Showing 3001 words to 6000 words out of 58684 words

Chapter 2 - BAMAGUJIYA HAUSA NOVELS BY OUM HAIRAN.pdf

17 Nov 2025

121

number na kamar haka 09013718241. Normal group 300, Special 700.

*Page 3*


★★★~~~★★★~~~★★★


Tunda ya fara mgnr suke kallonsa yana ida faɗin abinda yake faɗi ya juya yayi tafiyarsa wani
kayan takaici wanda akace yana sonta da ƙawancen har yasha kwana yama riga tafintan nasa
barin gurin taɓe baki tayi tayi gaba suna tafe babu me cewa wani Saida suka kusa rabuwa
Lantai tace. “Nifa lamarin ƴan birnin nan ya fara bani tsoro musamman akanki Bibo meye kuma ƙawance
tsakanin namiji da mace?" Kawar dakai tayi tace “to basai yayi da gyatumarsa ba tunda shi
bashi da ɗa'a aiko mahaukaci yasan wannan ba daidai bane"
Shigewa tayi gdansu Lantai ta wucce nasu gdan, tana shiga tayi watsi da komai ta shige
dakinsu ta faɗa kan shimfiɗa ta kwanta tare da lumshe idanunta wannan wanne irin mutum ne?
Meye yake nufi da ƙawance tsakaninsu? Tambayar data kwana da ita a ranta kenan har
wayewar gari tada tashi wanke fuskarta tayi suka gaisa da uwarta ta nufi wajen gyatuminta ta
ishe shi zaune yana shan kunu ta zauna suka gaisa tace “inason dama zanje gona ne" dubanta
yayi duba irin na tsanaki yace “gona kuma?" Meye zakiyi a gona?" Sunkuyar da kanta tayi ƙasa
tace “Sallau jiya yake cewa da Jumme ciyawa ta ɓata yabanyar gonarka idan ba'a cireba zatayi
ɓarna wannan tasa naga ya kamata naje nagani koda abinda zan iyayi" jinjina kai yayi yace
“shikenan kije Allah ya tsareki"




Ƴar ƙaramar dariya tayi ta miƙe ta fita saboda murna ko sallama batayiwa Jumme ba ta bar
gidan ta nufi gonar tanata yan waƙoƙinta.
Tsakanin gonar da cikin gari akwai nisa sosai amma sabo yasa basa ganin nisan haka taci gaba
da kurɗawa tayi nisa sosai daidai wata itaciya ta rinƙa jiyo ƙamshi me kwantar da zuciya tana
dosarta ƙamshin na ƙaruwa harta isa jikinta, gabanta ya faɗi “Wayyoh!" Tana mgnr tana ja da
baya ga mamakinta sai taga yayi murmushi ya taso daga gurin yace “kin tsorata ko?" Wata
ajiyar zuciya ta saki me ƙarfi jin dirin saukar muryarsa har cikin lakarta.
Sake matsowa yayi yace “Ina zaki?" Yana mgnr yanakai hannunsa ga buhun dake saɓe a
kafadarta, batayi Masa gardama ba ta sakar masa ya fara dubawa yana kallonta Saida ya gama
dubawa tsaf koda baisan amfanin kayan ba alama ta nuna masa gona zata hakan yasashi
ɗagowa yace “gona?"

Da sauri a ƙoƙarinta na ganin ya barta ta tafi ta ɗagansa kai yaja fasali ya karyar dakai yace
“zan iya rakaki inason na iya aikin gona...." Zaro idanu tayi tare da kunshe dariya ya zubanta
idanu har Saida ta saita kanta yace “meye ya baki dariya?" Taɓe baki tayi tace “ba haɗi saniya
da tallan kilishi" da sauri ya dawo da hankalinsa gareta yace “sabida me?" Gaba tayi taci gaba
da tafiyarta tana cewa “ko cikin malalata akwai gwarzo kaikam ko riƙon lauje bazaka iyaba bare
noma"
Murmushi yayi yabi bayanta yace “iya magana kamar ƴar mahauta kuma haka zaki koyamin ba"




Tsayawa tayi tare da haɗe fuska tace “Idan muka tafi gona tare zakasha wahala kuma mutanen
garin mu zasuje su faɗawa Jimo Ciwake harma su ƙara da sherri ka taimakeni ka barni naje
nayi abinda ya fito dani"
Fuzge buhun hannunta yayi yayi gaba batare da ya sake cewa da ita komai ba dole tasa ta
rinƙa binsa da sauri tana cewa dashi “bakaji ba kagafa akwai nisa jikinka bai saba da wahala ba
banaso kasha wahala....." Tsayawa yayi ta iso gareshi ya kai hannu zai riƙota tayi saurin ja baya
tace “Aa haram giya a gdan Mallam kada ka kuma taɓani jiya daka taɓani Saida Jumme ta kusa
ganewa da kuwa ta gane da tuni na zama tarihi don jefani za'ayi cikin ruwan wankin zunubi
kuma zunubin nan bazai barni na tsira ba"




Zubanta idanu yayi yace “wanne zunubi kenan?" Taɓe baki tayi tace “ai babban zunubi ne
namiji ya taɓa jikin mace a nan garin idan har hakan ta faru to duk inda tayi za'a rinka jin warin
maza a jikinta kuma zaija mata ƙyama da tsangwama wannan dalilin zaisa taƙi auruwa domin
babu wanda zai ɗauki karya yakai gidansa a matsayin uwar ƴaƴansa" Murmushi Habeeb yayi yace “Al'adarku nada kyau da tsafta kamata yayi ace baku kuke da
wannan tsarin ba mu musulmi mune zaifi cancanta da mu kasance a haka domin ubangijinmu
ya hanemu da kusantar zina" daga wannan basu kuma mgn ba sukaci gaba da tafiya har suka
kai gonar Habeeb ya tsaya yana kallon gonar ba wata babba bace amma tayi kyawun yabanya
da ta burge shi.




Tsinkayo muryarta yayi tana cewa “kaje ka zauna ga bishiyar mangwaro can tunda ka nace
Saida ka biyoni” miƙa mata kayan hannunsa yayi batare da yayi furuci ba bai kuma bi umarninta
ba, ganin abin nasa na yine yasata wuccewa ta fara aikinta tanayi yana kallon yanda take
tafiyar da komai yana gane irin ciyawar da take cirewa da haka shima yakai hannu ya fara
tayata.

Ba ƙaramin mamaki ta shiga ba da taga ko ita data saba aikin bata kaishi kwazo ba ta ɗago
tasa gefen zaninta ta sharce gumi ta zubansa idanu tana mamakin inda ya iya aikin gona da
kuma yabawa kyawun surarsa tabbas yakai kyakkyawa na gaske duk da ba fari bane amma
yanada wani sihirtaccen kyawu da hasken fata na tsabar hutu da jin daɗi da yake bayyana
kwanciyar hankalinsa.




Ɗagowa yayi ya zubanta idanu tayi saurin kawar da kanta tare da basarwa ta sunkuya tana
tattare kayan tana cewa “naga abubuwan mamaki a iya yau dana zauna dakai naga kana isa
waccan ƙoramar kana wanke jikinka kana dungura goshinka ƙasa meye hakan yake nufi.... "
Cikin mugun mamaki Prince Habeeb ya Kalli Bibo tare da kafeta da manyan idanunsa, yanzu ita
a nufinta batasan sallah ba? Mamakinsa ya kawar da cewa “koda yake a ina zata sani?"
Tayata tattare kayan yayi yace “Kada kiyi gaggawa da sannu kuma a hankali zakisan komai
game dani tunda kin yarda da abotarmu" miƙewa tayi da sauri tana girgiza kai tace “Aa Nifa ban
yarda da wata ƙawance ba...." Hannu yasa saman bakinta ta ɗago ta dubeshi idanunsa nakan
fuskarta yace “kar kija da ƙudurina inason abota dake kuma ta ƙullu daganan har zuwa lkcn da
zan bar garin nan naku kiji a ranki a koyaushe kuma a kowanne yanayi zamu kasance a tare
Habeeba bana nufin cutarwa gareki saidai ke kin kasance ƙaddarata"




“Ƙaddara" ta faɗa tare da ɗagowa da sauri, bai tsaya bata amsa ba saima gaba da yayi dole
tasa ta bi bayansa suka nufi cikin gari duk inda suka wucce hankali akansu yake har suka je
ƙofar gidansu taja ta tsaya shima ya tsaya sun jima a tsaye ganin bashida niyyar furuci sai
kafeta da yayi da manyan lulu eyes nasa yasata juyawa tana cewa “Na gde ka huta gajiya" Shigewa tayi ciki yabi bayanta da ido abubuwa da yawa na ayyanuwa a ransa waɗanda ya kasa
tantance yuwuwarsu ko rashin yuwuwarsu koda yake Hausawa sun ce da tsoro ake cire saa
shikam zuciyarsa na rawa akan abubuwa da dama amma dai zai jarabba kalar tashi nasarar
yagani idan yanada rabo. Da wannan tunanin ya isa masaukinsu Najeeb daya gaji da kiran wayarsa har ransa yayi ƙuna
ya tareshi da cewa “Ina kaje?" Tambayar ce ta bashi haushi ya zabga masa harara ya nufi cikin
gdan gdane me kyau nesa da cikin gari kaɗan ginin zamani dakunansu harda A C ga babban
inji da aka sanya musu me bada wuta kowanne lkc sannan duk wata kalar kayan jin dadin
rayuwa sun siya sun zuba a gdan a taƙaice dai idan ka shiga gdan bazaka gane a ƙauye kake
asalin ƙauye irin Tsaunin gawo ba.




“Habeeb tambayarka nakeyi ina kaje...." Juyowa yayi ya kafeshi da idanunsa wanda ba kowa ke

jure sanya ƙwayar idonsa cikinsu ba ya tako gabansa yace “Ni kamar ni kake tambaya ta ina
naje kamai dani wani ƙaramin yaro ne ko kamai dani mahaukaci da kake gadi na?"
Yayi mgnr yana zare ƙafar wandonsa, harara Najeeb ya watsa masa yace “ka kuwa ɗaukowa
kanka abinda zai dameka banga uwar da ta ɗauki hankalinka akan wannan yarinyar mara
addini ba da har ka zaɓi zubar da mutumcinka akanta....."
Tsawa ya daka masa yace “Wlh tallahi ka ƙara faɗar wata kalma mara kyau akan Habibah
saina...."
“Sai kayi me? an faɗa mara addini kayi duk abinda zakayi sakarai da idanunsa yake rufewa
idan yaso abu kamar babu wani abu bay....." “Najeeb...." Ya faɗa tare da ɗaga hannu zai
daukeshi da mari me kuma ya tuna saiya fasa jikinsa yana tsuma yace “Ficemin daga ɗaki kafin
na illataka..."



Hayaniyar tasu ce tayi yawan da har ta fito da James daga ɗakinsa koda bayajin Hausa yasan
lallai koga yanayin fuskokinsu ran maza ya ɓaci ganin yanda Habeeb ke tsuma yana ruwan
bala'i yana nunawa Najeeb hanya yasa James kama hannu Najeeb suka fice yana cewa “Kuma
ka rubuta ka ajiye wlh indai ina raye zamu koma Dutse wlh saina rusa duk wani shirinka baka
isa ka auro mana Arniya mara addini ka kawo mana cikin zuri'armu ba wawa kawai da baya
lissafa rayuwa wannan abinda kake shirin aikatawa ai ya cika abin kunya ace duk matan da
muke dasu a Family saika fito waje wajen ma ka rasa wacce zakaso sai BAMAGUJIYA to saika
aura mu gani ai...."
A hassale yace “Idan Allah yayi saika hana ai ɗan hana ruwa gudu kawai Ni na taɓa jin wannan
jaraba kun dameni na kawo matar aure na kawo wacce nakeso nakasa samowa yanzu kuma
lkc yayi kwatsam ta faɗo rayuwata amma kaine na farko da zakayimin hassada to barima kaji Ni
kuma naci alwashin ko zan rabu da kowa da komai saina auri Habeeba....." [3/31, 7:39 PM] AM OUM HAIRAN: *BAMAGUJIYA*
*(HOT LOVE AND DESTINY)*

NA


*FAUZIYYA TASIU UMAR*
*OUM HAIRAN*



*Tsokaci*
Labarin BAMAGUJIYA labarine me dauke da manyan darrusa da jigogi masu muhimmanci,
zakuji salonsa daban da sauran salo please kuyi hkr kubini a sannu kamar yanda kuka bini a
Juhud Gidan Uncle Ruwan jira insha Allahu zan warware muku zare da abawa.

*Jan kunne*
Allah daya bazan dauki zagi cin mutumci a wannan karon ba babu wacce nayiwa dole ta
karanta littafin nan bana son shisshigi da katsalandan cikin lamura na domin bana shiga lamarin
kowa kowa yasan wannan, harkar gabana nakeyi.



*Sanarwa*
Kamar yanda kuka sani ne ba wani sabon abu ba littafan OUM HAIRAN na kudine zaifi ki biya
ki karanta cikin kwanciyar hankali, bana Miki/maka fatan kaci haƙƙin daba naka ba domin nasan
Allah bazai bari ba musamman yanzu da zamu shiga wata me alfarma.
Ki biya ta waɗannan hanyoyin acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko ku turo katin
waya MTN ta WhatsApp number na kamar haka 09013718241. Normal group 300, Special 700.


*Page 4*


★★★~~~★★★~~~★★★

Tsaki Najeeb yayi yana huci kamar kububuwa ya fice daga gdan gabadaya shikuma ya nemi
guri gefen katifarsa ya zauna shima yana fitar da iska me zafi sosai kalaman Najeeb sun taɓa
zuciyarsa kwafa yayi ya miƙe ya shige bayi ya watso ruwa.
Ba ƙaramar gajiya yayi ba ashe haka manoma sukeshan wuya lallai dole a gaida manoma
sallar magrib yayi domin yasan ba kiran sallah zaiji ba Saida yayi Isha yayi shafa'i da wuturi
sannan ya haɗa tea yasha dake shi ba ma'abocin abinci me nauyi bane indai da shayi to lfy lau
ne.



Tunda ya kwanta yake sakawa da warwarewa majigin hoton Habeeba yanayi masa gizo a
idanunsa, tashi yayi ya zauna baisan meye ya tafi da ruhinsa gareta ba ba kowacce mace tafi
komai ba ganinta kwana ɗaya yanajin kamar yayi shekara guda da ita baiji zai iya rabuwa da ita
ba, saidai abubuwa biyu suna mugun kada masa hantar cikinsa baisan da yaya Sarki Khalil da
Hajiya Kilishi mahaifiyarsa dama sauran danginsa na gdan sarautar dutse zasu karɓi wannan
zabi nasa ba.
Karfafawa kansa gwiwa yayi da sama kansa ƙumajin nasara tabbas zaiyi duk mai yiwuwa ya
kafa kansa a wajen Habibah da iyayenta duk da suma a yanda suke da tsattsauran ra'ayi yasan
za'aja daga kafin su bashi damar auren ƴarsu.
Numfashi ya sauke ya koma ya kwanta daidai lokacin da wayarsa ta ɗauki ruri, gabansa ya faɗi

ya mike ya ɗauki wayar numfashi yaja me ƙarfi ganin sunan mahaifiyarsa na yawo a saman
sensor ɗin.




Cikin mutuwar jiki ya kara wayar a kunnensa ta sauke ajiyar zuciya tace “Autan Mama kaji daɗin
garin arna ka manta dani ko kiran ma da kakemin tun jiya da safe banjika ba ince dai lfy kake?"
Wani wahalallen numfashi ya sauke ya shafa sumarsa yace “sorry My love wlh abubuwa ne
sukayi min yawa shiyasa lissafin komai ya kwace min ya kike ya Mai martaba da sauran ƴan
gida ina Hajiya da Inna duk ince dai suna lfy?" Lfy Alhmdllh ya jikin naka ina labarin surukata...."
Wani damm ƙirjinsa ya bayar da sauri ya basar da cewa “Ohhh Mama wai nikam na dameki ne
duk kunbi kun damu sai kun ɗora min nauyi nawa nake ne har yanzu ban rufa 30 years ba"
katseshi tayi da cew.




“Kai ar ɗan ƙaniyar uwa to so kake sai kakai ka wucce duk mazan gdan nan waye yayi
girmanka babu aure? Faɗamin shi haba ubana shi aure ai ƙima ne kuma garkuwa ne ga ɗa
namiji nikam gsky nima inason ganin ƴaƴan auta na kada ka manta fah ku biyu gareni maza
daga babban yayanku sai kai yan uwanku duk mata ne ai Yakamata ku karɓi girman tunda
wataran kune iyayensu duk girman mace ƙasan namiji take domin raunin mu faɗaɗɗe daga
bakin ubangijinmu...."
Wa'azin nata yaji zaiyi tsayi yace “Is ok Mama kin kusa samun suruka indai suruka ce very soon
kinji" murmushi tayi tace “Ubana kenan Sarkin daɗin baki shikenan Allah ya kawo mana
rabonmu na alkhairi" ajiye wayar yayi yana murmushi Hajiya Kilishi kenan kullum maganarta
Habibunta yayi aure zaidai yi auren nan ko ta sake masa mara yayi fitsarinsa a nutse.


******


Ɗagowa tayi jikinta a mace tace “Na rantse da abar dogaro ba Rabe bane ya rakani gona baƙo
ne ɗan birni muka haɗu dashi a hanya shine yace yanaso ya koyi noma Jumme saida nace
karya bini yaki ji to ya zanyi masa tunda kince babu kyau jayayya da babba"
Shiru ce ta ratsa gurin Jimo Ciwake ya ɗago yace “Shikenan amma dai banason wannan
tarayyar taku saboda ƴan birni basu da gsky idan kin sake haduwa dashi ki faɗa masa nine
nace banason alakarku ya nemi wata abokiyar bandake wannan sakarcin da shashancin
shashatau ɗin baza ayisa dani ba" Jinjina kai tayi tace “Na gde zan kiyaye" miƙewa tayi ta koma ɗaki tayi tagumi a haka Kande da
Lantai suka shigo suka ishe ta Lantai ce ta sanya hannu ta cire mata tagumin tace “yo yau naga

watsiyar watsewa Jimo ne ya mutu ko Jumme da zaki rafsawa mutane tagumi haka?"




Numfasawa tayi ta ɗago idanunta ya ciko da kwalla tace “yauma shine ya aiko ku?" Zama
Kande tayi ta kama hannunta tace “Na rasa wannan wacce irin masifa ce kwana ukun nan
kullum sai yazo dandali yasa an kiramu ya tambayemu meye yasa bakya fitowa? Munce masa
baki da lfy to yau dai sakomu yayi a gaba wai sai mun rakosa munyi masa iso ya dubaki...." Dafe kirji tayi tace “Na shiga uku kada ku barshi ya shigo kuje kuce masa na tafi hayin
badarawa gdan kakata kuma ba'a bin hanyar da dare saboda akwai wata mahaukaciyar
damusa da take kashe mutane....." Zaro idanu sukayi.
Lantai ta matso tace “Tabɗi bakisan yanda mutumin nan yake da naci ba ai na rantse da abar
dogaro cewa zaiyi mu rakashi garama kiyima su Jumme wayo muje ku gaisa saiki dawo...."
Motsin shigowar Jumme ne yasa su miƙewa cikin zaurancensu na ƴammata tayi musu nuni da
suje su jashi bayan gidansu.


Jumme ce ta dubeta tayi ƙasa dakai tace “don darajar Baba Tsauri uwarki kibarni yau naje
dandali da Lawai me kura ake wasa inason wasansa" murmushi Jumme tayi tace “kin gamani
da ƙarshen daraja jeki saikin dawo Allah ya tsareki" tsalle tayi ta saki ihun murna ta fice da
gudu. Bayan gdan nasu tayi da sauri ta nufeshi duk wata gaɓa ta jikinta tana rawa ta baza gashin nan
nata me taushi da aka ƙawatashi da kitso kananu iyakar gaban bayan aka barshi duguzunzun
rigarta iya ƙirjinta ta rufe cikakku tsayayyu masu faɗin tushe da ɗaukar hankali ta killace su
ɗamɗam cikin rigar saƙin. Cibiyar ta a waje take shafaffen cikin nan zanen tatu na kibiya anyi mata zanen flower me
ɗaukar hankali ƙugun nan yaci uwar jigida kusan naɗi kusan hawa talatin ta cika mata faffaɗan
ƙugun nan zaninta iyakar gwiwarta tukatukin ƙafar nan an ƙawata su da nadin duwatsu.



Tunda ta taho ya zubanta manyan idanunsa da suke lumshewa fari tas yake jin zuciyarsa tana
isowa ta tsugunna a gabansa ta kama ƙafarsa ta ɗaga ƙafarsa ta ɗora tafin ƙafarsa a tafin
hannunta ta ɗago kyakkyawar fuskarta ta sakar masa murmushi da yaja dimple dinta ya lotsa
Jan lips dinta suka baje a fuskarta tace “Aminci da nasara su tabbata gareka mutumin birni
inata kewarka banganka ba banjika ba har rashin lfy nayi da Jimo Ciwake ya hanani fitowa
saboda ka rakani gona...."
Hannunsa yasa tsakanin ƙirjinta da hammatarta ya ɗagota suka fuskanci juna damdam haka
ƙirjinta yake bugawa inda shima yake jin wata muguwar faduwar gaba ƙamshin wani turare
daya kasa tantance wanne irine yana tashi a jikinta ya hadu da sanyin yanayin damunar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login