Showing 48001 words to 51000 words out of 58684 words

Chapter 17 - BAMAGUJIYA HAUSA NOVELS BY OUM HAIRAN.pdf

17 Nov 2025

122

Rufe mata baki Baba Larai tayi cikin kaɗuwa da jin kalamanta tace “Shi Yariman ne yace
Miki kina shaye-shaye?" Girgiza kai tayi tace “Ba cemin yayi ba kamani yayi dumu-dumu...."
Zaro idanu Baba Larai tayi tace kina shaye-shayen?" Cikin kuka tace “Eh.... Eh Baba Larai
kusan hakan ne ki duba gabas dake duk wani nau'i na abinda mata ke amfani dashi na
shaye-shaye gashi can a ajiye to waye ya ajiye idan bani ba?"




Shiru ce ta gauraye É—akin babu abinda kakeji sai sautin kukan Beebah Baba Larai na share
mata hawayen, daƙyar Baba Larai ta aro juriya tace “Wannan abin shiryayye ne akayisa don
asa kokwanto a cikin yardar dake tsakaninki da mijinki kiyi hƙr ki ƙara haƙuri insha Allahu
wannan makircin bazaije ko inaba Gimbiya Yarima yafi kowa sanin halinki idan yaje ya zauna ya
samu nutsuwarsa ta dawo shi da kansa zai ƙaryata idanunsa da zuciyarsa amma fah sai kinyi

hƙr kin jure lamarin gdannan namu Gimbiya akwai makirci idan akaƙi mutum aka sakoshi a
gaba ba dune yake kaiwa labari ba ke ki godewa Allah mijinki na sonki uwarsa na sonki bata
karɓar suka kowacce iri ce indai akanki ne kai tsaye take cewa bazaki aikata ba"
Da wannan kalaman tayita rarrashinta har tasamu ta daina kukan ta tashi ta É—ebe kaskon
shisher da kwalin sigarin ta bawa Baba Larai tace ta fice dasu daga sashin nata, har Baba Larai
ta juya zata tafi ta juyo tace “Yarnan kiyi iya bakin ƙoƙarin ki kiga bakiba da ƙofar da za'a a gane
da damuwa tsakaninki da mijinki ba kinji?"


Amsawa tayi da to Baba na gode Allah yabar ƙauna" ko bayan fitar Baba Larai ta daɗe a tsaye
kafin ta shiga ɗakinta ta rubuta masa gajeren saƙo ta tura masa lokacin yana tare da Najeeb a
gdansu yaji alamar shigowar saƙo Najeeb ya dubeshi yace “Waye?" Zaro wayar yayi daga
aljihunsa ya buɗe saƙon murmushi ya dubi Najeeb yace. “Bansan meye yasa muke kokawa da zuciyata wajen tabbatarwa kaina Wyf bazata aikata ba
amma wani sashi na zuciyata yana gargaÉ—ina É—an Adam a cikin sakanni yakan canza É—abi'a"
Murmushi Najeeb yayi yace “Guy kana masifar son yarinyar nan kada kabawa munafukai dama
su shiga tsakaninku kada fah ka manta akanta ka rantse zaka iyayin komai to meye ma idan
tana smoking ɗin kawai hƙr zakayi kuci gaba da rayuwarku a haka....."
Miƙewa yayi yace “Koda Wyf na smoking zan iya rayuwa da ita badon abin ya girgiza ni
Najeeb duk da nasani kaima baka goyon bayan aurena da Beebah ka faÉ—a min wannan shiri ne
makirci ne haka Kilishi ma da na faɗa mata tace min wannan ƙarya ne Habeebatullah bazata
taɓa aikata barnar nan ba sannan ta kuma horona a karo na barkatai na ƙara sa ido a takun
zaman gdana, Najeeb na yarda Beebahta bata shaye-shaye amma to meye yake sata bacci
tunda na dawo kullum cikin bacci take?"



_Wannan Page Bonus ne bayanshi duk wani page da zaku gani paid ne kiji tsoron Allah ki
biyani haƙƙina ki karanta cikin salama_
[5/17, 8:26 PM] AM OUM HAIRAN: _*BMGJY Bonus 41-42*_


_Ku biya ta acct detail 3184512451 First bank ko kati MTN ta WhatsApp number
09013718241._
_Normal 300 PC 700_
_Ƴan Niger zaku biya 500f ta wannan number +227 95 04 58 22_


_Ban amince a juyamin littafi ta kowacce siga ba_


Assalamu alaikum My Fan's shin ko kunsan cewa bigi sai bigi babban goro sai magogin ƙarfe,

tabbas ramin kura sai Æ´aÆ´anta,
Nasan zakuce yau dame kuma Oum Hairan tazo mana? To ku daina tambayar kanku sabbi
kuma shahararrun kayan mata ne masu ban mamaki daga taskar Siyat yar mutan Katsinawan
dukko da Oum Hairan.
Muna da kayayyaki kamar haka👇🏼
Maganin gyaran Nono, maganin ƙarin hips, Sirrin matsi na musamman, gumbar dagake babu
wata, humra mai taken madarar ƙauna, muna dafa kazar amarya da haɗin jijjiɓi musamman don
masu jego tare da aikawa ko ina kuke a fadin Nigeria, munada maganin sanyi wanda duk
shaharar sanyi muddin kikayi amfani dashi yanda ya dace to kin rabu dashi kenan. Sannan munada kaloli na kayan Malama A'isha Mai Da'ira musamman turaruka wanda ke da
kanki saikin dawo idan kikayi amfani dasu domin zasu janyo Miki hankalin mijinki zasu sanya
nutsuwa da fahimtar juna tsakaninku zaki zama tauraruwarsa domin an haÉ—asu ne da wasu
keɓantattun ayoyin Alkur'ani mai girma domin sharewa mata hawayensu babu boka babu
Mallam, karki manta cikin kalolin turarukan mu akwai wanda Bama taɓa siyarwa me kishiya
saboda haka kiji tsoron Allah in kinsan kina da kishiya karki siyeshi domin gudun shiga haƙƙinta.
Mai buƙata DM me 09013718241.

★★★~~~★★★~~~★★★

Miƙewa Najeeb yayi yana cewa “Kada kayi mata hukunci da baccinta waina watanka nawa da
dawowa ne?" Baisan meye halaƙar tambayarsa da tambayar da Najeeb keyi masa ba amma
haka yace masa biyu na shika na uku ina tunanin ma sati me zuwa zan koma" murmushi
Najeeb yayi yace. “Kuma sau nawa ka kusanceta daga dawowarka zuwa yanzun?" Kafe Najeeb yayi
da ido Najeeb ya numfasa yace “Ta iya yiwuwa kaine matsalar ko lkcn da kana London kullum
maganarka kayi missing Beebah kayi missing Beebah ta yuwu ka sake jefa ƙwallo a raga ne
tunda naga Khalisa tunda ta samu ciki batada aiki sai bacci ƙila itama nata ne yazo da haka...." Dariya Habeeb yayi yace “Da gaske zai iya zama hakan ko?" Ɗagansa kai yayi yace “Don
tabbatarwa kana zuwa gida ka É—auketa kuje a dubata hakan zai cire maka kokwanto"




Numfasawa yayi sukayi musabaha tare da sallama kowa ya kama gabansa zuciyar Habeeb ta
kasa gasƙata masa abubuwan daya gani amma shaiɗan yanata taka rawarsa na son sai ya
tabbatar masa.
Koda ya shiga gdan baiyi ƙasa a gwiwa ba ya nufi part ɗinta Khausar na ƙoƙarin
ɗauke masa hankali da salon kirsarta ya watsa mata wani mugun kallo ya buɗe ƙofar ya fice ya
nufi sashin Beebah tana zaune saman sallaya da alamun sallah ta idar Hudais na zaune a
gabanta da kayan wasa yanata yan kararrakinsa kamar gyare inda ita kuma ta kifa kanta a
cinyarta bacci na fusgatta taji an buɗe ƙofar ta ɗago idanunta cike da mayen bacci ta saukesu
cikin nasa, shi É—in ma itan yake kallo fuskarsa babu wani yanayi da zaka tantance walwala ko
akasinta.

Haka ya tako ya zauna yana É—aukar Hudais da ganin uban nasa yasashi sakin wasan da
yakeyi ya fara miƙa masa hannu, lakacewa yaron kumatu yayi yana maida dubansa gareta yace
“Meye yake damunki?" Yanayin yanda yayi tambayar yasa ta kasa gane me yake nufi sai kawai
tayi ƙasa da kanta tace “Wallahi tallahi Hero ko maganin mura bantaɓa sha ba da niyyar ya fitar
dani daga hayyaci na Please kada ka fara dasawa rayuwata kokwanto bayan Allah banda wani
gata bayan...."




Rufe mata baki yayi yace “Ya isa nasani ina nufin game da lafiyarki kamar akwai wani abu dake
damun jikinki ina ganinki saɓanin yanda nasanki" numfashi ta sauke tace “Ni babu abinda yake
damuna yanzu É—azun ne ma kafin shigowarka ta farko kaina yayi ciwo shine naje na kwanta
bacci ya ɗaukeni" Jinjina kai yayi yace “tashi ki rakani unguwa" da sauri ta dubesa ya ɗaganta
gira ta sani yanda ya haÉ—e yaci ganye ta tabbata babu kalmar data isa ta furta masa da zai
saurareta hakanne yasata miƙewa ya ɗauki Hudais suka fita.
A babban parlourn suka wucce Khausar itace tayi mata sannu bata samu damar amsawa ba
saboda wani malolon baƙin kishi da takaici dayake neman kassara mata zuciya, har suka shiga
Mota suka tayar tanata takaicinta.




Jifa tayi da glass na cup na hannunta ta cire É—ankwalinta ta jefar ta nufi É—akinta kamar sabon
kamun hauka ta ɗauki wayarta ta kira lambar Deedah tana ɗagawa tace “Saida nace Miki mu
canza salo wannan bazai yiwu ba kikace zai yuwu to yanzu me gari ya waya mun haÉ—a makircin
ƙarshe gashi can ya ɗauke ta da ɗanta sun fice nikam hƙr na ya ƙare a gdannan babban burina
ko zan rasa inga na rabashi da wannan Æ´ar Iskar Yarinyar wlh indai tana rayuwa a da'irarsa
bazai taɓa kallon wata mace ba"
Tsaki Deedah tayi tace “Nifa wlh da kinbi shawarata ta da tuni tabar mana gdannan amma kika
tsaya kina cewa wai kinfiso kibi komai a sannu to ai ga sannun nan kina gani mijinki kusan
shekara da watanni ya gagareki saidai kiji dariyarsa a makotan...."





Cigaba sukayi da tattaunawa can sukayi sallama Deedah tace zasusan yanda zasuyi, itakam
Khausar bata yarda da shawarar Deedah ba ta kira Hajiyan ƙofa bugu ɗaya ta ɗaga tace
“Hajiya nifa lamarin nan ya fara isata wlh idan bata barshi ba ni zan barshi Mama tace mu
shigar da boka na bakin kogi maganar ke kince a'a kuma alamu sun nuna itama hanyar da
kikace kar mubi ita yakebi.
Yanzu ace duk kyauna da ƙirata bantaɓa burge Prince ba indai ba aikin asiri ba, haba Hajiya a

duba wannan lamarin fah mazan titi ma haÉ—iyar yawu sukeyi idan sun ganni sai mijina ne zaice
banyi masa ba nikam na gaji wlh na gaji sha'awar Habeeb na neman kasheni"




Murmushi Hajiyan ƙofa tayi tace “Yaro yaro ne to ke banda abinki kina tunanin akwai asirin
dayake cin waÉ—annan kafaffun mutanen ne? Haba Khausar kamar baa wannan ahlin aka tsirar
dake ba ai in faÉ—a Miki indai jinin Khalil ne to ba asiri ba ko tsafi ne asarar kuÉ—inki kawai zakiyi
basajin bayaƙi da kiranye, Khausar mantawa ma kikayi shekara nawa kikayi keda uwarki kuna
badda kuɗi wajen ganin kun samu Habeebun amma yaƙi samuwa? To ki nutsu wannan aikin
bana gaggawa bane akwai shirin da nakeyi duk zakujishi amma sai bayan Habeeb ya koma
shine aikin zaifi tafiya yanda akeso ke nifa Khausar na daɗe da ƙayyadewa wannan
bamagujiyar adadin kwanakinta a wannan gidan kedai kiyi duk me yuwuwa kiga kin cusa
kokwanto a zuciyarsa kafin yabar ƙasar nan"




Kwantar da murya Khausar tayi tace “Kina gani fah nasa mata kaskon shisher da kwalin sigarin
da kwalbar maganin mura har uku har buÉ—ewa nayi na zubar a kan carpet É—in Hajiya sigarin fah
har kunnata nayi Saida ta ƙare na kashe kuma na zubar da tokar a Carpet ɗin amma hakan
baisa yaji wani ɗar ba yanzu haka ma ya ɗauketa da ɗan su sun fice sun barni da gadin gida" Murmushi Hajiyan ƙofa tayi tayi ƙasa da muryarta tace “zan rubuto miki mataki na gaba" saurin
katse wayar tayi lokacin da taji an turo ƙofar, daga bakin kofar ya tsaya fuskarsa a washe kai
bazakace ya taɓa shiga damuwa ba ya tsaya yana kallon Khausar taja numfashi tare da ƙoƙarin
saita nutsuwarta don tasani karamin abu baya kawosa ɗakinta tace “Ina farin ciki da farin cikin
me sani farin ciki halan anyi maka albishir da sarautar Dutse ne?"




Murmushi yayi ya kwantar da kansa jikin ƙofa yace “zan iya samu taimako daga gareki Wyf ce
takeson wainar fulawa ta manja" murmushi tayi tace “to ai akwai komai a kitchen ɗin parlour tayi
mana" murmushi yayi yace “batada lfy ashe duk wannan kasalar shigar ciki ke gareta...."
Da wani mugun sauri ta ɗago tace “Ciki kuma?" Annurin fuskarsa ne ya ɗauke ya zubanta
manyan lulu eyes ɗinsa nandanan ta daburce tace “Nothing karka kawo komai a ranka kawai
naga Hudais baifi five months ba.




Naji tsoffi suna cewa idan yaro yasha ciki lalacewa yakeyi...." Juyawa yayi ya fice yana cewa

babu abinda zai sameshi zan tafi dasu London a kula dasu acan ina jira ki kawo min wainar" da
wannan ya fice ta zube a ƙasa ta ɗora hannu aka tana shirin rusa ihu tayi saurin toshe bakinta
ta miƙe jiri na ɗibanta ta nufi kitchen ɗin parlour harta haɗa kayan wainar wata zuciyar ta hanata
kawai tayi komawarta É—aki. Shima yana can yanata lelen matarsa ya manta da batun wata waina bai fito a É—akin ba sai sha
biyu da rabi sukayi sallama ya tafi ya kwanta.
Kacokan ya É—auki kulawarsa da tattalinsa ya É—orawa kanta ita da cikinta da É—an su gefe kuma
kullum sabbin abubuwa ɓullowa sukeyi zaman kullum ƙara rikicewa yakeyi Khausar ta dage
kuma tana samun nasara donma ubangiji yana tare da me gaskiya a duk inda yake baya sanya
makircinta yin dogon zango. To yauma tun safe yayi asubancin tafiya Lagos zai karɓo saƙo dake tafiyarsa saura
kwanaki uku, Beebah ke kwance a ɗaki ko parlourn ta kasa fitowa saboda zazzaɓi batasan
wainar da ake toyawa a wajen ba sai yamma liƙis taji hargowar mutane a babban parlourn,
zuciyarta bata bata taje taga su waye ba tunaninta mutanen Khausar ne. A hankali taji hayaniyar na matsota ta tashi da sauri dake kwance take daga ita sai under sikert
ta ɗauki hijjab batakai da sawa ba aka buɗe ƙofar aka shigo babu zato babu tsammani taji wani
ƙato da aka cukuikuyo yana cewa “Hajiya ki taimakeni kice su sakeni wlh ba halina bane kece
kika takura sai na zo Hajiya idan suka kasheni ya Iyata zatayi Ni kaÉ—ai ta haifa saboda lafiyarta
na yarda da sharaÉ—in da kika gindaya min na zuwa yau mijinki bayanan......"





Bata gane komai cikin maganganun da Saurayin yakeyi ba saidai bin waÉ—anda suke zagaye
dashi da kallo da takeyi Mai Martaba Alh Lukman Mahaifin Khausar Hajiyan ƙofa Hajiyan soro
da Jakadiya sai Baba Larai da keta sharar hawaye da Hudais a bayanta sai Hajiya mandiya
Khausar da keta taunar cingam. Cikin rawar murya Beebah tace “Wai meke faruwa ne? Waye kai?" Wata shaƙa Mai Martaba
yayi mata data sanya numfashinta ɗauke wa yayi watsi da ita a gefe cikin ƙunar zuciya yace
“Shiyasa tun farko naki amincewa Habeeb auren wannan bamagujiyar yarinyar saboda duk
yanda kakai ga son kaga sunyi daidai bazasuyi maka daidai ba domin basu gaji daidai É—in ba
mutanen da suke bautar gumaka da duwatsu ace sune zaka zaɓawa ƴaƴanka matsayin uwa?
Tur da wannan zaɓin wannan zaɓen tumun dare ne....."
Hajiyan soro ce tace “Allah ya taimake ka duk da ance ba'a shaidar mutum amma fah komai
yakan nuna alama Habeebatullah batayi kama da wacce zata aika....."




Tsawa ya buga mata ya nuna ta da yatsa yace “Dake da Ummusalma bakinku ɗaya kuna goyan
bayan rashin gaskiya to bari kiji Wlh tallahi na rantse da girman Allah yau yarinyar nan sai tabar
cikin ahlina Ni a matsayina na uban daya haifi Habeeb na sawwake mata aurensa kuma mun

karɓi Ibrahim ta fito ta fice min daga gidan ɗana kafin nasa a fitar da ita.........




_Ku ƙara yimin uzuri my lovely Fan's aradun Allah duk inda nayi kuna raina koda yake nasani
soyayyarku da wannan labari me farin jini ke gajarce uzurinku gareni, wlh tun jiya nayi muku
typing kamar yanda na alƙawarta wani uzurin yazo yasha kaina.🤗_


_Wannan Page Bonus ne bayanshi duk wani page da zaku gani paid ne kiji tsoron Allah ki
biyani haƙƙina ki karanta cikin salama_
[5/18, 8:31 PM] AM OUM HAIRAN: _*BMGJY Bonus 43-44*_


_Ku biya ta acct detail 3184512451 First bank ko kati MTN ta WhatsApp number
09013718241._
_Normal 300 PC 700_
_Ƴan Niger zaku biya 500f ta wannan number +227 95 04 58 22_


_Ban amince a juyamin littafi ta kowacce siga ba_



Cikin ƙunan zuciya ɓarin jiki da tashin hankali ta miƙe tsaye idanunta na ganin duhu ta nufi
wardrobe domin ɗauko kayanta tasa Hajiyan ƙofa tace “Matsiyaciya ubanme kikazo dashi da
zaki É—auka? Ina haka akazo dake a cikin tsumma zaki wani buÉ—e wardrobe kinga maza zo
kama hanya kafin dare yayi Miki" lumshe idanunta tayi ta juyo ta dubesu ta girgiza kai zuwa
yanzu furucinta ya ƙare batada wata kalma da zata iya furtawa domin kare kanta tabbas komai
nisan gona dole zaaje kunyar ƙarshe wannan shine dalili na farko da yasa taji a ranta zata iya
rabuwa da Habeeb rabuwa ta har abada.
Ƙofa ta nufa tana shirin fita ta juyo ta dubi Hudais dake bayan Baba Larai kawai sai taji wani
kuka ya ƙwace mata ta matsa takai hannu zata kwanceshi, Baba Larai batayi mata gardama ba
ta kwanto mata shi Hajiyan ƙofa tayi saurin karɓeshi tana cewa “Allah ya kiyaye ya ƙara raɓar
jikin wannan annamimiyar matar maci amanar ƙauna kekam kin cika butulu....." Wani kallo tabi
Hajiyan ƙofa dashi ta juya ta fice da sauri Hajiyan soro na ƙwala mata kira amma bata juyo ba
saboda Zuciyarta ta riga ta gama ƙeƙashewa batajin daidai da second ɗaya zata iya ƙarawa
cikin wannan ahlin gara ta fita kamar yanda suka shirya tozartata dayi mata ƙazafi.

Abin takaici da mamaki wai maigadin da komai a gidan ita keyi masa shine ne cewa da ita
“Ummah tagai da Assha" wai harda cewa yake “aje aci gaba da tallan Burkutu....." Ko tana cikin
hayyaci itan ba ma'abociyar kula kowanne shirme bace bare yanzu da takejin jiri na É—aukar ta
bata iya gane komai kawai daɓa ƙafarta takeyi ko ina. Batayi aune ba batasan meye ke faruwa ba kawai saiji buɗe idanu tayi taganta a gadon asibiti
hannunta da ƙafarta nannaɗe da bandeji, ta rinƙa raba idanu tana kallon asibiti da wani irin
yanayi na rashin tabbaci.




Ji tayi ance mata “sannu!" Ta karkata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login