Showing 6001 words to 9000 words out of 131659 words

Chapter 3 - Mazan Ko Matan Complete Hausa by M Shakur.pdf

M Shakur   

13 Nov 2025

367

bangaren akace “Ya Nura ina yini” “how
are you Aminatu ya jikin Hajiya kunje asibitin”? Kasa magana tayi sai bakinta yahau rawa,
dasauri yasa hannunshi yadauki wayan gabanshi ya mugun fadi yakai wayan kunnenshi dasauri
yace “what happen jikin Hajiya ne meya faru?” Cikin kuka tace “dazun nan tafadi abayi yanzu
haka muna asibiti” bugawa kirjinshi yahauyi sosai anatse yace “Dr Tanimu ne ke ganinku”?
Dasauri tace “eh shine” dan ijiyan zuciya yasauke yace “daina kuka ya isa babu abinda zai sami
Hajiya kinji” kaman yana gabanta gyadamai kai tayi, cikin dan taushin murya yace “is okay,
zanyi magana da Tanimu I think zan muku booking flight gobe kutaho nan Abuja taje babban
asibiti anan don’t cry again hankalinta zai tashi, akwai kudi awajenki”? Dasauri tace “eh akwai”
ahankali yace “to stop crying bari nai magana da Dr Tanimu” nan da nan ya katse wayan yakira
Dr sunyi magana da dadewa sannan ya katse wayan dakanshi yamusu booking first flight na
gobe da safe sannan yasake kiran sister nashi yace zasu biyo jirgin safe gobe suzo koya ake
ciki tadinga gayamai yatashi ya idasa shiryawa duk mood nashi ya chanza sannan yafito anan
falo yaga Aman da Amal suna kallon cartoon a iPad nasu duk an musu wanka sunyi kyau
gwanin ban sha’awa kaman ya debesu yafita dasu Amal kaman ba itane mara lafiya ba
karasawa yayi inda suke ya duka yamusu peck agoshi yace “Dady zaitafi aiki” dasauri Aman
yace “Dady zan bika office” shiru yayi kaman mai tunani yana shafa kansu yace “shikenan zanje
daku amman sai ranan Saturday jibi kaga gobe akwai school yau bakuje ba dukanku” Dasauri
Aman yace “hadda Anty Ummi zamu itama taje taga Daddy’s bigggggg office” ya ware
hannunshi biyu yana nuna how big office na babban shi is, dan murmushi yayi yana kallon
Aman din kafin ahankali yace “yes Son hadda Anty Ummi” dasauri Aman yace “love you Dady u
the best Dad ko Amali? Dadyn mu is the best” dasauri Amal yace “yeeeessssss Dady is the
best” murmushi yayi yace “my princess and my Aman are the best nima” harzai tashi yace “ina
take?” Aman yace “Anty Ummi”? Gyadamai kai yayi dasauri yace “itama taje tai wanka
adakinta” jinjina kai yayi yamike yace “to natafi bye” bye sukamai yawuce yafice.


Wani babban shago ne girmanshi zaiyi wani super market din sama da kasa ne, kasan abayoyi
ne irin na yan millions din nan designers dan babu abayan yan 100 ashagon saikuma sama
asalin designers bags da shoes ne latest collection ma kuwa, zaune take cikin wani office dake
nan sama babban office ne na gaske dawasu mata guda biyu suna hira, daya daga cikin matan
biyu ne tadaura tissue kan idanunta tana kuka Hadiza taje tsaki tace “kodai nazo nai magana da
mijin nan naki ne Baraka”? Dasauri Baraka tazare tissue dagakan idanunta takalli Hadiza
idanunta sunyi jazur tace “so kike ya koreni? Not everyone is as lucky as u are kinada miji
kaman Nura mai hakuri da share magana, idan nama Ubale abinda kikema Nura saiya
lakadamin duka halan saiya korani gida” wacce ke kusa da itane ta tureta tace “dallachan ai
gashinan saisa sai gallaza miki azaba yake waya cemiki anama maza good girl yanzu??”
Dasauri Hadiza tace “ahh tohh tell her ooo my dear, tell her Zee cus good girl no dey pay again,

kima miji good girl ya tattakaki yayi using naki do dambu yaje ya watsar a shadda, ai yanzu
zaman Auren fire for fire ake yana baki kada kibari yakai kasa give him back gbasgbos kawai
saikaga yasha jinin jikinshi yasan keba kanwar lasa bace, kinga Nura ko giyan wake yasha
yasan bai isa ya tunkareni da nonsense nashi ba cus bana ma dauka ne kuma gashinan
nasama ma kaina lafiya I do duk abinda naga dama duk abinda raina yaso agidana to waima
tsaya idan nai aure banyi whatever naga dama agidana ba yo menene fa’idan auren? Menene
banbancin gidan mijina da gidan iyayena? Abeg ke waye Ubale yana cemiki kule kicemai chass
wlh zakiga kun zauna lafiya” dasauri Zee tace “Allah yasa ta dauka, itane kullum yamata ihu
kaman ubanta, fita saiyaga dama yake barinta, yahanata business ya kulleta agida kullum ciki
yake duramata won’t you speak up kinuna mishi kefa duk lokacin dakikaga dama fita zakiyi ki
kwatarma kanki yancinki, ki nunamai kedashi are equal sabida yana namiji baya nufin zai dinga
juyaki, munafa zamanin feminism ke duk inda namiji yau yataka aduniya kema zaki iya takawa
to akanme zaki maida kanki slave dinsa? Jibemu kawayenki yanda muke more rayuwa
muncigaba ke kinachan kina bautama mijin dake hanaki fita sana’a, yakuma miki ihu” tissue
takara dauka dan maganganun su nasata jin badadi datasan hakane da da Zee tazo daukanta
batabita ba, tace “nidai kubarni duk randa nazo wajenku saikun sani ina feeling bad inajin kaina
kaman banda sa’a aduniya, kaman I’m the unlucky one, Ubale na sona ina sonshi kuma ya isa
yace nayi nayi karnayi karnayi ya is…….” Mtswwwww Hadiza taja tsaki dayasa Baraka tai shiru
takalleta Hadiza tace “takuraki dai baya bari kiyi yanda kikaga dama, imagine yaranki uku har
yanzu kece ke komi agidanki, girki, kula da yara uku fa da sauransu ke jakace Baraka? In nice
ai sai na mutu, Idan yana sonki bazai sama miki yar aiki ba haba akan mene zaki dinga shiga
kitchen kina girki awan nan zamanin da masu kudi ke hiring intercontinental chef yana musu
girki agida that’s my next plan ma ni nadauko professional Chef daman na share zancen ne
bayan na sami wannan current yar aikin nawa Ummi but still zan dauko” dan murmushi Baraka
tayi tace “Allah baki sa’a, kowa nada abinda works for him, ninaji naga kuma zan iyane ne,
mubar maganan please kona tashi nayi tafiya ta gida daman Zee takawoni, I don’t have to be
like you ladies, tundadai ba dukana ko wahalar dani mijina keyiba ko neman mata
Alhamdulillah” dasauri Hadiza tace “to abar maganan amman wlh sabida kawai ke kawarmuce
duk tare muka taso da tuni mun rabu dake danni banga dalilin dazaisa kene ke duka aikin
gidanki ba mijinki na miki ihu kaman wata jak…….” Karan da wayanta yayi yasa takasa karasa
maganan takalli screen din ganin Nuri yasa tai murmushi sosai tajuyo da wayan tace “kun gani”
tanuna musu screen din wayanta tace “tsakanina dashi kar tasan kar ne amman jibi yanda yake
bibiyana maza fa saida hash treatment kana musu taurinkai ki nuna musu ke fire for fire ce cus
sun iya raina mace kai mai sanyi irinsu Baraka” Zee tace “kwarai kuwa Aminiyata”.


Tashi Zee tayi takalli Barakan tace “muje mu duba abayoyin to” tashi tayi tabita suka fice ba
walwala kan fuskanta, Hadiza na kallon kiran sai murmushi take dake kara fito da kyawun
fuskanta saida wayan yayi gab da katsewa ta dauka takai kunne ayangance tace “ka gama
nunamin matsayina menene kake kirana kuma yanzu”? Dan shiru Nura yayi yana jinta ba
sallama bakomi kafin yamace wani abu tai magana, yana addu’a duk wani namiji dabai Riga
yayi aure ba to Allah yarabashi da auren mai baki kaman na Hadiza, saikuma chan yace “Hajiya
tafadi abayi yau an kaita asibiti but hankalina bai kwanta ba namusu booking flight na safe gobe

zasu taho nan da ita da Amina zan kaita hospital taga kwararren Dr, specialist” wani abu Hadiza
taji ya tsaya mata arai zai cigaba da magana ta tareshi tace “wai Nuri what gives you the right
kadinga making decision regarding our family on your own eh? Wai meke damunka ne zakace
Hajiya bama ita kadaiba harda kanwanka suzo gidana bazaka fadamin ba kaji me zance kafin
nan kai kadaine agidan? Kodon kaga gidanka ne? Koma da gidanka ne ai nima ba zaman
banza nake agidan ba aure ne yabani gidan dan haka u have no right to invite koma waye into
my home without telling me, without seeking my approval” tunda Nura yake baitabajin urge na
yadaga hannu ya mari mace ba sai yau wlh he feels kaman yadaga hannu ya kifama Hadiza
marin da saiya maida fuskanta keya, keyanta yadawo fuska, mahaifiyarshi ba lafiya bama ta
tambaya yaya jikinta ba or anything sai maganan gida, menene agidan? What is house? Me
Hajiya zatayi agidan? Yau shekaransu nawa da aure Hajiya bata taba zuwa Abuja bama
ballema gidanshi so menene abinda matan nan ke fadi? What can a sick old woman zata
possibly iya miki agida tana fama da kanta fisabilillahi?Yanada mahaifiya mara lafiya da zatazo
garin abuja for the first time yaje yakama mata hotel ne sabida matanshi batason wani yazo
wajensu???

Daurewa yayi yarike zuciyanshi yana controlling anger yadan sauke ijiyan zuciya Hadiza
tabugamai ihu da tsawa tawaya. “Ina maka magana kamin banza are you deaf ne or what Nuri?
What gave you the right to invite a third party to my house baka fara sanar dani ba” shi Hadiza
ke kira deaf??? Innalillahi, cikin wani irin murya datai sanyi sosai tsabagen bacin rai yace
“mahaifiyata ce third party Hadiza? Maman mijin dakike aure uban yaranki, kakan yaranmu
itane 3rd party”? “Well u can translate it duk yanda kaga dama is none of my business just listen
to wat am about to say” tadan gyaran murya tace “first of all bada yawuni aka kawota ba don’t
expect anything from me babu abinda ya shafeni da dawainiyan ku, sabida Hajiya bazan fasa
fita aiki na ba, kuma bazan shiga kitchen ba, kuma bani acikin tafiyan zuwa asibiti ko rakiya kai
infact banda any business with anything dazai faru daga goben nan zuwa harta bar gidan, dan
haka kaika sani ni please sai anjima I am busy with work, I don’t have time for ur unnecessary
demand” ta katse wayan Nura yadade yana kallon wayan kafin ya fuzar da iska kaganshi dole
kai saluting nashi dan namiji ne mai hakuri dayay composing kanshi bai duramata zagi ba,
dama kiranta yayi yaroketa kada taje aiki gobe sabida su Hajiya sannan kuma ya tambayeta me
da me babu agida amman jibi abinda tayi rasa abinda zaiyi yasa yayi dialing number Gardner
na gidanshi ruwa ringing daya ya dauka anatse Nura yace “Amadu banda number Ummi danje
ka buga kofa ka bata wayan” dasauri Amadun yace “gasuchan inajin muryansu a garden takai
yaran suna buga kwallo bari nakai mata” anatse Nura yace “ok”.

Bata wayan Amadu yayi yace “gashi Alhaji yakira zai magana dake” sa wayan tayi a kunne
kaman yana gabanta ta duka tace “Alhaji ina wuni” baisan what just happen ba amman har cikin
zuciyanshi yaji sanyi aranshi na muryanta, dan ijiyan zuciya yasauke ahankali yace “Ummi
mahaifiyata da kanwata zasuzo gobe dasafe Mamana bata da lafiya zataga likita agarin nan”
da zuciya daya Ummi tace “Subhanallahi Allah yakara sauki, Allah yasa kaffara ne, Allah kuma
ya iso dasu lafiya ya tsare hanya” Wallahi he cannot even explain wani kalan dadin addu’an ta
da sanyinsu dayaji aranshi, jin yanda yayi shiru yasa Ummi tace “Alhaji kanaso na gyara musu
wajen kwanan su ne namata abincin da marasa lafiya keson ci”? Harga Allah ta dauka abinda

takira yafada kenan cus ana bata wayan abinda yafara fada mata kenan mahaifiyarshi ba lafiya
kuma gobe zatazo. Yarinyar nan is not just good with kids tanada great sense of humor tanada
hankali tasan meyakamata and tanada natsuwa, though abinda yakira was yanaso ya tambaya
menene babu agida but tambayanta made hum wanna talk to her more, ahankali yace “menene
abincin marasa lafiya Ummi”? Kai tsaye dan babu komi aranta tace “meke damun Mama
Alhaji”? Yanda tafadi Mama ba Hajiya ba dan yasan batasan Hajiya ake kiranta ba wani sanyi
yaji aranshi baisan lokacin dakaman wani dan karamin yaro yace “ciwon sugar da hawan jini ke
damunta” dan shiru Ummi tayi kafin ahankali tace “abincin dayakamata tanaci abinci ne da babu
sugar aciki, babu Gishiri kuma dan Gishiri yana kara hawan jini, zan mata tuwon Alkama ko
tuwon garin plantain dabai nunaba amman duka biyun bamu dashi agida, da miyan ganye,
Gwaggo na a kauye nada hawan jini da ciwon sugar duk nasan irin abincin datake ci dake
taimakamata bata cika ciwo sosai ba, idan Mama tazo itama zan dinga dafa mata zakagani zata
ji sauki da izinin Allah” dan murmushi kadan yayi a tsane yace “nagode Ummi kituramin sunan
abubuwan da zan sayo dakuma abubuwan da babu agida, saiki gyara musu wajen kwanan”
Ahankali tace “to” dan shiru yayi itama tai shiru tana jiran taji ko akwai wani abun jin shiru yayi
yawa yasa tace “hello” batare daya amsa ba yace “inaso naci tuwon shinkafa da miyan taushe
ki dafamin kinji” yanda yayi maganan ataushashe saida taji wani iri dasauri tace “too” yasake
shiru itama tai shiru tana sake jiran maganan shi maganan su Aman da Amal dayaji suna Anty
Ummi come come let’s continue yasa yace “to saina dawo ko” ahankali tace “too Allah dawo
dakai lafiya” lumshe idanu yayi tareda zare wayan daga kunne he just wish da matanshi yayi dis
dogon magana wlh babu abinda yake craving yanzu aduniya irin kwanciyan hankali, Allah ya
azurtashi, yakuma bashi yara, kwanciyan hankali ne kawai yarasa, yesterday yafara magana da
yarinyar nan why is he enjoying conversation da ita haka?.

See y’all Saturday




Let’s keep HADIZA in one place, one of the major abu dake kawo matsala agidan miji is
shigowan baki, guest ko visitors aturence.

Mata will always say ban isa nakawo baki batare dana sanar dakai wane ko wance zatazo ba.

Maza kuma sai sun gama cema mai zuwa Allah kawoshi lafiya za’a cemiki babe wane ko kaza
na hanya fa zaizo ko zatazo tamana kwana biyu hakan na batama Mata dayawa rai.

My question is, is it okay for mijinki ya yarda kowa yazo kafin yazo yafada miki daga baya wane
ko kaza zaizo?
Koko yakamata yafara neman yardanki ne kafin wane ko kaza yazo?? Cus I keep wondering
gidan aure belongs to waye exactly??
Does it belongs to the wives ne sabida ai cewa ake za’a kaiki gidanki ko it belongs to mijin kadai
ne koko gidan aure belongs to the TWO OF YOU???

To idan gidan na dukanku ne biyu maisa ba’a making decision kan wanda zai shigo tare???

Mata ayanzu daku nake ko sabida maza sunsan mun tsani ace wane ko kaza zaizo ne koda an
gayamana bazamu yarda ba saisa gwara suyi accepting wane yazo kafin asanar damu cewa
wane zaizo rana kaza????

How do you think za’a iya magance yawan issues da ake samu idan za’ayi baki agidan miji??

Let’s discuss this
MATAN?? Ko MAZAN??


✍M SHAKUR


Novel din nan is FREE bana kudi bane.
Chat me up don saki a group

wa.me/+2347012181461


EPISODE 4️⃣
Wuraren 7:30 Hadiza tashigo gidan gabaki daya ranta amugun bace yake, Aman da Amal sai
Ummi ne afalo dukansu ukun suna zaune kan dogon kujera suna kallon videos letters sound for
Amal dudda Ummi bawani boko tayiba iya kanta JS3 but ta iya all this basic things na school
shima sound din dan bata iyabane zamanin su da ABCD sukai karatu ba da sounds ba saisa
suke koya tanan youtube yanda Amal ke koya itama haka take koya dan sabida koya musu, jin
an bude kofa kai tsaye ba sallama yasa suka jujjuyo dukansu hada idanu Ummi tayi da Hadiza
dake mata wani kalan kallo dayasa dasauri tamike tsaye daga kan kujeran ta duka kasa danta
gane kallon me take mata cike da girmamawa tace “barka da dawowa Anty, ina yini” Hadiza da
dama ta shigo da mugun bacin rai dan tun kiran da Nura yamata ashago ranta yake abace tace
“ke ban gayamiki koda wasa kada duwawunki yazauna akan kujerun gidana ba, ke kinada
darajan dazaki zauna inda nake zama ne yar aiki dake, ubanwa yagaya miki yan aiki nada
matsayin zama akujerun gida” Ummi da kanta ke kasa ahankali tace “kiyakuri Anty mancewa
nayi Amal muke koyama karatu” baki Hadiza tabude zatai magana daga Aman da Amal da duk
suka tashi suna kallon Maman nasu Aman yace “stop shouting at Anty Ummi Mommy” dasauri
takalli yaron ta ballamai harara, turo baki Aman yayi yace “u are always fighting and screaming
Mommy our school teacher tace anger causes sickness” hararanshi Hadiza tayi bata tace
“nakusan fasa bakin nan naka mara kunya kawai” turo baki yayi dan haushin Mommy shi yakeji
sosai sabida yanda koda yaushe fada takema Anty Ummi su, bata sake cewa komiba tun
maganan Aman tacire heels din dake kafanta awajen tawuce dinning straight taja kujera ta
zauna tana sauke jakanta kan table din tace “idan kinga dama kizo kibani abinci” tashi Ummi

tayi da sauri ta taho dinning din Aman kuma yakoma kan kujera yayi zamanshi yadauki IPad
itakuma Amal tayi hanyar dinning din cikeda shagwaba tace “Mummy babuuuu, ki goyani zanyi
bacci” cikeda masifa Hadiza ta nunata da yatsa tunkafin takarasa dinning din tace “don’t even
come here wuce kitafi wajen Aman kiyi karatu yanzun nan nadawo zaku fara damuna, goyon
kaniyanki zan miki, jeki jira yar aikinku tazo tagoyaki, Oya go back” juyawa Amal tayi tafashe da
kuka dasauri Ummi takalleta kaman tadaina serving Maman taje ta dauketa, ta tsani taga yaran
na kuka wlh har cikin ranta, ahankali tawuce wajen Aman tafada jikinshi rungumeta yayi yace
“stop crying Amali Anty Ummi is coming yanzun nan kinji” Gyadamata kai tayi yana share mata
fuska yace “let’s play game”.

Tunda Ummi tafara serving tuwo a plate Hadiza ke kallonta zuciyanta na wani kalan tafarfasa
kawo tray gabanta Ummi tayi ta ijiye bata idasa jaye hannunta ba Hadiza ta daga tray gabaki
daya ta mike tsaye ta kwarama Ummi akai da tuwon dake a leda da miyan taushen da
kwanukan da cokulan duka suka bare akanta wani kalan mahaukacin azababben mugun ihu
Ummi ta kwala tafashe da kuka dayasa su Aman suka firgita dukansu suka juyo ganin Anty
Ummi ta tsugunna a dinning ga miya tundaga saman dan kwalin kanta har goshinta da idanunta
ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login