Showing 96001 words to 99000 words out of 131659 words

Chapter 33 - Mazan Ko Matan Complete Hausa by M Shakur.pdf

M Shakur   

13 Nov 2025

369

bama Hajiya labarin sama sama,
Hajiya tai shiru kaman wacce ruwa ya cinye tanajin muryanshi dake breaking sosai, ance
tsakanin d’a da uwa sai Allah dudda he’s trying to show her he’s fine but she could feel pain din
danta piercing through every organ na jikinta, she feel yanda voice nashi is so weak, shaking
with lots of sorrow atattare dashi, cikin dauriya da kokarin so tabashi karfi dakuma tsananin so
irin wacce mahaifiya kema danta tace “are you okay yanzu? Kun gama zancen kotun? Hope
babu abinda ya sameka? Did anybody hurt you Nura? Tell me wani abu yasameka kun gama da
kotun, are you fine Son?” Hajiya ya jeromai tambayoyin cikeda damuwa, da tausayi dakuma

matukar son danta, baki Nura yabude zaiyi magana sai yaji abu ya tokaremai wuya, dagewa
yayi cikin karfin hali irin na maza zaiyi magana yakasa sai hawaye sharrrr, duk yanda yaso ya
danne kukan yakasa abinda he can’t remember the last time yayi arayuwanshi sai kawai kukan
yashiga flowing, cikin murya mai bala’in rauni da bata nuna kaman mutum na kuka but at the
same time kuka yake yace “Hajiya I don’t know why all this is happening to me?” Yadanyi shiru
cus muryanshi na rawa kukan dayake yazama so obvious yace “Hajiya Hadiza hurt me deeply,
she crushed my ego today, laifine dan na sota? Hadizan danai soyayya da ita harna aura was a
hardworking obedient wife, muna dawowa Abuja ta chanza, I put up with every attitude nata cus
idan akwai soyayya dole akwai sacrifice da hakuri da juriya, she did so many mistakes ina
yafemata and overlook nama manta something like that ever happened, all because of one slap
Hajiya wanda in all this years da muna tare ban taba mata ba can’t she forgive me, I am human
Hajiya, I get angry too, banfi karfin kofsawaba haka banfi karfin aikata kuskure ba babu abinda
fushi baya sawa, but sabida a single slap ta makani a kotu tabatamin suna batare datayi tunani
how this action will affect me ba, or my children, Hajiya mata yakamata tazama mai rufawa
mijinta asiri, idan yamata kuskure ta rufamai asiri, tanuna min cewa ita ba matan da zata iya
rufamin asiri bane and bata damu da self respect dina ba, I love Hadiza alot, I’ve done all I
could but tunda abin yakai ga haka gwara na hakura da ita for good!” Hajiya jitayi kaman tayi
kuka sabida yanda taji Nura is seriously crying, bazata iya tuna the last time da Nura yayi kuka
ba maybe tun yana primary school, Nura grew up as a strong hardworking man, baida magana,
ita badadan tazo Abujan nan sabida ciwon taba batasan kalan rayuwan dayakeyi da iyalinshi
ba, ko sunzo kano babban salla Hadiza bata zama gidanta gidan su take zuwa to ta ina zata
gane wani kalan rayuwa suke ciki? Nura ba gayamata zaiyiba, banda hakama is not proper tasa
kanta arayuwan gidanshi, datazo Abuja taga zamansu saisa dayazo mata da maganan auren
Ummi bata hanashi ba, saisa take sonshi da Ummi dantaga itane yarinyar dazai iya tankwarawa
dan ayanda taga Hadiza wlh wlh tafi karfin danta, babu yanda zatayi ne dan yana sonta amman
babu mahaifiyar da zataso taga mata na ganama danta azaban da Hadiza kewa danta, tun
ranan farko data shigo Abuja taga kallan zaman dasuke ta dage sosai da yima danta addu’a
kan Allah yakawo mai karshen wahalan nan, idan aurensu akwai alkhairi to Allah ya daidaitasu
idan babu Allah yakawo musu mafita su biyun. Anatse dakuma soft tone ganin danta is weak
tace “Nura bazan maka karyaba auren ku dakai da Hadiza has become toxic, the space will do
the two of good, burina shine Allah ya zaba maka abinda yafi maka alkhairi, Allah ya takaita
muku wahala, ka kawomin yaran nan kano gobe” kaman maraya Nura yace “tohh” Hajiya jitayi
zatamai kuka tadai daure no one can understand the pain of a mother idan taga danta na
wahala, Nura is suffering sosai cus yanason Hadiza, Hadiza kuma ta maida Nuran kaman
abokin fadanta, Nura yabata tausayi sosai daurewa kawai tayi hatası ta fashe da kuka
damuwan takaramai yawa, ahankali tace “kazo kano gobe Ummi na nan wajena” dasauri cikin
muryan da ba karfi har lokacin yace “eh”? Ahankali Hajiya tace “Ummi na gidana bataje
kauyensu ba” lumshe idanu Nura yayi ahankali saikuma yabudesu baice komiba, Hajiya tace
“you will get true this Nura, duk abinda bai ragazaka ba will only make u stronger, rayuwa yagaji
haka, Allah ya kyauta ina kuma yima Hadiza fatan shiriya, Allah ya shiryata, Allah ya ganar da
ita, sai kazo gobe kaji, Allah tamaka albarka Allah ya rage maka zafin dakakeji azuciyanka, May
Allah grant you comfort my Son” ahankali Nura yace “Ameen Hajiya” Ahankali tace “kagama da
kotun gabaki daya yanzu?” Gyadamata kai yayi yace “eh ina tareda Alhaji Musa ne zamu tafi

gida” Ahankali Hajiya tace “to kuje gidan first I will call u later, don’t forget ka kira mahaifin
Hadiza koka turamai sakon message” gyadama Hajiya kai yayi ya katse wayan yashiga aikama
Mahaifin Hadiza message dan baijin zai iyamai magana yanzu ba.

Hajiya jitayi kaman akwai dutse akan zuciyanta duk yanda zatai bayani bazaku fahimta ba Nura
is her only son, shine amatsayin mahaifi ga duka kannenshi mata, shine komi nasu, shine
school nasu, shine kayan dakinsu, shine komi, shine abincinta, maganinta daidai da electric bill
na gidan nan da swan bottle water datake sha da komi ma shine and Hadiza is trying to kill her
son for her, bawai ta tsani Hadiza bane but zuciya batada kashi, datake Abujan nan taga
abinda ke faruwa Hadiza ta siremata tatas daga zuciya babu uwar dazatazo matar dake
wulakanta mata dan datasan zafin haihuwan shi, Hadiza fitinanniyan mata ce ta fitini danta
haba! Aisha takira wacce itace gist partner Hajiya dan banda Nura itace yatta tabiyu kuma
kunsan mata da iya relating to pain din maman su.
Aisha na kiran Hajiya back Hajiya tafashe da kuka tace “Aisha Hadiza zata kashemini yaro
wannan wani kalan abune me d’a yamata? Aisha cikinku babu wacce kema mijinta yanda
Hadiza kema Nura, kunama mazanku girki, kuna girmamasu, why is my son so unlucky da mata
eh? Kashemin yaro takeso tayi? Zata haifamin waninshi ne eh? Yarona sai kuka yake all
because of her, why are so women so heartless? I know babu excuse na marin mace, Nura was
very very wrong daya mari Hadiza, mari ba kyau musulunci yahana amman akwai forgiveness a
aure, tsakanin mata da miji yakamata akwai yafiya, jinkai tausayi wanda duka naga Nura nama
Hadiza, what’s the point na makashi a kotu uban yaran dakika haifa aduniya fa, sabida ya
mareki? Idan ma so take abimata hakkinta for marin daya mata she can call me wlh saina
sabamai, zata iya kiran mahaifinta takai karan Nura akira amai kashedi kada ya kara taba
lafiyanta, kotu all sabida mari is too harsh, so take Nura ya wulakanta aduniya dayau beda
kudin bail da yana gidan yari yanzu haka, ga yarinya mai ladabi da biyayya ya aura amman
hankali shi baya kanta yafison wacce ke bashi kashi wai yaya kan maza yake ne mesa sun
fison abinda ke cutarda su? Hadiza ce kadai mace aduniya akan wani dalili zata dinga
wulakanta min da shirun dataga nayi ta dauka tsoron ta nakeji koko ta dauka bansan darajan
dan cikina bane”? Cikeda lallashi ganin ran Hajiya na tafarfasa Ya Aisha tace “Hajiya please
stop crying is not good for you kada su Meena su jiki suzo suna kuka suna duk hankalinsu
yatashi” cikin kuka Hajiya tace “basanan sun tafi lesson din da Meena keyi da ita da Ummi,
Aisha I don’t care Nura ya haihu da Hadiza sunada yara all I know shine ko yau Allah zai dauki
yara koda Ummi bata karbesu ba ku zaku amshesu bazasu taba wulakanta ba Aman da Amali,
wlh wlh idan yarinyar chan takaini bango karshen auren su kenan koda Nura zai maidata saina
hanashi, if she’s not ready ta zauna da yarona let her go gabaki daya” calming Hajiya down
Aisha tayi sosai, tadinga bata hakuri da kyar tashawo kan Hajiya ta huce tayimata hira har saida
su Meena suka dawo gida sannan tabarta tamata sallama.


Saida sukai magrib suka wuce gida, Nura na sallama su Amal da Aman dake wasa da yaran
Alhaji Musa afalo suka taho da gudu suka rungumeshi suna oyoyo Dady, yaran Musa ma haka
boye duk wata damuwarshi yayi yayi murmsuhi suka daddauki yaran suka shigo gidan cikeda
girmamawa Maman Humaira ta gaida Nura ya amsa Humaira ma ta gaidashi cikeda

girmamawa Nura ya shafa kanta yace “Humaira is now a big girl fa yaushe aka haifi Humaira
nazo na dauketa a baby showel a hospital” akunyace Humaira ta rufe fuskanta duk akai dariya,
abinci Maman Humaira takawo akaci suka fice dan yin isha’i Humaira ta wanke komi da sukai
amfani dashi suna dawowa daga mosque suka tafi gidan yarage daga Nura saisu Aman dake
wasa da toys akan rug, dago kanshi Aman yayi yakalli Babanshi saikuma yabar toys din yahayo
kan kujeran yazauna kusadashi ahankali yace “Daddy are you fine?” Dasauri Nura yakalleshi
saikuma yamai murmushi ganin yanda yaron ke kallonshi yace “yes Dady is fine” dasauri Amal
itama tabar wasan ta hayo kujeran ta zauna kan cinyanshi takai hannunta ta taba fuskanshi
tace “Dady you look very sad today right Ya Aman?” Gyadamata kai Aman yayi yana kallon
Baban nashi shima, murmushi Nura yamusu baice komaiba sai kawai ya kama kansu ya manna
musu peck cikeda so, ahankali Aman yace “Dady where is Mom? Bata dawoba” shiru Nura yayi
yana kallonsu they have the right susan meke faruwa dudda yarane, anatse yana kallonsu duka
biyun dake kallonshi kur kaman tv saikuma yakama hannunsu cikin tsantsan so da kamanta
magana ta yanda yara zasu fahimta yace “Mommy will not be living with us again, Daddy is not
together with Mommy” Sosai yaran ke kallonshi sukai shiruu dukansu biyun suna kallon
fuskanshi chan Aman yace “Momy started doing those bad things again right Dad? Is that why
your eyes are read”? Dasauri Amal abunku da yarinyar takai duka hannayenta kan kumatun
Babanta tajuyo da fuskanshi saitin nata tawani leka idanunshi kaman wacce ke leka rijiya, cikin
muryan yara tace “Mommy hurt my Dad, Aman daddy eyes are red like he criedddddd” taja
cried din tana sakin kuncinshi tai kwaba kwaba da fuska zatai kuka da sauri Nura yace “no
Amali don’t cry ni banyi kuka ba, Dady ai baya kuka, idanuna na ciwo ne saisa sukai ja”
ahankali Aman yakama hannun Babanshi shima kaman zai fashe da kuka yace “Dady I promise
I will never hurt you like Mommy does, and we will never ever yelled at you or scream or be
stubborn ko Amali”? Gyadamai kai Amali tayi ashagawabe tace “I love my Dady very much Ya
Aman I hate seeing my Daddy looking sad” ta rungumeshi, Aman shima ya rungumeshi yace
“Dady you are my superhero and I love you alot Dad, you are the best Dady don’t be angry kaji
Dady, kayakuri, Anty Ummi said Innallaha….” Dasauri Amali ta taso daga jikin Baban tace “ma’a
sabireen” atare suka hada baki sukace “lalle Allah yana tare da mai hakuri, Dady kayakuri kaji”
gyadamusu kai Nura yayi yanaji kaman yayi kuka maganansu ya mugun sosamai zuciya kawai
ya rungume yaranshi kowanne side side gam gam, arayuwanshi yanason yaran nan, su biyun
nan are his soul, yaranshi are just so adorable and sweet kuma suna sonshi sosai, sai yaji
Ummi takara shiga ranshi, akwai some small small abubuwa datake koyama yaran da he so
much appreciates, kaman son junansu tanunama yaran su biyu are one and Aman should
always take care of Amali, wlh dawuya kaga Aman da Amal nafada ko sunyi sharp sharp
zakaga Aman ya rungume Amali ya lallasheta he’s so protective of little sister nashi and is all
thanks to Ummi da yan tatsuniya da labaran datake basu. Banda haka kana ganin kaman
basusan meke faruwa ba they understand everything, saisa ko fada bayaso yanayi da Hadiza
agabansu especially Aman dan yaron is very smart.
Sun dade ahaka saida yaji dukansu sunyi bacci sannan ya daddaukesu yaje ya kwantar da su
adakinsu, wanka yayi anan bayin Aman yafito yaje dakin Ummi yadauko wani jallabiya yasaka
yadawo dakin Aman ya kwanta yayi shiruuu sai chan hawaye ya gangaro daga gefen idanunshi
dasauri yasa hannu ya share tareda fuzar da iska yace “enough!” Tashi yayi yadauki wayanshi
yaciro number Hadiza yayi deleting, yashiga files nashi yashiga deleting komi nata messages,

pics, yashiga whatsapp yayi blocking nata ta ko’ina, ya maida settings na wayanshi ta yanda
unknown number bazai iya kiranshi ba, yanaso from daren yau yarufe babin Hadiza gabaki
daya and just move on with his life, harga Allah he wish her well koba komi itane mahaifiyar
yaranshi he wants her to get everything datakeso in this life to tayi rayuwan datakeso, he wants
her to excel and attain success in business nata, but for him ya yafe Hadiza koda zai mutu he
don’t wanna ever be together da mace kalan Hadiza ma balle Hadiza, he just wanna live his life
yanzu da wacce keda opposite of all abubuwan da Hadiza kedashi.
Washegari as usual da wuri ya tashi yana dawowa tea yashiga kitchen yamusu yayi
microwaving abincin da Maman Humaira ta dafa yayi arranging komi a dinning yaje sama
yatadasu ya musu wanka brush yasa sukai salla yafito yabasu abinci tsaf suka cinye daidai
wata babban mota na zuwa gaban gidan, sama yakai yaran dakinsu yabasu iPad nasu sannan
yafito ya shigo da maza su 7 aka shiga kwashe kayan gidan ana fitar da su, dudda duka kayan
gidan na Nura ne, dasukai aure da kayanta aka kawota gidan su na Kano dazasu dawo Abuja
yasa ta kyautar da komi yamata komi sabo but he wants her to have it dan Allah yasani da
sunanta yasai everything agidan kap, kayan dakin Ummi da gadajen dakin yaran ne kawai ba’a
taba ba but hatta kujerun falon sama tass aka fitarda komi gidan looks empty yar kayan kitchen,
frames menene menene, address na gidan iyayen Hadiza yabasu a kano yariga yabiyasu
kudinsu aka tafi sosai ya tsaya yana kallon gidan da babu komi ciki banda pentin bango, kawai
yawuce sama dakin yaran ya shiga yahada kayansu tsaf a akwatinan su dan idan yabar gidan
nan sabon gidanshi zasu koma next time, shima ya tattara kayanshi awani akwati yasauka kasa
shida mai gadi suka ijiye a boot already yaran sun gama exam badai suyi closing school ba
tukunna amman yakira school nasu yagayamusu tafiya takamashi yadawo yadaukesu suka
sauko yasasu amota ya kulle gidan yashiga mota office yaje yayi some ayyuka da komi
yabarma manager shi aikin sannan by 2:00 suka tafi airport dan 2:45pm jirgin zai daga, yaran
were so happy zasuyi tafiya they’ve missed traveling daganan sukai flying sai kano inda direban
Hajiya ke jiransu already.

Kuna ganin Nura made the right decision na rufe chapter Hadiza gabaki daya in his life??

Koko kuna ganin is not the right decision daya kamata yadauka??

Me aganinku yakamata yayi??

In his statement “I want mace complete opposite na Hadiza” yana nufin wacce is not as
educated as Hadiza, expose as Hadiza dadai sauran su, kuna ganin that’s the best thing for
him??


What are the perks na auren educated independent woman??
And what are the perks na auren uneducated uncivilized lady???

Don’t forget ku shigo class dina na matan Aure with just 2k chat me up today
wa.me/+2347012181461

MATAN?? Ko MAZAN??


✍M SHAKUR


EPISODE 2️⃣9️⃣

https://chat.whatsapp.com/JgukZW7wzUHL8lbg9IraqN

INDAI KAYAN SAWAN YARANE TO GA KANKAT NAKAWO MUKU❤️
Do you want your kids to look like those yan gayu kids you admire on instagram? Definitely yes,
Eshamin kiddies got you covered. mun shiga mun fita mun tattaro the best for your kids, with
chikini money zamu fito muku da yaran ku tass. We make beautiful dresses (rtw and bespoke)
headbands and turbans. When it comes to kids fashion you know I no get no 2
You can also check us on IG
https://instagram.com/eshamin_kiddies?igshid=OGQ5ZDc2ODk2ZA==


29
Mota suka shiga instead instead sutafi gidan Hajiya direct super market yasa driver yafara
kaishi, tsaraba ya kwasa dayawa yakai wajen kayan zaki tsayawa yayi yana kallon roban
mentos cingum Ummi ne tafado ranshi sanin tanaci, ahankali yasa hannunshi yadauki roba
daya yasa a cart su Aman ma suka kwashi abubuwan dasukeso dukansu yaran were so happy
sukaje suka biya direba ya deba yasa a boot suka wuce gidan Hajiya.

Yaran sunsan gidan Hajiya sosai ko sunzo salla anan suke zama sai idan Mommy su tazo takan
dauke su suje gidan su adawo dasu wajen Hajiya da yamma.
Suna shiga gidan Hajiya da gudu suka sauko daga mota sukai ciki, matan dake taya Hajiya
aikatu na kayan abinci sai sannu da zuwa sukema Nura dayayi kyau gaidasu yayi cikeda
girmamawa ya ciro ragowan cash na aljihunshi yamikama babban ciki su raba sai godiya suke
yawuce ciki daidai bakin kofa yaga Hajiya tabude mai hannu rungumeta yayi warmly yace
“Hajiyaaaaa” “barka da zuwa Nura, sannu sannu, maraba lale” sakinshi tayi sabida Aman da
Amali dasukace “Grandma where’s Aunt”? Gwaggo na murmushi tace “sunje school amman
sun kusan dawowa” shiga falon sukayi Nura yasami waje ya zauna yana kallon yanda Aman da
Amal ke guje guje suna fadawa kan lumtsa lumtsan kujerun Hajiya falon a gyare sai kamshin
turaren wuta yake, sosai Hajiya ke kallonshi yadan rame yafada, yama danyi duhu kadan,
kusadashi ta zauna tareda shafa kanshi cikeda so tace “ya kake”? Murmushi yamata yace “I’m
fine Hajiya kada ki ramu I’ve moved on” sosai Hajiya ke kallonshi feeling at ease da yanda yayi
maganan kanshi ta shafa tace “Madallah, to jeka wanke hannu kazo kaci abinci da kaina
namaka girki yau” cikeda kulawa yace “Hajiya bana hanaki aiki ba, me Meena keyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login