Showing 9001 words to 12000 words out of 58684 words

Chapter 4 - BAMAGUJIYA HAUSA NOVELS BY OUM HAIRAN.pdf

17 Nov 2025

108

haka ki kula da
kanki”



******

Washegari da safe a fada Baba Uda ya miƙe ya zabgawa Habeeb Mari Najeeb ya miƙe da sauri
yayo kansa Habeeb ya riƙe shi da sauri, nunashi Baba Uda yayi yace “Ƙarya kakeyi yaro baka
isaba kayi kaɗan ka koma gurin munafukan da suka turoka ka faɗa musu kaidai baka isa mu
baka aure ba kai bakai ba wani ma da yafika kama da galihu muddin daga birni ya fito bai isa
mu ɗauki jininmu mu bashi ba haba! haba!! Yaro aikai tawayar ma tayi maka yawa gaka
musulmi kuma a zuri'ar mu kaje ka nema dai a wani gurin Habeeba tafi ƙarfinka"
Ɗagowa Habeeb yayi ya dubi Uda yace “kayi hƙr Baba bani na jarabci kaina da son Beebah ba
Allah ne ya jarabceni inasonta kuma itama alama ta nuna ta karɓeni duk abinda kuke tunani
bazaku sameshi daga gareni ba"
Dariya Uda yayi yace “ƙaryar banza to bazamu bayar ba son ya kasheka in yana kisa mune sai
muka haifi Habeeba munce bazamu bayar ba"



Miƙewa sukayi suka fice daga fadar suna ƙunkuni suna Harbin iska suna zuwa gdan kuwa suka
gindaya mata sharruɗa tare da sanya mata sarka a ƙafarta gabadaya sun haramta mata fita
daga gda hakan bai wani dameta ba tayi jinyar jikinta kwana biyu ta warke kullum saidai su
Kande suzo su bata lbrn abinda ya faru a dandali da kuma halin da Habeeb yake ciki na irin
damuwar da yayi da rashinta saidai tayi murmushi kawai ta share don tasan ajalinta ne kawai
zaisa tayi karambanin fita daga wannan gida.
Kullum sai Habeeb yazo ƙofar gidansu Bibo haka Baba Uda da Baba Jimo zasuyi masa korar
kare gashi da baƙin naci yaƙi hƙr haka yayita zarya tsakanin masaukinsu da gdansu amma
ganinta yafi ƙarfinsa saidai ya gaji da aikensa da magiyarsa ya hƙr ya koma ya zama kamar
wani zautacce cikin abinda bai rufa wata guda ba ƴa macen da yake ɗauka ba'a bakin komai ba
macen da abaya yake ganin bazai iya sanyata cikin rayuwarsa ba sai gashi cikin lkcn da bai
shirya ba bai tsammata ba ta faɗo rayuwarsa tana sauya masa taswirar rayuwa.



Sosai Najeeb ya mayar dashi mahaukaci baya bawa duk wani abu daya shafi Habeeba
muhimmanci ko zama sukayi suna tattaunawa abinka da abinda ya damu ruhin mutum indai
Habeeb zai sako shafin Beebah cikin hirar to zata ƙare domin Najeeb zai kama faɗar
maganganun da in yayi wasa ranar ko ɗaki ɗaya bazasu kwana da Habeeb ba wannan tasa
suka raba tsaki da Najeeb mgn ma sai ta zama dole Habeeb ke tsayawa suyi da Najeeb haka
dai lkc yayita tafiya duk wata hanya da yake ganin zata zame masa me sauƙi wajen haɗuwa da
Habeeba ya rasa dole yaja ya dangana da gdan hakimi da rasa masa kuka yana roƙonsa ko
nawa sukeso kome sukeso matsayin sadakin Habeeba a sanar dashi zai bayar kuma yayi
alƙawarin matukar ba ita taso musulunci ba bazai rabata da addininta ba.
A zahiri Mati Dagaci yaji matukar tausayin Habeeb musamman dake yana yawan kawo masa
gaisuwa yasanshi yana lura da yanda ya susuce ko aikin daya kawo shi garin ya dainayi
shikenan daga ka sameshi a bakin kogi ya zubawa ruwa idanu saidai ace anganshi a jeji a
zaune ko kuma yana gda yana karanta wasiƙar jaki. Ɗagowa Mati Dagaci yayi yace “Yaro hakikanin gaskiya duk da bambanci addini naji tausayinka

matuƙa domin so mugun ciwo ne da bashida magani sai saidai samun abinda zuciya ta
kwaɗaitu dashi Habibu banida maganin matsalarka na rantse da Allanku da Bibo ƴata ce nice
na haife ta a yau bazaka bar gurin nan ba saina bawa Limamin Hayin Fulani damar ɗaura muku
aure bisa tsarin addininku amma kash banida wannan damar” Numfasawa Dagaci Mati yayi ya sake duban Habeeb da idanunsa suka rine suka koma jajaye
yace “duk da haka bazan kashe maka gwiwa ba kaje kaci gaba da addu'ar kasa malaman
addininku su tayaka Habeebu inda rai da rabo"




Miƙewa yayi cikin mutuwar jiki yace “Shikenan Baba Dagaci na gde amma bazan iya ci gaba da
zama a garin nan ba zan koma Garinmu saidai inason kafin na tafi kayimin alfarma ɗaya” da
sigar tausayi Dagaci yace “Wacce iri ce Habeebu" sunkuyar da kansa yayi yace “Ka aika a kira
Habeebah nasan idan Baba Jimo yaji kiran nakane zai barta ta fito inason magana da ita kalma
ɗaya tak nakeson ji daga gareta wlh indai har Habeebah tace bata sona zan hƙr da ita domin
nasan ƙaddarar sai soyayyarta ta wahalar dani ce tasa na zaɓi wannan garin matsayin inda
zanzo idan kuwa ta amsa min tanasona to ko duk dangina da nata zasu ƙare saina mallaketa
domin itaɗin mahaɗin raina ce"
Shiru Dagaci yayi yana jinjina kalaman can ya ɗago yace “shikenan Sarkin zagi tashi kaje ka
sanar munason ganin Bibo yanzu a gabanmu" babu ɓata lkc sai gata tun daga nesa ya kafeta
da manyan idanunsa da suka rine da damuwa itama shi take kallo ganin ya zabura ya miƙe
yasata tsayawa a inda take jikinta ya ɗauki ɓari saboda tuna mugun kashedin da Baba Uda yayi
mata.
Ji takeyi kamar ta juya amma batada ƙarfin gwiwar hakan domin Zuciyarta tana kwaɗayin ganin
ɗan birni ko ba komai tasan zata samu sauƙin abinda take ji a ƙasan ruhinta.
Takowa yayi gabanta ya tsaya ta gyara tsayuwarta cikin dakiyar zuciya ta dubesa kafin yayi
mgn ta rigashi da cewa “Dan birni meye ya sameka ka rame kamar kayi jinya?" Tana mgnr
tanakai hannunta fuskarsa ta shafa ƙasumbarsa da ta kwana biyu bai gyarata ba hakan yasashi
lumshe idanunsa ya kamo hannun nata yayi kissing nasa yace “Ha... Habee..bah kina iya
rayuwa me daɗi batare da kinsan halin da nake ciki ba?" Da rashin fahimta ta dubesa zatayi
mgn ya ɗora yatsansa a saman bakinta yace zo muje inason tambayarki ne a gaban Dagaci
duk amsar da kika bani ita ce zatayi aiki wajen sama mana mafita Ni dake baki ɗaya"




Kama hannunta yayi suka isa gaban Dagaci suka zauna Dagaci ya dubeta yace “Habeebah
kwana biyu kin ɓuya ɗan goron ma da ake siyowa a kawomin na toshi an daina kodai an daina
auren dani ne?" Murmushi tayi tayi ƙasa da kanta tace “Aa su Baba ne suka tsareni suka hanani
fit...." Girgiza kai yayi yace “to ai shikenan dama Habeebu ne yakeson ganinki zai koma garinsu
yanaso kuyi sallama" ɗagowa tayi tace “Habeeb!"
Ɗagowa yayi tare da jinjina mata kai yace “Sunanan kenan Habeeba don Allah ki nutsu ki bani

amsa ɗaya tak ita kaɗai nake buƙata daga gareki kada ki cutar da kanki ki faɗa min iyakar gskyr
abinda ke ranki game dani Habeebah kinaso na?"



Ɗagowa tayi da sauri ta kalleshi shima itan yake kallo cikin tsoro ta kawar dakai gabanta na
faduwa ta miƙe ya riƙe Rigarta ta baya yace “Wlh bazaki bar gurin nan ba saikin amsa min
tambayar nan don itace hadafin mafita ta Habibah kalma ɗaya ce eh ko a'a zata cireni a zullumi
sannan zata ƙarfafamin gwiwa Please ki faɗamin matsayin da kika ajeni kinasona zaki aureni ko
baki sona?" Ido ta zubawa Baba Uda sake shigowa zauren majalisar dagacin shima ya kafeta
da idanu yana nufosu tana ƙoƙarin ture Habeeb ta kasa saima riƙon tsauri daya ƙara yima
damtsanta wata ƙara kakeji kau... Kau... Abinda yasata saurin sauke idanunta kan babanta
Jimo dake tsaye da wani yaro Lanti ya zare wuƙa yayi kan Habeeb Najeeb ya taso da gudu ya
nufosu ya riƙe wuƙar ta yanke shi hakan yasa ya saki ya sake nufar Bibo da Habeeb ya ɗaga
wuƙar zai cakawa Habeeb Bibo tayi hanzarin tureshi wuƙar ta soke ta a gefen cikinta take ta
saki wata ƙara me nuni da irin azabar da taji hakan yasa Habeeb juyowa don shi kwata² baima
lura da dalilin tureshin da tayi ba.




Ganinta a ƙasa a zube cikin jini yasashi sakin ihu da dira kanta ya ɗagota yana jijjigata yana
kiran sunanta yana cewa “Habeebah wayyoh matata don Allah kada ki mutu bamu cika burinmu
ba wlh in kika mutu nima mutuwa zanyi....." Sunkutarta Najeeb yayi suka fice da ita da mugun
gudu suka nufi gdansu Dagaci yana biye dasu saboda haukan iyayen Habibah ya wucce
tunaninsa baitaɓa tunanin da gaske sukeyi zasu iya kashe ƴarsu da hannunsu ba.
Tun a hanya suka rinƙa kiran James dake babban likita ne shine yake kula da lfyrsu suna zuwa
ya dira akanta ya fara treatment nata sai bayan ya gama sannan su Jimo suka shigo Jumme ta
shiga ɗakin da sauri ta faɗa kan Habeebah da take farfaɗo wa yanzu tana faɗin shikenan nikam
rayuwata ta lalace Jimo zaka kashe mana ƴarmu ɗaya tilo akan wani bare meye yasa kukeson
kubawa zuciya dama ta barku da nadama...."
Ajiyar zuciyar da Bibo ta sauke ce ta sanya Habeeb saurin tashi daga inda yake ya nufeta ta
kuwa buɗe idanunta akansa ya riƙe hannunta yana jera mata sannu ta sake ƙanƙame hannunsa
cikin kuka da Muryar jinya da wahala tace “Meye ribata idan banbi wanda naji a raina zan iya
sadaukar da rayuwata don kare tasa ba? Habeeb bazan zauna dasu Baba Uda ba inka tafi
kasheni zasuyi ka tafi dani garinku na amince zan aureka ina sonk....." Tsalle Jimo yayi ya haye
ruwan cikinta ya naushi bakinta jini yayi tsartuwa zuwa sama ........
[4/7, 9:16 PM] AM OUM HAIRAN: *BAMAGUJIYA*
*(HOT LOVE AND DESTINY)*


NA

*FAUZIYYA TASIU UMAR*
*OUM HAIRAN*

https://youtube.com/channel/UCZ5Vt2--iGyJfTwItSzAnGg


*Paid book*
Ki biya ta waɗannan hanyoyin acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko ku turo katin
waya MTN ta WhatsApp number na kamar haka 09013718241. Normal group 300, Special 700.




*Free Page 7*


★★★~~~★★★~~~★★★


Ya wankewa Habeeb fuska da yake ta kokarin daga Jimo a kan cikinta daƙyar aka ƙwaceta don
cewa yayi kasheta zaiyi ya huta da baƙin ciki ya furta da haihuwar Habibah Gara ɓarinta yafi
sau ba adadi, Jumme banda kuka babu abinda takeyi saboda tunda take a rayuwarta bata taɓa
hasaso tashin hankali kwatankwacin wannan ba, rayuwa sukeyi me daɗi wacce ta cika da
kwanciyar hankali da rufin asiri sunason junansu da ƙaunar farin cikin juna.
Yau gashi rana a tsaka komai ya goce tabbas Habibah takai mahaifinta ƙarshe don kuwa a
tarihin rayuwa bai taɓa yi mata irin bugun mutuwar da yayi mata yau ba bare kuma har a halin
jinya ita wannan wacce irin ƙiyayya suke yiwa mutanen birni da har suka zabi kashe tasu
akansa? Tambayoyin da suke ta yawo a ranta kenan batada me bata amsa don zuwa yanzu ta
rayuwar Habibah akeyi da ta shiga wani yanayi na buƙatar agajin gaggawa, a wannan yanayin
James ya dubi Habeeb da jikinsa ya keta rawa tabbas badon Jimo haihuwar Beebah yayi ba da
babu abinda zai hanashi rama mata wannan dukan zalumcin da yayi mata.




Hararar juna kawai akeyi tsakaninsa da Najeeb duk da cewa Najeeb ya fara saukowa yana ɗan
tausaya masa akan wannan soyayya ta masifa daya faɗa ciki amma abubuwan da suka faru
yau yasa yaji ya ƙara tsanar Habiba da garin Tsaunin gawo sukam wanne lefin sukayiwa Allah
ya jefosu wannan gari na arna marasa imani waɗanda suke jin a ransu zasu iya kashe jininsu
don wani dalili nasu mara kan gado? Ya rasa wacce jaraba Habeeb ya liƙewa jikin yarinyar duk
da yasan ta fita babu algus ta zanu ba ƙarya amma a tunaninsa sai yaga batakai yayi wannan
haukacewar akanta ba meye ma abinso a mutum mara gamsasshiyar nasaba?

Wannan tunanin yasashi yin tsaki ya fice daga ɗakin daidai lokacin da Jimo shima ya hassalo
ya matsa zai sunkuci Beebah Habeeb yayi saurin dakatar dashi ta hanyar dafe ƙirjinsa suka
kalli juna cikin mugun bacin rai yace “karka taɓata na rantse da Allah idan ka taɓata sai nasa an
ɗaureka" baƙauyen mutum da tsoron tozarcin hukuma hakan tasa Jimo da Uda komawa gefe
suna huci kamar wasu mayunwatan zakoki.



Da haka aka samu ta dawo cikin nutsuwarta ta sauke ajiyar zuciya tare da buɗe idanunta
Jumme ta matso gabanta da sauri tace “Bibo kin tashi sannu..." Juyowa tayi ta kama hannu
Jumme ta kafe Habeeb da ido shima ita yake kallo ya sakar mata wani tsadadden murmushi
daya sanya jikinta mutuwa ya tako ya sunkuyo kanta yace “Inane yake ciwo?" Lumshe idanunta
tayi ta kawar dakai yaja numfashi yace “karki damu komai zai hucce soon Ni kaina nasan akwai
yaƙi a gabana amma zan jure don ke Beebah indai zan sameki wlh duk wata wahala zan
ɗauketa"




Fincikota Uda yayi ta zube a ƙasa baya ko tunanin ciwon dake cikinta wannan abun ya hassala
Dagaci ya daka masa tsawa yace “Wai meye yake damunku ne ko an faɗa muku ƙiyayya
haukace da zaku nemi kashe yarinyar nan meye laifinta akan abinda ba ita ta dasawa kanta ba
to wlh ku dawo hayyacinku ku kiyayeni idan kuka fusatani tsaf zan yanke hukuncin da bazai
muku daɗi ba sakarkaru"
Sakinta sukayi sarai sun san halin Mati idan suka fusatashi babu abinda bazai iya yi ba shiyasa
suke shayinsa, miƙewa tayi ta nufi Jumme ta faɗa jikinta ta rungumeta tana kuka tace “Jumme
kema baki sonsa" ajiyar numfashi tayi tace “Inasonsa mana tunda kina sonsa Uwata nidai
nafison kiyiwa iyayenki biyayya bazasu cutar dake ba ki cire komai a ranki bakida gatan da
yafisu" ɗagowa tayi taga idanunsa akanta tayi ƙasa da nata ya matso ya riƙo hannunta yace
“Kada ki sanya damuwa a ranki ki kulamin da kanki nabar amanarki gurin Dagaci zan dawo
bada jimawa ba zamu mallaki juna soon insha Allahu"



Janye hannunta tayi daga nasa Dagaci ya kamata suka fice ya nufi gidansa yanata faɗa kamar
zai ari baki, suna shiga ya fara ƙwalawa uwargidansa kira ta fito daga Madafi tace “gani Mati
meye yakar buzu da ranar Allah?" Mika mata Bibo yayi yace “Marka ga Habiba nan ki bata
kulawa da tsaro daganan zuwa lkcn da ƙura zata lafa nan ya kwashe lbrn komai ya sanar mata
ta tafa hannu tace “To banda abinsu shi wannan lamari ai abin asa idanu aga ikon me sama ne
yaran nan ba wanda ya haɗasu su suka haɗa kansu Inma mutum yace zai raba saidai yasha
wahala bare ma meye laifin Habibu yaron kirki da hayaniyar ma ba damunsa tayi ba kagani fa
Mati tunda suka zo garinnan kullum sai yazo ya gaisheni da ɗan alkhairinsa to maji ma gani wai
an binne rayayye"

Kama hannu Bibo tayi suka shiga daki ta nufi madafin ta haɗa ruwa me ɗumi ta kamata suka
nufi bayi da kanta ta rinƙa gasa mata jikinta tun tana wash² har ta dawo tanajin daɗin ruwan.



Suna zaune Marka na shafe mata ƙafafu da mai me gurguwa ya shigo da sallamarsa babu
wanda ya amsa sai maraba da Marka tayi masa suka gaisa tace “Habibu ɗan makaranta ashe
kuma haka abu ya faru babu daɗi sai hƙr kasan mutanen namu ne sai shiru sai saurare basuda
dadin sha'anin akan abinda suka jahilta musamman irin gidan Sarkin Noma Nomau tsaurinsu
akan ra'ayinsu yayi yawa"
Murmushinsa yayi me daraja idanunsa akan Beebah data daga kanta sama tazuba idanunta
akan rufin azarar dake ɗakin yace “Zai wucce kamar ma ba'ayin ba Baba Marka nidai roƙona ki
kulamin da ita kafin na dawo ba jimawa zanyi ba inason naje na shirya komai ne ayi a wucce
gurin idan na ɗauke ta dai inace shikenan?” “Shikenan kuwa yaro” Marka ta faɗa ya janyo ledojin daya shigo dasu ya miƙawa Marka yace
“magungunanta ne Dagaci yasan yanda ake amfani dasu Baba Marka a kula wajen shansu,
naga nan kunada service ga waya nan ƙarama nasa layi ta rike a hannunta saboda in rinƙajin
lfyrta kafin na dawo ba jimawa zanyi insha Allahu" Buɗe ɗaya ledar yayi tsire ne sai tiriri yakeyi duk ya cika dakin da ƙamshi ya ɗauka ya kai mata
bakinta.




Kautar dakai tayi ta kalli Marka itama kau dakai tayi ta miƙe ta fice musu daga ɗakin yayi
murmushinsa me cike da isa yace “Bazakici ba?" Daga masa kai tayi ya sake ɗaukowa yakai
bakinsa ya tauna yace “kuma kinga sai kinci tunda kikace kina sona" miƙewa yayi ya zagaya
bayanta batayi aune ba kawai sai jinta tayi kwance a ƙirjinsa ya daga kanta ya riƙe sosai yanda
bazata iya ƙwacewa ba ya sanya bakinsa cikin nata ta kuwa rintse idonta da ƙarfi cikin wata
masifaffiyar faɗuwar gaba da tashin hankali ta rinƙa kiciniyar ƙwacewa shi kuma ya matseta ya
lumshe idanunsa yana sake saƙalo harshen ta me masifar zaƙi yana fitar da wani numfashi me
wuyar fahimta yana kusa sake shigar da ita jikinsa ya saki fuskarta don yasan yayiwa bakinta
riƙon da bazata iya ƙwacewa ba ya sanya hannunsa tsakanin ƙirjinta da cikinta shafaffe wanda
zaka iya rantse wa bata sanya masa komai.
Yawo yake da hannun a hankali tsakanin cibiyarta da ƙirjinta yana son kaishi ga kyakkyawar
dukiyar fulaninta dake tsaye kam kamar zasu tsonewa mutum idanu duk da bata taɓa sanya
musu bra ba a tsayin shekarunta sha bakwai a duniya amma hakan baisa sunyi komi ba.....




Wata zabura yaji tayi tare da shiɗewa lkcn da ya ɗora hannunsa kan yar ƙaramar rigar data rufe
su dasu hakan yasashi saurin janye hannunsa ya cire bakinsa daga nata yana sharce gumi

gabadaya jikinsa ya mutu murus sai zufa dake karyo masa ta ƙofofin gashin jikinsa, wata ajiyar
zuciya yaja me ƙarfi yana arowa kansa juriya yana sawa kansa ya sake ta ta janye jikinta sai
rawar mazari yake ƙirjinta kuwa banda bugawa babu abinda yakeyi ta zabura ta miƙe zata
runtuma da gudu yayi saurin riƙota ta zame ta rushe masa da kuka yayi saurin zama yace
“Nikam banason kuka wlh Beebah meye na kukan?" Tureshi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login