Showing 57001 words to 58684 words out of 58684 words
ƙwari haka ta miƙe ta ɗauki mayafinta ta yafa ta fice daga dakin ta nufi ɗakin baƙin
gabanta naci gaba da faɗuwa.
Tura ƙofar tayi ta shiga tare da sallama idanunta ya sauka kan Jumme dake zaune gefenta
mahaifinta ne riƙe da Hudais sai Kilishi dake dauke da Ayyana, tsayawa tayi turus tanajin wani
faduwar gaba na shigarta tare da bin iyayen nata da kallo ɗaya bayan ɗaya.
Riƙo hannunta akayi ta juya ta dubi wanda ya riƙe hannun nata ganin Habeeb ne ya ɗaganta
gira tare da janta har zuwa inda mahaifan nata ke zaune tana isa ta zube a gabansu da sauri
jikinta na rawa tana wani irin kuka ya ƙwace mata data kasa sanin na meye farin ciki ko
nadama? Tabbas tayi farin cikin ganin iyayen nata sun taso takanas dominta, sannan
nadamarta ta tsayin watanni ta dawo mata sabuwa tabbas da tabi umarnin Mahaifanta ta nuna
jajircewarta da bata fuskanci wani wulaƙancin ba tasani yan ɗakin da mijinta yafito da
mahaifiyarsa sun sota sun kaunaceta da kaunar da mijinta yake yi mata, duk da tasan cewa
bata isa kaucewa kaddararta ba tunda Allah ya ƙadarta Habeeb shine uban ƴaƴanta to ko
bataso sai ya zama mijinta amma tayi wasarairai da ƙimarsu.....
Cikin kukan me taɓa zuciya ta buɗe baki tace “Jumme Baba nasani na cusa baƙin ciki da
damuwa a zuciyarku duk da cewar kunyi ɗawainiya dani tundaga samuwata har zuwa girma na,
a lokacin da zan nuna muku tabbas kuɗin iyaye ne na kwarai duk da rashin hasken musulunci a
cikin rayuwarku baisa kunyi wasarairai da tarbiyya ta ba, kawai sai ƙaddara ta jefomin shi cikin
rayuwa ta har naji a raina gara na barku dana barshi, inason Habeeb nasani shima yayi domin
Ni yayimin halaccin da maza masu irinsa sunyi ƙaranci a duniya saboda Ni ya amince ya rasa
komai daya mallaka ta bangaren mahaifinsa ƙarshe kuskuren mu mu biyu ya haifar min da
damuwar da har na mutu bazata goge ba, ko sanda bana cikin musulunci ban kaunaci zina ba
na ƙyamace ta na tsaneta har kawo lokacin da Habeeb ya zama mijina, kwatsam waini
Habeebah saboda son zuciyar kishiyata kishiyar surukata da iyayen kishiyata yasa sukayi
amfani da ƙiyayyar da mahaifin mijina yakemin aka barratani da mijina a lokacin da nake
buƙatarsa aka rabani da ɗana da nake kallonsa a matsayin gata na..."
Kukanne yaci ƙarfinta daƙyar ta buɗe bakinta tace “nasani haƙƙinku ne wlh badon banason
Habeeb ba amma na zaɓi yi muku biyayya wannan karon matuƙar zaku yafemin kuskurena na
baya da rudin ƙuruciya yasani aikatawa kuyimin afuwa ku yafemin don...."
Rufe mata baki Jimo yayi yana murmushi yace “Kayyah Bibon Baba wannan ai ya zama
shuɗaɗen labari ƙaddararki ce kamar yanda Liman ya fada mana ina zamukai rabon Waɗannan
yaran Habeebah dakin matsa ma wajen yimin biyayya da tuni ba labarina akeyi ba kila da tuni
ƙasa ta jima da rufe idanuna kece da hƙr Bibo da ban hau dokin zuciya ba da baki wulakanta ba
kuma da da haka ta faru mu zaki nufo mu share Miki hawayenki nikam na yafe Miki tun ranar da
hasken musulunci ya ratsa Zuciyata Habeebatullah kije ki rayu da mijinki da yaranki cikin aminci
kuma na tabbatar kafin Ni mahaifiyarki ta jima da yafe miki"
Kwantar da kanta tayi saman cinyar mahaifinta taci gaba da rera kukanta na farin ciki tana gdy
ga Allah da ya ƙadarta mata ganin wannan rana itakam da basu yafe mata ba da batasan ya
zatayi da rayuwarta ba.
Ji tayi an kama gashinta anja ta ɗago tare dayin murmushi ashe Hudais ne ta miƙa masa hannu
ya taho jikinta ya kwanta luf yana sauke ajiyar zuciya ta dubi Kilishi tace “Kilishi dama a gurinki
yake ba a matar babansa ba?"
Murmushi Kilishi tayi tace “babanshi ai bashida mata tun washegarin ranar da kika bar gidan
itama ta bari gara kema kullum muna hasashen dawowarki itakam ta tafi kenan yanzu haka ma
tayi aure shekaran jiya ta tare a gidanta" ajiyar zuciya ta sauke dama tasan auren Khausar da
Habeeb wataran dole zai ƙare don da gaske Habeeb yake Khausar bata tsarinsa amma bataso
ace itane sanadi ba.
Ranar yini akayi ana hirar yaushe gamo iyayenta kamar su mayar da ita ciki Safeenah sai
hidima takeyi da baƙi tsakanin Beebah da Habeeb kuwa Saidai kallo kawai Allah yasani tasan
baiyi mata komai ba amma ta ƙudurce a ranta matukar ba Mai Martaba ne ya amincewa
zamansu matsayin ma'aurata ba to ta hkr dashi itakam ta daidaita da nata iyayen shima tanaso
taga ya samu daidaito da mahaifinsa a washegari suka ɗauki hanyar Dutse harda Beebah
tunda suka taho gabanta ke faduwa bata fatan ace su sauka a gidan sarauta saboda komai zai
dawo mata sabone.
Ga mamakinta sai taga sun nufi wata babbar unguwa ta manyan attajirai an buɗe musu wani
get sun shiga yayi parking suka fito shine yayi musu jagora har cikin gidan yana nuna musu ko
ina Saida ya gama nune nunensa sannan ya juyo ya dubi Habeebah yace “gidanki ne da zaki
rinƙa sauka idan kinzo hutu daga London saboda ina tunanin nan da 2 weeks zamu tafi" Saida
taji wani dam a ƙirjinta tayi masa wani mugun kallo sannan ta kawar dakai anan sukaci sukasha
kukunsa ya shirya musu komai Saida suka gama sannan ya ɗebesu suka nufi tsohuwar
unguwar su shima tsohon gidan cikin watanni biyar zuwa shidan ya gyara shi sosai ya sake
masa kayan cikinsa Saida suka gama dubawa sannan ya dubeta yace.
“Wannan kuma nakine halak malak Habeebah bansan dame zan saka miki soyayyarki gareni
ba sannan bansan dame zan goge Miki tabon mikin da akayi Miki a duniya kawai saboda a
rabani dake ba wlh tallahi Habeebah tun kafin bayyanar gaskiya Ni nasan bazaki taɓa aikata
abinda akace kin aikata ba kuma Kilishi ma da su Hudah sun shaideki akan hakan, mun riga
mun yanke hukunci Baba da Jumme zasu zauna cikin wannan gidan saboda wata hatsaniya da
tasa suka baro garin Tsaunin gawo dalilin karɓar addinin Musulunci da sukayi"
Tunda ya fara maganar take kallonsa idanunta na zubar da hawaye tana girgiza masa kai har
Saida ya gama sannan tace.
“Bana bukatar komai daga gareka Habeeb Ni burina naga kun daidaita tsakaninka da
mahaifinka yaci gaba da sonka da janka a jikinsa kamar yanda yake yi a baya burina ya karɓeni
matsayin suruka nasani inasonka saidai so bazai rufe mana idanu a karo na biyu mu kara yin
abinda zamu zo yaci gaba da bibiyarmu har jikokin mu ba, nasan kafini sanin girman haƙƙin
mahaifa akan ƴaƴansu...."
Tunda ta fara maganar yake kallonta har ta gama yayi murmushi yace “hakane kema kince wani
abu saidai ki sani Mai Martaba jikinsa yayi sanyi tun lokacin da naje na nuna masa hotunan
Ummi na na sanar dashi kin haifa min ƴa mace a ranar yake cemin naje na dawo dake ɗakinki
komai ya wucce a manta da duk wani abu daya faru dama shi tunda abin ya faru yake
tuntuntuni akan abin sai gashi yaron da kansa yazo ya ƙaryata kansa batare da wani ya
takurasa ba yace sashi akayi yazo a daidai lokacin aka shirya plan na yanda za'a gayyato Mai
martaba yazo ya kamaki da kansa,
Idan baki gasƙata abinda na faɗa Miki ba yanzun mu wucce gidan sarautar kiji da kunnenki....."
“Basai kunzo ba Ni nazo" sukaji an faɗa a bayansu juyawar da zasuyi sukaga Mai Martaba
tsaye da dogarawansa jikin ƙofa ya tako fuskarsa dauke da murmushi har gaban Beebah ya
riƙo hannunta yace “So da yawan lokaci munayin hasashe baibai da daidai mukan hasaso
abinda yake saɓanin gsky sai zukatanmu su tafi akansu har su rinƙa tursasamu akan cewa
wannan abin shine daidai, na hasashi kuskure na tafi akansa nayi jayayya da abinda ubangiji ya
hukunta karshe nayi zaɓi sabanin na ubangiji na takura masa Saida ya karɓa bisa shawarwarin
Ƙanina Lukman da Hajiyan ƙofa ashe duk a keken ɓera suka ɗora ni yanzu gashi Ni da idanuna
yayanku Ahmad ya ɗaukeni ya kaini wani hotel na kama Khausar da hannu na da maza tana
shaye-shaye turr da wannan asara da taɓewa Habeebah duk da an daɗe ana faɗamin Khausar
ba sa'ar auren Habeeb bace bantaɓa yarda ba sai ranar kuma abin mamaki harda yaron da
akace kece kika gayyato shi don buƙatar kanki saboda Kinga mijinku bayanan daganan na
tabbatar duk wani abu daya faru makirci ne akayi amfani dani don shiga tsakaninki da mijinki
Habeebah kiyi hƙr ki rayu a gdanki tare da ƴaƴanku kamar yanda nakewa kowacce ƴa dana
haifa fata"
Sosai Habeeb yaji daɗin yanda mai martaba ya wankesa ya sani ba don Allah ya kawosa yayi
bayani dakansa ba da babu kalmar da zai yi amfani da ita wajen fahimtar da Beebah,
Shida mai martaba da Kilishi ne suka tafi inda suka bar Beebah da iyayenta sunata mamakin
karamcin surukanta sunata hirarsu ta yaushe gamo nan suke faɗa mata mutuwar Baba Uda taji
mutuwarsa sosai har hawaye tayi.
Rayuwarta me takeyi ita da iyayenta saboda Kilishi ta hanata komawa gdansa tace ta bari tayi
arba'in ransa baiso ba hakanan ya hkr ya haɗa nasa ya nasa ya wucce London.
Yanda Habeeb ya mayar da hankalinsa wajen kula da iyalinsa abin ba'a cewa komai bayan tayi
arba'in ya harhaɗa masu nasu ya nasu suka ɗauki hanyar birnin London daga wannan lokaci
komai ya wucce rayuwa ta saitu kamar babu wani abu daya taɓa faruwa komansa Beebah
komai ya tashi yi da ita yake shawara, ga yaransu dagwai dagwai gwanin ban sha'awa Saida
Ayyana ta shekara Biyar sannan Beebah ta sake haihuwar yaronta namiji yaci Sunan Mahaifin
Beebah wato Muhammad kasancewar bayan musuluntarsa cewa yayi akirasa da Muhammad.
_Tammat bih hamdullah_
_Wannan littafi Mai farin jini nan na kawo karshensa kuskuren dake ciki Allah ka yafe mana ba
don halinmu ba Allah ka bamu ikon amfana da abubuwan amfanin cikinsu._