Showing 39001 words to 42000 words out of 131659 words

Chapter 14 - Mazan Ko Matan Complete Hausa by M Shakur.pdf

M Shakur   

13 Nov 2025

355


yaron dake neman Auren Auta ko”? Gyadamata kai yayi yace “eh Hajiya amman tana aure
xakibar kano ki dawo gidana da zama bazan barki ki zauna ke kadaiba gaskiya” dasauri Hajiya
tace “kai barni da Abujan nan wlh ba sonta nake ba nafison kano” dasauri yace “Hajiya akwai
flat dinki daban agidana, nan da wata biyu za’a gama komi bazaki zauna ke kadaiba a kano
gaskiya” ahankali tace “to baridai lokacin yayi sai muyi wannan maganan, tashi kaje masallaci
an tada salla leka min Meena da Ummi kagani Allah sa sun tuna sun hada kayan su Amal ba
sun tsaya hira ba” wucewa tayi yafita dakin da Meena take yaje yadaga labule yayi Ummi
kadaice adakin tana shirya kayan su Aman bama tasan da zuwanshi ba sai aikin take harta ga
Amal zaune gefenta hannunta da tuwon madara tanasha dan murmushi yayi akan Ummi
yasoma sanin akwai wacce zata iyaso yaranka tsakani ga Allah koda ba ita ta haifesu ba saidai
basu da yawa a duniya, gyaran murya yayi dasauri Ummi tadago kanta ta kalleshi folding hannu
yayi akirji yace “awanki nawa baki sani a ido ba”? Murmushi tayi kaman mai tunani tace
“uhmmmm awa biyu da minti ashirin da uku da sakan shidda kenan bansa Dadyn Amal a idona
ba” dasauri yace “shine kuma kike murmushi” hadiye murmushin tayi tace “tuba nake nadaina
Yallabai” kwafa yayi yace “kinci sa’a akwai Princess anan” dasauri tajuya taja hancin Amal tace
“ai princess zaki dinga cetona koda yaushe ko?” Amal tace “yesssss Anty Ummi na” dariya tayi
takalleshi tace “kaji ko” hararanta yayi yana murmushi yace “kuyi salla ku shirya nadawo zamu
tafi” gyadamai kai tayi tace “to mijina, adawo lafiya asamu a addu’a fa idan kana cikin jam’in nan
kaji” juyawa yayi yace “naji matata” yayi murmushi yawuce Meena tazo da gudu tace “ke Ummi
haka kuke soyewa keda Yayana, zona koya miki zama da Hadiza……..”


Yana dawowa aka zuba komi a mota harda abincin dare Hajiya tasa Meena tazuba musu a
babban kula dantasan matan gidan bata dafaba kuma bazatazo Ummi tahau aiki da daddaren
nan ba suka musu sallama suka tafi saida ya tsaya yayi salla ma……….

Parking motarshi yayi Ummi taji gabanta yafadi kallon gidan tayi takasa fitowa su Amal dake
tareda ita sukace “Anty Ummi muje gida” daidai lokacin Nura na bude musu baya yakalleta suka
hada ido yace “muje” gyadamai kai ahankali, ganin yanda tayi yasa yamika mata hannunshi
ahankali takama yafito da ita sannan yadauki Amal itakuma takama hannun Aman gateman

namusu sannu da zuwa yana bude boot na mota dan kwaso akwatinan su, bude kofan falon
Nura yayi ahankali da sallama abakinshi Hadiza na zaune kan kujera daga ita sai wani material
data saka na batic mai shegen kyau gown yana walkiya walwal kyau purple hannunta rikeda
wayanta dake kunne tana magana ga MacBook nata kan cinyanta tana aiki tadan saka farin
reading glasses a idanunta kanta da kalaba yan kananu ganin Nura rikeda Amal yasa dasauri
tace “I will call you back Hajar just send the order ta IG ko WhatsApp me” takatse wayan
dasauri tayi tana kallon Nura dashima yake kallonta batare datacemai uppan ba dan fushi take
dashi sosai sabida abinda yamata, shigowa Nura yayi saikuma yajuya yakalli Ummi data tsaya
gaban kofan batare data shigoba Nura yace “shigo” gyadamai kai tayi tashigo ahankali kanta
akasa tana rikeda hannun Aman Hadiza tabita da kallon mamaki irin mugun mamaki daidai nan
Gateman na shigo da akwatinan su yabarsu anan falo yawuce yafita bayan yagaida Hadiza
dako kallonshi batayi ba balle yasaran zata amsa, ahankali Ummi kanta na kasa tace “ina yini
Anty” har lokacin Hadiza kallon Ummi data chanza mata take a ido sosai ganinta tareda mijinta
a ina yaganta? Taya suka hadu? Tayaya suka dawo gidan tare? Yarinyar dake kauye? Yanda
tambayan ke cinta arai yasa batare data amsa gaisuwan ba tace “meya hadaki da mijina
dakuka shigo gidan tare ko ince kuka dawo gidan tare? Kumama bance kada ki kara dawomin
gida ba tunda kin tafi ganin kakarki nariga nakoreki, na sallameki me kike dawo yimini agida
kuma sannan kika shigo tareda mijina”? Sauke Amal Nura yayi yakalli Aman yace “kuje dakinku
asama kujira gani nan zuwa” dasauri Amal tace “Daddy zakazo ka karanta mana stories?”
Gyadamata kai yayi dasauri sukai stairs suka wuce sama without saying a word to Maman su
kaman ma bata falon.

Dudda Nura yaji ciwon ko gaidashi batayi ba balle amsa sallaman dayayi ko cemai sannu da
zuwa batayiba amman saiya daure yakalli Ummi yace “zoki zauna nayi magana daku” Ummi
kanta na kasa ta taho Hadiza jitayi jikinta da kafafunta sun fara rawa hakan yasa tasauke
MacBook nata dake kan cinyanta ganin wani attention da care da Nura kebama Yarinyar nan
wanda bata taba ganin yayiba tsawon kusan a year datake aiki agidansu, shida ko kallo yar aiki
bata isheshi bama, ganin Ummi takasa motsi yasa Nura yazo da kanshi ahankali yakai
hannunshi yakama hannunta dawani kalan sauri Hadiza tamike tsaye tana kallon Nura dataga
yariko hannun Ummi, shigowa da Ummi yayi cikin falon yazaunar da ita kan kujera shikuma
yazauna kan 1 sitter yana facing nasu yakalli Hadiza dake tsaye yace “sit” cikin bugawan kirji
trying to calm herself down but takasa sabida yanda kirjinta ke tafarfasan bala’i ganin yanda
yakamo hannun yar aikinta tace “Nuri just say abinda kakeso kafadi basaina zauna ba cus I
don’t understand sa yar aikin nan zama kan kujera na dakayi kana rike mata hannu, maganan
me zakamin eh”? Sosai Nura ke kallonta ganin rashin mutuncin ta da rashin kunyanta na nan
dudda yadan punishing nata kwanan nan saikuma anatse yace “Hadiza Ummi ba yar aiki bace
yanzu, naje har kauyensu na nemi aurenta an bani, yau kwana goma sha hudu da daura mana
aure! Ummi is my wife!”.

Today da Matan Auren gidan nake when was the last time kika daga waya kika kira Maman
mijinki just to say Hi Mama yakike?? Makesure kin kira yau


Idan kuna gari daya when was the last time taci abincin ki?? Yau weekend yi lafiyayyan girki ki
aikamata

When was the last time kika siya mata gifts? Kikai making nata happy??
Do that yauma�

Ance akwai a thousand ways to zuciyan miji and one of those ways is when you carry his Mom
asaman kanki, lokacin dazaki dinga kula da mahaifiyarshi kaman taki.❤️

Like I said still yau zan fada this book badan fun ko dadi nayi ba nayishi ne for US maybe this
book yarage rate na divorce da ake samu Kwanan nan agidajen aure.
Everything in this book is a lesson not just the kishiya part, zamantakewa, kyautatawa, soyayya,
yara da sauransu duka nakawo.❤️

I have a question for Mamas, duba da maganan na batai failing as a Mom ba cus tana sayama
yaranta heaven on earth and tabasu the best yar aiki dasuke so inaso naji view naku kuna
ganin GIFTS kesa yara su shaku da Mom nasu ko spending quality time dasu??
And is it possible yara su fison wacce ba ita ta haifesu ba kan wacce ta haifesu????
Maisa Aman and Amal prefers Ummi to Maman su?????


WEEKEND PROMO

I have special announcement masu son shiga class na MATAN AURE you can all pay 1k now
kafin Monday yakoma 2k, registration is still ongoing kafin murufe.


Don’t miss MATAN AURE dina class for anything, I will give you all!!
Sirri zan baku da dama
Zan koya muku how to love mijinki in your own way kaman yanda Ummi keyi.
Shagwaba, iya magana
Uwa uba iya kwanciya❤️, yanda ake siyan zuciyan miji, how to steal heart na Inlaws naki and
so much more.�
Idan kina tunanin asiri ko kayan mata ke siyan zuciyan miji come to my group na nuna miki
gaskiya.
HAUSA CLASS NE BA TURENCI BA

REGISTRATION IS 1k NOW

6353995766 M Shakur world Moniepoint
Send ur evidence of payment ta PC zanyi adding naki a group.
click on this link and chat me up directly
wa.me/+2347012181461
MATAN?? Ko MAZAN??


✍M SHAKUR

EPISODE 1️⃣2️⃣
Ga KAYAN MATA PLUG nakawo muku.
Ummu Fua’d tahada wasu lafiyayyan magunguna kaman su
Shu'umar humra
Bita zaizai
Matar so
Alajab
Na tsugono
Al oud special na kaya
Mowar mace dashi zata turara jikinta
Sai till we meet ruwan wankane a toilet dinta
Night queen shi take shafawa da daddare
Makhmaria tana shafawa ajikinta
Sunshine kuma shi take shafawa angon a inner wears tana turare masa inner wears dinsa da
turaren matar so.
Just chat her up koku shiga group dinta

‎Open this link to join my WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/Izv1KgHEcNl5uwqalMM9Oe



Episode 12
Wani irin kallo Hadiza kema Nura kaman wacce hankalinta ya gushe ta tsare bakinshi da yanda
labbunshi ke motsi da kallo kanta yayi wani dummmmmmmmmm, kunnuwanta sunyi wani
shuuuuuuu kaman irin ana hura tsakiyan gwangwani kanta yamata nauyi kaman an daura block
kawai kallon Nura take da bakinshi dake motsi, tanajin wasu maganganun wasuma bataji,
anatse Nura yace “for now anan zamu zauna dukan mu kafin nan da 2month an gama gidana
zamu koma kowaccen ku nada flat dinta, for now ita zata dauki dakina ke kina dakinki ni zai
zamto banda daki, duk wacce yake girkin ta zan kwana adakinta wanda zan raba muku
2-2days, da zan iya daukan dayan dakin dake kusada naki but sabida baki gwara kawai ni
nahakura da rashin dakin ai is just 2month or less ma, kece Babba Hadiza ga Ummi nan
amana, Ummi kece karama ban yarda ki sabama Hadiza ba, kuyi zamanku lafiya nariga nabiya
kudi yau za’a hadoma kowaccen ku akwati, sannan Hadiza ki duba gidan komene babu saiki

sanar dani nakawo kinji” sosai Hadiza kecikin wani kalan state dabazata iya tantance kowani
yanayi take ciki ba hakan yasa takasa magana shock yarufe mata baki, shi Nura har kasan
ranshi yaji dadin shirun datayi dan baiso tai haukan nan agaban Ummi koma menene tamai shi
adaki kokuma kawai dai not in present of Ummi dan baison abinda zaisa Ummi ta rainata, kallon
Ummi yayi yace “tashi kitafi dakinki asama saida safe” gyadamai kai tayi tamike tawuce tana
tafiya ahankali tayi hanyar staircase daidai ta daga kafanta zatahau bene cikin wani irin murya
dashi kanshi Nura baisan Hadiza nada itaba tace “Um……….mmi!” Chak Ummi ta tsaya tareda
juyowa dasauri gabanta nafaduwa, awani kalan zuciye Hadiza ta taho zatai wajen karaf Nura
yarike mata hannu yace “ina zaki” cikin wani buhun uban ihu Hadiza tace “sakeni Nuri kafin na
daukeka da mari, tell yar aikin chan tabarmini gidana right this minutes dan I just want to
assume all abubuwan dakagama fadi yanzun nan wasa kake is a prank Nura, let’s pretend you
are just joking, baka isa kamin kishiya ba Nura, Nuri nace baka isa kamin kishiya ba! Kai baka
isa ka kara aureba Nuri! So tell this village girl to get out of my house right this minute before na
salwantar da rayuwanta! Nuri ka gayama yar aikin chan tabarmini gida” Hadiza tai maganan
tana tura Nura so kawai take ta fizge kanta taje wajen da Ummi ke tsaye gaban bene, “Hadiza!”
Nura yakira Hadiza azafaffe yana rikeda ita ya jijjigata yace “look at me” juyoda kanta tayi from
kallon Ummi datakeyi, kallonshi tayi da jajayen rinannun idanunta tana kallon cikin kololuwan
idanunshi kaman yanda yake kallon nata yace “nakara aure Hadiza! Nayi wani aure Hadiza!
And Ummi na aura! Na aure Ummi! Yes Ummi is my wife! Matata………” “Noooooooo!” Hadiza
tayi wani kalan ihu da saida gidan yadauka tadaura duka hannayenta biyu akan kunnenta
takara kurma ihu dako maigadi zai iyaji tace “nooooooo! Nooooooo! Nuri I said No! Yar aikin
chan can never, ever become your wife!” saukowa su Aman dasukayi ji ihu yasa Nura yajuya
yakalli wajen, wajen Ummi yaran suka tsaya tareda rikemata hannu Aman yace “Anty Ummi
menene”? Nura na kallonsu yace “kaisu sama su kwanta Ummi” gyadamai kai tayi takamasu
sukai sama dagudu Hadiza ta yunkura zatai wajen kaman mahaukaciya tace “karki sake kije
saman gidana, zokibar gidan nan” dasauri Nura yariketa gam yakalli Ummi data dake tsayawa
yace “go” wucewa sukayi yaran duksun tsorata ganin abinda Maman su keyi, Nura saida yaji
karan sun rufe kofa sannan yasaki Hadizan, babu alamun wasa kan fuskanshi yace “Hadiza
nakara aure because of so many reasons which I don’t wanna go into details of that dan kin fini
sani, please ki kama kanki don’t start with this your drama” Nura yamata magana babu alamun
wasa akan fuskanshi, Hadiza na wani kalan kallonshi da idanunta dasukai jazur ganin ya
chanza mata kaman bashiba dan da dane tai abubuwan nan shareta zaiyi bazaimace wani
abuba saikuma tadaga hannunta tanuna kanta muryanta yayi sanyi kaman kankara tace “Nuri
ni? Ni? Wai ni Hadiza kama kishiya Nuri?? Nura!?” Takira sunanshi cikeda mamaki, shiru
tasakeyi tana kallonshi tana kara kara kallonshi, sai kawai takai duka hannayenta ta kama
gaban riganshi kaman akace ta dakeshi zata iyane tace “Nuri ni zaka yaudara haka da yar aiki
na? My slave fa? Wacce kecin kashin gidana dana yarana? Yarinyar dani nakira agency aiki
aka kawomini ita all u ever did was to pay salary nata, Nuri wai am I dreaming did u just say ka
auri Ummi yar aiki na? Nuri wannan wani kalan bakin cin amana? Yar aiki na fa Nuri, Ummi,
Ummi this Ummi dakemini gyaran gida da wanke baya da wanke wanke ita kaje ka auro??
Nooo I don’t believe this it’s a lie, Nuri wai ni Hadiza kama kishiya da yar aikina”? Yana kallonta
yace “let it sink in your brain nakara aure, and yes yar aikin taki Ummi na aura haramun ne?
Ummi is my wife now so cikani” sake chakumeshi HADIZA tayi da kyau zuciyanta na tafarfasa

kaman ta mutu takeji tace “amman Nura kacika annamimin, makirin, munafuki maci amana da
tsoron Allah, Nura wato all this while you’ve been fooling me kana soyayya da yarinyar nan
kazo kasata tacemin zataje kauyensu duba kakarta kuka tafi kaje ka aurota, Nura yau 14days
sau daya nayi magana dakai u don’t return my calls, u don’t reply messeges dina, Nura ni
Hadiza kama kishiya wai Ummi, Ummi dai yar aiki na? Nizaka yaudara kaci amanata Nura, eh”?
Hannunshi yadaura kan nata yacire daga gaban riganshi yace “bandawo gidan nan to fight with
you ba so just respect yourself kidena haukan nan kar co wife naki ta rainaki” kaman ya zubama
Hadiza fetur wucewa tayi stairs tace “durun uwan cowife, ita Ummi hartanada liver aure mini
mijina? Wlh Nura auren nan trust me dream kakeyi baka isa bane kuma kayi kadan kamin
kishiya na rantse mama da Allah sainasa gidan nan ya gagareta zama billahillazi la’ilaha
illahuwa, babu macen data isa ta auri mijin Hadiza kai ko yar boko mata masu usuli da daraja
basu isa su auremini mijina ba balle kuma yar aiki, mijina Ummi ta aura ni? Aiko tanaso ta mutu”
da gudu gudu take hawa stairs daidai takai falon sama Nura daya biyota ya fizgota azuciye tai
ihu tace “saken mini hannu Nuri” kobi takanta Nura baiyiba dakinta yabude ya jefata ciki yashigo
shima tareda maida kofan yana rufewa yana saka key yazaro key ya jefa a aljihu dasauri ta
taho wajen kofan tayi ihu tana dukan kofan da hannu tace “kabude mini kofa nafita I need to
show that girl her proper place which is trash, wlh, wlh I will never share mijina da wata balle
kuma Ummi yar aiki, kabude kofa! Nura open this door ko na fasa kofan nan” “Enough!” Nura
yadaka mata tsawa da saida tadan firgita dan kaman zai daketa, nunata yayi da yatsa yana
kallon kwayar idanun ta da idanunshi da sukai jajir yace “enough of your nonsense Hadiza! The
only reason I even let you back into this house sabida Hajiya ne! Aure is not a do or die matter,
idan kinga bazaki iya cigaba da zama amatsayin matata ba let me know I will let you go, but
wannan haukan naki nagama dauka Hadiza your time is up, koki natsu and live peacefully
under me ko u can leave the Marraige nagaji, nagaji da stupid, wild attitude naki always barking
woo woo kaman karya haba! Don’t you get tired of shouting? Why do you think violence is
always the way out for you? Kina behaving kaman ba mace ba, is something wrong with you
upstairs I can take you to the asylum adubamini ke, nayi aure and so wat?” wani kalan kallo
Hadiza kema Nura tunda ta aureshi yau kusan 10yrs kenan dan bata haihu da wuri ba yaune
rana na farko da Nura yabude baki yamata masifa haka, bawai basa fada bane no sunayi but
masifa ya kwakkwance mata haka yaune rana na farko, sosai take kallonshi Nura jikinta na
bar-bar duk yanda taso ta daure ta cije tahana kanta saita kasa sabida yanda yakirata karya,
harda mahaukaciya ma dan cewa yayi zai kaita asibitin mahaukata aduba ta, yana kuma
threatening nata da rabuwan aure kawai saiga hawaye sharrrr ya sauko daga idanuwanta masu
mugun zafi, muryanta babuma karfi balle kuzari tasake nuna kanta tace “Nuri ni? Ni kake
gayama bakaken maganganu haka? Nuri nika tsana haka? U just called me a dog,
mahaukaciya and so much more, Nuri you hate me sabida kayi aure? You hate the sight of me,
Nura ni zaka cima mutunci ta hanyar auren yar aiki na? Idan ka tsaneni haka kagaji dani zaka
iya cika ragowan saki biyun dasuka rage why marry maid dina? Kasan yanda nakeji azuciyana
Nuri ni, kaci amanata, ka yaudareni, ka munafinceni” wucewa tayi dasauri taje gaban gado
tazauna akasa ta kankame kanta tana shaking kaman ta haukace, saikuma tafara buga kanta
ajikin gado jikinta ko’ina da bakinta na rawa tana maganganu. “yar aikina, yar aiki, Nuri ya auro
mini yar aiki na, Nuri ya tsaneni, ya tsaneni, ya tsani ganina, ya cuceni, ya wulakanta ni, ya
toxarta ni, Nuri zoka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login