s okay you have to be strong anan” gyadamai kai Nura yayi batare
daya iya magana ba, Dr yace “I will suggest ka kira all family members nata, duk wani
masoyanta should be here for her, koda wasa kada ku kara batamata rai for now, kutaru make
her happy and show her how important she is to all of you, like I said bansan mene asalin
problem din ba but I strongly believe your wife is depressed and suicidal dan haka you people
should show her love” gyadamai kai Nura yayi, Dr yace “Alhaji Nura daga yanzu do kome
zakayi kayi dan karta sake having this cardiac arrest dan believe me she might not be lucky the
second time!” Gyadamai kai Nura yayi yace “İn sha Allah this is the first and last time” Dr yace
“you can go” tashi Nura yayi yafice ahankali yafita waje wani dan dakali yasamu yazauna yayi
shiru yana kallon paper expensive scans da test din zuciyan da za’amata sannan yaciro
wayanshi yakira Jams ya sanar da ita komi da ake ciki yace “zai samata kudi tama kowa
booking flight su taho da Mama da sisters dinta Hadiza needs love that she might be suicidal”
katse wayan yayi yatura mata 1M sannan yakira Hajiya ya sanar da Hajiya ma komi, anatse
Hajiya tace “Hadiza bazata taba kashe kanta ba Nura kasan likitoci da zancen banza wani
zubin” Nura feeling so bad yace “Hajiya duk ni naja komiko”? Tashi Hajiya tayi daga falon ganin
Ummi tafito daga kitchen tawuce dakinta ta zauna anatse tace “no Nura bakai bane kaddara ce”
muryanshi na rawa yace “Hajiya I push Hadiza so hard da tana kokarin kashe kanta ko Allah
yasan ban auri Ummi dan kuntata mata ba Hajiya u know me kinsan danda kika haifa am not a
wicked person, inason mata ina kuma tausayinsu sabida matane kannina gabaki daya” cikeda
so dakuma lallashi Hajiya tace “don’t beat yourself too hard Nura, mata munada zafin kishi,
wasunmu sun iya handling kishi wasu kishin zai iya hallakasu stop blaming yourself Son, aure
ba haram bane Alhamdulillah da ranta yanzu abinda zance maka is tundadai case din yakai
haka karaba musu gida kaji” shiru yayi hakan yasa Hajiya tace “you have too nasan yanda
kakeson yaranka su taso kansu daya but dole ka hakura dan at this point akwai cutarwa tunda
Hadizan ba lafiya gwara yanzu ka dauke Ummi daga gidan nan ka kaita wani waje, idan
kagama sabon gidan ka maida Hadiza chan saika ijiye Ummi anan kaji” gyadama Hajiya kai
yayi yace “to” anatse Hadiza tace “kayı sallan asuba”? Sai a lokacin yaga gari yamadan soma
haske ahankali yace “banyiba bari naje nayi” dasauri tace “tohhh” ta katse wayan.
Karfe goma family Hadiza na asibitin dan Max air suka samu na 7:30 shima dan anyi delay, da
mahaifiyar Hadiza, da Anty Jams, da kannin Hadiza guda biyu dake binta Rabi da Hafsat
dukansu kowa yayi aure duk jugum kowa yayi a asibitin har lokacin Hadiza bata tashiba, Mama
dake kallon Nura dake rikeda hannun Hadiza tace “kaje gida kayi wanka ka kimtsa Nura” girgiza
mata kai yayi yace “bazan iyaba Mama, bari saita tashi ai Dr yace nan da awa daya alluran zai
saketa ta farfado” saikuma da sauri yakalli Anty Jams yace “ga car key na jeki dauko mata su
Aman idan ta tashi ta gansu zataji dadi Batai musuba Anty Jams takarba key Rabi da Hafsatu
sukace zamu biki bata hanasu ba duk motan Nura suka shiga ta tada Rabi tace “wlh sainaci
kutumar uban yar aikin nan dan durun uwatta” wani kallo Anty Jams tamata tana tuki tace
“kinsan Allah idan abinda kike shirin yi kenan zan iya kwana naje na saukeki a asibiti” cikin fushi
Hafsat tace “Anty Jams waike mesa kike abu kaman Mama, inda mu Hadiza takira da tuni bamu
zo mun tayata koran shedaniyan yarinyar ba takama takiraki bayan tasan u will just talk like
Mama look at her yau, inda ta mutu shikenan fa mun rasa yar uwanmu Nura yacigaba da
rayuwanshi like nothing happen mukuma fa? Munrasata har abada, duk yanda zaki kalli abin
Nura yariga yaci amanar Hadiza daya auri yar aikinta, ai da kishiyan gida gwara ta waje,
yarinyar da Ya Hadiza tadauka aiki tamata komi I remember lokacin da Ya Hadiza muna waya
tana yaban yarinyar wai tanada kirki tanason su Aman saisa take biyan yarinyar 50k ni kaina
saida nayi ihu nace yar aikin kike biya 50k abinda akano 5k ko 8k ake biya duk wata, tacemin
yarinyar nada kirki ne but shine munafukar ta aure mata miji akanme Ya Hadiza bazata hadiyi
zuciya ta nemi mutuwa ba is it easy? anty Jams are you even relating the pain Ya Hadiza is
going through everyday agidan nan tana kallon yarinyan” ta share hawayen daya zubomata da
sauri tace “Wlh sabida Nuran ma babba ne kuma akwai Mama awajen da bazan gaidashi ba,
munafuki kawai mayaudari mugu sai yanzu dayaga takusan zuwa barzahu shine yaşan yana
sonta” Rabi tace “bar munafuki ai maza! Maza! Wlh namiji ba dan