Showing 21001 words to 24000 words out of 58684 words

Chapter 8 - BAMAGUJIYA HAUSA NOVELS BY OUM HAIRAN.pdf

17 Nov 2025

120

ya
faskara da zai tafi ne ya shiga ɗakinta ya ajiye mata wani tsadadden card a gefen kayanta sai
wani ƙaramin akwatu da ATM card da wasu takardu. Sai yamma liƙis suka dawo sun kuwa yi muguwar gajiya suka zube a parlourn suna mayar da
numfashi kowacce ta jefar da mayafin itakam Beebah kwanciya tayi saboda sosai tafi kowa
gajiya Gara su sun saba da komai da akayi musu ita kuwa komai sabo ne a gurinta hakance
tasa jikinta ya gaji zuciyarta ta gaji brain nata shima ya gaji ta baje a parlourn tana juyi gashin
nan yasha gyara sai kyalli yake abin ba'a cewa komai gashi an gyara musu farcensu harda jan
lalle ya zauna das a fatarta tayi wani sihirtaccen kyau na ban mamaki Kilishi da kanta satar
kallon surukar tata takeyi duk da yammatan nata ma ba baya ba amma sun samu uwarsu a
fannin kyau hasken fata kawai zasu faɗa mata sai murjewa itama kuma fatar tata me karɓar
sauyi ce cikin sati biyun har wani glowing takeyi.
Gyaran murya Kilishi tayi tace “nayi magana da Dr Mas'ud da dare zai zo Habeebah ki zama
ready" cikin ɗoki tace “Ok Hajiya"




Miƙewa tayi ta nufi ɗakinta ta cire kayanta ta ɗaura towel ta faɗa wanka dake tana fashin sallah
alwala kawai ta ɗaura kamar yanda Kilishi ta koyar da ita zama da alwala a kowanne lokaci ta
dawo ta zauna saman dressing stool ta gyara gashinta ta ɗaure da ribbon a tsakiya ya sauka
har tsakiyar bayanta ta shafa powder ita kanta tasan tayi kyau na mamaki ta tsaya tana ƙarewa
kanta kallo taji an buɗe ƙofar ta madubi taga yanda suke kallonta Hudah tace “Barakallahu
ahsanal kaliƙin Beebah wlh koni mace ban gajiya da kallonki saima boko ta ratsaki tukunna"
murmushi tayi ta zauna tace.
“Yunwa nakeji Wlh" dariya sukayi sukace “waima kekam wanne irin cikine dake zakuwa ki iya
azumin Ramadan gashinan yana tahowa saura wata biyu?" Harararsu tayi ta miƙe tana cewa
“in kukayi wasa ma saina fiku yi" tana mgnr tana rankwashinsu suka kuwa zuba a guje ta zille
musu ta nufi ɗakin hutawar Kilishi ta shige bayanta ta ƙanƙameta tana dariya itama sun bata
dariya tace.
“Dama haka kukeso mala'ikin naku ya tafi zaku addabeni zakuyi bayani rubuta duk kalar rashin
jinku zankeyi a littafi in yazo na bashi" zaro ido Beebah tayi tace “na shiga uku an fasa aurena

Kilishi Wlh idan kika haɗamu da Bro kisa ne kawai nikam na nutsu na daina kai taking care Wlh
Bro zai hukunta ku babu ruwana"




Hudah ce tace “ai kafin ya dawo ta manta yauwa Kilishi wannan karon wacce ƙasa zamuje
siyan kayan sallah?" Harararsu tayi tace “Aifa nice marainiyar wayon ku to kuje ku tambayi Mai
martaba mana ko kuma ku kira Babban Yaya ku tambayeshi" langwabar dakai Khaly tayi tace
“Ai ko Ya Naseer bamu isa mu tambaya ba yanzu asamu gwale² Hajiya kece dai zaki faɗa mana
inda zamu Ni dama zaki yarda Allah banson azumi a kasar nan Dubai nakeson muje muyi
azumi ko Saudi" Hajiya Kilishi akwai son farantawa yaranta hakanan tace “Shikenan zansa
ayima Habeebah passport saiku tafi Saudiyya tunda ita bata taɓayin Umrah ba in yaso dagacan
in kunyi sati biyu saiku wucce Dubai ɗin" wani tsalle sukayi suka rungumeta itakam Beebah
jikinta ne ya mutu komai ya kwace mata zuciyarta tayi rauni “to wannan wanne irin family ne
Habeeb ya koka mata matsaloli haka Hajiya Kilishi ranar da aka kawota amma ita har yanzu
bata fara ganin matsalar ba ya kawota matsayin ƴar aiki amma mahaifiyarsa ta ɗaga darajar ta
ta mayar da ita ƴa a gurinta Bama ta jinginata da aikin in har ba'a gaban sauran mutanen gidan
bane, su kansu mutanen gidan cewa suke Hajiya wannan yarinyar tamafi Sakina samun fada a
gurinki" saidai tayi murmushi tace “to ai kowa da kalar baiwarsa wai yau ita Habiba bamagujiya
ita ce zata tafi ƙasa me tsarki ta gana da ubangijinta data sanshi ta fahimceshi kwanan nan?"
Saurin share hawayenta tayi saboda tasan sarai Kilishi batason kuka ta miƙe zata fita ta riƙota
tace “Akwai damuwa ne Habeebatullah?" Girgiza kai tayi ta rusuna ta kama hannun Kilishi tace
“a duk lkcn da kukayimin wani abin alkhairi nakanji bankai nan ba yaushe matsayina yakai aimin
haka sannan shine sila kuma tunanin mahaifiyata da Babana yakan bijiromin irin rabuwar da
mukayi dasu dutsi a hannun riga dominsa....."




Rufe mata baki tayi lkcn da Hajiyan soro take shigowa tace “Shikenan Habeebah Sarkin rigima
bazaa kuma ba ku tashi kuje" miƙewa sukayi dukkansu Hajiyan soro tabi Habeeba da harara
bata daina harararta ba Saida suka fice ita kanta Beebah ta fahimci Hajiyan soro da Hajiyan
ƙofa basa sonta saboda kullum cikin harararta suke wannan tasa bata fiye shiga sharafinsu da
ƴaƴansu ba komanta tafi yinsa a inda aka ajeta wai a haka ma gara Hajiyan soro ita Hajiyan
ƙofa yaranta ma ta hanasu mu'amala da Habeebah a cewar ta ita kawai yarinyar batayi mata ba
har tana cewa garin yakabe²n Kilishi saita ɗauko musu ajalinsu sauƙin ma da take samu dake
ana shayin Kilishi da ƴaƴanta tunda sune manya kuma sune masu faɗa aji a gidan shine kawai
yasa take shanyarta a inda takeso.
Kilishi ce ta katse shirun da cewa “Soro ya akayi ne?" Hankalinta ta dawo dashi ga Kilishi tace
“Gulma ajali Hausawa sunce in baayi ba a mutu yanzu na fito daga gurin Mai martaba ina
turakarsa yana Parlour naji Wannan makirin Lukman ya shigo yana cewa wai akwai wani abu
da aka rufe a gdannan da ya kasa gane menene amma tabbas bincike yana nuna masa akwai

wata rufaffiyar ƙura da take shirin tashi a gdannan, to kinsan Mai martaba bai fiye sauraron
shirme nan ya dagansa tsawa yace baison shiririta, shine suka koma mgnr ƴaƴan nan shine Alh
Lukman ɗin yake cewa tunda an samu Habeeb ɗin ya tafi yanzu ayi maganar aurensa da
Khausar shi kuma Naseer za'a haɗashi da Mufeedah Yassir da Hanifah su kuma matan
Khaulatu da Aliyu Amna da Bashir Khalisa da Ibrahim Hudah da Isma'il kuma Mai martaba yace
dukkan auren za'ayi su ne nanda shekara ɗaya...."




Gumi ne ya karyowa Kilishi tayi saurin tashi zaune tace “Habibu da Khausar Mai martaba ya
manta yanada wadda yakeso bayan nan ma ya manta cewa kaf wannan family ɗin babu
yarinyar da Habeeb ya tsana irin Khausar kayy ina gsky a sake lale nikam inajin tsoron lamarin
Habeeb irin kafiyar mahaifinsa gareshi" taɓe baki Hajiyan soro tayi tace “Yo tunda bashi ya haifi
kansa ba haihuwarsa akayi ai dole ya haƙura kamar yanda kowa ya hkr Ni Wlh nama ɗauka ya
hƙr da yarinyar nan daya sheƙa yaga babu ƙwayar"
Miƙewa Kilishi tayi tace “Shi Allah Sarkin daidai ne amma Wlh nima ban karɓi Khausar matsayin
suruka ba haba koda dai naka sai naka amma ai kowacce ƙwarya tanada abokin burmi Meye
Habeebu zaiyi da Khausar kawai saboda yaro bashi da ƴanci shine za'a koramin shi Japan
sannan ayi masa tukuici da wannan fitsararriyar yarinyar da iyayenta suka jiƙa suka lalata to
wallahi da sake dadai abawa me kaza kai gara a bashi romon koda bread ya lasa"




Riƙe haɓa Hajiyan soro tayi tace “Ni Zulaihatu to banda abinki Ummusalma wannan hukunci ai
kinsan kamar da ƙasa tabbatuwarsa inji me ciwon ido tunda suka shiga suka kulle da wannan
makirin ƙanin nasa bare dama ku ya daɗe yana haƙonku kada ki manta tun akan Hisham
babban Yaya yaso haɗashi da kanwar Hajiya Indo Safiyya kuka zille dole aka barta to yanzu
kuma kema kinsan ba ƙaramin shiri zakiyi na rusa wannan shiri ba domin kuwa Khausar ƴarsa
ce ta cikinsa daga ita sai Aliyu ya haifa kinsan kuwa ko duniya zata tashi saidai ta watse don
kuwa me hana auren nan sai ƙudurar Allah babba"
Sosuwar da zuciyar Hajiya Kilishi tayi ta sanyata barin dakin hutun ta nufi ɗakinta tana kaiwa da
kawowa saboda ba Habeeb ba ita kanta Allah ya sani bata kaunar jinin Hajiya Indo ganin
shaiɗan yanata yimata ayyane ayyane yasata dauro alwala ta tayar da sallah tana roƙon Allah
ya bawa Habeeb mafita cikin wannan cukurkuɗaɗɗen lamari na rayuwarsa gabaɗaya sai taji
tana tausayinsu dagashi har Habeebah ta shaida ta haƙiƙance Habeebah nason mijinta so na
gaske shima kuma son kyautar rai yakeyiwa matarsa batajin akwai wani dalili da zaisa Habeeb
ya iya hƙr da Habeebatullah matuƙar ba mutuwa ba.



_IDAN KIKA KARANTAR LITTAFI BAKI BIYANI BA BAN YAFE BA._

[4/18, 1:30 PM] AM OUM HAIRAN: BMGJY



KIYIWA GIRMAN ALLAH KI BIYANI HAƘƘINA KAFIN KI KARANTA NORMAL 300 PC 600, KI
BIYA TA WANNAN HANYOYIN ACCT DETAILS 0255526235 FAUZIYYA TASIU GTBANK KO
KATIN WAYA MTN TA WHATSAPP NUMBER NA 09013718242 ƳAN NIGER ZAKU TURA
KATIN AIRTEL 400CF TA WANNAN NUMBER +227 95 04 58 22 SAIKU TUROMIN
SCREENSHOT NA SHAIDAR KUN TURA MATA NIKUMA NASAKU A GROUP.



*17-18*

★★★~~~★★★~~~★★★


Zaman kusan awa biyu tayi kan sallayar ta rasa tudun dafawa hakanan gwiwa a sage ta tashi ta
fita dinning ta tarar masu kula da ɓangaren abincin har sun shirya komai na dinner ta zauna ta
buɗe tuwon shinkafa miyar zogale ta dauki mazubi zata zuba Beebah ta fito da sauri tana cewa
“Ayyah Hajiyanmu yau kin manta nice zan haɗa Miki abinci tun dazun naketa leken jiran
fitowarki"
Murmushi tayi ta gyara zama tace “To Beeban auta a haɗamin" kunya Hajiya ta bata ta juya
zata gudu taji an riƙeta ta ƙyalkyale da dariya tace “Allah Hajiya kunya kike bani in kince
Beeban auta dinnan waima kunyi waya dashi kuwa ya sauka ko har yanzun suna saman
gajimare" Tana mgnr tana langwabewa salon shagwaɓa Hajiya ta harareta tace “ai kin fini kusa dashi ba
mijinki bane ki kirashi mana kiji lfyrsa" shiru Habeebatullah tayi da mgnr don batada kalmar
ƙarawa itadai tasan yanda tsoron Bro ya ɗarsu a ranta bazata iya haike masa ba gara ma idan
shine ya kira.....



Ƙirrr wayar Kilishi ta fara ruri bayan ta gama haɗa mata abincin suka kalli wayar a tare “Autana"
sunan da Hajiya tayi saving numbersa dashi kenan suka haɗa idanu da Hajiya tayi saurin
juyawa zata bar gurin Kilishi tace.
“Kai kajini da kitifaffiyar yarinya yanzun ki titsiyeni kina tambayata mijinki sannan ya amsa ya
kira ki gudu" Turo baki tayi tace “Kayy Kilishi bafa niba ke yakeson jin...." Rankwashi ta zuba
mata tace “Kaniyar me gardama ɗauki Ni kibani guri" ɗaukar wayar tayi ta danna accepted ta
nufi ɗakinta ta kulle ta kara a kunnenta ya sauke numfashi yace “Matar da bata damu da ya
mijinta yake ba" lumshe idanunta tayi tace “ya akayi kasan nice?" Wani gwauron numfashi ya
sauke yace “zuciyata ce ta amshi saƙon mahaɗinta anya Beebah zan iya rayuwa Ni kaɗai a

ƙasar nan Wlh ina cikin yanayi bansan Meye ke damuna ba nikam tunda aka sarƙamin rigar
girma aka ɗaureni da igiyoyinki uku na fara fuskantar canji inajin kamar bazan iya cika alkawarin
dana ɗaukar wa zuciyata akanki ba"
Abinka da ƙuruciya bata fahimci komai ba cikin kalamansa saima kwantar dakai da tayi tace
“cikin kane yauma yake ciwo?" Fasali yaja yace kusan hakane gashi ina buƙatar bargo me
taushi wanda yake numfashi kamar Ni Beebahta garin akwai sanyi waither ɗin su zata wahalar
dani...."



Dariyarta ce ta katse masa furucin tace “Wai bargo me numfashi to a ina ake samun bargo me
numfashi koda yake rayuwarku ta birni babu abinda bazaku iya samarwa ba ɗan birni nikam ina
ganin tunda bazaifi ƙarfinka ba ka siya kada sanyin yayi maka illa" takaici ne ya sashi yin ƙwafa
yace “shidai yaro kawai sunansa yaro bayan wanda nake dashi ƙarfi da yaji yafi ƙarfina kawai ki
tayani addu'a kuma kiyi fatan kada a dawo Miki da gawar mijink....."
Da sauri tace “Bari don Allah Bro banaso Wlh ina tsoron mutuwa saboda itace Ummul aba'isin
komai na lalurar rayuwata na tabbata da ace yaya Tani bata mutu ba da yanzu aurena dakai bai
zama silar tuɓe rigar albarkar iyayena ba Bro inasonka fiye da yanda nakejin kaina a zuciyata
amma ina tsoron irin abinda kayimin jiya don Allah karka ƙara banaso Nima na mutu banga
ƴaƴana ba....."
Sosai kalmar ta ta ƙarshe ta bashi dariya yayi me isarsa sannan yace “is very funny My wyf
kinajin tsoron matakin farko har kina roƙona karna ƙara sannan kuma kinason zuwa matakin
ƙarshe to ta yaya wannan shirmen naki zai yiwu?"
Biye mata yayi sukayita shirmensu ko ba komai yana samun nutsuwa da muryarta sun ɗauki
dogon lkc suna hira kafin suyi sallama yace ta kaiwa Kilishi ta fito takai mata a kunyace ta karɓa
suka gaisa tanayi masa tsiyar yanzu tunda yabar zuciyarsa a gida ai ta rinƙa jinsa kullum.....




Itadai sulalewa tayi ta nufi dakin baccinsu ta tarar duk sun kwanta suna latsa waya taja bargo ta
kwanta tana karanto addu'ar data sawwaƙa bacci yayi gaba da ita, sai asuba suka farka tayi
wanka kamar yanda taga al'adar su Khaly da Hudah ta koma tana gyara musu ɗakin
kasancewar itan ba sallah zatayi ba bayan ta gama ta nufi kitchen shegen karambani ne da ita
Habeebatullah komai da ruwan ka kowa ya santa kuku har nemota yakeyi in zaiyi aiki saboda
tace masa itama girki takeson koya har tana cewa ko ruwan tea ya dafa bai kirata ba wuta
balbal aikuwa ranar Hajiya Kilishi da sauran yaran gidan sunci dariya wai wuta balbal shida
aikinsa.
Dake tanada fahimta sosai babu wani abu da yake bata wahala indai taji a ranta zatayishi a
wannan taƙin ne kuma Hajiya Kilishi tayi ruwa tai tsaki aka mayar da ita makaranta Dr Mas'ud
yayi mamakin kwanyar yarinyar da akace masa daga kauye take SS one yasata sai gashi tana
neman fin yan SS one ɗin ganewa saboda lesson ɗin da takesha a gida Hajiya Kilishi tayi mata

Hudah da Khalisa suyi mata shima mijin ɓoyen idan ta saci jiki ta saci wayar Kilishi ta ƙule ɗaki
yayi mata sukayi jarabawar zangon karatu na ƙarshe dake dama karshen shekara aka kaita da
ƙyar bayan ankai ruwa rana ta samu na biyu don badon maths data samu matsalar maki ƙalilan
ba ita zata karbe kambun first class aikuwa Ashe tun kafin ma a bayyana musu sakamakon
Habeeb ya sani don result na Habeebatullah Habeeb ya jima a wayarsa.
Kowa Saida ta burge shi a wannan rana hatta Hajiyan soro dake lecturer ce Saida taji
Habeebatullah ta mugun shiga ranta kyauta kuwa harda Mai martaba a bata gift gift na ban
mamaki Mai martaba ya bata zoben gold da agogo yasa Hajiyan soro ta siyo mata masu kyau
da tsadar gaske familyn yan boko sarakai kuma masu tashen hatimin nasara a Afrika ma ba iya
Nigeria ba Allah ya jarabci wannan family da son mutum gifted yanzu darajar ka zata ɗaga.
Itakam Hajiyan soro ɗan kunnen gold ta siya mata babba, Habeebatullah banda hawaye babu
abinda takeyi wai yau ita bamagujiya wacce take yawo tsirara² mara galihu wacce ake ƙyamata
itace kowa keson gani da kuma ɗaukar hoto da ita.




Allah kenan tabbas idan ka rikeshi zai isar maka amma fah idan ta tuna ɓoyayyen matsayinta a
gidan da kuma tsohuwar aƙidar mutanen family ɗin jikinta ya kanyi sanyi harta kasa katabus,
Ranar haka ta yini tulus babban tashin hankalinta yanda Mufeed yayan Rasheedah Turaki class
met ɗinta Kuma ƙawarta ɗaya da tayi a ajinsu ya takura mata da kallo da hotuna duk inda tabi
haskata yakeyi idan suka haɗa idanu yayi mata murmushi itakam tsoronsa ma takeji Mufeed
Turaki Soja ne hutu yazo ya ishe bikin canjin ajin na ƙanwarsa rabon haɗuwa da ƙaddararsa
yasashi jin shauƙin kasancewa a gurin.




Yaukam jinsa yakeyi kamar shine sarki Khalid saboda yanda zuciyarsa take haske yanajin
tabbas yayi matar aure, hakanan taro ya watse suka nufi gda a motar Kilishi ita da kanta ke
jansu Saida takaisu wani Gidan gyaran jiki aka gyara mata ƴammatan nata tayi musu siyayya
sannan suka wucce gida suna zuwa Habeebah ko wanka ƙi tayi ta nufi dinning ta zuba abinci
tanaci hanu baka hannu ƙwarya saboda yunwa sunata yi mata dariya Kawai jikinta ya bata ana
kallonta ta daga kanta gabanta ya faɗi ta zaro idanu waje tace “Lahhhh Kilishi ya dawo....." Bata
gama isar da saƙon ba ta kwasa da mugun gudu ta haye saman ta ruƙunƙumeshi tana kissing
nashi ta ko ina tana cewa “I miss you My Bro double miss you....."
Mamaki ne ya cika Hudah da Khalisa ganin yanda ya wani lumshe idanu yana shafa bayanta da
alama ma ya manta da akwai mutane a ƙasan ya ɗago fuskarta ya ɗora harshensa a lips ɗin ta
ya sauke mata wani irin kiss me hucin bayyana sirrin zuciya ya janye ya ɗaga idanunsa da suke
wani lumshewa kamar me jin bacci yace “Really My Wyf kinyi miss ɗina kamar yanda nayi
naki?"
Dubanta takai ƙasa inda Mai martaba yake tsaye gabanta ya faɗi tayi saurin janyewa daga
jikinsa ta nufi hanyar ɗakinta ya bita da kallo yana haɗiye wani mugun yawu gabaɗaya cikin

watanni shida tayi mugun canzawa kamar ba Beeban sa ba wata ajiyar zuciya ya sauke ya fara
taka step na benen ya sauko ya rusuna cikin ladabi da girmamawa ya gaishe da Mai martaba
Sarki Khalil bai wani dami zuciyarsa da tunanin wani abu ba saboda yariga yasan dabi'ar family
ɗin nasu da mazansu da matansu duk jinsu sukeyi abu ɗaya musamman Beebah yarinya me
tsayawa a rai duk ɓacin ran da kake ciki indai tazo guri saita sanyaka dariya shiyasa bai damu
da yanayin daya gansu da Habeeb ba.




Dafa kansa yayi yace “Autan Kilishi Meye ya dawo dakai ne wata uku na ɗauka sai kayi
shekarar?" Shafa sajensa yayi yace “Allah ya taimakeka wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login