Showing 1 words to 3000 words out of 58684 words

Chapter 1 - BAMAGUJIYA HAUSA NOVELS BY OUM HAIRAN.pdf

17 Nov 2025

107

 OUM HAIRAN: *BAMAGUJIYA*
*(HOT LOVE AND DESTINY)*

NA


*FAUZIYYA TASIU UMAR*
*OUM HAIRAN*


*Sadaukarwa ga Ahlina*
Hon- Tasiu Umar Munture (My mahaifi)
Haj Mariya Tasiu Umar (Kaunata uwa ta gari)
Aunty Khadija Tasiu Umar Dije (My yayas)
Mahraz Tasiu Umar (Dan kanina)
Sailuba Tasiu Umar
Ibrahim Tasiu Umar
Halima Tasiu Umar
Hauwa'u Tasiu Umar
Safwan Tasiu Umar (Autan Ummuh)


Allah ya karama Mana zaman lfy da kaunar juna cikin wannan family kadan me albarka.


*Special gift to My kids*
My jinin jiki my ruwan jiki ƙalbi na.
Hairan & Affan Allah ya rayamin ku ya albarkaci rayuwarku data yaran musulmi baki ɗaya, My
Affan naji kokenka insha Allahu ilahi zai amsa, yace Momynsa taƙi siyo masa ƙani sai auntyn
Momy ce ta siyo masa ƙani.


*Tsokaci*
Labarin BAMAGUJIYA labarine me dauke da manyan darrusa da jigogi masu muhimmanci,
zakuji salonsa daban da sauran salo please kuyi hkr kubini a sannu kamar yanda kuka bini a
Juhud Gidan Uncle Ruwan jira insha Allahu zan warware muku zare da abawa.



*Jan kunne*
Allah daya bazan dauki zagi cin mutumci a wannan karon ba babu wacce nayiwa dole ta
karanta littafin nan bana son shisshigi da katsalandan cikin lamura na domin bana shiga lamarin
kowa kowa yasan wannan, harkar gabana nakeyi.

*Gargadi*
Haramun ne wani ko wata ya canzamin littafi ta kowacce siga batare da izinina ba idan
kina/kana ganin bazan iya nemoka na dauka mataki ba akwai Allah yasan duk inda ka boye a
fadin duniya Kuma da sannu zai fitarmin da hakkina.



*PAGE 1*


★★★~~~★★★~~~★★★




“Bibo! Bibo!! Jummala wai ina Bibo ne nifa gsky na fara kosawa da abinda takeyi Mana Kullum
zamuje gurin bauta saita makarar damu karshe ma tace bazata ba Jummah idan bazata rinka
zuwa ba ta fadamin na daina wahalar da kaina"
Fitowa tayi daga dakin kasar da take ciki tace “Kincika korafi lantai Nifa bawai gurin bauta ne
banson zuwa ba samarin garin nan ne suke takurani amma yau naji inason zuwa da alamun
addu'a ta zata karbu gurin uwa me tsarki"
Jerawa sukayi kowacce dauke da yar salkarta ta ruwa suna tafe suna taɗinsu suna dariya,
Lantai da Ladiyo da Innu sune suke ta shewarsu itakam Bibo hankalinta yabar garesu kamar
yanda ta saba ji idan sun tunkaro wajen bautar yauma hakan ta rinƙa ji gabanta na faduwa
zuciyarta na harbawa da ƙarfin da takasa sanin dalilinsa. Ajiyar zuciya suka sauke a tare suka dubi juna Lantai tace “Bibo yau ranar zagayowar haihuwar
ki saboda haka ranar ta zama takice me daraja saboda haka kece zaki jibanci lamuranmu zuwa
ga mika bukatunmu ga uwa me tsarki"




Lumshe dara²n idanunta tayi ta buɗesu tare da karyar dakai suka fara hawa saman Tsaunin
gawo wanda wannan Tsaunin shine ya samar da asalin sunan wannan ɗan karamin kauye me
dauke da albarkatu birjir a cikinsa kama daga ma'adanan ƙarƙashin ƙasa dake da jiɓi da
manyan duwatsun da sukayiwa ƙauyen ƙawanya da kuma albarkar noma data samu tushe da
tushiya tun kaka da kakanni da kuma albarkar ruwa wanda yake kewaye da manyan duwatsun
da suka zagaye garin,
Wannan tasa al'ummar wannan ƙauye suke rayuwa cikin wadatar buwayi gagara misali.
Al'ummar Kauyen Tsaunin gawo sun kasance Asalin Hausawa na fil azal marasa sallah wato

waɗanda ake kira maguzawa, asalin kakanninsu suna rayuwa a saman wannan tsauni da ake
kira Tsaunin gawo wanda ya kasance shine tushensu.




Mazansu da matansu yaransu da manyansu sun kasance suna bautawa wani dutse ne a
saman wannan tsauni da suke kira Uwa me tsarki.
Shi wannan abin bauta tasu ya kasance wani mulmulallen dutsene da yake tsaye cikin hukuncin
Ubangiji saman wani babban dutse kamar dai ka ajiye kwai kwaya ɗaya saman faifai.
Asali ba wannan ne yaja ra'ayinsu wa bautawa wannan dutse ba face ya kasance wannan
dutse Ubangiji ya gina shi kamar ganga in ka sanya hannunka ka daki dutsen zakajishi da tauri
ko kara bayayi amma idan kasami itaciya ko dutse ka buge shi dashi sai kaji yana baka wani
sauti me zaƙi da daukar hankali kamar dai kana kada ganga haka zakaji sautin na tashi ya cika
dukkannin dajin da wannan tsauni yake.
Ba iyanan bane abin ya tsaya a gefe da gefen wannan dutsen bauta akwai wasu dogayen
massu guda biyu da suka kangeshi daga gangagewa idan iska ta busa, kuma su wadannan
massu duk wata canza kala suke yi batare da kowa yasan lkc da sa'o'in da yake canzawa ba
sannan ta saman su tsinin mashin kenan yana fesar da ruwa a kowanne lkc yana gangarawa
kasa yana haɗewa da wani babban kogi da suke kira kogin wankin zunubi, shi wannan kogi
aikinsa na zuwa ne a duk lokacin da wani ko wata ya aikata wani aiki da wannan al'umma take
dauka na tur ne da Allah wadarai.
To a wannan lokacin ne za'a kama mutum a daure shi da sarkoki ajashi a ƙasa a kaishi a jefashi
wannan kogi a tafi a barsa idan yayi kwanaki uku za'a dawo a dauki gawarsa to wannan shine
yake nuna ya mutu salihin bawa domin sunada tabbacin uwa me tsarki ta yafe masa shiyasa ta
karɓi rayuwarsa, idan kuma ba'a ga gawar mutum ba to wannan yake tabbatar da cewa wannan
bai samu yafiya daga uwa me tsarki ba.


*****

Isa sukayi gaban abin bautar suka dunkule hannayensu tare da lumshe idanunsu suna karanto
wasu addu'o'i da su kadai suka san meye suke cewa,
Tsayin lkc a haka sannan suka buɗe idanunsu Wacce suka kira da Bibo ta durƙushe saman
gwiwowinta ta kika hannunta tafin yana kallon sama ta ɗora kanta samansa dogon gashinta ya
bazo ya rufe mata fuskarta gabadaya bata damu da gyarawa ba domin tayi imanin a gaban
majiɓinciyar lamuranta take, Cikin siririyar muryarta me kama da busar sarewa tace “Mun kasance masu biyayya a gareki da
gujewa saɓa Miki ya abar bauta meye yasa kullum nake kawo kukana gurinki baki sharemin
hawayena Jimo Ciwake ya kasance me yawan ziyartarki da hidimtawa gareki, yau gashi can
cikin halin jinya baya iya gane kowa da komi saidai ayi masa komai. Yake wannan Uwa me tsarki idan har kin tabbata abar nufi da bukata to a matsayina na wacce
bantaɓa aikata zunubi ba ina nemawa mahaifina lfy da amincewark....."

Da sauri dukkansu suka dago lkcn da ƙarar faduwar wani abu me karamin sauti ta ziyarci dodon
kunnensu suka zubawa sashin da sukaji motsin idanu tare da miƙewa a tare saboda ganin
baƙin halittun da suke takowa daga nesa dasu.
Turawa ne su uku sai wasu baƙin fata biyu samari, Ja suka fara yi da baya suma wadannan
baki suka tsaya suna kallon kallo can Lantai tace “la ashe idan mutum yana mafarki gani shikayi
uwa me tsarki jiya nayi mafarki naga fararen kwaɗi ashe turawa zan gani" yanda tayi mgnr ya
Bama daya cikin bakaken fatar nishaɗi har Saida ya dara inda shi kuma dayan hankalinsa ke
kan Bibo da ta sunkuyar da kanta ko dagowa batayi yana mata wani kallo na sama da ƙasa
zuciyarsa na bugawa da ƙarfi hakanan yaji ruhinsa ya kwaɗaitu da son ganin fuskarta.




Ɗaya cikin turawan ne ya dubi abokan tafiyarsa yace “ ma iya tafiya ko?" Cikin harshen nasara
yayi mgnr, inda wanda aka kalla ɗin yayi firgigit ya dawo hayyacinsa yayi gaba, suka rufa masa
baya har zuwa lkcn idanun Bibo na ƙasa Saida ta fahimci sunyi nisa sannan ta dago idanunta
tabi inda suka bi da kallo karaf idanunta ya faɗa cikin na dayan cikin bakaken hakan ya
haddasa masa tsayawar da bai shirya ba zuciyarsa na bugawa da ƙarfi yace “Hasbinallahu wa
ni'imal wakil........"
Tashin hankali wanda baasa masa rana jin kalamin wannan mutumin yasa Bibo saurin watsa
sumarta baya ta zari kallabinta ta zuwa takalmanta ta nemi hanyar tsira da mugun gudu
hakanan suma su Lantai suka rufa mata baya.
Sunaji wadannan baƙi na kiransu amma tsoro da tashin hankali ya hanasu juyowa saima
ƙarawa gudun su ƙaimi da suke yi.




Baƙuwar kalmar tayi mugun firgita su karma Bibo Sarkin tsoro taji lbr musamman data tuna
sanadin haɗa idanunsu ne yasa shi yin wannan furuci, to me yake nufi? Kodai tsorata yayi da
ganin fuskarta kamar yanda da yawan mazan ƙauyensu suke faɗa? Ko kuma dai wannan
kalmar ɗin waƙe ne a gareshi? Batada amsa har suka isa cikin garin basu dakata da gudun ceton ran da suke yi ba inda suka
bar waɗannan baƙi da mamaki gami da dariyar yanda suka razana da ganinsu amma banda
wannan matashin mai furuci shi a bangarensa zuciyarsa ce tayi masa nauyi tsoro ya mamaye
ruhinsa tunani barkatai suka cika masa kansa kardai ya tabbata duk abinda ya gani cikin
mafarkinsa saiya zama gaske yayi mafarki zaije wani ƙauye na marasa addini kuma abubuwa
da yawa sun faru ciki harda wannan fuskar daya gani yau a saman Tsaunin gawo wadda a
lissafin falsafar mafarkinsa itace ƙaddararsa ta zuwa wannan ƙauye.......

“Meye ma'anar hakan?" Ya furta lkcn da suke isa ga dutsen da suka zo bincike akansa.... Duba
na tsanaki Najeeb abokin tafiyarsa yayi masa “sauyin yanayi cikin ƙanƙanin lkc Abokina meye
ne yake faruwa na lura daga kallon fuskar wannan ƴar maguzawan komanka ya canza anya ba
gamo mukayi garin kurɗe kurɗenmu na masifa ba?" Haɗiye wani ɗaci yayi a maƙwallatonsa ya furzar da iska ta bakinsa ya saita injin narkakakun
idanunsa masu zubawa abin kallo kasala kan Najeeb yaja numfashi yace.
“Ba gamo mukayi ba Sarkin Gida ita ce ƙaddarata......" Da sauri ya kalleshi yace “Bamagujiyar
Prince Habeeb meye haɗinka da BAMAGUJIYA da har zata zama ƙaddara?" Yarfa hannu yayi
cikin halinsa na ko in kula yace “shine nima bansani ba Sarkin Gida gabana yana faduwa zan
bar dajin nan na koma cikin gari kuyi duk abinda ya dace" [3/27, 10:12 PM] AM OUM HAIRAN: *BAMAGUJIYA*
*(HOT LOVE AND DESTINY)*

NA


*FAUZIYYA TASIU UMAR*
*OUM HAIRAN*






*Tsokaci*
Labarin BAMAGUJIYA labarine me dauke da manyan darrusa da jigogi masu muhimmanci,
zakuji salonsa daban da sauran salo please kuyi hkr kubini a sannu kamar yanda kuka bini a
Juhud Gidan Uncle Ruwan jira insha Allahu zan warware muku zare da abawa.



*Jan kunne*
Allah daya bazan dauki zagi cin mutumci a wannan karon ba babu wacce nayiwa dole ta
karanta littafin nan bana son shisshigi da katsalandan cikin lamura na domin bana shiga lamarin
kowa kowa yasan wannan, harkar gabana nakeyi.



*Gargadi*
Haramun ne wani ko wata ya canzamin littafi ta kowacce siga batare da izinina ba idan

kina/kana ganin bazan iya nemoka na dauka mataki ba akwai Allah yasan duk inda ka boye a
fadin duniya Kuma da sannu zai fitarmin da hakkina.



PAGE 2


★★★~~~★★★~~~★★★



Yanda suka shigo garin ya janyo musu kallo gurin jama'ar dake kai kawo kowa mamakin dalilin
wannan gudun mara iyaka yakeyi,
Saida suka isa ƙofar gidansu Lantana sannan sukaci birki suna mayar da numfashi daƙyar suka
kai ga wani kurutturen itace dake ƙofar gdan wanda da gani kasan an ajiyeshi ne don hutawa.
Sun jima suna sauke numfashi daƙyar Kande ta kawar da shirun da cewa yau naga masifa ke
waɗannan bakin anya ba aljanu bane Nifa tunda nagansu gabana ya rinƙa faɗuwa" fasali Bibo
ta sauke tace “wlh Nima bakiji yanda suka tsoratani ba ni saida nayi tunanin ma sace mu suka
zo zasuyi...." Kekam da daukowa mutane ɗaukakkiya Ni wannan kyakkyawan ne ya firgitani da surkullen da
naji yana ambatawa



Dariya Bibo tayi tace “ke dallah ba surkulle bane addu'arsu ce ta addininsu kwanaki naji da Jimo
Ciwake yayi baƙi yan burni sunayi a wannan abar da suke karawa a kunnensu...."
Mgnr ce ta tokareta a maƙoshinta lkcn da sukaga machine ya tsaya a nesa dasu kaɗan
idanunta ya sauka kan wannan kyakkyawan inji Lantai da faɗa,
Sauka yayi daga babur ɗin ya zubanta idanu daga nesa yana ƙarasowa garesu sukuma suna ja
baya suna ƙara matsar gdan nasu Lantai, takun maza dana mata ba ɗaya ba hakan ne yasa su
cimma su juyawa Bibo tayi da sauri zata kwasa da gudu taji numfashinta ya tsaya cak ƙirjinta ya
fara lugude ta ɗago da mugun sauri ta tureshi jikinta na rawar mazari ta shiga waige² kawai sai
hawaye ya tsiyayo mata tayi ƙasa da sauri tace “Na shiga uku kayi hkr ka yafemin koma laifin
meye nayi maka na rantse da uwa me tsarki idan Jimo Ciwake yaji hakuma tazo nemana ruwan
wankin zunubi zai jefani shikenan rayuwata ta galgalce...."




Wani ihu ta saki jin ya sake sanya hannunsa ya riƙe ta sosai da sauri ya ɗauke hannunsa daya
ya rufe mata baki tare da zaro mata manyan idanunsa.
Motsa bakinsa yayi kamar zaiyi mgn batasan meye ya tuna ba taga ya sake ta yayi gaba sakin

baki tayi da rawar jikinta da taki barinta tasa hannu ta share hawayenta ta koma ta zauna Lantai
dake laɓe ta fito dafe da ƙirji tace “Yau naga abinda yasa buzu ture naɗinsa nikam Bibo
mutumin nan ba ɗan yankan kai bane kinga fah aradu irinsu ake bamu lbr suna shigowa jeji da
motoci suna satar mutane suna zuwa sunayin kuɗi dasu" Sharrrr hawaye ya sake zubowa Bibo tace “ni ba wannan bane matsala ta kinga fa har taɓamin
jiki yayi nashiga ukuna ya zanyi yanzu Jimo Ciwake ina shiga zaiji warin maza a jikina....." Sai
kuwa ta kuma rushewa da kuka zama Lantai tayi itama ta rushe da kuka tace “Nima na gani naji
Miki wannan tsoron amma kinsan me? Tashi muje gidanmu in dafa Miki ruwa me zafi kiyi wanka
bazaiji ba ai an ce ana watsa ruwa warin yake bajewa"



Wani numfashi ta sauke me nauyi ta mike suka nufi cikin gdan suka ɗebi yayi suka haɗa wuta
suka dafa ruwan komai cikin gaggawa suke yinsa saboda kar Kakatu tazo ta tarar dasu,
Man gyaɗa ta shafa suka fita tanata sauke ajiyar zuciya suka isa gidansu Bibo sunata raɓe²
Ɗantala ƙanin mahaifinta ya sawo kai ganinsu tsaye cirko² ya dakansu tsawa yace “durun
uwarku kukeyi anan da kuka tsaya kuna tsinkawa mutane hanji” zabura sukayi Lantai ta kamo
hannun ƙawar tata suka shiga gda sumsum, wuf suka faɗa ɗakin Jumme ta miƙe da sauri
sukayi dako² kamar sunwa megari ƙarya da sauri Bibo tace “ba abinda kike tunani bane muna
tafiya ta zame ta faɗa dagwalon kwatami shine muka biya gidanmu ta wanke jikinta" riƙe haɓa
Jumme tayi tace “anya kuwa Habibah..." Nan suka kama rantse rantse da duk wani abu da
zaisa a yarda dasu wannan ya kwantar mata da hankali tace.




“Ai shikenan ga abinci can na ajiye muku a madafi ki dauko muku kuci ki ɗauki kunun zaƙin
kikai dandali" zama sukayi suka fara cin abincin kusan Lantai kecin abincin idan taga ta tafi
tunani ta zungureta da haka suka gama sukayi kwalliyarsu anan suka dauki bahon kunun zaƙin
suka fice suka nemi ɗan dako ya ɗauka. Ko a dandalin batada wata walwala ɗan wasan da sukeyi da gaɗa duk bata da walwala kowa
dake gurin ya fahimci hakan damma Lantai nata tausarta suna zaune ta rafsa uban tagumi wani
almajiri ya iso ya tsaya yace “Bibo wai kizo inji Manuwa yana bakin tukuba"
Tsaki tayi ta kalleshi ta watsar Lantai tace “Kai kaje kace tana zuwa" miƙewa tayi ta zari bahon
kunun zaƙinta tayi gaba tana cewa “ɗan baƙar jaraba kutumar ubansa zanyi masa ɗan
Shegiyar"
Binta Lantai tayi ta riƙeta tace “bai kamata ba abinda kike yi ni banga uwar da Manuwa ya nema
ya rasa ba da baki ƙaunarsa kinga fah babansa Sarkin Noma ne...."




Wani uban tsaki taja tayi gaba tana ƙara jan zaninta sama suna tafe Lantai nayi mata mitar

wulaƙancin da takewa Manuwa.
Can nesa sukaga an haskesu basusan sanda suka rungume juna ba tsabar tsoro da firgici,
ƙamshin daya gauraye hancinsu ne yasa su buɗe idanunsu a tare suka saukesu kan Najeeb
dake tsaye a gabansu yanayi musu kallon wulaƙanta wulakantacce ya dubi Bibo yace “Meye
sunanki?" Ɗagowa tayi me arhar hawayen har idanunta ya kawo ruwa tsawa ya daka mata yace “banason
ƙauyanci tambayarki nayi meye sunanki?" Cikin in...ina tace “Ha...bee...bah...." Lumshe idanu
Najeeb yayi yace “Da gaske?" Kaɗa kai tayi yaja numfashi yace “ok dama Mun zo wani aiki ne
nan shine ubangidana yakeson ƙulla ƙawance dake...." Zaro idanu sukayi sukace “ƙawance?"
Ɗaga masu gira yayi yace “wannan shine gsky duk inda mukaje mukanyi ƙawaye Abokina kuma
ubangidana baya ƙawa baitaɓa ƙawa ba amma yasoki kasance ƙawarsa kada kice a'a domin
wannan abu ne da bazaki iya kaucewa faruwarsa ba".............
[3/30, 7:32 PM] AM OUM HAIRAN: *BAMAGUJIYA*
*(HOT LOVE AND DESTINY)*

NA


*FAUZIYYA TASIU UMAR*
*OUM HAIRAN*



*Tsokaci*
Labarin BAMAGUJIYA labarine me dauke da manyan darrusa da jigogi masu muhimmanci,
zakuji salonsa daban da sauran salo please kuyi hkr kubini a sannu kamar yanda kuka bini a
Juhud Gidan Uncle Ruwan jira insha Allahu zan warware muku zare da abawa.



*Jan kunne*
Allah daya bazan dauki zagi cin mutumci a wannan karon ba babu wacce nayiwa dole ta
karanta littafin nan bana son shisshigi da katsalandan cikin lamura na domin bana shiga lamarin
kowa kowa yasan wannan, harkar gabana nakeyi.



*Sanarwa*
Kamar yanda kuka sani ne ba wani sabon abu ba littafan OUM HAIRAN na kudine zaifi ki biya
ki karanta cikin kwanciyar hankali, bana Miki/maka fatan kaci haƙƙin daba naka ba domin nasan
Allah bazai bari ba musamman yanzu da zamu shiga wata me alfarma.
Ki biya ta waɗannan hanyoyin acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko ku turo katin
waya MTN ta WhatsApp

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login