Showing 18001 words to 21000 words out of 131659 words

Chapter 7 - Mazan Ko Matan Complete Hausa by M Shakur.pdf

M Shakur   

13 Nov 2025

366

kuma ba yaro ba sannan sunga yanda Hadizan keyi itama
borkonon kanta ce yasa sukai Na’am dudda haka saida suka amshi 20k a hannunshi kafin su
tafi, suna tafiya ya tsaya ya jingina da mota yadan sauke ijiyan zuciya baiso ya yanke decision
cikin fushi yakai 5min awajen sannan yakoma ciki afalo yaga Hadiza jikin window tana ganinshi
ta taho tana ihu tana tafi tace “u bribe them and send them away sabida kar ayi arresting sister
ka da Maman ka ko? To rest assure wlh wlh I will so deal with them, wlh saisun barmin gida,
babu wani mahaluki dazai shigo gidana and snatched my peace of mind for me to menene
amfanin karatun danayi? Ina zaman zamana wata Maman miji ta dawo gidana da zama is that
even fair? Ba manyan asibitoci ne a Kano? Why here why Abuja? Let’s be fair fa Nuri, lokacin
da Maman ka ke gidan mijinta mother inlaw dinta tazo ta tare mata agida? Then why me? Kuma
ace ban isa nayi complain ba? Still sun shigo ur sister nada taurin zuciyan ta daken ni? Ni
Hadiza? Wlh u have to choose one koka tattarasu kaje ka nema musu hotel ko ka maidasu
kano, this house belongs to me and you Nuri aure yabani gidan nan, dan haka wlh sai sunbar

gidan nan” girgiza mata kai Nura yayi, cikin kakkausan murya yace “wlh saidai ke kibar gidan
nan not my mom! ki tattara kayanki kibar gidan nan don’t sleep in my house Hadiza, Na Sake Ki
SAKI DAYA!”.



The foundation of Marriage is built on trust, respect, biyayya and love which I think Hadiza broke
all awajen Nura, now do you all support sakin daya mata? Or do you think he should’ve done
something entirely different???

Now the major abu da matan aure fears dayasa basason yan uwan miji suzo is because Men
always tends to take side din yan uwansu and neglect side na matan su tambaya na anan shine
Nura shima yadauki side din yan uwanshi kenan?? Or kuna tunanin he should’ve done
better???

As a woman can you stand kiga an zagi mahaifiyarki data haifeki? Do you support action din
Meena or not? Dan two things are involve Hadiza matan yayan tane sannan Hadiza ta girmeta
far far and surprisingly Nura bai cema kanwarshi Meena anything ba….hmmmm share your two
cents on this
Now overall tambayata is kuna tunanin basics na mata akan basason yan uwan miji suzo
gidansu uhmmm to some extend sunada gaskiya dan maza always takes side na family su
gaskiya ne???
How should a family Man dazai sami kanshi a tsakiyan conflict tsakanin relatives nashi da
matanshi address the matter??

See y’all Saturday






MATAN?? Ko MAZAN??


✍M SHAKUR


BONUS
EPISODE 6
Dum dum dum!! Hadiza taji kalman sakin ya daki zuciyanta kaman saukan aradu cus ko

amafarki, like ko amafarki dai wannan bata taba tunanin Nura zai taba bude baki yace yasake ta
ba, duk yanda takeson tai kokarin controlling yanda hannunta ke rawa kasawa tayi wani kalan
reflex rawa hannayenta suka fara tama kasa magana sai idanunta data kwalaloo kaman zasu
fadi akasa tana kallon Nura daya hade rai kaman wanda baitaba murmushi ba aduniya ya nuna
mata kofa yace “get out of my house, out!” Yadaka mata tsawan da saida ta firgita, ganin taki
motsi yasa yayi inda take azuciye yasa hannunshi yakama hannunta datake rike da key
motanta yawani jata dan ranshi yabaci ainun ta daukoma Mamanshi da kanwarshi Police haba
nooo enough! Dasauri Hadiza tashiga cewa. “Nuri, Nuri, Nuri” bude kofa yayi yafito da ita har
zuwa wajen motan ta yace “get out of my house” dasauri tace “Nuri ni zaka cewa kasaka are u
for real? Wait mafarki nake? Nine zaka saka because of your family now can u see why I was
against zuwan family miji cause all they bring into your home is chaos? Nuri ni Hadiza zaka
saka? Ni zaka kora from my home”? Wani kallo yamata yace “you are dumb, foolish and you
are crazy Hadiza, bakin halinki yasa I don’t have any feelings left for you azuciyana, duk matan
da have no regard towards my mother can never have space in my life or home dan haka get
out, go and do your feminism awani waje not inda uwata take” yana maganan yawuce ciki ya
maida kofa yarufe da key yabarshi ta yanda she can’t come in, Hadiza was completely in a state
of shock ita Nuri zai saka, ita Hadiza, wajen kofan tayi tadaga hannu zata buga saikuma tace ai
sai su Meena su mata dariya damai gadi, tama zubar da ajinta kenan rokonshi zatayi yabude
mata kofa kome? Yasaketa tayi tafiyanta mana, deep down zuciyanta cike yake fal da damuwa
sai tambayan kanta take ita Nuri yasaka just now? Ita Hadizan nan saki fa? Saki dai datakeji
anama wasu matan itama yau anmata so yanzu she’s a divorcee? Ta tambayi kanta saikuma ta
juya tashiga motanta tazauna takai awa daya ahaka dataga dai da gaskene yasaketa ta tada
mota ta tafi yanzu inama zataje ta tambayi kanta taje gidan kawarta ne? Ina zata? Parking tayi
cikin premises na shagonta tai dialing number yayanta ringing daya ta daga kafin Anty Jamila
tai magana Hadiza tace “Anty kinga yasakeni ko”? Shiru Anty Jamila tayi irin shirun son gane
abinda tayi, saikuma tace “ai yamiki kyau gashinan jikinki yayi sanyi hankalinki yafara dawowa”
cikeda karfin hali da tsiwa tace “jikin wa yayi sanyi? Da ace namai laifi ne sai jikina yayi sanyi?
Ni Nuri zai saka sabida yan uwanshi wlh zai gane he’s mistaken idan yana tunanin yasakeni
kuma na sakun mai wlh karya yake yacimini mutunci haka yakoreni wl…..” takasa karasa
maganan sabida kukan daya taso mata tai shiru Anty Jamila tace “kinason mijinki Hadiza, kina
mutuwan son mijinki amman bakin hali da al’adan yahudu da nasara yasa kin zama shaidaniya,
shine your eye and accept keda shi are not one amman kin dage ke da shi are one kin dage, kin
dage kaman bakar mayya accept cewa ba komi ne arayuwan nan must always go your way ba,
idan haukan dakikeyi ko feminism din dakikeyi na solving matsala go and solve this one mana
da feminism din look at abinda shegen feminism din yasa kika girba saki and this is just the
beginning saikin rasa mijinki sannan zaki gane kene da kanki kika saka kanki a wahala, yanzu
bama wannan ba Meya hadaku”?

Dudda akule take ahaka tabawa Anty Jamila labarin komi salati Anty Jamila tayi tace “wlh da
niyyata muna gama maganan nan nakira Nura nabashi hakuri amman wlh, wlh bazan kiraba
saidai Mama takirashi, Hadiza uwarsa kika zaga? Wai aljanu gareki ne koko kin fara having
mental disorder ne? Konine bazan tsaya wata tazagi Mama agabana ba sai inda karfina yakare,
Meena tamin daidai ke baki girmama nagaba dake ba tayaya nakasa dake zasu girmama ki?

Kadan kika gani Allah yab…….” Ihu Hadiza tayi tace “ni dama nasan u will never support me
what’s wrong with abinda nakeyi? I am just going with the trend? A home belong to the woman
so she should be the one to call the shot, Anty Jamila fisabilillahi da aurena agidana amman
bazan fadi ajiba banda say, haka akeyi eh? Nasa yar aiki tamin girki yahanata, yasa yan
uwanshi suzo bazai tambayi permission dina ba ita Hajiyan haka aka mata eh? Ta kawai shigo
gidana tahanani sakat ana cewa batada lafiya kinga abincin danaga tana zakalkala aciki ne
tana zuba surutu? Tanaji aka sakeni aka korani bata fito tasa baki ba that’s shows plan work ne,
All I ever yearn for and I ever do was to be incharge of my home, kome zai faru inhar it has to
do with gidana nizan fadi ayi ba Nura ba, duk fadan dazanyi dashi akan abinne, idan zaimin
haka nima zanmai komi yanada abokai yasan haka akeyi a Abuja har kunya nake kar kawayena
suzo suga abinda ke faruwa agidana su bahaka sukeyi agidan su ba” dan ijiyan zuciya Anty
Jamila tayi tace “Hadiza baka forcing control da ownership, Nura zai iya bari kina calling shots
agidanshi idan yaso amman means dakike bi is not right, tell me one thing dakike yima mijinki
tell me?” Cikeda bakin takaici kaman ta make Anty Nafisa ganin taki fahimtan ta tace “Anty
Nafisa pls pls understand nan ba kano bane this is FCT for crying out load, city of wealth, a
Abuja u don’t have to do anything for mijinki as a wife, a woman is a queen dayakamata tanada
ma’aikata which I have, su yakamata suyi komi, in this aspect banyi any laifi ba nagaya miki I’m
just going with the trend zamanin damuke kenan, I don’t have to cook, sweep, take care of the
kids or anything akwai masuyin aikin abiyasu duk wata Anty Nafisa nan ba kano bane kigane
there’s nothing extraordinary anan abinda ke faruwa kenan wlh” hmmm! Anty Nafisa tasauke
ijiyan zuciya dan lamarin Hadiza mai girma ne tace “Hadiza kinyi nisa are you saying yanzu
kuka koma Italy al’adan Italians zaki dauka kicema mijinki dan Nigeria dole sai yayi? When will u
understand mijinki bazamfare ne girman kano, Sana’a ce takawoshi Abuja, Nura is educated
but rayuwan bokon nan da wayewa tamasu kudi dakikeso shi baya gabanshi, ace yana aurenki
bazaki bashi ruwa dakanki yasha ba menenen ma amfanin ki? Wai kuma ahaka bakimai komi
kuma kinaso shi yamiki komi, kome kikace yace Naam ko tunda gaki mamallakiyan Nura sannu
Hadiza mai fadi aji, yanzu kina ina?” “Shago na” cikeda isgilanci Anty Jamila tace “maisa bakije
gidan kawayen naki ba to”? Ahankali tace “ai abin kunya ne suji abinda yasameni, that means I
don’t even have any power or influence agidana inhar mijina zai koreni daga gidana sabida yan
uwanshi wlh wlh abin nan yamini ciwo Anty Jamila, you have no idea yanda matan Abuja are
powerful agidan su amman ni Nura bazai bari nai enjoying that luxury ba, kuma wlh wlh wlh zai
sani” anatse Anty Jamila tace “Hadiza keba yarinya bace you’re 32, ke kinsan abinda kike bai
dace ba, uwarmiji uwarkice, ita tahaifo abinda kikeso and nurture him, groom him into the man
he’s today, miji ba abin wasa bane dazaki dinga experiment naki akanshi, this is just 1saki Nura
yabaki, idan ba u wanna loose him for ever ba ki gyara, all it takes is apology, kije kibama
mahaifiyar shi hakuri kibashi hakuri ki gyara the way kike abubuwa agidan ki before it will be too
late for u kina jina? Idan zaki dawo kano ne kidawo, zandai gayama Mama nasan zata kirashi
amman ni Allah yasan bazan iya kiranshi ba take care Allah kuma ya ganar dake kafin lokaci
yakure miki”.
Katse wayan tayi tadade zaune amota saida aka tafi magrib sannan tafito ta tafi sama tabude
shagon tashiga tamaida tarufe tawuce sama office nata ta shiga kwanciya tayi kan dogon
kujeranta tayi shiru tanada kudin kama hotel ta kwana abinta amman takasa, takasa zuwa
wajen kawayenta kada amata dariya tagama cika baki, da kyar ta lallaba taje tai salla wasa

wasa har 12 nadare takasa bacci sai juye juye take yanzu shikenan Nura yasaketa ya koreta
daga gidanta shikenan bata da gata? Itane yau da kwana a shago? Hakanan kawai saitaji tana
kewan yaranta koba komi kobadan suzo wajenta ba amman muryansu da hayaniyansu datakeji
da Ummi is something sai kawai taji tayi kewansu sosai din nan, lema lema dataji akan fuskanta
yasa takai hannunta dasauri ta taba ashe kuka takeyi dasauri ta tashi zaune tace “no feminist
don’t cry, with or without Nura I can create my world why am I sad? Dan yace yasakeni,
yakoreni daga gidanshi? Why nakejin badadi nakasa bacci 9 nayi bacci jibi lokaci yanzu nakasa
why?, Yanzu Nura harya isa yacusamin bakin ciki? Then menene amfanin the belief I stand for?
The whole feminism an fito dashi ne dan anunama mata they don’t need men or approval na
men to survive on this world, all she need is herself” share fuskanta tayi tass tace “Nura kayi
kadan kasamin kunci” ijiyan zuciya tasauke tafara fadama kanta words of affirmation. “I’m
Hadiza diyar Tijjani, I’m strong, independent and beautiful dudda tsinanniyar yarinyar nan tamin
scars din yakushi yanzu awuyana, I’m smart, unapologetic, resilient and bold, I don’t need a
man ko anybody to be happy, Hadiza is enough for kanta, a man can’t downgrade or belittle
Hadiza, I’m as tall as the mountain ,as hard as rock, as thick as thicker, no one can break
Hadiza saidai ni nai breaking, I’m unbreakable, I’m happy, I’m happy, yesss I am happy!!” Tafadi
ma kanta tana murmushi tana dukan kirjinta saikuma wasu munafukan hawaye suka kara fitowa
daga gefen idanunta tadaura hannunta akan fuskanta tafashe da kuka sosai tace “na shiga uku
why am I sad? Nura ni zaka saka awanan sad mode din? Ni Hadiza zakama saki Nura? Ni
kanwarka zatama duka sannan kayi throwing dina out kahadan da saki jibeni a shago zan
kwana? Ni Nura?? Wlh saina gwada maka kayi da diyar halas wlh kuwa” wani shegen kunci
takeji the state datake ciki ita kanta batasan Nura is this important to her ba sosai take sonshi
but bata saniba, she’s extremely sad takasa bacci, kaman ta hadiye zuciya takeji tamutu.


Wajajen 3:30AM Hajiya ta tashi daga bacci, Meena tagani agefenta dasu Amal duk suna bacci
komi daya faru dazu dawo mata yayi sauka tayi daga gadon da dafa bango tafito dakin Nura
taje sallama tayi ahankali ga mamakinta bude kofan yayi yana sanye da jallabiya hannunshi
rikeda charbi dasauri yariketa yace “Hajiya kin tashi” shigar da ita dakin yayi yamaida kofa
yarufe akan couch na dakin ya zaunar da ita shikuma yazauna agabanta akasa yakama
hannunta yarike ahankali yace “Hajiya kiyakuri sabida ni Hadiza tamiki rashin kunya yau”
girgixamai kai tayi kafin tazare hannunta daga nashi daya rike ta tallabo fuskanshi cikeda
tsantsan soyayya irin na d’a da mahaifi tace “maisa baka taba sanar dani abinda ke faruwa
agidanka ba? Nura yaushe Hadiza takoma haka? Kamata wani abu ne”? Duk yanda yaso ya
daure kasawa yayi ahankali yadaura fuskanshi sanan cinyan Hajiya murya chan kasa yace
“Hajiya nagaji I’m tired, sometimes I feel maisa namayi aure? Da auren nan gwara rashin sa but
then nakalli yarana Aman and Amal sainace Alhamdulillah Allah has already blessed me with
the most beautiful kids aduniyan nan” yayi shiru yace “Hajiya I don’t have peace of mind idan
nabar gidan nan kaman kada nadawo tunanin yarana kesa nadawo, babu one single thing da
Hadiza kemin amatsayinta na matana and bantaba mata wani abuba, Hajiya sometime ina
zama na gayama kaina indai this is wat comes out of auren educated mace to gwara auren
gidahuma jahila dazata maka biyayya and be a wife for you cus Hadiza is a wife for herself not
for me, tanada masters in business Administration tanada business kudin sun shiga hannunta,

yanzu taga am useless koda ace yau zan rabu da ita tanada future she has money, and money
is everything idan kanada kudi baka bukatar komi kuma zata iya kula da kanta, everything data
mini I tolerated it dudda she’s 32 but kallon mahaukacin yarinya nake mata Hajiya she insulted
you today tayi magana dake kaman ita ta haifeki saisa nace tabarmini gida taje na sake ta saki
daya” dasauri Hajiya ta kalleshi dago kanshi yayi idanunshi sunyi jaaa sosai yace “Hajiya kin
sanni sama da kowa kinsan inada hakuri kawaici juriya dakuma yafiya yaune rana na farko
dazan rokeki Al farma kada kice nadawo da ita please I want a break from this auren mu
besides I’ve grown feelings for someone kuma inaso naje garinsu na nemi aurenta” Hajiya na
kallon fuskanshi tace “Ummi?” Dasauri yace “tayaya kika sani Hajiya”? Dan murmushi tayi tace
“sabida nina haifeka” dan shiru yayi chan yace “Hajiya nakamu da son Ummi sosai, tagayamin
ta taba aure tama haihu……” yabama Hajiya labarin yace “Hajiya inason Ummi sabida some
odd dalilai” ahankali yace “Hajiya nakamu da son Ummi sabida duk wani abu da Hadiza kedashi
ita batada shi” yadan sauke ijiyan zuciya yace “inason ta sabida she’s not educated, sabida
batada kudi, sabida she’s not independent, sabida she’s innocent, sabida she’s polite, sabida
she respects me, sabida she pay attention to me, sabida tanason yara na, sabida she feed me,
sabida tana magana dani calmly her voice is so soothing to my heart, I love her sabida she’s
weak, fragile, sabida she’s a soft woman not strong woman, ina sonta sabida matace da idan na
aureta nine zan zama ragamar rayuwanta and she will let me be the husband and above all nayi
istikhara akanta naji azuciyana na natsu da ita, Hajiya inason na aureta amman saikin bani go
ahead” murmushi Hajiya tayi tana kallonshi hannunta takai ta share dan guntun hawayen daya
fito daga gefen idanunshi tace “na amince kaje kauyensu ka nemi aurenta amman da sharadin
kadawo da Hadiza” dasauri yakalli Hajiya, murmushi tamai tace “Nura no marraige is perfect,
kowani aure da crisis din dake ciki har Ummin idan ka aureta you guys will have ur differences
and issues but what makes Marraige works and last is the ability to work on your issues
understand each other better, forgiveness and moving on without holding grudge, kaga all this
fadan yanasa akara fahimtan juna, kuskuren Hadiza shine tunanin datake itada mijinta daidai
kuke wanda bahaka bane u are the leader and she’s your subordinate dole ta bika, but I’m sure
yanzu she learnt her lesson sabida duk ranan da mace zata kwana awani waje ta dalilin saki
ranan bata iya bacci mai kyau ko itace da laifi ko ba itace da laifi ba, saki babban abune, saki is
powerful, duk randa aka yishi alarshin Allah na girgiza, duk randa akai saki shaidan na party’s
jin dadi, duk inda Hadiza take yanzu tana cikin damuwa sosai, kayakuri kadawo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login