Showing 21001 words to 24000 words out of 131659 words

Chapter 8 - Mazan Ko Matan Complete Hausa by M Shakur.pdf

M Shakur   

13 Nov 2025

358

da ita kodan
yaranku, kada ka manta Annabi yace akama mace saki daya yakamata tana zaune agidanta ne
kacigaba da bata ci da sha har zuwa ka maidata dan haka bring her back karka sabama
koyarwan addinin mu” dan ijiyan zuciya yasauke yace “dazu Mamanta takirani tabani hakuri I
just told her naji” dasauri tace “yauwa ka kyauta, yaushe zakaje neman auren Ummin? Ka sanar
da ita kana sonta?” Girgizama Hajiya kai yayi yace “saina kaita kauyensu zan fada mata inaso
sai mun koma
Munga Dr gobe naji mai zaice game da ke, kafin nasan ranan dazan kaita” shiru Hajiya tayi ita
bataso tacigaba da zama agidan nan ahankali tace “koma me ake ciki gobe daga asibiti ka kaini
gidan kanin marigayi mahaifinku daganan suma ai zasu dinga iya kaini asibitin ballama nasan
magani zaa bani ace nadawo bayan one week, koma menene inason jibi ka maida Ummi gida
ka sanar da yan uwanta banson yanda soyayyanta ya kullu aranka tana zama karkashinka
shaidan is real kana jina kaje garinsu jibi ayi magana muji me ake ciki idan da hali zasu baka sai

adaura auren achan ma sai kaje tareda kanin Babanka da wasu abokan naka, da Meena kuma
Ubangiji Allah yasa albarka ni kaina na yaba da natsuwan yarinyar kuma ta kwanta mini arai.


Ba karamin fada mahaifiyar Hadiza tamataba kuma tace tabama Hajiya hakuri da Nura, washe
gari ba dudda idanunta a kone suke amman kana ganinta tai zuru zuru sanda Mamanta tagaya
mata Nura yace takoma har ijiyan zuciya tasauke aboye baro shagon tayi wajajen 8.
Around 9 takai gidansu tana parking motanta Nura na fitowa daga gidan rike da Hajiya da
Meena suna hira suna dariya yayi wani irin kyau yana sanye da soft material milk yasa
sunglasses a idanunshi, hada ido tayi dasu dasauri ta dauke kai haderai tayi tamau ta taho
saida tazo dab dasu tace “sannu ya jiki” bata jira amsan Hajiya ba tawuce ciki tabude kofa ta
shiga ta bugo kofan Nura yajuya yakalli kofan Hajiya tace “muje kaga 10 fa likita zai ganmu”
wucewa sukayi suka tafi.

Tunda Ummi taga Hadiza tadawo ta shiga ta natsu tana gama aikinta ta tafi bayan gida a
garden ta zauna akan kujeran lilon su Amal da wayanta a hannu tana buga game, ringing
wayanta yayi dasauri ta kalla batasan number ba amman tadauka takai kunnenta ahankali tace
“hello” anatse Nura yace “Hajiya Ummi” batasan lokacin datace “laaaaa Alhaji yakuri bansan kai
bane, ina yini, Ya Hajiya kunkai asibitin? Wani abu kake bukata nayi?” Duk ta jero mishi
tambayan atare, cikin kwantacciyan murya yace “Hajiya natare da Dr, tagama ganinshi kuma
zan kaita chan Gwarimpa anan zata cigaba da zama gidan kannin Abba na” “okay” Ummi tafadi
but zaka iyajin nuna jin dadin ta a muryanta, ahankali yace “kinada katinki na kasa? National
identity card?” Dasauri tace “eh inada shi” shiru yasakeyi yace “kituramin hoton shi ta whatsapp
sannan ki shirya kayanki gobe zan maidaki kauyenku Adamawa ko?” Maganan yazomata
abazata dasauri tace “eh” saikuma chan asanyaye tace “wani laifi nayi”? Ahankali yace “kin
manta alkawarin dana miki zan kaiki kiga Gwaggon ki shine zan cika” murmushi tayi taushi tace
“Allah yasaka maka da alkhairi” murmusawa yayi shima yace “kinga kayanki cikin kayan danasa
gateman yakawo miki?” Dasauri tace “naga slippers dina na dauka, naga wasu kaya duk
sainakai store na ijiye” cikeda so yace “nakine akwai wani black abaya mai stones ahannunshi
shinakeso kisaka gobe kinji” gyadamai kai tayi kaman yana gabanta tace “to nagode Alhaji”
shiru yayi bai sake cewa komiba tagaji da shirun tace “hello” kaman daga sama yace “zaki
aureni Ummi?.

Matan Abuja!
Matan Abuja!!
Matan Abuja!!!
Haaaaa, HADIZA has been making countless reference daku, the women of Abuja come close
are you all the way Hadiza ke suffanta ku? Ance idan miya yayi yaji??? Ai dole yaji ne zai saka
miyan yaji ko??
So kunada dogon explanation you guys need to come clean


But then again all I see in Hadiza is so much soyayya for her man but this stupid mentality nata

is leading her astray, why must you be the one to call shots agidan mijinki? To shi mijin is there
for what? Name ko fame????

Hello Ladies both married and unmarried are you learning one or two lessons from this novel
nawa???



But again kuma let’s not be sentimental, mu kalli Hadiza da kyau, all she ever wanted is power
which is normal akwai dominating mata dama, itama tanason kawayenta susan tana juya mijinta
but maganan yayanta is valid sabida kunje Italy saikice saikin maida mijinki Italian???
Share your 2cents ladies and gentlemen ❤️
See you asabar
MATAN?? Ko MAZAN??



✍M SHAKUR


EPISODE 7️⃣
THIS PAGE IS FOR YOU ZEE, MY NUMBER 1 MOTIVATOR, I LOVE YOU❤️❤️
Saukan tambayanshi Ummi taji kaman daga sama saikuma takai hannunta ta taba kirjinta daya
buga, to kodai sabida yanda taketa tunaninshi tun jiya yasa taji kaman yace mata zata aureshi?
Ta tambayi kanta, me Alhaji zaiyi da itama in banda shirmen tunainta hakan yasa tace “na’am
banji abinda kace ba Alhaji?” Ijiyan zuciya Nura ya sauke wlh yadade baiji murya mai dadi
kaman na yarinyar nan ba komi nata sanyaya mai zuciya yake, the feelings he’s developing for
her is growing a fastest rate, cikin taushashiyar murya dake kashewa mace zuciya yace “ina
sonki da aure Ummi zaki aure ni?” Yanda gaban Ummi ke bugawa saida tacire wayan dasauri
daga kunninta takifa shi kan cinyanta tadaura duka hannayen ta biyu kan wayan ta runtse
idanunta tana breathing so fast this is unbelievable, yasan tana sonshi ne? Yasan tana
tunaninshi ne? Ta tambayi kanta takai almost minti daya sannan tamaida wayan kunneta daidai
Nura nacewa bakice komiba, itama wlh bala’in nauyi da kunya takeji tace ta yarda haba saikace
jira take, kaman yana magana da little Amal yace “Ummimy” yanda yakira sunanta har cikin jinin
jikinta taji itama anarke tace “Na’am” cikeda so da bege Nura yace “ataimaka abawa Alhaji
amsa eh Hajiya Ummi na” rufe fuskanta tayi dasauri akuma kunyace, murmushi yadan subuce
daga bakinta da yaji karan kadan hakan yasa yayi murmushi yace “Ina jinki” Abala’in kunyace
tarufe fuskanta da hannu daya tarike waya da dayan hannun akunnenta tace “idan munje
kauyen mu ka tambayi Gwaggo na” murmushi yamata shi babba ne this amsan kadai ya
wadatar da curiosity dinshi yace “okay yanzu kije kiyi sallama da matan gidan kice mata zakije
kauyenku gobe an kiraki daga gida, kada ki fada mata wani abu bayan haka kinji” gyadamai kai
tayi tace “toh” dan ijiyan zuciya yasauke kaman kada yayi sallama da ita yace “tom saina dawo”
akunyace still tace “mezan dafa maka”? Cikin kashe murya yace “nabarwa Hajiya Ummi zabi”

dasauri ta cire wayan daga kunnenta takashe sai murmushi take, amsanshi melt zuciyanta, wai
itadai Alhaji keso ya aura ikon Allah, takai awa daya awajen zancen zuci take ita kadai sannan
ta tashi tawuce sama sallama da knocking tayi gaban dakin Hadiza akace shigo bude kofa tayi
ta shiga Hadiza na kwance kan gado da babban IPad dinta na apple tana kallon cctv footage na
shagonta yanda yau takasa zuwa shagon dan batada karfin zuwa dukawa Ummi tayi tace
“sannu da hutawa Anty” kallo daya Hadiza tamata tadauke kai tace “lafiya?” Kan Ummi na kasa
tace “Anty tafiya takamani kauyen mu gobe!” Dasauri Hadiza ta yunkuro ta kalleta hakan yasa
Ummi tace “Gwaggo na batada lpy tace tanason ta gani maza maza” wani kalan harara Hadiza
tamata tama kasa magana to idan ta tafi yaya zatayi da yaran nan gashi kafin su sami wata yar
aiki dazasu saba da ita sai an wahala, cikeda asalin rashin son ta tafi tace “inhar kinsa kafa
kinbar gidan nan da sunan tafiya to kisani na sallameki daga aikin nan kinajina”? Gyadamata
kai Ummi tayi ahankali tace “toh” tsaki Hadiza taja danta dauka she will start begging her tace
tafasa tafiyar, rai abace tace “sabida dan rashin lafiya ne yanzu harsai anwani kiraki kinbar aikin
ki dake ciyar dasu kinje kauye? yanzu ma tukunna kwana nawa zakiyi idan kinje? Kan Ummi na
kasa tace “sati daya ko biyu hala” Hadiza jitayi ranta yabaci datana da wani power da wlh saita
hana tafiyan nan cus yaranta zasu shiga wani hali yazatayi dasu yanzu? Ga agency nan kokai
requesting yan aiki unless akwai akasa shine zaka samu fast Inba hakaba sai an kawo, tsakin
takaici takaraja tace “tashi kifita ki tabbatar dai goben kin shirya yaran nan sun tafi school kafin
kibar gidan nan dan da sassafe zanje aiki yanda yau banje ba din nan” “to zanyi Anty, nagode”
Ummi tafadi tana mikewa tafice daga dakin tawuce kasa yan karikechan ta tashiga hadawa
bayan tagama taje tayi girki, yaran suka dawo ta shirya su bayan sunci abinci takaisu islamiyya
dake nan cikin estate nasu itama takasa gayamusu zatai tafiya dan tasan kuka zasuyi sosai
amman wlh zatayi kewansu sosai.


Wuraren 10 yashigo gidan zama yayi a dinning yaci abinci bura busko Ummi tamai da wani
miyan veggies mai dadi abincin dayaci saida yabashi tsoro tass yagama yakalli dakinta yayi
murmushi yawuce sama ga mamakinshi Hadiza yagani a falon sama kwance kan dogon kujera
daga ita sai wani dan black short mai kaman pant yanada lace abakin wandon very sexy, tasaka
half vest milk na silk material mai kyau shima, dan juyowa tayi suka hada ido itada Nuran
sannan ta maida kanta kan throw pillow ta kwanta tana kallon tv, ita kanta bama tasan maisa
tayi gayun nan tazo nan ta kwanta ba, deep down so kawai take ya kulata, dakin Aman Nura
yashiga yadubashi yamai addu’a yafito ko kallon inda take baiyiba yashiga dakin Amal yamata
addu’a yafito ta gefen ido Hadiza keta binshi da kallon ganin su Hajiya basu dawo tareda shi ba
to ya komar dasu Kano ne? Ko yamaka musu hotel ne?.
Dakinshi yashiga bayi yafada direct yayi wanka fitowa yayi daure da towel a waist ga
mamakinshi Hadiza yagani kan gadonshi ta kwanta tana kallonshi exactly irin kallon shima
yamata yadauke kai yawuce gaban madubi ya shafa mai ya feffesa lafiyayyun turarenshi yaje
gaban wardrobe yaciro pajamas nashi yakoma bayi yasaka yafito, ganin ya dumfaro gadon
yasa Hadiza tasoma jin dadi aranta agaban gadon ya tsaya yasake kallonta ido cikin ido itama
kallonshi take right in the eye amman bazata iya bude baki ta gaidashi kota cemai sannu ba
taga shigowanshi gida tun dazu, dauke idanunshi yayi daga kanta, filon dake gefenta yasa
hannu yadauka yayi wajen kofa yabude yafita yawuce dakin Aman kan gadon Aman yahau

yana kashe wuta ya kwanta abinshi yana sauke ijiyan zuciya.

Bugo kofan Hadiza tayi tashigo ta kunna wuta dakin yayi haske takalli Nura tace “kanka akeji
daman sabida Mama tamin fada ne nazo turakan ka amman jibi yanda ka wulakanta ni, ka
shanyani agado kataho dakin danka zaka kwana anjima kahau cewa ban maka komi na aure,
oya kajika gabanka aruwa kasha mana kasan ai ka iya biyo sahu idan jarabanka yataso maka
ka lallabani nabaka, ina jiran ranan zakasha mamaki na nima wlh” tajuya fuuu tafice daga dakin
ta bugomusu kofa saida Aman ya firgita cikin bacci dasauri yarike Aman yana patting head
nashi, chan bayan yakoma bacci yatashi yakashe wuta yadawo ya kwanta yayi bacci abinshi.
**


Washegari normal aikinta Ummi tayi Hadiza tasauko tai breakfast around 8 tawuce tafita abinta
ko biyar bata bawa Ummi ba dan ba son tafiyan takeba, saukowa Nura yayi yana sanye da
wata farar shadda yayi kyau bana wasa ba har gaban dakin Ummi yaje yayi knocking bude kofa
tayi chak numfashin shi ya tsaya ganin Ummi tana sanye da sabon black dogon rigan daya
saya mata, ta tsife kanta jiya da daddare ta wanke da sabulun wankanta abinta ta taje tayi
Parking batada cikan gashi at all dan kanta ma small head gareta amman wani kalan coily
blonde-black hair gareta dan gashinta ba baki sidik bane irin jajajan nan ne orange orange baki
baki, fari fari irin gashin agwai haka gashinta yake ta yana gyale akai daya dan ja baya tasa
kwalli a idanunta, rigan yamata chass ajiki ganinshi dan tun jiya sai yanzu suka hadu yasa ta
juya dasauri zata koma cikin daki karaf yakamo hannunta dasauri tajuyo suka hada ido ta
zubamai fararen idanunta dasuka sha kwalli ta diga kwalli in between giranta guda biyu tayi
wani kalan unexplainable kyau, ahankali yasaki hannunta dayaji yamai taushin gaske kaman
yarike hannun Amal sai kawai yajuya dasauri yayi dinning dan rabon dayaji wani abu yatadamai
da sha’awa harya manta, ganin Ummi da dan kama hannunta dayayi just awaken libido nashi
zama yayi a dinning yayi crossing leg da sauri batare daya juyoba yace “kin gama hada komi
ina gama breakfast zamu wuce” daga chan ta dakinta tace “eh nagama” itama komawa daki tayi
dasauri yanda taji hannun Alhaji cikin nata sai taji tana fitar da numfashi kashi kashi.

Tass yayi lafiyayyan breakfast sannan yazo wajen kofan yace “kawo kayanki mutafi” bude kofa
tayi rike da ghanamasgo dinta akunyace kallon Ghanamasgon yayi sai kawai yajuya yace “ina
zuwa” sama yakoma yadauko babban suitcase nashi yakawo har gaban dakinta ya duka
yabude ya karbi Ghanamasgon baiji kunya ko kyama ba da kanshi yabude yashiga jera mata
komi a suitcase din, yarinyar nada tsafta dudda kayanta sun mutu but komi awanke alinke ga
dan black leather dayakai hannunshi zai taba dasauri Ummi ta duka tarigashi dauka hakan yasa
ya kalleta sai kawai yayi murmushi dan yasan menene turawa tayi akasan akwatin nan da nan
yagama hadawa suka kulle yaja akwatin waje Ummi na biye dashi har mota gaba yau yabude
mata yana kallonta shiga tayi ahankali ta zauna yakallulle yadawo gaba shima yatada mota har
Gwarimpa bakaramin addu’a Hajiya tamusu ba sannan Meena da Baffan shi da ita suka tafi
airport ga mamamkin Ummi abokanshi tagani a airport already suna jiransu da Musa da
engineer sunci manyan kaya sai kallo Ummi suke munafukai saijin dadi suke, jirgi suke shiga
kalan tsoron da Ummi taji a ko tadauka mutuwa zatayi haka sukakai Yola motoci taga suna

jiransu guda daya daya security personnel sauran nasu nan aka dauki hanyar kauyensu though
sun tsaya a hanya anyi sayyaya na ban mamaki kayan abinci shopping da sauransu.
Tunda Ummi taga sun dauki hanyar kauyensu gabanta ke faduwa hannunta suka fara rawa
komi nadawo mata sabi fill
Hannunta Meena tarike tace “ga dukanmu, ga mopol yan sandan chan babu abinda wani katon
dan daban kauye ya isa yamiki” tafiyan awa daya da rabi yakaisu kauyensu, kauye ne da
yamayi developing ga government work akwai government school, burtsatsai, primary health
care da sauransu sai kallon ko’ina take komi ya chanza ta dade rabonta da garin har gidansu
wanda yake babban gida ginin kasa irin na da din nan.
Wata tsohuwa sosai haka na zaune a tsakar gida tana mulmula hura taji ihuuu hayaniya a waje
tace “Allah yasa ba shaidanin yaron nan ne yazo dawani bala’in ba yau” da gudu wata yarinyar
mai kama da Ummi yar karama da bazata wuce 13yrs ba tashigo tana hakki. “Gwaggo
Gwaggooo Ummi, Umm…..” kafi takarasa magana Ummi tashigo gidan tareda Meena, mikewa
tsaye Gwaggo tayi saikuma tasa zani ta murje idanunta tasake kallon Ummi data tsaya tana
kallon Gwaggo, Gwaggo tace “Kodai mutuwa ce tazomini yasa nike ganin kaman Ummi achan
tsaye dawata balarabiya” dawani kalan gudu Ummi tazo tafada jikin Gwaggo sai kuka ga
kanwar Ummi ta biyun itama tashigo sai kawai dukansu sukahau kuka dagota Gwaggo tayi tace
“Ummi kene binni ya karba haka kin ganki kuwa ya akayi kikazo? Banace kada kizo ba duk sati
sai Mudi yazo gid…..” fuska Ummi ta share tace “Gwaggo akwai baki maza awaje dauko
tabarma Aisha ki shimfida wajenki zukazo” dasauri Gwaggo tace “bakin yan uwan baturiya nan
ne, yaki yarinya gaki fara kaman madara” murmushi Meeena tayi tazo ta gaida Gwaggo,
Gwaggo ta aika Aisha ashigo dasu nan da nan aka shigo dasu wai bakin Gwaggo yaki rufuwa
taga manyan dattijawa ansha shadda fura tashiga hada musu kowanne a kwarya mai kyau su
Aisha harda Ummi dama Meena natayasu har Baffa saida yasha huran sun dade basu sami
aslin ingantaccen fura irin wannan ba sukai salla.
Daukan nasu huran sukayi su Ummi duk suka tafi daki saida aka gama Baffa ya gabatar da
zancen daya kawosu wai Gwaggo kasa boye farin cikinta tayi nan ta sanar dasu komi game da
Ummi da aurenta ada tace zancen aurenta kuma maigari ne mai bada yaran aure Dan haka
atafi wajenshi nan akanshigo da komi aka shiga mota aka tafi wajen mai gari shima yayi naaam
babu wani wahala Dan Auren bazawara ba wahala and tanada right Ummi tafito da mijinta
yanzu tunda nabiyu ne kuma itane takawoshi har kauyensubnan da nan su Musa suka ijiyema
abokinsu sadaki dubu dari uku aka daura aure tsakanin Nura da Zainabu Ummi akan sadaki
300k mutane dayawa sun shaida aka kawo su goro cingam menene menene aka rarraba wai
Nura sai murmushi yake he just can’t believe it duk suna wajen Aisha tazo da gudu tace
“Gwaggo ga Mudi chan yazo amman yan sandan nan sunmai duka” tashi Nura yayi da
sauransu Maugari yace “dan Allah kukai yaron nan gidan yaro ya addabi mutanen Hm kauyen
nan” komawa sukayi akai arresting Mudi nan fa Gwaggo tayi throwing small party itadai Ummi
taja makale adaki taki fitowa Meena ko tafito sai video take yanda matan kauye ke rawa Musa
yakawo bakinshi saitin kunnen Nura yace “kai mutumina bura’uban chan haka kauye keda tsala
tsalan mata bazanyi wuff dawata ba kuwa anan kai jibidai kirjin wanchan dake rawa” tureshi
Nura yayi yace “dan iska” dariya Musa yayi yana kallon yammatan, Musa yataba engineer yace
“kaga yara amman Allah yamusu kindirmo a kirji” Nura yayi kaman baijishi ba aranshi yace “na
Matata Ummi tamafi kowa nan kindirmo” yadan lashe lips yana kallon agogo, Aisha ne tazo tace

“Gwaggo tace kazo” binta yayi zuwa falon Gwaggo tana zaune

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login