Showing 99001 words to 102000 words out of 135036 words
Chapter 34 - Wa Yasan Gobe Compelet Book by Safiya Abdullahi Musa Huguma .pdf
bata nan,basu ga shigowarsa ba sai sumayya kawai don rabi'ah na kitchen duba
girkinta,fadila kuwa gashin da ya rufe mata fuska da yadda film din ya yafi da hankalinta sosai
yasa sam bata lura ba
Sumayya ta bude baki zata yi masa sannu da zuwa ya dora yatsansa kan labbansa,gum kuwa
tayi shiru,ya bata umarni na gaba da ido alamun ta tashi a hankali ta haye samansu,ba musu
kuwa cikin sada ta haura saman,gurbin da sumayyan ta tashi nan ya maye,harda dan jawota ya
jinginar jikin gwiwoyinsa,fadila uwar 'yan son jiki kuwa ya jingina abunta harda cewa"yauwa
sumayya dama baya na ya gaji,calabar ko ashirin bata kai ba amma taqi tsefuwa ta dadin
rai?"baice uffan ba ya kama jelar kitson ya soma tsefe mata kamar yadda yaga sumayyan
nayi,ita kuma bata damu da rashin amsawar sumayyan ba ta bayar duk film din ne ya dauki
hankalinta,rabi'ah ce ta fito da sauri daga kitchen din don kada tayi missing wani gurin,turus tayi
ganin aliyyun a gun da sumayya tasan ta bari,itama yatsan ya dora mata kan lips nashi,yayi
mata nuni da ido kan ta koma kitchen,nan ne ma fadilan taga giftawar komawan rabi'an kitchen
din "rabi'ah za'a wuce gun da kike son kalla fa" "ina zuwa anty ban qarasa hada miyar bane"
Gaba daya ya shagala,wani irin farinciki ke ratsa shi,santsi kyau da qyallin gashin ya hanashi
ganin wahalar tsifar,sai gashi sun kusa gamawa saura guda daya,yana ankare da yadda take
bawa film din muhimmanci,murmushi kawai take zubawa hadi da sakw gyara zama,sai da aka
zo wani gu da yayi masifar qayatar da ita ta saki murmushi tana cewa "hmmmm......soyayya" ta
dan waigo tana cewa"don Allah sumayya basu burgeki ba yadda....."kasaqarasa maganar tayi
ganin aliyyu zaune dare dare saman kujerar yaa mata tsifa,to sumayya ce ta rikide ta zama shi
ko idanunta ke mata gizo?.......
*Mrs muhammad ce*
✍✍✍
[10/16, 2:12 PM] Salma: 
*WA YASAN GOBE?....*


*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

*PART 3*
1⃣1⃣&1⃣2⃣
Sai da yasa bakinsa ya hure mata idon sannan ta dawo hayyacinta,da hanzari ta miqe sannan
kuma a guje tayi sama tamkar wadda taga dodo,binta shima yayi a hanzarce yana kiran ta
tsaya,ganin da gaske take ba tsayawa zata yi din ba ya sanya shi cafkota a matattakalar
qarshe,cak ya dagata yayi dakinsu rabi'an da take son shigewa,cikin sauri sumayya dake zaune
saman dressing chair ta fito ta bar musu dakin
Tsakiyar gado ya direta sai haki suke dukkansu saboda gudun da suka kwasa a step din benan
bugu da qari yadda zuciyar kowannensu ke bugawa,sun zubawa junansu ido cirko cirko da su
kamar zakaru,a hankali yake hawowa gadon yayin da ta soma ja da baya har ya qureta,suka
sake zubawa juna ido,shi nashi na tsantsar so da qaunace da suke sake huruwa cikin zuciyarsa
take kuma aika saqonni zuwa sassan jikinsa,yayin da nata kuma na jin haushi tsoro da fargaba
ne don bata manta wannan dare ba,kasa jurewa yayi sai da ya miqa hannunsa ya janyota ta
fado jikinsa ya matseta gam a qirjinsa
Cikin fusata haushi da mamakin aliyyun ta soma tureshi,saidai ko motsi baiyi ba don qarfin ba
daya bane,a hankali ya soma sinsinar wuyanta cikin kunnuwanta zuwa gashin kanta,ya dago
fuskarta a hankali ya tura harshensa cikin bakinta,tsotsa yake sosai tamkar wanda ya samu
sweet yayin da ita kuma take turje turje hadi da yunqurin tureshi daga jikinta saidai sam ma shi
baisan tana yi ba,ganin duk iya qoqarinta ta kasa barin jikinsa sai ta fashe da kuka,hawayen da
ya gangaro fuskarta ya taba nashi fuskar shi ya ankarar da shi,ya zare bakinsa daga nashi ba
tare daya bari ta bar jikin nasa ba,kukanta take sosai yayin da ya zuba mata ido,gaba daya ya
marairaice ya koma kalar tausayi " *fadeelahhhhh*"ya kira sunanta cikin wani irin yanayi tamkar
mai rada,da sauri ta dago kanta ta kalleshi don wannan shine karo na farko da ta taba jin
sunanta a abakinsa, "fadeelah" ya sake kiran nata ta sake itama kallon nasa "please fadeelah
forgive me,I know I hurt you I break your heart,babu wanda ya wuce kuskure,fadeelah I love you
more than words can say,I can't do without you,na kamu da soyayyarki,pls kada,pls kada kice
zaki hukuntani da tarin laifuffuka na,if bazaki iya yafemin ba ma na amince kiyimin kowanne irin
hukunci zan dauka,amma bazan iya jure rashin ki ba"
"Haka aliyyu ya shahara da yaudara?,haka aliyu yake?,taya mutumin da ya qika ya kuma sanar
maka bazai taba sonka ba yanzun yace yana sonka?,bazai taba yiwuwa ba it can't"ta fadi hakan
cikin zuciyarta tana girgiza kai,tayi wani kukan kura ta shammaceshi ta fusge daga
jikinsa,jikinsa ya riga da ya mutu shi yasa ta samu nasarar qwacewar,tana yunqurin sauka shi
kuma yana yunqurin sake cafkota aka turo qofar dakin,tuni fadila tayi amfani da wannan damar
ta shige toilet "qaniyarka,qaniyarka nace" cewar momi dake watsowa aliyyu
daquwa,sunkuyar da kansa yayi qasa yana Tsakiyar gadon da tuni ya bedsheet dinsa ya
yamutse,ta qaraso cikin dakin tana riqe da murfin qofar dakin da daya hannun ta nunawa aliyyu
waje "zo ka fice ka bawa mutane guri mara kunya,ka keta idanun qannenka ka biyota har kan
gadonta" "kai momi kamar ba mata ta ba"ya fadi hakan cikin zuciyarsa yana ficewa daga dakin
Momi ta qarasa bakin qofar toilet din ta qwanqwasa tana cewa "fito" fadilan kanta a sunkuye
kunya da takaici na sakadarta ta fito,momin ta dafa kafadarta tace "ko wani bak gaya min ba na
sani kina son ali,muma kuma bamu taba fatan aurenku ya rabu ba har a qiyama,munyi hakanne
don ya sake sanin darajarki da qimarka ta yadda ko nan gana bazai sake wasarere da
lamuranki ba,ki samu yi duk mai yiwuwa ki tabbatar da soyayyarki cikin zuciyarsa kin
fahimceni?" Cikin gamsuwa ta gyada kai tana yabawa momin ta yadda son kai bai rufe mata ido
ba,bata duba cewa aliyyu danta bane bare ta bari tana gani a cutar da ita ba,qaunar momin da
qimarta suka dadu cikin zuciyarta
*_1:30 am_*
Qarfe daya da rabi na talatainin dare fadila na kwance rub da ciki tsakiyar gadon ta,gaba daya
ta rasa bacci cikin idanun nata,duk juyin da zatayi qamshin turaren aliyyu take ji daga bakinta
har kayan jikinta,har kaya ta sauya amma a banza man kare don bata daina ji din ba,tana kallon
yadda su sumayya ke baccinsu hankali kwance sai take jin dama ita dince su,basu da wata
damuwa,wayarta dake gefan pillow dinta ta soma haske wanda ke nuna alamun kira ne ke
shigowa,cikin mamakinta daga wayra tana duban kiran baquwar numbace,ta zubawa kiran ido
har ya katse,ba'a fasa kiran nata ba har sai da ta tashi da missed call bakwai ana takwas dinne
ta yanke shawarar dagawa ko wani abunne ya faru,ta danna ok ta kara a kunannta tayi shiru ba
tare da tace komai ba
"Bakiyi bacci ba fadeelah?" Ya tambaya cikin wata iriyan sassanyar murya wadda har sai data
sanya fadila runtse idanun ta,tana jin qaunarsa na yawo cikin jinin jikinta,shiru tayi masa har ya
qara cewa "me ya hanaki yun bacci a irin wannan lokacin fadeelah?" Nan ma shirun ta sake yi
masa,saidai ita kadai tasan yadda take ni'imtuwa da jin muryarsa mai tsada "nasan kika jina
fadeelah,kuma bana tantama abunda ya hanani bacci shi ya hanaki....,sau da qauna ne ke
dawainiya damu baki daya,tunaninki shi ya hanani sakat kamar yadda na san cewa tunani na
shi ya hana miki yin bacci,da zaki ganni a yanayin da nake ciki zaki tausayamin,da zan iya ciro
zuciyata kiga dumbin qaunar ki da ta cikata fadeelah da nayi,na tabbata da sai kin min addu'ar
Allah ya rage min,jin shirun yayi yawa yasa yace "hello,are you there?" Ya duba phone dinshi
tana nan bata yi hanging up ba,ya sake maida wayar kunnensa yana cewa "please fadeelah
say something ko zan samu relief,am sorry fadeelah and I said it really" tsananin mamaki ne ya
mamaye fadila,shin da gaske ne ba mafarki take ba aliyyun ne kuwa?aliyyu salim maitama?
Aliyyunta?,mafarkinta na kullum,burin zuciyarta,shike gaya mata wadan nan tsadaddun
kalamai?....kalaman da ta dauki tsawon shekaru tana dakon jinsu?irin qaunar da ta jima tana
lalubenta daga gun aliyyun,shin da gaske ne a yanzu ta samesu?,eh...yes ta samesu but he
didn't deserve ya samu amsarta a arha har irin haka,now its her turned,its her field to play her
game.....
Muryarsa ta tsinto cikin sanyi yana cewa"fadeelah I know you gave me happiness and I gave
you a reason to cray,u gave me your care and I stabbed you from behind,am sorry for having
given you nothing in return for you having given me everything am sorry kiyi haquri....." kasa
jure ci gaba da jin kalamansa tayi,tasani ko iya wannan ya isheta,ta samu qauna daga gun
aliyyun,ta samu soyayyarshi,ya kawo mata kansa yana begging dinta ta bashi
soyayyarta.....,tuni ta katse wayar wani dadi na nuqurqusarta,ta sani tabbas zai kuma gwada
kiranta saboda haka ta kashe wayar gaba daya,cikin zaqi da gardin kalaman da aliyu ya
kasheta da su bacci yayi awon gaba da ita tamkar dama au take jiran ji,bacci ne mai cike da
mafarkan aliyyun a yanayi daban daban,shi kam tsai yayi da wayar a hannunsa cike da al'ajabin
yaushi mace ke kashe wa waya?,tabbas ya sake yarda fadilan tana da wani matsayi da babu
wata 'ya mace da ta kama koda gefanta
⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Tunda ta kashe wayar bata kunnata ba sai washegari sha daya na safe tana shirin tafiya office
sha daya na safe,cikin shadda take pinch sai maiqo take dinkin doguwar riga aka mata,cif cif
rigar tayi mata kamar a jikinta aka dinkota,ta bude sosai daga qasa rigar,tana cikin yafa orange
mayafinta sumayya na koda kyawun da tayi"wallahi anty kyawunki na daban ne Allah kuwa ba
don wai nayi ziga ba,ko bakiyi kwalliya ba kyanki fitowa yake,zanso yaya yaga wannan
kwalliyar"
Harararta fadilan tayi"ke dai kin shiga tara,tuni rabi'ah ta dade a school ke kin zauna kanzagi
kinqi fita,to bazai ga kwalliyar ba,sumayyan ta qyalqyale da dariya hadda kwanciya saman
gadon"wallahi anty kiyi a hankali kada amiki qwace don har yau yayin ya aliyyu ake ba'a dena
ba,kullum Allah ne da kullum wallahj dai ya fatattaki 'yammata,kada ki dauka qananu,a'a wlh
anty hadaddu masu ji da kansu 'ya'yan manya kuma",fadila ta tabe baki kishi na cin ranta duk
datasa haka dinne amma sai tace "dawar wani karkarar wani abincin wani kuma gubar wani"ta
dauki wayarta dake gefan sumayyan zata fice sumayyan nata sheqa dariya,text ne taji ya shigo
hakan ya sanyata dakatawa daga yunqurin fitar da takeyi,number din da aliyyu ya kirata ne jiya
Tun shidan safe saqon ya shigo "if u can't see the tears in my eyes,I beg you feel the pain in my
heart....fadeelah na rantse I will do anything and everything just to take away all d hurt that you
feel,please na roqeki give me and let me set thing straight,am sorry once again fadeela and I
love you I really love you...."gaba daya ya zare mata dukkan kuzarinta,jikinta ya saki,maimakon
fita sai ta koma bakin gado ta zauna,sumayya daketa leqen wayar tana qumshe dariya tace
"anty lafiya dai ko?" Ta saki ajiyar zuciya gami da dauke idonta daga kan screen din wayar
"lafiya lau me kika gani?"sumayya ta kada kai tana cewa "gani nayi kin shirya zaki fita kin dawo
kin zauna,jiya kuma fa anty naga cikin dare baki yi bacci ba ko" hararar fadila ta sake aika mata
tana kada kai cikin zuciyarta tana cewa "lallai na yarda ba qaramin illa soyayyar aliyyu ta yimin
ba,a fili sai kuma tace "naji to sai kuma akayi yaya?" Ta fada tana ci gaba da jifanta da hararar
wasa,miqewa summayan tayi tana ci gaba da qunshe dariyarta tace "k'n,uhmmmm,a'ah anty ni
bance komai ba daga wannan,amma dai anty kiyi a hankali saboda yayammu gwarzo ne kuma
gwani ne,he is hero,zai iya saaaaaace zuciyarki ba tare da kin sani ba"
Pillow dake kan gadon ta jawo ta jefi sumayyan da shi tana cewa "ban guri mara kunya" gocewa
tayi ta fice da gudu tana dariya,sake mai da kanta fadila tayi kan saqon taa sake karantawa,ba
shakka aliyyu shu'umi ne,so yake ta qarfi da yaji ya wargaza mata duk wasu makaman
yaqinta,ya shirya tunkararta da duk wasu makamansa wanda tana tsammanin indai haka ne
mawuyacine ta iya kubuta daga kaifinsu,duk ya kashe mata jiki kamar yadda ya saba ta qarfin
tuwo ta gayyato dauriya sannan ta samu ta fita,ta tadda momi da sumayyan a falo,ta yiwa
momin sallama,sumayya tace "a dawo lafiya anty.....momi dama inason baki labarin abinda na
gani dazu,wata soyayya ake mai fada fada aciki"ya fada tana satar kallon fadila dake qoqarin
ficewa daga falon fuskarta dauke da murmushi,a sace fadilan ta watsa mata harara mai nufin
gargadi a fakaice ta qarasa ficewa,sumayyan nata qyatunta tace "na fasa anty kada ki hanani
kudin ankon"..........
*Mrs muhammad ce*
✍✍✍

[10/16, 2:13 PM] Salma: 
*WA YASAN GOBE?....*


*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

*PART 3*
1⃣3⃣&1⃣4⃣
Qarfe hudu dai dai ta kammala sallar la'asar dinta a masallacin mata da nan cikin gidan
radiyon,ta goge kyakkyawar fuskarta da hoda,ta murza dan qaramin turarenta na (asaal brush
perfume)wanda bata rabo da shi cikin jakarta saboda dadin qamshinsa gashi kuma qaramine
baya da cika guri,ta saba jakarta bisa kafada sannan ta dauki wayarta ta nufi office dinsu don ci
gaba da aikin takaddun programme dinta na gobe da ta baro ta taho yin salla
Ta tura qofar ta shiga kasancewar babu kowa ciki fauziyya ta tafi yiwo wani aiki a a ministry of
education shi yasa bata damu da yin wani sallama ba,
Taja takardun gabanta bayan ta zauna ta dora daga inda ta tsaya,sosai yanayin tsarin
programme din na gobe ke burgeta muhawarar da za'a tafka cikin shirin,lokaci lokaci takan saki
murmushi gami da gyada kai,hakanan cikin jikinta ta dinga jin tamkar ana kallonta,cak ta tsaida
rubutun,kan ta kai ga yin komai an zuro hannu an zare takaddun,tabi hannun da kallo har zuwa
fuskar wanda ya gabatar da aikin,aliyyu ne tsaye qyam a agaban teburin nata,sanye yake da
shadda ruwan madara(milk colour) dinkin yarbawa,rigar iyakacinta gwiwa hakanan hannun rigar
shima gajere ne iya gwiwar hannu,sai manyan aljihu gefe da gefe,wandon dogo ne,kanshi babu
hula sai kyakkyawar sumarshi dake cike da gayu da tsafta,idanunsa na saye da gilashin nan
nasa fari qal wanda tana iya hango fararen qwayoyin idanunsa dake zube fes a kanta
Kallonta yake sosai ba tare da yace komai ba,da azama ta miqe hadi da ture kujerar da take kai
baya,tasa hannu zata dauki jakarta gami da qoqarin ficewa daga tsakanin table din,taku uku
yayi ya tsare mata hanyar ficewar,baya tayi da sauri saboda ganin yadda yayi gab da ita kamar
mai shirin fadowa jikinta,ganin ta sake yin baya ya sanya shi sake shigowa cikin shima,da haka
har ya danganeta da bango,sosai take jin fitan numfashinsa wanda ke cakude da qamshin
turarensa
Ya dage sai ya sanya qwayar idanunsa cikin nata,saidai sam taqi yarda hakan ya faru,lumshe
idanunsa yayi gami da nufar bakinta kai tsaye yana mai kwadayin tsotsar tattausan lips
dinta,tuni ta gano manufarsa ta sunkuya ta qasan table din ta zille,bai san hakan ya faru ba sai
da ya jishi ya dangane da bango,da sauri ya bude idanunshi,can ya hangota har ta dora
hannunta kan handle,cikin zafin nama irin na cikakken da namiji ya haura ta saman table din
don sai yafi masa sauri,taku hudu ya isa gareta,lokacin tuni har ta sanya qafarta waje
Jawota yayi har sai da ta fado jikinsa uasa hannayensa ya rungumeta,da qarfin tuwo take son
qwatar kanta saidai hakan ya gagara,batasan wani yazo gilmawa ya gansun a hakan saboda
qimar da take da ita agun dukka ma'aikatan gidan ba zata so hakan ya faru ba,ta kuma kasa
bude baki balle tace ya saketa sai kawai hawaye ya balle mata,Allah ya taimaketa sai ua
dauketa cak ya dawo da ita cikin office din hadi da murza masa maqulli ya kullesu
Kujera ya janyo ya dora ta akai yana maida numfashi,tsaye ya sake yi a kanta ya zube
hannayensa cikin aljihun wandonsa yana sake qare mata kallo kai kace ranar ya soma
ganinta,ita kuwa tana zaune sai qananun hawaye take,ya sake taku biyu ya matso gabanta
cikin wata iriyar cool voice yace da ita "fadeelah pls stop craying,I can't take it anymore,I know
shirun wanda aka ma laifi yake nufi...I know,ki hukuntani kawai fadeelah kimin hukuncin da kike
jij shi zai sa temper din da kike ji game da ni zai tafi,zan iya dauka,nasan duka girman laifi na ne
ya jawomin,amma fadeelah kinja bakinki kinyi shiru,kinqi cewa komai kwata kwata
why?,please(ya hade tafukan hannayensa)ko zagina ne kiyi fadeelah indai zakiyi magana indai
kuma hakan shi kadai ne hanyar da zai saki ki huce,ko duka na ne ma kike so kiyi indai shine
zai saki ki huce am ready fadeelah"
Ko daga kai ta kalleshi bata yi ba balle yasa ran zata ce wani abun,hakan take masa ko wani
lokaci,ya tsani shirun nan nata,yana ci masa tuwo a qwarya,ya fuskanci babu ta yadda za'ayi su
fuskanci juna babu ta yadda za'ayi ya samu abinda yake buqata matuqar ya barta taci gaba da
yin shirun bayan kullum bai cikin nutsuwarshi duk ta sanadiyyarta....duk ta sanadiyyar qaunar
da yake mata,bayan kk yaushe bashi da wani muradi sai nata,ta riga da ta gama kashe masa
jiki da qwayoyin sonta da bai taba tsammanin akwai kalarsu a duniyarmu ba,banda time to time
yana ganinta da yana tsammanin tuni ya dade da zaucewa,yana tare da ragowar matansa
amma ita yake gani,zaici abinci amma sai ua bude hotonta cikin wayarsaa fakaice yana kalla ko
da su salima na gun sanna zai samu ya iya ci
A yau dai yaci alwashin ba zaya qyaleta ba sai yaji ta bakinta,bazai barta ba sai anyita ta
qare,ya jawo daya kujerar ya zauna a gabanta gwiwarsa na manne da tata,yayi mata kane kane
ya hanata ta ko motsa duk lokacin da tayi yunquri sai ya maidata ya zaunar,idanunsa sun kada
jajur "I promised ko da yau zamu kwana anan indai bakice komai ba na shiryawa hakan,ni ko