Showing 39001 words to 42000 words out of 58684 words
tayi wannan takaicin yasashi baisan sanda
ya dannawa Khausar ashar ba saboda takurawarta garesa yasan duk tanayin hakan ne don ta
kuntata zuciyarsa data Beebah kuma tayi nasara saboda kallon da Beebah take binsa dashi
kaɗai ya ishe shi hisabi. Aikam duk nacinta bai bari sun shiga Mota daya ba haka ta ta shiga tasu Khalisa gwiwa
a sage Hudah nayi mata dariya can ƙasan maƙoshi kasancewarta dama abokiyar dabinta ce
duk da ta girme mata itan sa'ar Khalisa ce.
Iya jarabar nacinsa na son yasan halin da Beebah ke ciki abin ya faskara da yake
Sallah ce gidan sarautar a cike yake da baƙi yasa bai takura ba haka ya hƙr ya shige sashinsa
yayi wanka yayi Sallah ya miƙe a gado yana saƙawa da warwarewa, baiji shigowar Najeeb ba
sai ji yayi an zauna kusa dashi ya buɗe idanunsa suka zubawa juna idanu na tsayin lkc can
Najeeb ya kawar da shirun da cewa “Meyesa Khalisa bata sona ne?"
Yunƙurawa yayi ya tashi zaune yace “Dalilin da nake ta tambayar kaina kenan Najeeb kowa ya
kasa ganewa bazan iya koyawa kaina soyayyar Khausar ba zatafi rayuwar farin ciki idan ta auri
wani ba ni ba amma taƙi fahimta kowama yaƙi fahimta Najeeb zanyi wani abu da zai tada
hankalin kowa domin da wata damuwar gara wata....." “Zuciyarka tana faɗa maka ka saketa ne?" Da sauri ya ɗago yace “Ya akayi ka san
abinda ke raina?" Fasali Najeeb yaja yace “nasanka tun bamusan kanmu ba nasan irin
tunaninka a koda yaushe Prince kuskure ne babba zaka tafka da zai tone duk wani ɓoyayyen
sirrinka, kayi saurin kawar da tunanin sakinta, tana sonka kai kuma kanason Habeebatullah
zakayi amfani da soyayyar da take yi maka ka bawa Beebah guri a gidan da zaku rayu ka bata
ƴancin mace itama, duk lkcn da tayi yunƙurin fitar da mgnr kai kuma kayi mata barazanar saki
kuyita tafiya a haka har lkcn da gsky zatayi halinta don kasani na sani ramin ƙarya kurarre ne"
Sun jima suna tattaunawa kafin su miƙe su fice a gidan kai tsaye gidan Prince Habeeb suka
nufa wato ya kashe dukiya bata wasa ba wajen tsara gidan cikin watanni bakwai akayishi aka
gama rayuwa da buri komai don Habeebansa yayishi idan ya tuna wata akeso tazo ta rayu
cikinsa ba Habeebah ba sai yaji ransa ya bakanta komai yana neman kwace masa amma da
shawarar Najeeb yaji ya samu nutsuwa ya yarda da abinda ya faɗa masa a yau yakeson
yayima Habeebansa albashir na samuwar ƴancinsu amma taƙi sauraronsa ya lura zasu rina da
Habeebah domin dukkan alamu sun nuna irin matan nan ne masu masifar kishi bata ƙaunar
taga an raɓeshi ko kaɗan to shima baso yake yaga wata mace ta raɓeshi ba itanba saidai
yanzu da dole take neman kamasu.
Washegari tun safe yakeson ganinta taƙi ganuwa har ya gaji dayi mata aike da kiranta a waya,
gashi Kilishi tanada baƙi a bangaren bakuma son yawan magana ya cika ba shine kawai ya
hanashi zuwa ya nemota da kansa.
Har dare yana jiran tsammanin ganinta amma abu ya faskara dole ya hƙr ransa na
suya haka aka kuma kwana aka yini tafi-tafi har kwana biyar ranar dai ya muttsike kunyarsa ya
nufi sashin Kilishi yayi Sa'a kuwa duk sun tafi kallon hawan ƙarshe ya haura saman ya buɗe
ɗakinta bai ganta ba ya janyo ya rufe ya buɗe ɗakin Kilishi ya ishe ta kwance a ƙasan carpet sai
juyi takeyi riƙe da ciki Kilishi nayi mata sannu.
Tsayawa yayi ya zuba musu idanu ƙasa ƙasa, Kilishi ta ɗago ta kalleshi tace “Akai
yarinyar nan asibiti Habeeb wannan fetus ɗin na wahalar da ita....." Ƙasa yayi da kansa cike da
kunya yace “Kilishi fushi takeyi dani fah ko wayata ta daina ɗagawa rabona da sanyata a ido tun
a airport"
Murmushi Kilishi tayi tace “meye kuma na damuwa akan abinda kariga kasan zai faru Ni tayimin
kyan kai ma daya kasance kaiɗin take fushi dakai bani ba Habeebah tanada kawaici kuma kishi
halal ne dole tayishi"
“Amma Kilishi....." “Amma me Habeeb ka ɗauko mota akaita asibiti nace ba dogon
surutu ba" juyawa yayi ya fita bai jima ba ya dawo ya ɗauki Beebah da take cikin mawuyacin
hali ya fice yasata a mota Kilishi ta fito ta shiga duk akan idon Hajiyan ƙofa tayi murmushi ta
juya ciki su kuma suka fice daga gidan suka nufi Emirates Hospital ɗin aka bata gado suka fara
bata kulawa.
Haka ta kwashe kwanaki biyu a asibitin anata shagalin ɗaurin auren ƴaƴan gdan sarautar
itakam ta kanta kawai takeyi ranar da aka daura wannan aure Habeeb kamar mace haka ya
rinƙa kukan baƙin ciki itako Khausar har kyautar mota tayi saboda farin ciki burinta ya cika ta
samu muradin zuciyarta itakam Beebah baiwar Allah tanacan a kwance a gadon asibiti Kilishi
da ƴaƴanta da uban gayyar na bata kulawa, ji yake kamar ya cire ciwon ya dawo dashi kansa
duk ya susuce.
Duk da damuwar dake damun Najeeb ta watsin da Khalisa takeyi dashi amma yafi tausayin
abokin nasa saboda yasan yafishi shiga jarabawar rayuwa wacce ya kwallawa rai gata a
kwance cikin halin jinya ga kuma aure an ɗaura masa da halitta mafi bakin jini a duniyarsa.
_Idan kika karanta min littafi baki biyani ba ban yafe Miki ba, idan ka/ki karantamin littafi a
YouTube batare da izinina ba Allah ya fitarmin da haƙƙina a kanki/kanka da gaggawa_
[5/10, 8:33 PM] AM OUM HAIRAN: _*Paid book 33-34*_
_Ku biya ta acct detail 3184512451 First bank ko kati MTN ta WhatsApp number
09013718241._
_Normal 300 PC 700_
_Ban amince a juyamin littafi ta kowacce siga ba_
★★★~~~★★★~~~★★★
Abu kamar wasa Saida Beebah tayi kwana goma sha uku a asibitin sannan ta samu ƙwarin da
aka sallame ta, a zaman nan nata babu wani daga gidan sarautar da yazo dubata in ka ɗauke
Hajiyan soro da tazo itama don ta fahimci kowa ma a gidan fushi Habeeb yakeyi dashi ne kuma
ta fahimci da gaske ya damu da damuwar yarinyar fiye da yanda ya damu da kansa sannan
zuwa lkcn anyi walƙiya a cikin gidan sarautar duk wanda ya isa yasan Habeebatullah matar
Habeeb ce mai martaba ne har yanzu zancen baije masa ba yaketa sha da gwiɓa. Wani abu da yaso ya ja masu samun saɓani da Kilishi lkcn da aka sallami Habeebah daga
asibiti fir yace bazata koma Emirates House ba gdansa zata wucce domin kuwa baiga dalilin da
zaisa Khausar ta tare a cikin gidan daya gina da sunan Beebah ita kuma taci gaba da zama a
inda ba don ita aka tanadeshi ba. Kilishi taƙi yarda shikuma ya kafe itakam data gaji hakanan ranta badon yaso ba ta raka
Habeeba har Prince area inda gdan nasa yake ita kanta Beebah bata amince da wannan
hukuncin ba saidai batada mafita tunda Kilishi ta amince haka zata hƙr shikam ransa har kunne
zuciyarsa fari tas haka suka shiga gidan yana riƙe da hannun Beebah da gabaɗaya jikinta babu
ƙwari.
Kilishi ce tayi sallama babu kowa a parlourn farkon sai ƙamshi da yaketa fitarwa na amarci
Beebah ta lumshe idanunta ta sauke kan wani babban hotonta da sukayi kwanakin baya lkcn
bikin naɗin Maje Dutse, neman gurin zama takeyi ya hanata ya ja hannunta ya buɗe wata ƙofa
suka shiga parlour ne madaidaici da aka kashe masa manyan kudade wajen haɗashi sai wasu
ƙofofi biyu dake facing juna a cikinsa.
Kilishi ya kalla yace “ya kikaga gurin Kilishi?" Ajiyar numfashi tayi ta zauna tace “gurin
yayi kyau Habibu ina Khausar ɗin?" Nandanan fara'ar kan fuskarsa ta ɗauke ya bagarar da
zancen da cewa “Da alama kinajin yunwa Wyf ki kwanta naje kitchen na dafo Miki Indomie"
murmushi Hajiya Kilishi tayi ta miƙe tace “sai ayita hƙr da kai zuciya nesa zaman mata biyu
Habeeb sai ansa lura saboda abokan adawar junane ko dariya babu wacce keso taga kayiwa
wata fiye da wacce kayi mata, to nidai ina horon ka da adalci domin shine hanyar tsiranka"
Miƙewa tayi tayi musu sallama ta fice ya rakata ya dawo har yanzu baiji motsin Khausar ba bai
wani damu ba ya shige kitchen ya fara dube-dube yayi Sa'a ya tarar da shinkafa da wake ga
salat da cucumber da Bama an haɗa an yanka masa kwai gefe kuma ga soyayyen nama nan
ya taɓe baki yasan bai wucce baƙi zatayi ta girka musu ba ya kuwa ɗauki flat ya zubawa
Beebah ya haɗa mata komi ya ɗauka ya nufi part ɗin nata tana zaune inda ya barta ya zauna
yana hilatarta da hira taƙi kulawa saboda har yanzu zuciyarta bata sauka dashi ba.
Abincin kawai taja ta fara ci tana jin daɗinsa sosai rabonta da taci abinda yayi mata daɗi haka
harta manta, aikuwa taci abincin sosai sannan ta miƙe batare data kulashi ba ta nufi ƙofa ɗaya
cikin ƙofofin dake cikin parlourn, ta kuwa yi saa ta buɗe nata ta mayar ta rufe tanabin dakin da
kallo tashin farko wani ɓangare da aka jera akwatuna guda goma sha takwas ta fara bi da kallo
sannan ta sauke idanunta kan gadon da aka gyara shi yaji kayan ƙawa yayi kyau na sosai.
Ajiyar zuciya ta sauke lkcn da taji ya bude dakin ya shigo ya mayar ya rufe ya
kamota jikinsa ya janye tare da kallonsa da kallon akwatunan lumshe idanu yayi ya sake
janyota jikinsa ya haɗata da jikinsa sosai cikin sanyin murya ta bawan da yake neman tuba
gurin ubangidansa yace. “Kiyi afuwa a gareni Wyf ki daina yimin rowar kalaminki ko mara daɗi ne ki rinƙa
furtamin zan jure wlh nasan kallon da kikemin ki daina zargina ba laifina bane babu yacce zanyi
ne amma kinsani duniya ta sani ke nakeson......" Rufe masa baki tayi ta dago manyan idanunta
zatayi mgn ya toshe mata bakin da cewa “Karki ce don Allah babu amfani mu rinƙa jayayya
Beebah wasu hakan sukeson gani ki manta da komai muyi rayuwa me daɗi kinga mun samu
ƴanci inason mu raini bbynmu da kulawa"
Ƙwacewa tayi taje ta kwanta yayima Kofar key ya rage kayan jikinsa ya haura gadon tayi saurin
tashi ya cafke ta ya haɗata da ƙirjinsa ya ɗora lips ɗinsa a goshinta ta saki masa wani kuka da
ya sanyashi saurin janyewa ya zubanta idanu tanata ƙoƙarin ƙwacewa sake matseta yayi yace
“Ke wai ya kikeso nayi ne Wyf wannan wanne irin kishi ne daya hanaki tsayawa ki fahimceni ki
bani dama mu tunkari abinda ke gabanmu?" Magana takeson yi ya hanata dama saboda ya lura
sai ya saita mata tunani akansa da gaske sannan zasu daidaita idan ita taƙi fahimtarsa waye zai
fahimceshi bayan ya ɓata da kowa akanta Mai Martaba har baki yayi masa lkcn da yaji lbrn
Habeeba matarsa ce itace bamagujiyar daya hanasa aure, sunyi baram baram har yana iƙirarin
janye masa tallafi idan bai rabu da itaba shi kuma ya amince ya ajiye masa komai daya shafeshi
ya yarda ya rayu da ita, yanaji a ransa indai da ita to bashida wata damuwa.
Hajiya Kilishi ita kaɗai ta rage masa kuma ita ta haneshi yanke igiyar aurensa akan
Khausar tunda ita ce ta tona masa asirinsa itace burmawa cikinsa wuƙa, duk da yasan komai
daɗewa gsky zatayi halinta amma yaso ace shine ya tone komai in yaso komai za'ayi ayi lkcn
ya shirya. Haɗe bakinsu yayi suka rinƙa kokawa tana kuka tana tureshi shikuma yaƙi barinta kuma
yaƙi rarrashinta Saida ya rabata da komai na jikinta yaja musu bargo babu abinda ke tashi sai
shassheƙar kukanta tanayi masa magiya shikuma yaƙi sauraronta tunda ya fahimci itama bata
sauraron uzurinsa Saida yayi hani'an sannan ya ɗaga yana ajiyar zuciya.
Taja masa tsaki tare da jan blanket ta rufe jikinta tana ƴan ƙunƙuninta shidai bai kulata yayi
wanka ya shirya ya fice tare da ja mata ƙofar.
Ta daɗe tana juyi kafin ta ƙarfafa kanta ta tashi tayi wanka tayi sallar la'asar ta rinƙa jiyo
hayaniya a babban parlourn itadai ranta bai bata ta fita ba tayi zamanta a parlourn ta tana kallon
wani series Film da ake haskawa a MBC Bollywood wayarta tayi ruri ta janyota ganin numbersa
yasata ajiyewa taci gaba da kallonta tana nan kwance taji an buɗe ƙofar an shigo ta ɗago kanta
sukayi ido biyu da ƙannen mijin nata su miemie Miemie ce ta iso gareta tace “Sannu Aunty
Beebah ya jikin ya fetus ɗin mu?" Tashi tayi zaune a gajiye idanunta akan Khausar da Allah ya
sani Beebah ko kaɗan batason ganinta.
Ganin itama Khausar ɗin idanunta akanta yake yasata kawar da nata tare da cewa
“Alhmdllh Mimi ya amarci ku baku tare bane naga kuna yawo?" Murmushi miemie tayi tace “Wlh
kinsan itama Khausar rikicin aurenki yasata tarewa babu shiri kinsan ita matar cushe ba daraja
ta cika ba...."
Jin ƙanwar mijin nata na ƙoƙarin cin mutuncinta a gaban kishiya kishiyarma Beebah yasata
juyawa ta fice badon ta rasa abin faɗa ba saidon tuna kashedin da mijin nasu ya kirata yayi
mata.
Cikin ranta tana raya matakin daya kamata ta ɗauka akan wannan wulaƙanci da akeyi mata
akan macen da bata fita komi ba zama tayi ranta na suya ta rasa meye yasa dangin mijin nasu
suka rabu biyu wasu suna ƙin Beebah wasu suna ƙinta, ajiyar zuciya tayi ta kwanta tana
kwancen duk sun shigo sunyi mata sallama amma banda Miemie haka suka tafi itakam Miemie
gurin Beebah aka barta sunata hirar su har dare Mijinta yazo ya ɗauketa ya kaita gda, bayan
sallar Isha ne Beebah taji tanajin yunwa ta mike ta fito ta nufi kitchen ɗin dake babban parlourn
ta shiga, komai akwai a cikinsa hakan ya bata damar daukar doya ta fere tayi fatenta da wake
da busasshen kifi ta zubo a flat tana shirin fitowa taji an shigo ta ɗago sukayi ido huɗu ta
sunkuyar da kanta ganin yanayin fuskarsa babu walwala yasa tsoro shigarta cikin in...ina tace
“Sas...sannu da shigowa" ajiyar zuciya yayi ya karɓi abincin ya ɗauki juice din data dauko ya fita
daga kitchen ɗin cikin tsoron yanayinsa tabisa a baya suka wucce Khausar tsaye a babban
parlourn tana danne-danne da waya.
Babu wanda yace da ita itama babu wanda tacewa suka wucceta ta bisu da kallo tare da taɓe
baki, suka shiga ciki ya mayar da ƙofar ya kulle yace “Waye yace kiyi girki?" Kujera ta zauna
batare da tayi masa mgn ba ya matso gabanta yace “tambayarki nakeyi" cikin alamun ƙosawa
tace “Ji nayi inason yi" yanayin data bashi amsa yasashi ajiye mata flat ɗin ya zauna kusa da ita
ya ɗebo yakai mata bakinta ta karɓa ya sauke ajiyar zuciya yana bata yana kallonta tayi ƙasa
da idanunta yaja numfashi tare da kiran sunanta, ta ɗago idanuwanta da suka cika da ƙwallah
yasa hannu ya tallafe kuncinta yace “Idan kikaci gaba da kukan nan zaki iya sawa zuciyata ta
buga Please Wyf kiji tausayina ki daina kinji?"
Ɗaga masa kai tayi alamar eh ya ɗora bakinsa a nata yace “Ina zamuje honey moon?"
Kwantar da kanta tayi a ƙirjinsa a hankali damuwarta na yayewa tanajin wani farin ciki da
nutsuwa na shigarta, tabbas ta amince Habeeb shine duniyarta bazata iya barinsa ba....
Tunanin ya katse mata da cewa “Idan ina tare dake dukkan wata damuwa tawa takan
ɗauke na nemeta na rasa Wyf muyiwa juna halarci rayuwa mu rayu dake mu mutu tare wlh
kinyimin halaccin da babu wata mace da zata sha gabanki a duniyata ke ko a lahira nasani kina
saman kowacce mace cikin matana"
Hannu yakai ya shafa cikinta yayi murmushi yace “Zan kaiki Tsaunin gawo idan kin haifamin
Bbyna nasan ganinsa zaisa su amince ba butulce musu kikayi ba ƙaddarar rabo tasa muka
kasa control zuciyoyinmu har Saida muka mallaki juna Beebah inasonki"
Murmushi tayi wanda rabonta da tayisa har ta manta ta ɗago ta ɗora lips ɗin ta kan
nasa tayi kissing nasa tace “Nima inasonka Hero kawai idan na tuna....." Shiru tayi walwalarta ta
ɗauke kuka na neman kwace mata yayi saurin girgiza mata kai yace “Me kike tunawa?" Da
rawar murya tace “Bani kaɗai nake ikon ka ba Hero bani kaɗai ke mallakar ka ba wannan yana
saremin gwiwa inajin kamar na mutu saboda baƙin ciki komai yakanyimin baƙi harda kai, Hero
meye yasa dangin mahaifinka sukaƙi sona ne shima yaƙi sona? Meyesa bazasu karɓeni
matsayin da mahaifiyarka ta karɓeni ba?"
Zubanta idanu yayi yana murmushi