Showing 42001 words to 45000 words out of 135036 words
Chapter 15 - Wa Yasan Gobe Compelet Book by Safiya Abdullahi Musa Huguma .pdf
bangaren ta
gyara ko ina da ina,tana kuwa fama da aikin domin tsakanin samira ko salima babu mai iya yin
cangal kowacce haka take fita daga girkin ta tabar sashen a ahautsine
Tsakaninta da aliyyu sai girki ta shirya masa daddadan abinci ta zuba masa ya ci idan ya
kammala ta kwashe ta wanke kana ta ja qafarta ta bar sashen sai kuma washegari idan ta shigo
hada masa breakfast,da zarar kuwa kwanakinta ya qare bata bi ta kan kowa da zarar ta taso a
aiki ta shiga sashenta ta qulle qofa tofa sai washegari zata sake fitowa
Wai inji hausawa sunce jiki da jini kuma mutum da zuciya cikin lokacin sai sai qyamar girkin su
samira ya fara kama aliyyun ransa ya soma sosuwa da ganin sam gyara bai damesu ba,har
gwara ma.salima tunda at least akwaita da son ado da kwalliya zata yi wankanta tayi kwalliyarta
hakanan zata qoqarta ta dafa masa koda jallop ce albarkacin masifar son sa da take duk da
bata taba girki a gidansu ,amma samira kuwa babu daya qanwar biyu daga ciki
Cikin harshensa da zuciyarsa yana jin dadin girkinta sosai dandanon da bai taba jinsa ba gun
kowa ba baya ga mominsa,miskilanci irin nasa yasa ko a fuska bata taba ganin alamun haka
ba,takan tattare masa socks singlet handkerchief three quarters da duk inner wears dinsa harda
jallabiyoyinsa da yake sawa ta wanke su tas ta goge su sannan ta feshe su ta turare ta jera
masa su to ammafa insha Allahu bayan kwana hudu ta karbi girki zata zo ta tarar da su kamar
kamar ba su ba komai an hargitsa shi sai ta soma fuskantar wani abu akwai gayya a ciki ta
kuma san bazai wuce su salima ba don adawarsu gane da aikin nata a fili yake qara ra wani
lokacin takan jiyosu suna yan qana nan maganganu takan sharesu taqi tankawa don basu tari
gabanta sun gaya mata ba bare ta kula da shashancinsu
Abu daya ke qona mata rai aishi aliyyun na gani suke batawar shin bazai tsawatar musu ba
idan su basu da tunani?
Ga misali a farkon fara aikin nata kafin su soma adawarsu takan tsince kayan aliyyu ne kawai a
dakin a watse takan gyara ba tare da ta damu ba tunda tasan aikin ta ne dama,da tafiya ta
soma nisa sai suka dinga barin brassiere panties sleeping dress underwear musamman
salima wadda kullum sai ta tsince nata tunda samira ke fara girki sai ita wanda a qa'ida fadila ce
ya kamata ta zamo mai girki a farko amma suka maida ita ta qarshe ta qyalesu duka ta zuba
musu ido ,tasan da gayya take zub da kayan,zuciyar fadil na matuqar baci da hakan,a duk
lokacin da ta tsinci kayan takan bata lokaci mai yawa tana qissima dalilin barin kayan daga jikin
mai su wanda hakan ke qara ta'azzara kishinta ga aliyyu
Wani sabon rainin hankalin kuma sai ta fuskanci ya shigo ta soma gyaran sai ta shigo
tace"☺sorry fa don Allah,jiya na mance kayana akan gado wallahi dear ne ya rudani daren jiya
shi yasa da safe na manta da su ban dauka ba,kinsan shi akawai nacin abun,sai dai fa ba sauqi
shima fa gwani ne"wannan ya bata ranta fiye da abinda tayi mata,har ta soma hasashem
anya basu da masaniyar babu abinda ya taba gilmawa tsakaninsu?
Akwai lokacin da ta zube har da magungunan mata maau dauke da hotunan banza,wannan
fadila maganinta tayi ta dauko mata wasu wanda wata maqociyarsu a acan gida ta bata ita
basonsu take bame ma zatayi da su tunda ta bata ta jawo locker ta watsasu sai yau ta tuna da
su ta qara mata tace ga wasu sai ki qara naga naki basu kai wadanan tsada ba ni kinsan bana
amfani da su halitta ta bata buqatarsu komai nawa yaji ba sai da kwaskwarima ba"jiki a salube
ta karba duk da bata nuna mata hakan ba,ai kuwa da ta karanta kwalin sai taga tabbas sun fi
nata kyau to tun daga ranar bata sake bari ba
samira nata rashin mutuncin yafi ysakanin falo da kitchen parlour zuwa kitchen,zata dauko
plates ne kofuna ne da su spoon tayi ta batawa wani abun plate din ma leda ce ta chewing
gum ko biscuit zata dora akai kuma ta barshi a nan tunda ta sani cewa babu mai aikin gyara
gun sai fadilan,duk da wannan neman masifa da suke ba wadda ta isheta kallo a cikinsu
Su kansun so suke ta kulasun amma ta qi basu wannan dama
Mrs muhammad
✍✍✍
01:18 pm 05/11/1437
*wa yasan gobe?*
▶3⃣3⃣
Lahadi daya daga cikin ranakun qarshen mako ne wanda yake zama ranar hutu ga ma'aikata to
haka ne ya zama ga fadila hutun ya zame mata double babu zuwa office kuma bata da
girki,la'asar sakaliya ta ranar ta shirya tsaf cikin doguwar riga shigar da tafi so kenan ta material
ce ruwan qwaiduwar qwai dinkin rigar ya bude sosai dga qasa an mata dogon hannu tayi rolling
dinta kamar yadda ta saba da jan mayafi,takddunta ta diba na aikin office da takeson
dubawa zata yi wani aiki a kansu ta dauki yar madaidaiciyar dadduma da daya daga cikin
matashin kujerarta ta zira takalminta ta firo harabar gidan,sai ta tarar da saluma da samira
zaune kowacce a harabar sashenta bisa farar kujera plastic,novel a hannun salima samira
kuma na riqe da wayarta tana tana ta faman danne danne,tun kafin fadila ta kai ga zama ta
fuskanci zaman nasu ba na Allah da annabi bane don kuwa taba fitowa ta fara cin karo da
baqaqen maganganun da auke jifan juna da shi a fakaice ba tare da kowa ya kalli dan uwansa
ba
kamar ta koma ciki sai kuma ta duba agogon wayartataga biyar harda rabi da minti uku bata
da wani lokaci na duba takadddun idan ba yanzu ba cikin gidan kuma zafi yayi yawa sanadiyyar
hadarin da keta hadowa ana yin yayyafi dan kadan wanda ke qara tada zafin garin,ga injinsu
yayi tsiya yaqi tashi tun wajen uku bakaniken ke kansa yana fama da shi kasancewar ba dan
qarami bane yana daukar dukka freezers dinsu heater a.c da sauransu sun riga sun saba da
wuta ko yaushe 24 hours,sai kuma ta ahimfida dardumarta cikin ranta tana fadin _ina ruwan biri
da gada?_,tayi bismillah ta zauna ta soma aikinta,ashe duk suna ankare da ita,minti goma bai
cika ba da zaman nata samira ta soma receiving call "shegiya kina duniya?......heeeee wlh
gamu a cikinsa muna gogawa.......hahahahahaha aike kinsan fa hali tun ba yau ba"ta danyi
shiru sanna ta sake kecewa da dariya kamar wani gardi tace"a haba haba ke sai kace ba nice
samira ba?.....k kinsan saidai a gaji aqyale mana,kowacce qaramar shegiya sai ta kama
gabanta da qafafunta ,salima ta bude shafin gaba na littafin dake hannunta tamkar da gsken
karatun take tace"qaramin dan iska ma yaci uwatar ai yasan kansa,samira ta sake kecewa da
dariya "wlh har mai share share da goge goge ita wannan ai ba wahala zata bani ba.....yo
hannatu yar anacen ma ba komai bace a guna wallahi duk hasashen da take na ita wata ce a
gunsa
Sarai fadila ta san da ita take amma sai taga ba mutuncinta bane tsayawa tana cece kuce da
wadda batasan ciwo mutunci da kuma darajar kanta ba ,kan ta qare wannan tunani sai ji tayi
tas!
Da sauri ta dago idanunta don ganewa kanta wanda ka zubawa wannan lafiyayyen marin,aikin
salima ne tana tsaye a gaban samiran bayan ta kwasheta da marin tana huci,tuni samira ta
katse wayar hannunta na kan kumatunta ta miqe tsaye salima ta dora mata da bayanishiru
shirun da kike ganin ina miki ba fa tsoronki nake ba ki bar ganin kina min kina samun nasara
wallahi kin kaini bango nifa ba sa'ar yinki bace don uwarki"tasa yatsanta tan nuna qirjinta
tana cewa"ni kika mara?"an marekin kadan ma kika gani wata rana zaki ga abinda yafi marin
ma,kina tsammaninke kaďaice tantiriyar karuwa ko?to nima karuwace nayi nayi kuma
yaqon duniya fiye da naki ke da kika local ma
mamaki da tsoro suka kama fadiladama har akwai abun tutiya gun mace don tayi yawon
karuwanci?wannan wane irin zama nine da Allah ya kwomù da har karuwanci ya zama abun
ado?ita takaici ma sai ya sata ta maida kanta kanrubuce rubucentataqi kola kowaccensu
tana jinsu cacar baki mai zafi ta barke tsakaninsu tamkar zasu cinye junansu
Duf taji gun yayi shiru kamar an sanya musu kwado a baki,ta dago da hazari don ganin mai
ya sanya su yin shirun ba tare da kowa ya raba su ba?,aliyyu ne ashe ya ahigo kuma baau
ankara da shigowar tasa ba sai da ssuka soma daga hannu da niyyar kaiwa juna
duka,kowaccensu tayi sak saluma ce ta fara cewa wallahi tallahi ban kulata ba itace ta
fara takalatakuma ka tambayi fadila"jin sun sanyo sunanta cikin sha'aninsu ya sanyata azamar
taahi ta soma linke sallayarta,daidai lokacin da ya kai dubansa gun da fadilan take da salimar
ke nuna masa,ga mamakinsa tana gama ninke sallayar a nutse ta duqa ta mwaahe takardunta
ta juya ta shige sashen nata ba tare da ta kalli ko da daya daga cikinsu ba cikinsu ba sai aliyyu
ya bita da.kallo karon farko wani abu daga garetà ya fara burgeshi nutsuwarta ,sai da ta
shige ta kulle qofarta sannan ya dawo da idonsa kansu tuni samira har ta guduta rufe itama
qocarta cike da fargaba da tsoron fushin Aliyyu a akanta don ta tabbatar In dai ya bincika ya
tarar bata da gaskiya to la shakka fa kashinta ya bushe,ta ruwan sanyi yake ma hukuncin da
zaka raina kankà babu duka ba zàgi bà baqar magana,ya juyo ya dubi saluma da jikinta ke
rawa sai kawai shima ya gewayeta ya shige nasa part din
⚜⚜⚜⚜⚜
Kwana uku tsakaniya kamaqarshen wata ne,kamar yadda ya zama al'adar gidan fita aiyàyya a
iřin lokacin don sabunta abu uwan buqata na amfanin yau da kullum
Yaune za auyi fitar farko tun bayan dawowar salima gidan gidan
Fadila ta shiryq cikin shigarta ta bare bari tana nannade cikin lafayarta ,ta kammalà komai ta
kira umminta don su gaisa,hira suke sosai ta jiýo tashin horn ta tabbatar aliyyu ne don bai son
jira kuma baya jira saboda haka shima bai bari a jirashi tayi saurin maqale wayar a kafada tan ci
gaba da hirarta da ummin tasa daya hannunta dauki jakartata sa mèy ta kulle sashin,ta
qarasa jikin motar tana sallama da ummin ta ciro wayar daga kafadarta tana kashewa sai ga
salima da samira tamakar an jehosu kowacce na qoqarin bude gidan gana ta shige don badon
fadila tayi azamar matsawa ba da daita zasu yi awon gaba,ta rufe bakinta da tafin hannunta
dariya na shirin subuce mata,cikin zuciyarta tana cewa sunan wani film *qauyawa* Allah kayi
mana magani wannan ai kishin jahiliyya ne
Ku biyo *mrs muhammad*
✍✍✍
[10/16, 12:41 PM] Salma: 
*wa yasan gobe?*

*written by safiyya Abdullahi musa huguma*

▶3⃣4⃣
Allah ya sawwaqe tace,ta bude gidan baya ta shiga tana kallon drama,aliyu ne ya juyo don
ganin meke faruwa haka ake shirin cire masa hannun mota?cikin tsawa musu su matsa masa
daga jikin mota,bai wata wata ba ya figi motarsa ya barsu a gun sake da baki,gudu yake
zubawa abinsa bisa dukkan alamu ransa ya baci,duk sai fadila tayi tsuru-tsuru don da irin
wannan gudu da yake zabgawa gwara ya sauketa salun alun ,
Qiiiii...taji ya taka burki,ya gangara gefan titi ya faka motar cikin shaqaqqiyar murya taji yace"fito
ki dawo gaba don ni ba driver din gidanku bane"bata ce kanzil ba ta dawo gaban
Yanayin zaman yayi wa fadila kusa sosai,mayen turarensa ya soma raba mata hankali,lissafinta
ya soma qwacewa take kasala ta saukar mata,wani shauqin aliyyun ya mamayeta duk da
azahiri idan ka kalleta zaka yi tsammanin ko inuwar sa bata gabanta
Sun isa shoprite inda suka saba siyayyar duk qarshen watan,ta san tsarinsa bai shiga yana
tsayawa ne a waje yayi zamansa cikin mota,da sun gama siyayyar ayi masa total a turo masa
list da amount,da yake yana harka da su akwai kamfaninsa dake india wanda akwai hurdar
kasuwanci tsakaninsu,"u have twenty minutes idan kima gota haka so sai ki nemi motar mai da
ke gida"ta jinjina masa kai duk da idan da sabo yaci ace ta saba don duk sanda ya kawosu
mintina ashirin din yake basu basa kuwa darawar domin dukkaninsu sun san halinsa yana iya
tafiyarshi
A nutse ta shiga ta duba muhimman abubuwan da take buqata don tana lisaafin jibi ita zata
karbi girki duk da ba wani tsiya bane a ciki banda tsabar bauta ta gyare gyare da dafa masa
abinci wanda sau da yawa tare suke cinyewa da samira da salima ,sukan daidaici lokacin cin
abincinsa ne su shigo da nufin sun zo taya shi hira sai kuma su taya shi lamushe abincin
A gurguje ta kammala zabar duk abinda tasan bata da shi ba wani kaya ne mai yawa ba tunda
bata iya gama amfani da siyayyar tsohon wata suke sake sabuwa saidai ma wani abun ta bada
shi,sai ta soma dibarwa salima da samira abinda ta lura sunfi siya yawancin lokuta idan suka
zo,Allah ya taimaketa minti goma sha takwas ta gama komai,ta riqe leda daya ragowar aka biyo
ta da su
Tana fitowa suka yi kacibus da shi yana tsaye a hanyar wucewar tata,shi da wata matashiya ce
wadda a qalla shekarunta ba zasu gaza ashirin da shida ba,abunda ya bata mamaki shine
ganin hawaye bibbiyu bisa fuskarta,ta maida dubanta garesu a karo na biyu daidai lokacin
da aliyyun ya nuna ta da yatsansa yana cewa " this is d last warnings da zaki sake bina
wani guri ki kama kanki tun kafin ya gudu ya barki and respect ur self"
Sai taga kawai ya sa hannu ya rungumota kafadarsa sassanyan qamshinsa ya buwayi
hancinta suka bi ta gabanta suka wuce,cikin mamaki fadila ta waiwayo still tana tsaye tana
binsu da kallo hawayen na bin fuskarta,ta sake fashewa da kuka a guje ta nufi motarta ta
fada ciki,
Daf da zasu qarasa cikin motar wadda tuni an kammala zuba kayan taji ya tureta daga jikinsa
,ta tsaya a baya sai da ta bari yayi gaba sannan ta biyoshi,zaman kurame suka sakeyi cikin
motar har suka isa gida
Ta kammala shirin baccinta ya sanya night gown sannan ta dora dogon hijabinta mai hannu da
ya sauka har saman qafafunta ta sanya sannan ta kwashi ledojin da ta yima su salima ta su
siyayyar ta nufi sashensu,saidai ta tarar dukkaninsu basa nan don haka zuciyarta ta bata amsar
ba zasu wuce sashen aliyu ba
Can kuwa ta tarar da su kowacce ta debi fushinta akan ya wulaqantata ya tafi ya barta taje
masa da shi ,basu san ya fisu fushin ba don haka ci kanki ba wadda ya gaya mawa a cikinsu ya
watsar da su a falo ya shige dakin barcinsa ya shiga wanka,sun sani ba wadda tayi gigin binsa
ciki tunda suka ga ya musu banza to da tashi da su nan suka jibge a parlour zaman jiran sa,har
ya fito ba wadda ya kalla ya haye dining yana fama da girkin salima wanda,farar shi kafa ce
tsura babu salad ko cabbage bare akai ga batun nama,cikin qufula ya kira sunan salima da
suke zaune suna fama da 'yar harare harare,bisa kansa ta tsaya ita dole wadda akayiwa laifi ce
tace gani,ya dora gwiwar hannunsa saman table din ya hade yatsunsa cikin juna ya dora
habarsa a tsakiya sannan ya kalleta yace" sau nawa nake gaya miki I don't like such
cooking?,ko kayan cefanenki sun qare ne?ko sun qare ba zaki iya sanarmun ba kenan?,ta tabe
baki ta kawar da kai tace "kayi haquri "ya danyi shiru ya dafe kansa kamar ba zaice komai
ba,har ga Allah ba don yunwa ba baiga dalilin da zai sanya shi cin wannan abincin ba,ya shiga
tuna irin dandano mai gansarwa da yake samu duk ranar girkinta,ya dago kai yace bude fridge
dina ke debi cabbage da cucumber ki yankamin ki hada min da dafaffen qwai tunda yau ban isa
naci nama ba"ba tare da ta amsa ba ta juya
Mrs muhammad
✍✍✍
5:44 pm 5/11/1437
*wa yasan gobe?......*
▶3⃣5⃣
Da sallamarta ta shigo falon sam bata ma lura da shi ba bisa dining,ta dan dora murmushi bisa
fuskarta,salima ce ta masa sallamar itama ciki ciki kamar wadda aka cusawa tsumma a
baki,ta qaraso gabansu ta direwa ko wacce ledarta a gabanta tana cewa"sannunku,ga
siyayyarku nan Allah yasa na haso muku da abubuwan da kuke buqata " salima shiru tayi
saboda tafasa da zuciyarta keyi,yayin da salima yar takife tace" waye ya saki sarauniyar masu
shishshigi ,kina murna kina rawar kai an koro mu ke an tafi da ke,shine don digimi da neman
gindin zama harda wani yi mana siyayyar kaya ko?to ahir dinki wlh ni ba'a shiga gonata don kiji
na gaya miki,har wata fada ce dake a gunsa banda ta shara da zaki mana rawar kai?ko an gaya
miki sonki yake?"
"Hmmmm matar cushe kenan"cewar saluma da bata tofa ba sai yanzun,cikin wani irin mamaki
da al'ajabi ta dago tana dubansu,meke faruwa?a ina suka san wannan ?haka aliyyu ya gaya
musu cewar ba aonta yake ba?,wannan wane irin kwance zani a akasuwa ne?,wanne irin cin
kashi ne haka yayi mata?"take idanunta suka sauya launi,wani irin fushi da bata tsammaci tana
da shi ba ua sauko mata,kamar hadin baki suka miqe suna shirin barin dakim don dama
haushin kaza ne huce kan dami,tunda sunsan ko giyar wake suka sha basu isa su juye
haushinsu ba kan wanda ya musu laifin sai suka juyeshi kanta,suna shirin ficewa suka jiyoshi
cikin lion voice dinsa yana kiransu "ku kwashe kayan nan daga gun nan ku bace min da
gani"kunnen uwar ahegu sukayi niyyar yi a zafafe yace da su"�billahil azim duk wadda tabar
ledarta a nan tamu ce ni