Showing 54001 words to 57000 words out of 58684 words

Chapter 19 - BAMAGUJIYA HAUSA NOVELS BY OUM HAIRAN.pdf

17 Nov 2025

116

yace “Bro wake ba lafiya?" Kallon
Habeeb Wali yayi yace “Gashinan abokina ne da nake baka labari munyi karatu a Oxford dashi
ya fara karantar harkarku mahaifinsa Sarkin Dutse yasa ya juya zuwa ɓangaren mu kaganshi
nan ciwon soyayya ne ke wahalar dashi ko kunada maganin matsalar?"
Murmushi Dr Amin yayi yace.




“Turƙashi lamari ya ɓaci kenan ciwon so akwai wahala Nima gashi ina neman faɗawa a karo na
biyu duk da dai inata kwaɓar zuciyata kada ta shigar dani inda bazan fito ba" yana maganar
yana gwada BP ɗinsa ya dubeshi da sauri yace “Ya Salam Engineer ka rage wannan damuwar
kaga yanda BP naka yayi sama kuwa? Gaskiya ka rage damuwar komai zai wucce insha Allahu girgiza kai yayi ya sharce hawayen
dake ƙoƙarin zubo masa yace “Kayi aikinka kawai babu wani abu da zai iya rabani da wannan
damuwar sai dalilinta" daga haka bai kuma cewa komai ba Dr Amin ya gama rubuce rubucensa
ya bawa Wali ya juya yana cewa “Ka kula da kanka Please akwai yanayin hauhawar jinin da ka
iya haifar da komai Allah ya shiga lamarin" amsawa Wali yayi suka fita tare har asibitin suka
sayi maganin sannan ya juyo yana mamakin yanda yayan nasa bashi labarin yanda akayi ya
sami petiant ɗin tasa da ya dauki kulawar duniya ya ɗorawa.




Komawa yayi tare da yima Habeeb bayanin magungunan ya karɓa ya zubesu Saida ya takura
masa sannan yasha maganin yaci gaba da jinyar jikinsa tare da baza cigiyarta jaridu talabijin da
rediyo duk da kasancewar Amin ɗan nacin karanta jaridu kwana biyun yanayin jikin Beebah da
kuma rashin lokaci yasa baisan wainar da ake yi toyawa ba. A haka Beebah Saida ta shafe kwanaki arba'in a asibitin tana jinyar ƙafarta sannan taji sauƙi

sosai lokacin kuma cikinta ya fara bayyana sosai abinka da itan ba doguwa bace sosai shi yasa
cikinta baya ɓuya watanni biyar kowa na iya ganinsa, Dr Amin dakansa ya yankar mata katin
files na awo a asibitin sai lokacin ne ya fara tunanin ta yanda zaijewa da Safeenah maganar,
koda ya tunkareta tayi masifar bashi mamaki yanda ta nuna ai babu komi ya kawota su zauna
har zuwa lokacin da zatayi bayanin daga inda take ita da kanta take cewa dashi yarinyar ta bata
tausayi daga ganinta wartako akayi daga gidan mijinta kodai asiri ko kuma bakin ciki ya hanata
faɗar daga nahiyar da take.




Yaji daɗi sosai a ranar kuwa Beebah ta dawo gidan da zama Safeenah nata bata kulawa
musamman dataga cikinta ya fara tsufa haka tayita zolayarta hardai ta saki jiki sukaci gaba da
rayuwarsu a gidan gwanin ban sha'awa babu hantara bare kyara duk da cewa zuciyar Beebah
na gurin ɗanta da mijinta amma haka take daurewa saidai idan kewarsu ta dameta ta shige ɗaki
tayi kukanta ta ƙoshi idan Safeenah ta ganta ta rinƙa bata hƙr daƙyar Safeenah ta samu Beebah
ta bata labarin abinda ya fito da ita daga gidan mijinta sosai Safeenah ta kaɗu da jin wannan
mugun makirci ta tausaya mata taso ta faɗawa Dr Amin amma fir Beebah taƙi barinta ta rinƙa
roƙonta tabarshi batason komawa gidan Habeeb akanta abubuwa da dama sun faru dashi gashi
har mahaifinsa yanajin ta cancanci ya ari bakinsa ya saketa.
Ajiyar zuciya Safeenah tayi tace “Shirme ne kawai da ɓacin rai ai Shari'a ce kawai take da ikon
sakarwa mutum mata shima kuma sai idan ya amincewa hakan, Beebah har yanzu kinanan
matsayin matar mijinki kawai dai basu iskar yanada amfani amma dai don Allah karki azabtar da
bawan Allah ki daina cewa bazaki komawa aurensa ba yayi don ke basani kema kinyi dominsa
kiyi hƙr ki bayyana masa inda kike ko ya samu sauƙin damuwa kada kiyi kisan rai"



Batajin wannan magiyar abubuwa da yawa suke sata ƙin saurarar Safeenah idan ta tuna ta
rabu da komai saboda Habeeb ta rasa komai sabodashi ta zaɓeshi fiye da iyayen da suka
kawota duniya tabarsu tabisa amma ta kasa samun mafaka a gurinsa ɗan da takejin shine raba
gardamarta shima sun karɓe sun barta batada tsuntsu bare tarko. Takanyi kukan nadama da tunanin ta yanda zata tunkari iyayenta.
Kwanaki sukayita tafiya cikinta na tsufa har ta shiga kwanakin haihuwarta kullum sai sun fita
motsa jiki Allah kuwa ya kawo mata haihuwar da sauƙi a gida ta haifi yarinyarta mace cikin dare
ita kaɗai a ɗaki.




Sai bayan haihuwar ta kira Safeenah ta sauko tazo taga abin mamaki ta koma da gudu ta taso
Dr Amin dakansa ya gyara yarinyar suka gyara maijego Safeenah ƙin komawa saman tayi ta
zauna a gurinsu.

Karon farko taji tanason sanar dashi abinda ya shafeshi wayarta ta dauka ta latso number sa ta
rubuta masa gajeren saƙo kamar haka.
_“Inayiwa Mijina fatan alkhairi da nasara akan duk abinda yakeyi yanzu, ina mai farin cikin
sanar dakai yau ajiyar ka ta fito mun samu ƙaruwar ƴa mace....."_
[5/24, 8:42 PM] AM OUM HAIRAN: _*BMGJY Bonus 49-50*_


_Ku biya ta acct detail 3184512451 First bank ko kati MTN ta WhatsApp number
09013718241._
_Normal 300 PC 700_
_Ƴan Niger zaku biya 500f ta wannan number +227 95 04 58 22_


_Ban amince a juyamin littafi ta kowacce siga ba._



Tana gama rubutawa ta karanta tare da tura masa sannan tayi maza ta kashe layin.
Habeeb dake kwance saman kujera three sistar yaji shigowar saƙo kamar bazai buɗe ba ya
gyara kwanciya, zuciyarsa taƙi nutsuwa ya ɗauki wayar ya buɗe saƙon baisan sanda ya tashi
tsaye ba yana duba saƙon number babu suna ya sake duba saƙon yace “Habeebatullah kenan?
Kece kika turomin saƙo?" Da sauri ya fara kiran layin abin takaicin ta riga ta kasheshi wannan tasa shi zama daɓar tare da
dafe kansa yana furta Innanillahi wa inna ilaihirraji'un sake gwada wayar yayi har zuwa lokacin a
kashe ransa ne ya fara faɗa masa to ko ta koma Tsaunin gawo ne?
Da wannan tunanin ya tashi ya zari key na mota ya fice daga dakin komawa yayi ya zauna tare
da duba agogo 3:20am yasani koda yake motar kansa ce ba ƙaramin ƙalubale zai fuskanta a
garin Abuja kafin yace zaije Kano daga Kano ya ɗauke hanyar Tsaunin gawo kwanan zaune
yayi asubar fari zakara ya bashi saa ya ɗauki hanya wajen goma ya isa Kano ya ɗauki hanyar
Tsaunin gawo lokacin daya isa duk maza suna gona.




Jumme ya tarar tana shanyar ganyen albasa ya tsaida motarsa ya fito tana ganinsa ta nufi gida
da sauri ya bita tare da cewa “Barka da safiya Mama!" Tsayawa tayi ya rusuna ya gaisheta, cike
da kunya irin tasu ta mutanen karkara ta amsa ya sosa kansa yace “dama Habeebah nakeson
gani...." Da sauri ta juyo tace “Tana ina ɗannan Nima ita nakeson gani" Wani abu yaji me nauyi ya saukowa ƙirjinsa daƙyar ya miƙe tsaye ya koma cikin motarsa ya
kira wani yaro ya zaro kuɗi da baisan adadin su ba ya bashi yace yakaiwa Jumme ya tada
motar yabar ƙofar gidan baiyi nisa ba ya tsaya ya ɗora kansa bisa sitiyarin motarsa ya lumshe
idonsa hawaye suka fara sintiri Mai Martaba ya cutar dashi duk shine yaja masa amma yanzun
wai dashi yake fushi saboda ya sakar masa zaɓin nasa.

Ajiyar zuciya yayi tare da tada motar ya koma cikin garin Kano anan ya samu wani hotel ya
sauka ya huta yana kwance wayar Wali ya shigo yana gani amma ya kasa ɗagawa saboda
ransa a cushe yake kalma ko ɗaya bayajin zai iya furtawa me amfani.




Kira na biyu ne ya sashi ɗagawa Wali yace “nazo gdanka bakanan ina kaje?" Buɗe idanunsa
yayi cikin gajiya yace “ina Kano" amsawa Wali yayi yace “Ok dama inason ka rakani gidan
Al'Amin ne" a yatsine yace “
Ko kwanaki kace nazo muje nace maka banida interest akan hakan so waima meye Ni sai ka
rinƙa jana gidan matan aure?" Murmushi Wali yayi ya riga yasan halin izza da son isa irin ta
Habeeb shiyasa yace “Allah ya huci zuciya dama Ahmad abokinka ne ya dameni tun jiya nazo
naga bbynsu ƙanwar Mamansu ce dake zaune a gidan ta haihu shine dake naji kace kanason
zuwa ka gaisa da Ahmad na sanar dakai"
Numfashi ya aje yace “ok kaje inna dawo ka rakani tunda Ni yanzun saina shiga Dutse zan
wutto nan" sallamewa sukayi ya tashi ya fara shirinsa ya ɗauki mota sai dutse koda yaje bai
saurari mai martaba ba sashin Kilishi ya shiga suka gaisa cikin watanni biyar ɗin duk ya rame
ya susuce sai ido da hanci kawai taja fasali tace “Meye yasa bazaka fawwalawa Allah komai ba
Habeebullah ubangiji ba da kansa yake cewa (ashe haka zan barku kara zube? Shin bazan
jarabceku ba?) Habeeb Allah nason bayinsa masu haƙuri da fawwala masa komai daya
shafesu" hawaye ya share ya miƙe zai bar wajen ta riko hannunsa tace “meye ne?" Ƙasa yayi
da kansa




Yace “Ta haihu Kilishi yanzu Shikenan yarinyata bazata Sanni matsayin ubanta ba?" Da sauri
Kilishi tace “Habeeban? Yaushe ta haihu ina kaji kai ya akayi ka sani???" Ta jero masa
tambayoyin cike da ruɗewa ya kawar da kansa yace “yau da asuba naga saƙonta kuma tun
lokacin nake kiran wayar taƙi shiga" jinjina kai tayi tace “To a bibiyi number mana ai za'a gano
daga inda ta rubuto saƙon" sosai yaji daɗin shawarar Kilishi domin da gaske ya manta da ana
wani bibiyar number waya don gano daga inda ake amfani da ita.
Fasa shiga ɗakin nasa yayi ya fito ya kira Najeeb tare suka yini a campanyn layin wayar ba
ƙaramin al'ajabu Habeeb ya shiga ba da akace masa Beebah tana garin Abuja inda tayo test
ɗin ne suka kasa ganowa saboda layin ba akan waya yake ba.
Jikinsa har ɓari yakeyi da aka sanar dashi inda take ashe zuciyarsa ce a gurin shiyasa ya kasa
barin Abuja ko zaman London ya kasa ko yaje baya jimawa yakejin hankalinsa ya dawo Abuja.




A ranar bai kwana a Dutse ba ya wucce Abuja ya nemi Wali yayi masa bayanin komai shima ya

cika da mamaki nan suka kuma ɗimawa suka fice domin Habeeb ya hanashi kwanciyar hankali
gani yakeyi suna fita zasu ganota.
Haka suka shafe kwanaki suna jigilar nema abu kamar wasa sai gashi sun ɗauki kusan sati.
Ranar wata asabar tun safe suke zaga gari yamma suna zaune cikin wani garden Habeeb ya
kifa kansa saman tables ɗin abin duniya yabi yayi masa zafi, wayar Engineer Wali tayi ring ya
zarota a aljihunsa tare da manna ta a kunnensa suka gaisa yace “kace zakazo taron raɗin suna
kuma banganka ba" numfashi ya sauke yace “kayi afuwa abune yayi yawa Wlh amma bari
yanzu mu taho dama muna ta arear taku" kallonsa Habeeb yayi kamar yace bazashi ba Wali
yace “karkace komi don Allah inci wannan arzikin Dr Amin yafi ƙarfin haka a gurina"




Tashi yayi suka nufi mota daga inda suke zuwa gidan Dr Amin babu nisa suna isa suka ishe Dr
Amin ya fito raka baƙi suka gaisa yayi musu jagora zuwa parlourn baƙin aka cika musu gabansu
da abinci Habeeb dai tsakurar abincin kawai yakeyi Dr Amin ya kira wayar Safeenah yace “A
kawo ma su Engineer Wali Ummusalma su sanya mata albarka" Habeeba dake zaune saman
gado Safeenah ta duba tace.
“Kanin Dr ne yazo ki kai musu Bbyn su ganta" itadai Beebah hakanan taji gabanta na faɗuwa, ta
jima bata tashi ba Saida Safeenah ta matsa sannan Beebah ta tashi ta fito daga dakin ta ɗauki
kwalliya ta ban mamaki sai sheƙi takeyi.
Nufar ɗakin bakin tayi idanunta na kan Ummusalma.




Ta shiga dakin tare da sallama yana ganinta ya miƙe da mugun sauri ya fara nunata da yatsa
itama ɗagowar da zatayi tayi tozali dashi ta sake ware injin idanunta akansa tace “Hab...
Habeebullah....." Saurin juyawa tayi da mugun gudu zata fice a dakin yayi wani kukan kura ya
cafkota cikin tsananin farin ciki ya kira sunanta sai hawaye sharrrr a ijiyarsa itakam itama
zamewa tayi ta zauna a ƙasa ta rungume Ayyana mikin ciwon dalilin nesantata dashi yana dawo
mata sabo ta rushe da kuka me ciwo tare da rungume Ayyana ƙam a ƙirjinta.
Tausayin kansu yaji ya ƙara nunkuwa a zuciyarsa ya zauna yana share hawayen idanunsa yace
“Bantaɓa....." Saurin ɗaga masa hannu tayi tace “Don Allah kada kacemin komai Habeeb basai
ka sanar dani halin da zuciyarka ta shiga ba saboda yanayinka ya nuna hakan idan kace zaka
sanar dani zaka cusamin tausayinka a lokacin da tausayin bazai mana amfani ba nasan
kanasona ka rayu dani a ranka tsayin shekaru ka zaɓi rabuwa da manyan jigogin rayuwarka
saboda ni so amma hakan ta gaza samuwa kayi ƙoƙari inada yaƙini bazan taɓa maye gurbinka
ba....."

Yanda ya ambaci sunanta da ƙaraji yasata miƙewa yakai hannunsa zai karɓi Ayyana ta janye
har zuwa lokacin idanunta hawaye yake zubarwa yace “Meye yasa zaki hanani ɗaukar jinina"
girgiza kai tayi tace “Ba jininka bace" daga haka ta nufi hanya ta fice daga dakin da sauri tanaci
gaba da kukanta me taɓa zuciya. Safeenah data rako baƙi ta tsaya da mamaki tace “Beebah...."
Bata kulata ba ta shige daki ta faɗa gado ta rushe da kuka me sauti tana cewa “Na shiga uku Ni
Habeebah ya akayi Habeeb yasan ina garin nan har ya biyoni maɓoyata?"
Safeenah ce tace “Waye shi?" Ɗagowa tayi a gajiye idanunta ya kaɗa yayi jajir tace “Shine
wanda nake baki labari mijina a baya uban ƴaƴana, Maman Ahmad nasan mijina yana sona
amma inajin kamar mun rabu kenan"
Girgiza mata kai Safeenah tayi tace “ ba zaku rabu ba zakuci gaba rayuwa fiye da baya me daɗi
kuma kyakkyawa bari naje naga meye ke faruwa Beebah har abada Habeeb naki ne"




Ficewa tayi daga ɗakin ta nufi ɗakin baƙin ta zubawa Habeeb idanu babu ko tantama ga kama
nan a fuskar Ayyana.
Miƙewa sukayi dukkansu Dr Amin da jikinsa ya jima da yin sanyi tausayin Habeeb ya cika
zuciyarsa tabbas Habeebah ta cancanci soyayya a gurinsa shima ya cancanci ta soshi ashe
shiyasa kullum take cikin damuwa, hawayen Habeeb ya share yace “Insha Allahu zaka rayu da
matarka da yaranka wannan abu duka ya faru ne a cikin gaibu sama da watanni biyar Beebah
take gdana take zaune da iyali na nasani Tanaji da ganin mutumcin Safeenah ita kaɗai ce zatayi
maka aikin rarrashin zuciyarta nasan zata sauko"
Kallon Safeenah yayi yace “Mijinta ne kije ki ɗauki masa ƴarsa ya ganta ashe Ummusalma ɗin
da ta zaɓawa yarinyar sunan surukarta ne" fita Safeenah tayi ta dauko Ayyana ta dawo ta
miƙawa Habeeb ya rinƙa zuba musu hoto shida yarinyar don a yau yakeson zuwa ya dauko
Kilishi tazo taga takwararta tunda yasani yanzun ko giyar wake yasha bazaice zai ɗauki Beebah
yakaiwa Kilishi ba duk da alamu sun nuna cikin waɗanda ta riƙe a ranta babu Kilishi.




Kuɗi ya zara masu nauyi ya bawa Safeenah yace a bawa Beebah kafin yawo sukayi sallama
suka tafi zuciyar Habeeb wasai yau yaga abar ƙaunarsa, suna zuwa gidansa ya haɗa kayansa
yace da Wali yakaishi airport yau ɗin nan Dutse zai kwana.
Bakwai ya shiga gdansu ya tarar da kowa a babban parlourn ciki harda Khausar tana durƙushe
gaban Sarki Khalil tana kuka.
Bai sauraresu ba ya wuce zuwa ɓangaren mahaifiyarsa tana ganinsa tace “Ya kiraka kenan?"
Dubanta yayi da rashin fahimta yace “Wa ba?" Kawar da zancen tayi tace “Ina labarin ƴata da
jikata" fara'arsa ya faɗaɗa yace “yau naga Zuciyata taganni saidai taƙi aminta dani Kilishi Kinga
shaida" nan ya fara nuna mata hotunan ta rungumeshi tana dariya tace “Alhmdllh Ya sunan
Bbyn?" Shafa kansa yayi yace “yau da yamma yayan abokina Engineer Wali wato Dr Amin ya
kiramu ana suna a gidansa ƙanwar matarsa ta haihu muka tafi domin tayasu murna shine ya

kira matarsa domin ta kawo mana Bbyn abin mamaki sai ga Wyf ɗauke da wannan kyakkyawar
yarinyar tana ganina ta kira sunana na mike, amma fah Kilishi Wyf ta sanar dasu Ni mijinta ne a
baya banda yanzu inda Ni kuma nayi musu bayanin komai yanzu dai sun bani hƙr sunce zasu
tausheta" [5/25, 3:12 PM] AM OUM HAIRAN: _*BMGJY Bonus 51-52*_


_Ku biya ta acct detail 3184512451 First bank ko kati MTN ta WhatsApp number
09013718241._
_Normal 300 PC 700_
_Ƴan Niger zaku biya 500f ta wannan number +227 95 04 58 22_


_Ban amince a juyamin littafi ta kowacce siga ba._


_End! End!! End!!!_



Tunda Habeeb yabar garin Abuja yabar Safeenah da Dr Amin da rikicin Beebah don gabaɗaya
ta rikice musu cikin kwanakin batada wata walwala indai kaga tana dariya to ba'a sako mata
zancen Habeeb bane da zarar anyi mata zancen shi zata haɗe rai ta fara kumbura ga Safeenah
da nacin magana ta rinƙa nuna mata damuwarta da lamarin Habeeb kenan har sai taga ta ƙosa
tana shirin tashi tabar gurin sannan zata ƙyaleta.
Abin da yake bawa Safeenah mamaki bai wucce yanda tasha kama Beebah tana kuka ko kuma
cikin bacci taji tana ambaton sunan Habeeb ɗin ba amma kuma a zahiri idan akayi mata
batunsa sai walwalarta ta ɗauke, to yauma kamar ko yaushe tana zaune a ɗaki ta gama yima
Ayyana kwalliya tana taje mata gashinta taji Muryar Safeenah na cewa. “Ashe bakine damu a gidan sannunku da zuwa" duk da batasan su waye ba Saida gabanta ya
faɗi haka tadai maze taci gaba da yiwa ƴarta wasa a haka Safeenah ta shigo ta sameta fuskarta
wasai alamun farin ciki tace “Kizo kinada manyan baƙi a parlourn baƙi" bata jirayi abinda zata ce
ba duk da taga alamar cewar a tattare da ita ta juya ta fice bayan ta karɓe Ayyana a hannunta,
jiki babu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login