Showing 72001 words to 75000 words out of 131659 words

Chapter 25 - Mazan Ko Matan Complete Hausa by M Shakur.pdf

M Shakur   

13 Nov 2025

365

goyo bane, namiji butulu!
Namiji mayaudari! Maza yan duniya! Ba kunya ba tsoron Allah ba kawaici ya auremata yar
aiki!!! Wlh kaman naita surfafamai zagi dana ganshi!” Anty jams kasa cemusu komi tayi dan
itama bawai she’s happy bane she’s just feeling bad ganin kanwarta in that state saida sukakai
gidan tayi parking tajuyo takallesu tace “Hafsat, Rabi’a na rokeku da girman Allah kada kuyi
wani abu kungamai mahaifiyar Nura na gidan bawai kuma lafiya gareta ba please” da magana
ciki ciki sukace “munji” duk suka sauko suka shiga cikin gidan, Hajiya ce ke zaune a falo ga
Meena agefenta dake zuba mata kunu ganinsu yasa tace “a’a su Jamila ne”
Cikeda fara’a duk suka shiga gaigaisawa akayi anawa juna jaje, Anty Jams tace “ina yaran
Baban su yace nazo na daukosu daganan zamu dan daukanma Hadiza kaya adaki” dasauri
Hajiya tace “suna sama yanzun nan Ummi tahaura dasu dan yimusu wanka kuje kuhadama
Hadiza kayan kafin nan tagama shiryasu nima ina ganin zan biku asibitin nan naje na ganota”
Anty jams tace “Hajiya kina fama da kanki dakinyi zamanki agida wlh ai Alhamdulillah tunda
she’s out of danger” Hajiya tace “ina kafana kafanku kuzo kuyi Kari nasan bakiyi ba” duk sukace
Alhamdulillah suka wuce sama Meena tabisu da kallo zata mike Hajiya takama hannunta tace
“me haka ina zaki saikace sata zasuyi agidan”? Dasauri murya chan kasa tace “wajen Ummi
zani” girgiza mata kai Hajiya tayi tace “hakan zaiyi kaman munada wani manufa zuciya Jamila
nada hankali ai yi zamanki anan” badan tasoba ta zauna.

Daidai Ummi tafito daga bayi dauke da Amal a hannunta Aman tariga tamai yana zaune bakin
gado da towel yana jiranta tafito ta shafamai mai su Rabi suka bude kofa suka shigo chak Ummi
ta tsaya dantama tsorata cikinsu Anty Jams kadai tasani da duk suke kallonta, tsayawa tayi
gaban bayin ahankali tace “sannunku da zuwa ina kwana” azuciye Hafsa tataho gaban Ummi
tasa hannu ta karbe Amal azuciye ta nuna Ummi da yatsa tace “kina nema ki kashe mahaifiyar
su shine kuma kike nan nan da yaranta bakar munafuka” dasauri Rabi tai wajen ta nuna Ummi
daga sama zuwa kasa awulakance tace “ke kina gani kin auremata miji ko hmmm je asibiti kiga
menene soyayya wlh na tausayi miki dudda bakijin turenci but zan miki u mean nothing to Nura,
keba komi bane awajen Nura ba, Hadiza Itace komi nashi, mata ta daukeki tabaki aiki, ta biyaki
da kyau, tabaki ci sha sutura but kici amananta ta hanyar aure mata miji abinda kikama Hadiza
Allah yasa ama yaranki! Ama kanninki! Ama jikokinki ke duk Wanda kika hada jini dasu Allah
yasa amusu!” Dan lumshe idanu Anty Jams tayi tace “Rabi and Hafsat please ku dauki yaran
nan kuzo mutafi dakin Hadiza” daukan Aman Rabi tayi suka kwashi kayansu dasuka gani akan
gado wanda Ummi tafito dashi suka juya harsukai kofa Rabi tajuyo takalli Ummi da kanta ke
kasa tace “kuma wlh idan kina Tuna’nın kin kwace mata miji kinyi kuskure ki rubuta ki ijiye saikin
dawo abin tausayi kuma yar kallo agidan nan danko Nura kije asibiti kigani nadaman aurenki
yake, mema yakaishi gashi yanzu kin zama sanadin matarshi uwar yaranshi dayakeso na
neman ta mutu, duk wani addu’a da bokaye da malamanki gwara ki kirasu dan amiki addu’a
Allah sa kar Nura ya koraki, tana maganan suka fice wasu hawaye masu zafi Ummi taji sun
zubomata dasauri ta share tafito daga dakin tawuce ta shiga dakinta ta tafi bayi dasauri ta duka

tafashe da kuka sosai.

Har suka gama abinda zasuyi sukabar gidan Hajiya har sawa Meena tayi taje takirata
dantamata sallama zata bisu asibiti tace ma Meena taba bayan gida.


Ahankali take bude idanu dasuka mata nauyi sosai, dummmm kunnenta yakeyi kaman wacce
ake kwalama kira daga mesa haka takeji taji ana. “Momy, Momy, Momy wake up” rawa rawa
idanunta keyi dasauri jin muryan Aman and Amali daga nesa chan na gayamata ta tashi kafin
tabude idanun nata a juye tana kallon sama ganin mutanen da idanunta basa gane mata su da
kyau blurr blurr take gani saichan taji murya daga nesa ance “can you see me” sake runtse
idanunta dasauri tayi sannan tabude su Dr tagani akanta saikuma taji an rike mata hannu da
sauri takalli hannun ganin Amali da Aman suna kallonta suna kuka har lokacin suna kiran Momy
yasa azabure ta taso zaune Dr yace “woo wooo calm down kada ki tashi” dasauri tasaya dayan
hannunta dake rawa zata shafa kan zaman dake kuka sosai yana shesheka Dr yatayata kama
hannun tadaura kan fuskan Aman rike hannun yayi yace “Momy don’t be sick again I will never
be angry with you again I promise” gyadamai kai tayi Amal tace “me too Momy” ganin yanda
Hadiza ke yunkurawa tanason daukan yaran nata yasa Dr yadago gadon tayi zaman kwanciya
yasada yaran yasasu ko Wanne aside nata rungumeta sukayi kuka hawaye ne suka fito daga
idanun Hadiza ahankali Dr yaciremata oxygen din cikin murya mara karfi tace “A…..man,
Aaa….mal” “yes Momy” kankamesu tayi kafin in a very weak voice tace
“I……..na…..Da…….dy….” Dasauri duk suka dago suna mata pointing Nura dake tsaye dab da
bed din yana kallonsu yana murmushi wani kalan kallon Nura tayi sai lokacin ma taganshi da
duka mutanen dakin sai kawai tafashe da kuka sosai tana mikamai hannu dasauri Nura yaje
rungumeshi Hadiza tayi sai a lokacin karfin kukanta yakaru ta kankame Nura sosai tanajin
mugun sonshi aranta tace “Nuri kayakuri kayafemin duk abinda namak……” hannunshi yadaura
kan lips nata yace “shiiiii u talk too much daga tashinki just get better I love you My Didi”
hawaye na bulbulowa daga idanunta tace “I love you too my Nuri” Dr yace “tunda dai love
moment ake bari naje anjima madawo atafi da ita for lab investigation, yanzu have this moment”
yawuce yafita Nurse tabishi sakinta yayi Ahankali tana kallon yan dakin tace “Hajiya” dasauri
Hajiya taje wajen gadon tace “naam Hadiza ya jiki”? Cikin kuka tace “Hajiya kiyakuri kinji nasan
namiki laifi wlh Hajiya haushinki nadinga ji gani nayi kaman kene kika sashi yamin kishiya da
yar aiki na, bake kadaiba kowama haushinshi nakeji har Anty Jams dake gayamin gaskiya da
ina bayi naji numfashina yana tafiya I was trying nakira Nuri like azo ataimakamin but nakasa
naji wani murya nagayamin bazakizo ba sabida na cutarda ke sannan na zargeki abisa laifin da
baki aikata ba kuma baki tsaneni ba, Hajiya naji dadi da Allah yatasheni nayi alkawari dan nemi
gafaranki Hajiya kiyakuri kinji” share mata fuska Hajiya tayi tace “Hadiza nobody is above
mistake komi yawuce awaje bantaba rikeki ba kinji”….
***


Yau kwana uku Hadiza na asibiti tun ranan Nura bai kara kiran Ummi ba ko gida baya dawowa
shike kwana da Hadiza saidai akaimai kaya, yan uwanta ne ke dawowa gida kwana su shiga

kitchen suyi girki saiya zamto Ummi kullum taba daki muddin zata fito tahadu da Hafsat ko Rabi
saisun yada mata habaici, takira Nura sau uku bai dagaba tamai text daban daban duk ba reply
Hajiya kadai da Meena ke kula da ita dudda bata nunamusu komiba Hajiya ko ankawo abinci
idan sun gama girkawa ko Ummi na sama saita kirata tazo aci abincin da ita hakanan zata
sauko not feeling among, idanun Ummi sun fada babu abinda yafi damunta yanda Nura bai
kirata ba ba reply kullum saitai kuka kafin tayi bacci.

Yau kaman kullum wuraren 12 tana zaune ita kadai a falo Meena tashigo dakinta tace “tashi
muje asibiti tare” dasauri Ummi tace “ba’ace naje ba, kinga ko Hajiya batace najeba hakama
Baban Amali karnaje wani abu yasami Hadiza” Dasauri Meena tace “Hajiya takirani tace muzo
tare Allah shayi akasa nahada, tashi kisa Hijabi muje bolt na kira yana waje ya iso” badan
tasoba ta tashi hijab kawai taja maroon har kasa tasaka tabi Meena suka fice daman kowa na
asibitin har Hajiya suka wuce.

Wuraren 1:15 sukakai hospital din Ummi sai kallon asibitin take yahadu sukai ciki har zuwa
gaban dakin da Hadiza ciki Meena na gaba ta window dakin Ummi ta hangi Hadiza zaune kan
gado ga Aman da Amal sun rungumeta kaman zasu koma ciki Hajiya na bata kunu da spoon
tanasha su Yayyinta da Mama ana hira kowa na nan nan da ita, daidai Meena tasa hannu zata
bude kofan su shiga ciki kaman daga sama sukaji muryan Nura yace “Meena!” Dasauri suka
juyo Ummi ta tsare Nura da idanu sabida yanda tai kewanshi yaune rana na hudu dabata
ganshi ba dasauri sauri yake tahowa yana leken dakin kaman mara gaskiya yana zuwa wajen
cikeda fada yanuna Ummi yana kallon Meena yace “wayace ki kawo Ummi asibitin nan eh
Meena?” Wani kalan dum! Dum! Dumdum!! Ummi taji azuciyanta ta tsaya chak tana kallon Nura
dake kallon Meena ranshi abace kawai yasa hannu ya karbe flask din daga hannun Meena
yace “wuce kije ki komarda ita gida” daidai lokacin sukaji Hadiza tace “Hajiya kaman muryan
Nuri na nakeji ko” dasauri yayi kofan yace “gani nan My Didi” yashiga ciki ba Ummi kadaiba har
Meena jitayi ranta ya sosu da abinda Nura yayi daurewa Ummi tayi iya daurewa takalli Meena
cikeda Fara’a tace “kingani saisa nace miki bai dace nazo ba Hadiza batada lafiya, baidace ta
ganni ba kiramin bolt nabishi nakoma gida kesaiki zauna” Meena batace komiba cikeda bacin
rai tashiga tafiya tana neman bolt Ummi dan juyawa tayi takalli cikin dakin Nura na kusada
Hadiza ta daura kanta a kirjinshi yana shafa mata kalaban kanta da wani kalan shaukin so
dayan hannunshi yana nuna mata hotunan bikinsu sai murmushi suke both ita da shi looks so
happy, hawaye Ummi taji sun zubomata da sauri tasa hannu ta goge tajuya dasauri tawuce
awaje tasami Meena daidai bolt yazo Meena zata shiga Ummi takama hannunta tace “Meena
dan Allah sabida ni kada ki fasa zuwa wajen Hadiza ki gaidata please kije nizan koma gida ni
kadai please dan Allah” Meena da idanunta sunyi jaaa tace “Ummi sakeni” cikin lallashi Ummi
tace “inhar kinasona da gaske ki koma nizam koma gida please Autan Hajiya” badan tasoba
takoma Ummi tashiga motan bolt yaja motan suna fita daga asibitin Ummi tarushe da kuka
sosai dasauri mai bolt yajuyo yace “Hajiya lafiya”? Cikin kuka muryanta bama yafita da kyau
tace “bakomi kawai mutafi” yanda take kuka harda shesheka saitaji ta raina kanta duba da
yanda Hadiza keda komi, she’s surrounded da family dake sonta ga Miji ga yara saitaji ta raina
kanta, batada kowa batada komi! Allahu Akbar! Ranta ya sosu yau takara tuna ita marainiyace
Mamanta ta rasu! Babanta yarasu! Kakansu kadai gareta data tsufa tukuf sai kannenta yara su

Shatu su biyu 12 and 13yrs, jibi yanda Nura yayi da ita yau kaman wulakantacciya mara daraja!
Yasa she felt like she’s nothing to him! Yasa taji she don’t belong anan a family nan, ahankali ta
bude yar jakan data dauka taga tanada kusan 15k aciki cikin muryan kuka tace “direba dan
Allah kaini tasha dazan sami motan Adamawa yola” Dasauri direba yace “location zamu chanza
kenan jabi garage za’a samu” cikin muryan kuka tace “kaini” nan yakaita har inda ake lodin
Adamawa Yola tabiya direban 2k tana zuwa tabiya 13k kudin mota amman sai dare motan zai
tashi tafiyan dare ne tanemi waje kawai ta zauna takifa kanta kuka take mai tsuma rai bana
wasaba, gani take ko Mudi baitaba hurting nata this way ba dan shi physical damage yamata na
duka dasauransu, Nura just crushed her fragile zuciya dake cike da dumbin sonshi azuciyanta
kafin yakoreta gabadaya agaban jama’a gwara takoma kauyensu ya biyota da saki takara
rushewa da kuka.


Wayyo Allah na Ummi

Kai Maza maza maza!! One word for men please cus suna bani ciwon kai.
What exactly keep a Man?? Sex? Happiness? Respect? Ko Loyalty???
The list is long but in your opinion what keep a Man?





MATAN?? Ko MAZAN??


✍M SHAKUR


EPISODE 2️⃣0️⃣

@TRENDYOUTNET Modest fashion world ne inda zaki samu professional kayan zuwa office
masu kayatarwa, kyawawa, masu suturta jiki da mutuntawa, idanma casual kaya kike nema na
sakawa yau da gobe duka tanada sunadashi all you have to do is chat them up ta wannan
number wa.me/+2349093300112
Kokuma zaki iya zuwa shagonsu dake nan Shop C22C 2nd floor Platinum Mega Mall opposite
Ultra Modern Market Behind Next Cash and Carry Jahi, Katampe Road Abuja
And u can also check shagonsu a IG @trendyoutnet don’t forget to follow them cus anayi
baki

20
Saida tayi kuka ta koshi sannan tadago kanta taciro wayanta daga jaka tareda mikewa tabar
wajen taje chan wajen wata bishi ya ta duka awajen, duk duniyan nan batada kowa banda
kakanta duk wani abu data iya yau aduniya kakarta ta koyamata, Kakarta is her everything.
Dialing number ta tayi yana ringing ta daga tace “Yar Albarka kinganni nan fa tundazu nake jinki
araina amman Shatu nake jira tadawo tazo ta tayani kiranki amman ina tanachan tana buga yar
gala gala, ya kike yar Albarka ya mijin naki da kowa da kowa”? Kungane feeling dinnan da yaro
yakeji idan yana cikin damuwa yaji muryan iyayenshi kawai sai Ummi ta rushe ma Gwaggo da
kuka, hankali tashe Gwaggo tace “ke! Meya faru kike kuka haka? Waya tabamin jikata iyye?
Rabonda naga kinyi kuka haka tun zamanin azzalumin nan Mudi, meya faru kike kuka Ummi?
Ya isa, ya isa, bagani ba, da raina fa Ummi kike kuka haka sokike Mamanki tayi fushi dani
bayan tabani amanan ku, dena kuka kinji komeme ina nan fa, da raina kuma oya ya isa, zan iya
saida raina naga bakuda matsala arayuwan nan, ishuru Zainabu ishiru kinji, wayataba mini
yarinyata mai hakuri da kawaici da kunya? Wayatabamin jikana?” Cikin wani kalan kuka Ummi
tana shesheka tace “Nura!” Salati Gwaggo tayi da sallallami tace “Nuran ne yasamin ke kuka
haka? Mutumin danaganshi tsofai tsofai dashi zai iya haifanki sau biyar shine zai sakamin jika
kuka haka? Shi baisan badan naganashi tsoho babban mutum mai hankali daban yarda
nabashi ke ya aure ba, wato yagama tsotse kuruciyanki zai fara miki tijara, meya miki? Share
hawayenki fadamin meya faru, fadamin daga tushe zuwa reshe share hawayen ki imaza,
inajinki” share fuskanta Ummi tayi kaman yar baby tana kuka ahaka dai tabama Gwaggo labarin
komi dake faruwa gabaki daya bata boyemata komiba har zancen kannin Hadiza, Gwaggo tace
“amman mijinki yabani kunya Ummi, sabida shi tijararre ne katon banza, da girmanshi da
tsufanshi bai amfaneshi ni zaizo har gidana ya auremini ke, wato auren huce takaici yayi, yazo
ya chusama jikana soyayyan shi a zuciya haka sannan ya wulakanta mini diya? Jibi yanda
jikana ke kuka a tasha gaban dubbannin mutane sabida shashashan Nura” Gwaggo tayi shiru
tana karajin yanda Ummi ke kuka ko ba’a fada mata ba taji tsananin soyayyan Nura atattare da
Ummi, wannan karan ne yatta tafada soyayya bata taba son wani ba Ummi, lokacin da akamata
auren Mudi bamatasan menenen soyayya ba, da ace Ummi batason Nuran datace mata
tadawo gida dan dudda tana yar kauye tasan darajan jikokinta, lokacin da Mudi ke kirbama
Ummi duka tasan taje ta dauko jikanta tadawo da ita gida, tayi shige da fice akauyen nan
maigari da manyan gari tasa aka raba auren, dudda Mudi nashigowa har gida yadakesu still
batasa Ummi takomamai ba saidai tasan yanda tayi tafitar da Ummi daga kauyen, ina bata
yarda awulakanta jikokinta ba. Ijiyan zuciya tasauke ahankali tace “Zainabu” ahankali Ummi
tace “na’am Gwaggo” Gwaggo tace “Ummi dudda mu yan kauye ne ba yan binni ba Ummi
nabaki tarbiya nakoya miki dabarun zaman duniya ke Ummi ko birnin sin aka kaiki zaki iya zama
cikin mutanen yan boko sannan ki samama kanki lafiyayyen waje dan haka share fuskanka,
Alhamdulillah ina raye ban mutu ba, Nura ne dai ko wlh sai yasan yayi rashi dan jikata daban
take acikin jikoki dubun dabara!” Gwaggo tace “dudda za’ace kinyi gajen hakuri dakika taho ai
aure ya gaji yau ayi fada yau ashirya but ni kakarki nayi na’am da tahowan ki Ummi idan Mata
da Miji natare inhar akwai soyayya to ka tsaya koma wace ukubace zaka iya jajircewa ka
maganceta amman in babu soyayya a auren gwara kayi gaba, abinda Nura yamiki ya nuna
kaman dama chan baitaba sonki ba yakawai aureki sabida ya farkan da sumammiyan matanshi
Hadiza ne yanzu kuma data farka baida bukatanki dan haka saurareni nan Ummi kibawa Nura

tazara harsaiyasan amfanin ki, ke koda baya sonki ke wlh ma yayi karya yace baya sonki, Ummi
nabaki tarbiya da dabarun zaman duniya duk wanda yazauna dake saiyaji yana sonki Nura na
sonki kawai bairiga yasan dahaka bane amman yanzu zai sani, kalleni nan bazaki dawo
adamawan nan ba, sabida zai biyoki nan barni dashi yazo nemanki wlh wlh daina mishi wankin
bargo zan solleshi tas, saizan yarana nada daraja kuma babu abinda bazan iyaba akanku ku
ukun nan, kinsan mezakiyi yanzu?” Dasauri Ummi tace “a’a” tace “kowa yariga yasan ke
yarinyace mai tarbiya da hankali ce baikamata kitashi farat daya kibar gidanba yakamata ki
sanar da wani babba yanzu Hajiya na asibiti kada ki kirata dubama da bawani lafiya gareta ba
kira kanwar Nura dakika gayamin kwana kin baya kunyi waya wacce bata kasan kiraya maza
maza ki gayamata cikin hikima kinji” Gyadamata kai Ummi tayi Gwaggo tace “koyaya kukayi ki
kirani kisake sanar dani wayata na hannuna”.


@TRENDYOUTNET Modest fashion world ne inda zaki samu professional kayan zuwa office
masu kayatarwa, kyawawa, masu suturta jiki da mutuntawa, idanma casual kaya kike nema na
sakawa yau da gobe duka tanada sunadashi all you have to do is chat them up ta wannan
number wa.me/+2349093300112
Kokuma zaki iya zuwa shagonsu dake nan Shop C22C 2nd floor Platinum Mega Mall opposite
Ultra Modern Market Behind Next Cash and Carry Jahi, Katampe Road Abuja
And u can also check shagonsu a IG @trendyoutnet don’t forget to follow them cus anayi
baki




Kiran Ya Aisha tayi ringing daya Ya Aisha ta katse

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login