Showing 6001 words to 9000 words out of 58684 words

Chapter 3 - BAMAGUJIYA HAUSA NOVELS BY OUM HAIRAN.pdf

17 Nov 2025

109

ya
saukar masa da wata sihirtacciyar kasala baisan sanda ya hadeta da jikinsa ba yasa hannunsa

biyu saman ƙugunta ya kwantar da kansa a saman nata ya sauke wata mahaukaciyar ajiyar
zuciya da baitaɓa jin fitar irinta a cikin rayuwarsa ba.
[4/2, 2:43 PM] AM OUM HAIRAN: *BAMAGUJIYA*
*(HOT LOVE AND DESTINY)*


NA


*FAUZIYYA TASIU UMAR*
*OUM HAIRAN*

https://youtube.com/channel/UCZ5Vt2--iGyJfTwItSzAnGg


*Ramadan promo*
Kamar yanda kuka sani ne ba wani sabon abu ba littafan OUM HAIRAN na kudine zaifi ki biya
ki karanta cikin kwanciyar hankali, bana Miki/maka fatan kaci haƙƙin daba naka ba domin nasan
Allah bazai bari ba musamman yanzu da zamu shiga wata me alfarma wannan tasa nayi muku
discount nrml group 300 ya koma 200 PC 700 ya koma 500, wannan garaɓasar ta iya satin
farko na Ramadan ne
Ki biya ta waɗannan hanyoyin acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko ku turo katin
waya MTN ta WhatsApp number na kamar haka 09013718241.


*Sanarwa*


Maganar tsarin post da kuke tambaya ta insha Allahu na tsara shi yanda bazai shafi ibadarmu
ba zan rinƙa post kullum 9:30pm wato tara da rabi na kowanne dare.


*Page 5*


★★★~~~★★★~~~★★★



Ɓambare jikinta tayi daga nasa ta ɗago manyan idanunta suka shiga cikin nasa hawayen da
batasan sun taho ba suka gangaro kan kuncinta, gabadaya ilahirin jikinta rawa yakeyi saboda
tsoro da tashin hankali.
Juyawa tayi tana kokarin kwasa da gudu tare da toshe bakinta da kukan yake kokarin fin

karfinta, riƙe hannunta yayi da himmarsa cikin tashin hankali yace “ya Allah Habeebah me nayi
Miki meye yasaki kukan ko bakiyi murna da ganina ba?"
Durƙushewa tayi ta turmutsa hannunta cikin ƙasa ta rushe da kuka me ban tausayi da ɗaga
hankali, zama yayi da sauri yakai hannunsa don ɗago fuskarta ta tureshi da ƙarfi tace “ni nace
ka daina taɓani ɗan birni na shiga uku so kakeyi sai an kasheni a garin mu yanzu idan wani
yaga yanda ka kwaƙumani da jikinka zuwa za'ayi a faɗawa Jimo Ciwake kuma na tabbata
kasheni zaiyi nima da wannan abin kunyar gara ya kasheni na huta kowa ya huta, duk jikina
nasan yanzun warin maza yake...."




Rufe mata bakin yayi da hannunsa yace “Ke bafa haka bane tsoratar daku sukeyi amma babu
wani warin maza da ake ji a jikin mace don namiji ya taɓata amma tunda bakiso shikenan yi hƙr
nayi alƙawarin bazan ƙara taɓaki ba amma fah inada sharaɗina nima in kin yarda"
Da sauri ta ɗago tace “Wanne?" Lumshe idanunsa yayi ya ɗora habarsa kan tafin hannunsa ya
buɗesu akanta ya motsa ƙaramin bakinsa a hankali yace “Wannan shigar zaki daina ki rinƙa
killace jikinki kinga ita wannan shigar idan wani namijin yaganki da ita sako zai ɗarsu a
zuciyarsa idan ya ɗarsu kuma zaiyi ƙoƙarin ya aiwatar aiwatarwar kuwa itace babban tashin
hankali don zai rabaki da ƙimarki" sake kallonsa tayi tace “kamar ya?"
Miƙewa yayi zaune yace “Zaiyi yunkurin keta alfarmarki ta hanyar sanin ki ɗiya mace ma'ana a
gwari² zaiyi Miki fyade....." Miƙewa tayi a kiɗime ta dafe ƙirji tace “na shiga uku fyade irin wanda
aka yiwa Tani ta mutu?" Jinjina mata kai yayi cikin jin daɗin yanda ya samu nasara cikin sauki
yace “Wace Tani?"



Hawaye ta goge ta kama hannunsa suka nufi wani kurutturen ice suka zauna ta sake goge
hawayenta ta ɗago ta dubeshi shima ita yake kallo tayi ƙasa da kanta tace.
“Tani yayace a gurina ƴa ce a wajen wan babana wato Baba Uda, ta girmeni amma soyayyar da
take min tasa muka zama kamar ƙawaye komi namu tare mukeyi karshe ma Ni kusan a gdansu
Tani na girma saboda gidansu akwai wadar yara abokan wasa nikuma gidanmu Ni kaɗai
Jumme da Jimo suka haifa. Tare muke zuwa gona tare muke zuwa tallen kunun zaƙi baban Tani Uda yana dafa Burkutu tare
muke ɗauka mukai gurin bauta mu siyar, wata rana da bana mantawa ana bikin kamun kifi baƙi
daga gari² sunzo domin ganin wannan bikin gwaninta da akeyi duk shekara domin kaf yankin
nan a garin nan ne kawai akeyi kuma shi dama wannan ruwan na bayan gari da muke kira
ruwan tsarkakewa tun tale² baa kamun kifi a cikinsa sai shekara shekara wannan tasa duk kifin
da aka kamo zaka sameshi narkeke to wanda yafi kowa gwanintar kamun kifi a wannan
shekara shine zai auri sarauniyar ƴammata ta wannan shekara.

Za'a ɗaukeshi a kaishi gdan Sarki aje a ɗauko sarauniyar matan shekara a kawo ta a daura
musu aure kuma babu ruwan wannan bikin da cewa baƙone kai ko ɗan gari haka za'a bawa me
Sa'a matarsa ya tafi da ita.
Kasan meye ya jawa Tani faɗawar azal?" Numfashi yaja ya girgiza kai ta sunkuyar da kanta
tace “Kyau ɗan birni mu kininmu muna da wani irin kyawu da bansan ta ina muka sameshi ba
bawai zallar kyawun fuska ba a'a direwar halitta ga kuma wani farin jini da kakanninmu suka
roka mana abar dogaro ta bamu, Tani kyakkyawa ce ta wucce misali don duk kyawun nan nawa
da ake faɗa ni banfi rabinta ba saidai fatar mu iri ɗaya ce wankan tarwaɗa, hakan yaja mata
cincirindon masoya daga cikin garinmu da makota harma da ƴan birninku da suke zuwa kallon
ajabin da aka halitta a wannan ƙauye namu, amma taƙi tsaida gwaninta.
Kwatsam sai Wannan shekara abar dogaro ta nunata matsayin sarauniyar ƴammatan shekara
aikuwa maza suka rinƙa murna domin kowanne jarumi gani yake nasarar samun Tani tasace.




Haka muka dukufa shirye-shiryen wannan biki mukayi alibidi yafi kala goma Baba Uda da
mahaifina Jimo har awaki da toron agwagi suka yanka mana dake haka al'adar take a gidan su
sarauniyar ƴammata za'ayi girkin bawa gwarzon shekara.
Munata kaiwa da komowa munata hidima ranmu fes karma ni naji labari don ko hutawa banayi
nakai na kawo ina tsokanar yaya Tani, abin dana fahimta saidai tayimin murmushi kawai idan na
matsa mata sai ta kama hawaye inna tambayeta dalilin kukanta sai tacemin kawai tanajin tsoron
a dauketa daga gari a kaita wani garin itadai tafiso mu kasance tare. Idan ta fadi haka nima sai jikina yayi sanyi naji zuciyata ta karye mu hadu muyita kuka har sai
Lamunde uwar Tani ta fatattakemu, ranar Wannan babban biki na al'ada daya zame mana
idinmu mukayi kwalliya ta bam mamaki muka zauna a gda sai yamma muka nufi bakin kogi don
mu ganewa idanunmu gwarzon mu muna tafe muna rera ƴan wakokin yabo ga abar dogaro
domin gareta muke neman sa'ar wannan aure na ƴar'uwata Tani.




Tun a hanyarmu ta zuwa naji gabana yana faɗuwa nadai dake ban faɗawa kowa ba bayan mun
isa mun zauna gurin da aka tanada domin mu ina riƙe da hannun yaya Tani ina mammatsa
matashi naji taja ajiyar zuciya tace “Habibah" na ɗago da sauri don tunda nake da ita bata taɓa
kiran sunana ba saidai tace dani Ƙanwa. Idanunta naga yana zubar hawaye nayi saurin kai hannuna ina share mata ina girgiza mata kai
ta riƙe hannu na tace “gabana yanata faɗuwa Habibah inajin kamar wani abu zai faru a gurin
nan saboda jiya Liti ya rako Jamilu wannan ɗan birnin shine Jamilu yake cemin bai iya su ba
domin bai gada ba kuma har yanzu yananan akan bakansa na aurena babu ruwansa da kafirci
na indai zan aureshi domin shima ba ibadar ya damu da itaba, yace naje na faɗawa su Baba
Uda kada su bari a fara wasan nan tun a daren jiya su ɗaura mana aure idan kuwa sukaƙi to

shakka babu zaiyi kiran abokansa ƴan daba na Birni su ƙaddamar min ya rantse da Allansu abin
dogaronsu indai ba'a bashi niba saiya barwa Tsaunin gawo tabon da har abada bazai goge ba"
Sosai kalaman sun girgiza duniyata amma saboda son kwantar mata da hankali sai nace
“kayya yaya Tani kinada sanya abu a ranki kada kibar wannan soki burutsun haukan nasa ya
dameki babu abinda ya isa yayi Saida sahalewar abar dogaro kuma inada yaƙinin bazata
wulaƙantamu ba"



Numfasawa tayi ta girgiza kanta tace “Hakane amma fa nikam na tsorata" da haka na rinƙa
kwantar mata da hankali har zuwa wani lkc da aka buga tambarin nasara guri ya bushe da iface
iface da kaɗe kaɗe da bushe bushe.
Kwatsam saijin ihun mutane muka rinƙayi ƙura ta tashi muna ganin yanda mutane suke
runtumawa da gudu su kuma makasan suna ihu suna ina Amaryar yau sai sun kasheta... Ai
bangama jin hakan ba na mike na kama hannun yaya Tani itama ta rikeni muka runtuma da
gudu muka nitsa cikin daji ashe dama Mun san abinda muka tunkara da munyi tsaiwarmu a can
kilan abar dogaro ta bamu kariya.
Muna gudu muna haki duk mun sassoke da kaya jikinmu ya kakkarce muka iso wata sarƙaƙiyar
duhuwa muka tsaya muna mayar da numfashi, can mukaji motsi ta bayanmu yaya Tani ta rikoni
don na sake ta na nufi wata magudanar ruwa zan ɗebo mata kasancewar nasan bata jurewa
ƙishirwa, naji tace “Habibah da mutum anan mu gudu...." Bata ƙarasa ba suka bazar da ita a
gurin ta saki ƙara nima na saki Jami ya diro daga kan wata itaceyar mangwaro muna ganinsa
muka zaro idanu Tani harda ajiyar zuciya tayi tunanin me cetonmu ne nayi saurin kwacewa
daga hannun wanda ya riƙeni na nufesa ina sauke numfashi nace “Yawwa Jami kayi mana rai
kada su kashemu mun......"




Wata mahangurɓa ya sakarmin a baki yace “Shegiya kin ɗauka cetonku nazo kafiran banza
kafiran wofi uwarme zan ceta a icen jahannama kalidina fiha abada Nima rabona nazo ɗiba na
rama cin amanar da kuka yimin kuma agabanki zanyi komai kije ki faɗawa manyan kafiran nine
Jamilun Alh Kabirun Auta muga wanda karansa yakai tsaikon da zaija damu a fadin ƙauyen
nan...."
Yana faɗin haka ya dakawa wasu samari uku tsawa yace me kuke jirane kuyi aikinku" kafin na
Ankara sun kamani sun ɗaure sun sanya wani tsumma sun rufemin baki sun watsar dani a
karkashin bishiyar kusa da yaya Tani.
Yaya Tani ta fara yunkurin tashi Jami yasa ƙafarsa ya taka ƙirjinta ta saki wata kara da nima
bansan sanda na saki ba duk da bakina a daure yake don nasan ta azaba ce"
Zamewa tayi ƙasa daga kan icen ta rushe da kuka shima ya sauko idanunsa sun kaɗa sunyi
jawur jikinsa har rawa yakeyi yakai hannu zai taɓata sai kuma ya tuna ya janye yace “So....sorry
please inajinki Habibah kinga dare ya fara" ɗagowa tayi ta sanya hannu ta riƙo hannunsa tace

“A gabana akan idanuna ɗan birni suka ketawa yar'uwata haddi suka keta alfarmarta sukayi
mata kaca² su biyar ƙarata akanta ita kaɗai tana kuka tana Nishi tana gunjin azaba amma
roƙonsu takeyi kada su taɓani kada su cutar dani, nima kuka nakeyi inata kokarin kwance kaina
amma na kasa Saida suka gama abinda zasuyi lkcn ta gama galabaita sannan suka kwanceni
na angajesu da ƙarfin da bansan ina dashi ba na isa gareta ina kiran sunanta ina jijjigata suka
tsallake mu sukayi tafiyarsu sunata ƙyaƙyala mana dariya.




Na jima ina jijjigata sannan dabara ta fadomin na cire kallabina na nufi wannan gulbin dana nufa
dazu na jikoshi nazo ina danna mata a jikinta sai kuwa taja ajiyar zuciya ta fara buɗe idanunta
daidai lokacin da samarin garinmu suka shigo jejin suna nemanmu ashe wani manomi yaga duk
abinda ya faru ya bazama gdan sarki ya faɗa, hannunta ta ɗaga ta kamo nawa ta ɗora a saman
ƙirjinta ta sake buɗe idanunta akaina taja wata ajiyar zuciya me ƙarfi shikenan jikinta ya saki
ashe tafiyar kenan.
Tafiyar kenan ɗan birni tafiyar da ba'a dawowa tun daga wannan lokaci na kamu da wata irin
jinya da Saida na cinye wata bakwai ina kwance ba uhm ba uhm² saidai a kwantar a tayar haka
akayita Shari'a akan wannan abin da ya faru amma babu nasara saboda baban Jamilu ya tsaya
masa kasancewar shi kaɗai ya haifa kuma me kuɗin birni wannan dalilin yasa kwata² a cikin
danginmu Bama ƙaunar mutanen birni ko kaɗan wlh ba ƙaramar wahala nasha ba da akace da
Baba Uda anganni da ɗan birni cewa yayi ma da a ƙara bar musu mugun tabon da mutuwarsu
ce zata rabasu dashi gara su su kasheni suji a ransu sune suka barranta kansu dani"..............
[4/5, 9:11 PM] AM OUM HAIRAN: *BAMAGUJIYA*
*(HOT LOVE AND DESTINY)*


NA


*FAUZIYYA TASIU UMAR*
*OUM HAIRAN*

https://youtube.com/channel/UCZ5Vt2--iGyJfTwItSzAnGg


Kamar yanda kuka sani ne ba wani sabon abu ba littafan OUM HAIRAN na kudine zaifi ki biya
ki karanta cikin kwanciyar hankali, bana Miki/maka fatan kaci haƙƙin daba naka ba domin nasan
Allah bazai bari ba musamman yanzu da zamu shiga wata me alfarma.
Ki biya ta waɗannan hanyoyin acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko ku turo katin
waya MTN ta WhatsApp number na kamar haka 09013718241. Normal group 300, Special 700.

*Page 6*


★★★~~~★★★~~~★★★


Tashi yayi daga tsugunnon da yayi yana sauke wata ajiyar zuciya me ƙarfi ya juya ya nufi
hanyar da zata sadashi da masaukinsu, Saida yayi nisa sannan ya juyo yaga ta miƙe tsaye tana
me binsa da kallo,
Juyowa yayi ya dawo ya tsaya a gabanta ya zubanta idanu tare da numfasawa ya kira sunanta
da wata irin murya da tasa ƙirjinta bugawa da ƙarfi ta ɗago idanunta da suke tsiyayar da
hawaye yasa hannu ya kama fuskarta yana goge mata idanun ya buɗe bakinsa da yayi masa
nauyi yace “zaki auren....." Janyewa tayi dukan ƙirjinta na ƙaruwa tace “Aure...." Matsowa yayi
gabanta ya damƙi hannunta yace “Yeah Beebah Aure zaki aureni koda danginki duka basu
amince ba koda nima nawa bazasu amince ba kiji a ranki ke matata ce soon"
Sakin hannun nata yayi ya juya da sauri yabarta da sakakkiyar gwiwa data kasa turata ta kaita
ko ƙofar gdansu saima guri data samu ta zauna ta zabga uban tagumi hannu biyu tanaci gaba
da sharar hawayenta.




Ji tayi an daka mata tsawa ta zabura ta miƙe da sauri jikinta ya dauki rawa ganin Baba Uda
tsaye a kanta taja baya da sauri ya kuwa tusota yana surfa mata ashar yana cewa “wato ke
kunnen ƙashi ke gareki bakijin mgn ko to muje gdan uban naki naji daga inda kika samu ɗaurin
gindin kula wannan ɗan iskan yaron me siffar munafukai" Da gudu ta shiga gdan kamar an jefota Jumme da Jimo dukkansu suka miƙe ganin Baba Uda
yasa Jumme shigewa ɗaki yaci gaba da sababinsa yanata kundume² ashariya.




Cikin girmamawa Jima ya ɗago ya dubesa yace “Nifa yaya ban fahimci abinda kake nufi ba" “Eh
ai dama bazaka gane ba nasani bazaka gane ba Jimo ka saki yarinyar nan sasakai abinda taga
dama shine takeyi kaƙi matsa mata ta fitar da miji bare batun aure yanzu gashi garin sakacinka
taje ta janyo mana abinda zai kashem" da bayannaniyar rashin fahimta Jimo yace “menene
Yaya ka sanar dani" numfasawa yayi yace “wai har gida akaje akace min yarinyar nan Bibo
anganta ita da ɗaya cikin bakin nan da dagaci yasa akayi shelar zuwansu ƙauyen nan haƙar
ma'adanai...."
Tafa hannuwa Baba Jimo ya shigayi yana girgiza kai kawai sai yayi wuf ya cafko Habibah ya
rufe ta da duka ta saki ihun daya janyo hankalin mutanen da suke wuccewa gidan ya cika da

mutane daƙyar aka kwaceta hannun Baba Jimo yana haki yace “Ni zaki tozarta Habibatu kwana
huɗun can nayi Miki kashedi akan wannan yaron da labari yazo min yana binki gona shine ya
sake canza salon yaudararsa to na rantse da abar dogaro kasheki zanyi Habibah yankaki zanyi
da wuƙa na jefaki a rijiyar jeji domin bazaki zamemin haihuwar asara ba...."



Kuka takeyi tana matsawa daga inda take tsaye tana shirin fita Baba Uda ya cafko ta ta rushe
da kuka tace “kada ku kasheni bansan meye yasa bana iya bijire masa ba yana kalaminsa da
hankali kalaminsa na nutsuwa ne komansa a nutse yake bashi da hayaniya ku fahimceshi da
gaske ba irin Jami...." Zubewa tayi ƙasa hancinta da bakinta suna zubar da jini tsallaketa sukayi
suka bar gurin dukkansu da bayyananniyar damuwa a fuskarsu kai tsaye gdan dagaci suka
nufa idan ka gansu zaka zata korarru ne.
A ƙofar gida sukaga dagaci tare da baƙi suka tsaya a nesa dashi suna tattaunawa bayan dagaci
ya gama sallamar baƙinsa ya ƙarasa garesu suka gaisa yayi musu iso zuwa fadarsa ya dubesu
yace “yanayi ya nuna kuna cikin damuwa meye yake tafe daku?"
Numfasawa Uda yayi yace “damuwa babba ma kuwa ranka shi daɗe wato tun farko Saida
mukace bamasan sauke baƙi a garin nan aka nuna mana bamu isa ba saboda baku abin yake
shafa ba yanzu ga abinda hakan yake neman haifar wa wani a cikinsu yana neman lalata mana
tarbiyyar ƴar wajen ɗan'uwana Bibo nasan dai kasan Bibo...."



Nan suka kwashe duk abinda aka faɗa musu ƙarya da gaskiya suka zayyane masa ya jinjina
abin yayi shiru yana tunanin mafita can ya ɗago ya dubesu yace “yanzu dai zamu kira yaron
gobe da safe jimo Uda kuje gda zamu nemeku"
Miƙewa sukayi sukayi bankwana suka tafi ranar kwana sukayi suna saƙa irin matakin da zasu
ɗauka akan Habeeb.
Kwana tayi jikinta yana ciwo tana kuka Jumme nayi mata faɗan dalilin da yasa bataji kashedin
da iyayen nata sukayi mata ba, cikin kukan tace “Nifa bani nace yazo ba kuma bani nake
kulashi ba shine yake kulani sannan Jumme kece kike cemin babu kyau wulakanta mutum bare
sh....." Katseta tayi da cewa “naji banason ji nidai na faɗa Miki indai kinason naci gaba da sanya
Miki albarka to ki fita daga harkar wannan ɗan birni ba sonki yakeba cutar ki zaiyi ina me
tabbatar Miki duk dariyar da ɗan birni zaiyiwa na ƙauye cutarsa zaiyi saboda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login