Showing 12001 words to 15000 words out of 58684 words
tayi da ƙafarta tace “na daina
sonka tunda kaima irinsu Jami ne haka sukayita sa nonon Tani a bakinsu suna matsa mata shi
da hannunsu shine kaima zakayimin to banasonka...."
Da sauri ya rufe mata baki yace “Ya isa Ni ba irinsu bane Beebah na daina kiyi shiru karki
faɗawa kowa muje kici abincin yau banga sanda kikaci abinci ba" noƙe kafada shima noƙewa
yayi ta rufe idanunta tana dariya, dariyar tata ta sashi dariya ya cafko hannunta ya zauna da ita
da lallami ya samu taci tsoka uku ganin taƙi sakewa taci a gabansa ya sashi karkacewa ya zaro
kuɗi yan ɗari biyu rafa guda ya bata yace “ki riƙe a hannun ki saboda sa kati ban yarda a kira
kowa ba bayan Ni" zaro wayar yayi da kwalayen turare ya aje mata ya miƙe ya kama hannunta
ya sumbata ya fice da sauri saboda ganin idanunta ya kawo ruwa yasan tsaf zata karya masa
gwiwa gara karma ya tsaya domin tafiyar tasa tafi zamansa muhimmanci........
*Share please*
[4/9, 6:25 PM] AM OUM HAIRAN: *BAMAGUJIYA*
*(HOT LOVE AND DESTINY)*
NA
*FAUZIYYA TASIU UMAR*
*OUM HAIRAN*
https://youtube.com/channel/UCZ5Vt2--iGyJfTwItSzAnGg
*Paid book*
Ki biya ta waɗannan hanyoyin acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko ku turo katin
waya MTN ta WhatsApp number na kamar haka 09013718241. Normal group 300, Special 700.
*Free Page 8*
★★★~~~★★★~~~★★★
Koda ya fito tsakar gdan Saida ya bawa Marka kasonta sannan ya ƙara mata wasu masu tsoka
da zata kula masa da habibansa kafin ya dawo duk da ya ƙudurce a ransa bazai daɗe ba hakan
bai hanashi jin kewar abar ƙaunar tasa ba,
Cikin ƙaramin lkc yayi sabo da ita sabon da yake jin zagawarta a cikin jininsa yanajin zuciyarta
na bugawa daidai da bugun tasa zuciyar, yana shiga masauki jakar kayansa kawai ya ɗauka
drivern campanyn simintin na mahaifinsa ya ɗauke su suka ɗauki hanyar Dutse tsakanin
Tsaunin gawo da Birnin Dutse tafiya ce ta gaske kasancewar Tsaunin gawo cikin ƙasar Kano
take a rankin wata babbar ƙaramar hukuma.
Sun gajiya lkcn da suka shiga Dutse dare yayi nisa wannan tasa ba kowa ne yasan da
dawowarsu ba, kai tsaye sashinsa ya nufa ya watsa ruwa yayi sallar magrib da Isha ya kwanta
yana hucce gajiya amma zuciyarsa taki barinsa a Jigawa ta ɗauke shi ta mayar dashi Tsaunin
gawo, hakanan ya wanzu yanata murmushi yana tunano irin wani yanayi da ya tsinci kansa
ɗazu da yana kissing kyakkyawan bakin Beebansa tabbas akwai nutsuwa a cikin kasancewa da
abinda zuci take muradi dole yayi bakin kokarinsa yaga ya mallaki Beebah bada jimawa ba ko
ya samu zuciyarsa ta samu salama.
Da waɗannan tunane² bacci ya ɗauke shi me sihirtaccen daɗi cike da mafarkin abar ƙaunarsa
cikin kyakkyawan yanayi wanda ya sanyashi jin shauƙin kasancewarsu tare aikam yana tashi da
asuba ya watsa ruwa ya sanya doguwar riga ya nufi masallacin cikin gdan sarautar sai lkcn
ƴan'uwa barori da kuyangi suka fahimci ashe autan Kilishi ya dawo Auta me dakawa maza
gumbar wuya a hannu.
Kaffatan duk wani ma'aikaci dake cikin wannan gda yana masifar shayinsa bawai don tsabar
zalumcinsa ba a'a saidai don masifar kwarjininsa ko kusa baya ɗaukar raini da wargi tun ma
yana ƙarami bare yanzu da yake jinsa sama da kowa a duniya.
Bayan idar da sallah kamar yanda al'adar gdan take Saida suka gama gaisawa da juna
ƴan'uwansa sunata yi masa sannu da zuwa yanata jin daɗi duk da kacokan hankalinsa yanaga
Mai martaba domin shine dalilin zamansa so yakeyi ya samu damar magana dashi a yau ɗin
nan. Shi a burinsa ma baya fatan maganar aurensa da Beebah ta wucce wata guda saboda ji yakeyi
kamar zai iya zautuwa idan bai sameta ba.
Mai martaba yana karɓar gaisuwa fiye da rabi na hankalinsa yanakan Habeeb tabbas da yanayi
ya fahimci ɗan nasa yana cikin damuwa domin ya rame sosai ga wani duhu da yayi kamar
wanda ya tashi daga jinya, Saida Sarki Khalil ya sallami kowa sannan yayi gyaran murya yace
“Habibullahi an dawo lfy ya aikin muna fatan komai ya tafi yanda muka tsara?"
Ƙasa yayi da kansa yace “Muna fatan hakan Allah yaja kwananka..." Shiru ce ta ɗan ratsa har
yanzu mai martaba kallonsa yakeyi can ya numfasa yace “Kayi rashin lfy ne?" Da sauri ya ɗago
yana duban kansa ashe dai da gaske Najeeb yakeyi ya rame ɗin shi rabonsa da duba madubi
har ya manta bare yaga yanayinsa. “Muna sauraronka Habibullah" abinda mai martaba ya faɗa kenan hakan ya bawa Habeeb
damar karkacewa cike da faɗuwar gaba ya lankwashe kafa kamar me neman gafara yace
“Allah ya taimakeka dama mgnr da kuka daɗe kunayi min ce ta taso game da aure...." Sai kuma
yayi shiru kamar me jin tsoron furtawa, murmushi Mai martaba Khalil yayi yace “Masha Allah ai
dama hakan muke fata Habibu naji daɗin wannan labari a ina take, ya sunanta kuma ƴar waye
a ƙasar nan sannan meye matakin karatun ta ɓangaren Islama da boko?......"
Dam gabansa ya buga kwata² ya manta da dokar gidan nasu na cewa macen aure sai
saukakkiya wacce ta karanta ƙur'ani kuma ta haddace koda uzufi talatin ne a kanta matakin
karatun boko degree sannan ba ƴar kowanne mutum ake kawowa gdannan ba sai wanda aka
san sunansa a ƙasar, itako Beebah batada komai gata ba ƴar kowa ba gata ba musulma ba
bare ayi maganar karatun Kur'ani boko kuwa ba itaba duk garinsu ma baiga wanda yayi ko
gaba da primary ba.
Wani gwauron numfashi ya sauke lkcn da mai martaba ya katseshi da cewa “ka samu a gaba
kayi mana shiru ko abin faɗarka ya ƙare ne?" “Ba musulma bace....." Ya faɗa cikin son arowa
kansa dakiya, wannan kalma ta sanya mai martaba saurin ɗagowa yace “Wht? Ya Salam
subhanallah Habeeb wannan ai zancen banza da wofi ne da bazai yiwu ba kafira kuma kakeso
zaka auro mana cikin zuri'armu don taɓewa da lalacewa...."
Da sauri ya ɗago kalmar kafirar nan na mugun taɓa zuciyarsa miƙewa Mai martaba yayi ya
saɓa babbar rigarsa ya nufi hanyar da zata fitar dashi daga masallacin Habeeb yayi saurin
miƙewa yasha gabansa ya zube yace “Kayimin rai ka fahimceni wlh Mai martaba inason
Habeebah itama tanasona nasan zata iyayin komai donni bana ko tantama zata musulunta duk
abinda ake nema zata samu nidai burina ku yarda na aurota Allah ya taimakeka ka taimaka min
wajen wannan jihadin wlh saboda Ni Beebah har gdan iyayenta ta bari yanzu haka tana gdan
Sarkin garinsu....."
Ɗaukeshi da mari Mai martaba yayi ya nunashi da yatsa zaiyi mgn takaici da bakin ciki ya
hanashi iya cewa komai ya fice da sauri daga masallacin ya sake binsa yana masa magiya bai
saurareshi ba ya shige sashinsa ya datso ƙofarsa take Habeeb ya zube a gurin zuciyarsa na
tafasa tabbas wannan shine ake cewa yaƙi saida uwa shikam baiga laifinsa ba cikin son
farantawa zuciyarsa na auren Beebah ba kuma baiga dalilin da zaisashi janyewa daga ra'ayinsa
a faɗin duniyar nan ba.
Da wannan ya juya ya koma ɗakinsa ya rinƙa zagayashi yana dukan iska zuciyarsa tana masa
wani mugun tuƙuƙi daya kasa samawa sassauci.
Wanka yayi ya sanya kayansa ya nufi cikin gdan fuskar nan kamar hadari saboda damuwar
dake danƙare a ƙasanta Saida ya shiga ko ina suka gaisa yanayinsa yasa babu wanda ya
tankasa sunsan yanzun rai zai ɓaci, ɓangaren Kilishi ya nufa ya ƙwankwasa ƙofar tana zaune
saman sallaya da ƙur'ani me tsarki a hannunta tana muraja ya shigo ya samu guri ya zauna ta
dubeshi ta mayar da hankalinta ga karatun ta.
Saida ta ida inda takeson tsayawa sannan ta ɗago ta dubeshi tace “Autan maza Ina ka shiga ne
tun jiya naji lbrn dawowarka sabanin ko yaushe baka zomin ba" ajiyar zuciya yayi ya ɗago
idanunsa sun kaɗa sunyi jawur ya sauke ajiyar zuciya da tasa gaban Hajiya Kilishi faɗuwa tace
“naga ta kaina Ni Ummusalma Habibu na meye ya sameka ne naganka a ɗefare a lalace kamar
kayi jinya?"
Sunkuyar da kansa yayi yana wasa da yatsansa ta kafesa da idanunta tana mamakin ramar
ɗan nata tace “Habibu! Ɗagowa yayi ga mamakinta sai taga hawaye sharrrr a idanunsa gabanta
ya faɗi tace “Ina dalilin hawayen?" Numfasawa yayi taja fasali tace “to tashi kaje bazakazo ka
tayarmin da hankali ba bayan bankai sanin damuwarka ba...." Saurin ɗagowa yayi yace “Ba
haka bane Hajiya kawai dai ina tsoron kema kada kiƙi fahimtata kamar yanda mai martaba yaƙi
tsayawa ya fahimceni ne!"
Murmushinta na Dattaku tayi tace “Habibu kenan ai indai kaga ban fahimceka ba to yanayin da
kazo dashi ne baiyi daidai da a fahimceka ba maza ina sauraronka" numfashi ya sauke nan ya
zayyane mata komai taja wata ajiyar zuciya me ƙarfin gaske tayi kasaƙe tana tunana wannan
gingimemen aikin da Habib ya kinkimo duk da bataji taƙi abin a ranta ba duba da dalilin daya
zayyana mata amma ta hango hargitsi na gaske a tafiyar tabbas kafin aci Zomo sai anci gudu
tunda mai martaba yaki fahimtar Habeeb to batasan kuma waye zai samu nasarar fahimtar
dashi ba, tunda yaki wannan lamari bataga wanda zaisa yasoshi ba saidai in Allah yayi to
ikonsa sai yasa ya rusuna yabi ko bayaso.
Sosai jikin Habeeb ya ƙara sanyi lakwas yace “Hajiya kinyi shiru don Allah kice kuma kisa
albarka da bakinki me albarka inada tabbacin indai kika yarda kuma kika bani goyon baya Allah
zai amince kuma zamu samu lada in har Habeebah ta yarda ta karbi addinin Musulunci Hajiya
ki duba ladan da zaki samu ki aminta ki cire kokwanto"
Taguminta ta janye ta ɗago ta zubansa idanunta tayi masa murmushi na karfafa gwiwa tace “Na
baka goyon baya Habib kaje ka nemi auren Habibah ka aurota ku rayu cikin aminci amma fah
ina horon ka da kabi komai a hankali Kuma kayiwa mahaifinka biyayya shine kawai zaisa
nasarar ka ta ɗore"
Numfashi yaja cikin jin daɗin wannan nasara daya samu gurin mahaifiyarsa yayi mata gdy
yanajin wani haske ji yake yama samu Habeebah ya gama, da wannan ya miƙe ya fice daga
gdan ya nufi gdan babban yayansu da yake da yakinin idan ya samu Mai martaba da mgnr zai
ɗauketa seriously ya ishe shi yana shirin fita gurin aiki suka gaisa tare da nufar office din tare
suna tattaunawa akan abinda ya shafi fam ɗin nasu.
Bayan sun huta komai ya lafa ne Alh Ahmad ya dubi Habeeb yace “Kace kanada mgn dani
Habeeb ina sauraronka" sosa kansa yayi sannan yayi masa bayanin komai Alh Ahmad ya ɗago
yanayi masa kallon bashida hankali yace “Wannan shine tabbatar da har yanzu lissafinka ba
daidai yake ba tunaninka ya goce nikam bazan iya shiga maganar nan mara yiwuwa ba mai
martaba yaci mutuncina gara kai dama kaine ka siyawa kanka da kanka, Habeeb idan shawara
kake nema nikam ina baka shawarar ka hƙr da wannan aure da kakeson yi kazo ka zaɓa a
matan Fam ga ƴammata nan duk sun gama karatu wasu ma daga wasu ƙasashen suka dawo
amma kai kasan ba'a fara ba kuma bazaa fara akanka ba Bamagujiya Habeeb haba wannan
faɗuwar daraja tayi yawa da yawa to ka a musulmi Mai martaba baya aminta da ƴar talaka bare
kuma ƴar maguzawa......"
Miƙewa yayi ya dauki wayoyinsa ya zuba a aljihunsa ya fice daga office ɗin da takaicin meye
yasa ma zuciyarsa ta raya masa yazo gurinsa bayan ba mafita zai bashi ba? Tsaki yaja ya nufi
inda yayi parking motarsa ya shiga yaja ya fice daga harabar ma'aikatar.
*Share please*
[4/11, 7:44 PM] AM OUM HAIRAN: *BAMAGUJIYA*
*(HOT LOVE AND DESTINY)*
NA
*FAUZIYYA TASIU UMAR*
*OUM HAIRAN*
https://youtube.com/channel/UCZ5Vt2--iGyJfTwItSzAnGg
*Paid book*
Ki biya ta waɗannan hanyoyin acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko ku turo katin
waya MTN ta WhatsApp number na kamar haka 09013718241. Normal group 300, Special 700.
*Last Free Page 9-10*
★★★~~~★★★~~~★★★
Bai koma gda ba sai yamma koda ya fito daga ma'aikatar yayan nasa tasu ma'aikatar ya nufa
amma abin arziki ya kasa hassalawa sai juyi da yake a kan kujera wayar Beebah yaketa kira
taki tafiya duk damuwa tabi ta cunkushe masa zuciya sai bayan magrib ya nufi gdan babu wani
karfi a jikinsa saina imani wanka yayi yana shirin fita Masallaci sallar Isha wayarsa tayi ruri ya
ganin number Mai martaba yasashi haɗa nutsuwarsa ya daga Mai martaba yace “in ka dawo
kazo inason ganinka" amsawa yayi tare da fita yaje yayi Sallah sannan ya nufi kiran na Mai
martaba ya shiga da sallamarsa yana zaune saman shimfiɗun Kilishi da farin tabarau a
idanunsa ya amsa sallamar Habeeb ya nemi guri ya zauna yace.
“Allah yaja kwana gamu mun amsa kira" ɗagowa yayi yayi masa murmushi ya miƙe ya saita
zamansa yace “Am dama wani babban uzurine ya taso munason zamu haɗa gwiwa da wani
campany dake Japan domin haɓakar masana'antunmu" jinjina kai Habeeb yayi yace “hakan
yayi Allah ya taimakeka hakan zai kawo ci gaba ƙwarai" murmushi Mai martaba yayi yace
“shiyasa nakeson ka Habibullah to dama ba komai bane yasa na kiraka campanyn sun buƙaci a
tura mutum ɗaya daganan domin yaje yayi course na yanda ayyukan suke kasancewa kamar
yanda suma zasu turo nasu wakilan don faɗaɗawa juna fasaha.
Na duba naga babu wanda ya dace da wannan tafiya saikai duba da kwazonka da basirar ka
saboda haka kaje ka fara shiri nan da sati biyu zaka tafi in Allah ya yarda...."
Tunda Habeeb yaji ƙudurin Mai martaba gumi yake karyo masa yasan tabbas da manufa cikin
wannan shiri, a sanyaye ya ɗago ya buɗe baki zaiyi mgn Mai martaba ya ɗaga masa hannu
yace “banason kace komai kaje Allah yayi maka albarka shekara ɗaya ne babu yawa idan Allah
ya amince kafin lkcn zan sama maka matar data dace dakai na aura maka na turota tunda na
fahimci yanzu hankalinka ya hadu kana buƙatar auren" a kasalce yace “Habeeban fah ranka ya
daɗe...." Shiru mai martaba yayi masa shi kuma ya kasa tashi jikinsa har rawa yake saboda
tashin hankali bai iya jurewa ba yace “Na rantse da Allah bazan iya zama da duk wacce zaka
aura min ba Allah ya taimake ka indai bazaka amince nayi jahadin janyo Habeebah daga duhun
kafirci zuwa hasken musulunci ba idan bazaka amince min na rayu da abinda raina da zuciyata
suke muradi ba to ina roƙonka da kayi hkr ka barni na ƙarasa rayuwata ni kadai kamar yanda na
shirya yinta a baya...."
Tsawa Mai martaba ya daka masa yana huci yace “Ni Habeeb Nine nake faɗa kake faɗa harma
na zartar da hukunci kace baka amince ba lallai ya tabbata ka girma kakai shiyasa har kake
jayayya dani akan kafira, to na rantse da Allah kaji dai kuma ka sani bana saurin rantsuwa akan
lamarin rayuwa to nayi akan wannan yarinyar indai kaga ka aureta to kodai ka canza uba ko
kuma bana numfasawa, tashi ka ficemin a daki kafin na nakasaka"
Tsuma jikin Habeeb yakeyi saboda ɗimuwa da gigita rantsuwar mahaifinsa tayi mugun girgiza
shi Shikenan ta faru ta ƙare Mai martaba ya gama yanke hukunci yanzu babu bakin da zai iya
fahimtar dashi ya gane...."
Sashin Hajiya Kilishi ya nufa da ƙannensa biyu mata da suke ciki ɗaya da sauran matan gdan
duk suna babban falon suna kallo yazo ya shigesu ya nufi ɗakin mahaifiyarsa ya faɗa kan
gadonta saboda mugun sanyin da yaji yana keta ƙashinsa yaja bargo ya rufa.
Kallon kallo sukayi Hajiya Zulai ta dubi Hajiya Kilishi da Hajiya Hauwa tace “Salma?" Dubansu
Kilishi tayi tace “Naam Zulai" Hajiya Hauwa ce tace “Soja ƙalau kuwa?" Numfasawa tayi tace
“da alamun ba ƙalau ba wato ɗebowa yayi da zafi aure yakeson zaiyi kuma ba musulma bace
yarinyar da yakeson aure, nikam na fahimceshi kuma na bashi goyon baya to amma fah tunda
mai martaba bai fahimta ba babu wanda ya isa ya fahimtar dashi"
Miƙewa Hajiya Zulai tayi ta nufi ɗakin tace “Babana komansa daban banda rigima irinta tarar
aradu daka inashi ina kafira matsayin mata...." Tana faɗin haka ta bude dakin ta shiga yanda taji
gadon na rawa yasata nufarsa da sauri ta yaye bargo tace “Innanillahi Ni Zulaihatu Babana
meye hakan kuka kamar wani ƙaramin yaro...." Tashi yayi zaune ya kama hannunta yace “Don Allah ku ceci rayuwata ku faɗawa mai martaba
zanje Japan ɗin amma ya barni na auri Beebah Hajiyan soro bazan iya taɓuka masa komai ba
indai ya rabani da Beebah nasan itama bazata iya rayuwa babu Ni ba"
Numfashi taja tace “Akan mace kakeson kashe kanka dubi fa yanda kake rawar sanyi Habeeb
yanzu waye kake tunanin zai iya tunkarar mahaifinku yace zai fahimtar dashi?"
Hajiya Kilishi ce ta cafe da cewa “kaje inda ya umarce ka kayi masa biyayya insha Allahu zaka
dace idan kace zakaja yaja kaine zaka faɗi ƙasa" zama sukayi sunata rarrashinsa shikam
banda zafin jiki ma babu abinda suke ƙara masa kafin wane wannan zazzaɓi me zafin gaske ya
lulluɓeshi Hajiya Kilishi ta shiga damuwa tabbas bada wasa Autan mazan nata ya ɗauki lamarin
ba da gaske yakeyi don duk abinda yasa a ransa har yakai masa jinya to ya isa kallo.
Ranar sai ɗakin tabar masa bayan likita ya duba shi baccin wahala ya ɗauke shi zuciyarsa taƙi
samun sukuni
Washegari da asuba ya duba wayarsa ya zabura ya tashi zaune yana latsa wayar bugu biyu ta
daga cikin muryarta me cike da gajiya da kasala tace “Tunda ka tafi nake kiran ka naji ko kun
sauka lfy bana samu ɗan birni ina fatan lfy kake..." Wata gwauruwar ajiyar zuciya ya sauke yace
“kamar bakida lfy meye yake damunki?" Kukan da ta kwana ta nayi shine