Showing 3001 words to 6000 words out of 135036 words
Chapter 2 - Wa Yasan Gobe Compelet Book by Safiya Abdullahi Musa Huguma .pdf
ta fannin abubuwan ci da na sha,
Awa daya da rabi ta kammala komai ta koma dakinta tayi wanka ta shirya kasancewar tara da
rabi tana da lacture,dakin ummi ta shiga bata nan sai muhammad ta tarar yana kan gadonta
yana bacci,dala masa duka tayi tace"tashi malalacin banza eight thirty amma kana bacci ina
school din?"cikin magagin bacci yake murza ido yace"wlh nayi wanka bacci ne ya
daukeni"tace"oya tashi ka shirya idan zan wuce na sauke ka na baka eight minute"da sauri
kuwa ya duro daga kan gadon ya shige toilet
Bangaren abbansu ta wuce tare da diba masa breakfast dinsa ta tafi masa da shi,yana zaune
kan kafet din falon hannunsa dauke da jaridar daily trust,haka yake a al'adarsa bayan ya dawo
a masallaci yakan yi azkar da tilawar qur'ani idan gari ya dan sha kuma sai ya karanta jarida
kafin ya fita aiki,fadila ta shigo da sallama, ya masa yana dubanta fuskarsa dauke da
murmushi,ta dire kayan abincin ta rusuna tana gaidashi ya amsa yana fadada fara'ar shi
yace"sannu fadila da qoqari hala yauma anada da lacture din safen"kanta a sunkuye tana
qoqarin hada masa kunun shinkafa da yasha madara tace"eh Abba",ummi ce ta fito daga
bedroom din Abban hannunta dauke da doster da alama goge goge ta gama,fadila ta gaidata
tana qoqarin tashi tace"abba zan tafi"ya dubeta sannan yace"ai banga kin ci komai ba haka zaki
tafi?""abba zan karya a capteria idan na..........
Ummi tayi saurin katse ta da cewa"yi mana shiru wlh abbansu idan taje ma bacin take ba farida
ai ta gaya min wai ba zata iya cin abinci a waje ba,wannan yarinya na rasa meke damunki anya
lafiyarki qalau kuwa?",abban yayi murmushi yana dakatar da ita"dakata umminsu,fadila lafiyar
ta qalau,kin manta yawon asibitin da muka dinga yi da ita tun tana qarama?,haka dai halittarta
take"ya juya ga fadila yana tura mata cup din da ta hada masa kunun yace"maza zauna kici
wani abu kada ki qara bata ran umminki kinji ko?"tamkar zata sa kuka ta zauna tana cewa"to
abba"yaci gaba da cewa"gashinan fadila tafiki abin arziqi shi yasa ta rainaki tana ganin kanku
daya,ummin tace sai rawar kai da gwanintar yin girkin amma saidai wasu su ci mata,abban yayi
murmushi yana kallon yadda take tura abincin kamar magani
Kafin ta kammala muhammad ya shigo don haka abban ya sallamesu suka fita tare,suna mota
muhammad ya dameta da surutu,ta daga masa hannu ✋hadi da cewa kaga malam bafa aku
na dauko baidan kuma kai aku ne ka gayan"ya qyalqyale da dariya yace"anty ke dai
ba dama mutum yayi hira dake sai kice ya dameki shi yasa yaya farida ke burgeni ke halin ya
ahmad kikayo kun fiya kwafsawa wlh,ta harareshi sannan tace"ai da itan da kai duk zamuce ta
tadda mujemu idan mutum baiyi surutu ba baya burgeku,kada Allah yasa mu burgekun muyita
kwafsawar,idan ka qara magana kuma sai na saukeka anan" take ya rufawa kansa asiri yayi
shiru
Taso makara saboda ajiye muhammad da tayi don ita ta saba da wuri take zuwa don ta samu
sit din gaba,bata da wata qawa bare ta tarar mata hakan ya jawo batayi parking din motar ta
daidai ba ta nufi ajin cikin sauri
Lacture din ta daukesu awa uku har da mintina,kanta ya dauki chargy sosai,don haka da
fitowarta ta samu wani guri dake nesa kadan da ajinsu bashi da yalwar jama'a sosai yafi kusa
da inda suke ajjiye motocinsu idan sunzo,gurine mai wadatar shuke shuke ita kuwa ma'abociyar
son tsirrai ce [8/8, 3:24 PM] LOADING......
gun na burgeta saboda son tsirran da take dashi,tamkar a cikin iska ta ke jiyo
qamshinsa,gabanta ya tsananta faduwa,ta gefan ta ya wuce saidai bayansa kawai take iya
gani,ahigar suit ne a jikinsa masu dan karen kyau da sheqi,kayan baqaqene sai tsintsiyar
hannunsa da ta gani wadda yake daure da agogon fata baqi,gefansa wani ne ke biye da shi riqe
da takardu da brief case,sam sai ta kasa dauke idanunta daga kanshi,hakanan gabanta
yaci gaba da faduwa cikin zuciyarta take fadin inna lillahi wa inna ilaihir raji'un"har ya danyi nesa
da ita sai taga ya waiwayo,cikin wani irin sauri ta dauke kanta tayi wani sashen da shi zuciyarta
kamar ta tsinke ta fado,ganin yayi gaba tayi hamdala da Allah yasa bai lura da ita ba,tana
tsammanin jikinsa ne ya bashi ana kallonsa,a sace taci gaba da kallonsa har ya bacewa
ganinta,taja ajiyar zuciya sannan ta dauke idonta daga kallon hanyar ta jawo jakarta ta zuge ta
fiddo da wayarta tana danne danne,ta doshi kusan minti aahirin a gunbtana hutawa sai sannan
ta tuna zata fa gidan ya ahmad,da sauri ta miqe tana gyara yafen gyalenta,atamfa ce ajikinta
dinkin riga da skirt ne,atamfar England ce dark green mai ratsin yellow,sai mayafinta da
takalminta agogo da jakar hannu duk yellow,fadila ba qarya ta iya daukan wanka don duk munin
atamfa takai aka mata dinki ya saka komai kushe da hassadarka baka isa kace batayi kyauba
haka Allah ya bata wannan baiwar,tana tattare komatsanta tana sanyawa a jaka taji ana kwada
mata kira,a nutse ta dago tana neman daga ina wannan kiran mafarautan ke fitowa?,wata class
mate dinta ce binta auwal fadila taci gaba da binta da kallo har ta qaraso,"fadila abbas yaufa
kinyi tabargaza"abinda ta soma cewa kenan,fadila tace"kamar ya fa?"tana dubanta tace kinyi
wrong parking kin toshewa A.s mai tama hanya"ta sake dubanta cikin rashin fahimta tace"waye
haka kika bi kika rude?'binta ta zaro ido tace"kar dai kice min baki san a.s mai tama
ba,hadadden guy din da duk nigeria bama kano ba ansan da zamansa"fadila ta dakatar da ita ta
hanyar cewa"na gode"taci gaba da mayar da kayanta jaka
Iya dube dubenta ba wanda ta gani sai mutum daya,a tsammaninta idanunta ke mata
gizo,sai dai har ta qaraso gun shi din dai ta gani,yana tsaye hannayensa harde a qirjinsa
fuskarnan a murtuke,ta qaraso ne da niyyar bashi haquri sai dai lura da irin kallon qasqancin da
yake mata mata yasa tayi banza da shi kai tsaye ta nufi motarta ta bude,ta zauna a seat din
tana qoqarin jan murfin ta rufe taji an dafe murfin motar,ta dago ta dubeshi,yana tsaye yana
mata irin kallon dazun,cikin qasaita taji yace"baki da ladabin bada haquri ga wanda kika
aikatawa laifi?"duk da yadda zuciyarta ke sake ninqaya a zuciyarta,muryarsa mai sanyi ta
kwanta a zuciyarta,amma ta dake gami da cewa cikin zuciyarta"duk da dumbin qaunar da nakeji
taka a zuciyata hakan bazai sa na bada girma da jan aji irin na 'ya'ya mata,ta dauke kanta
sannan tace"ai shi wanda akawa laifin baisan darajar bil'adama ba"ya saki murfin motar hadi da
watsa hannayensa yace"ok,ba laifi"ya saki murfin motar,cikin wata iriyar gaggawa taga ya amshi
key din tasa motar daga hannun wanda suke tare ya bude motar sa ya shiga cikin gwaninta ya
take motar ya kurda ya matse motar fadilan ta yadda itama bata isa ta fita ba harsai da ya
gogeta,ya kashe motar ya zare maqullin ya rufe motar ya fito yana cilla maqullan yana cafe wa
ya danyi tsalle ya haye bayan motar ya zauna,da hannu ya kirashi yadan yi masa rada ya amshi
tak ardun hannayensa shi kuma ya juya da sauri ya bar gun
Sarai fadila ta fahimci abunda yake nufi saboda haka ta zaro wayarta ta nemi number farida ta
kirata"hello farida kin shigo school?"tace"eh ya akayi?""kizo ina parking space ki daukeni mu
wuce"farida tace"me ya sami motar ki?""kinga idan zaki zo kawai kizo malama""ok sister gani
nan" Cikin 'yan mintina sai ga farida horn tayi mata ta miqe ta fito ta kulle motar ta gabansa ta shige
ta nufi farida,dai dai lokacin ta jiyo saukowarsa daga bayan motar,wata yar qaramar mota ce
tayi parking a gabansa kusan tare suka shige motocin,ta madubin motar farida suka hada ido ta
sakar masa tsaki hadi da murguda baki,cikin zafin nama ya balle murfin motar ya fito da sauri
tacewa farida"yi sauri ki bar gurinnan,tamkar kuwa tasan meke faruwa ta figi motar ta bar gun
Muje zuwa
[10/16, 12:21 PM] Salma: 
Wa yasan gobe?
Safiya Abdullahi musa huguma

▶4⃣
Sai da motar ta saitu akan titi sannan tace mata"gidan ya ahmad fa zamu"ok" inji farida,"sister
wai me ya faru naga kamar wadda aka biyo a guje?"taja tsaki tace"wani dan rainin hankali ne
yaso wulaqantani bai san bana daukan wulaqanci ba"ta bata lbr yadda sukayi da shi akan toshe
ma juna hanya da sukayi,me farida kuwa zatayi idan ba dariya ba,"kefa 'yar wulaqanci ce shi
yasa ban fiya saki cikin lamarina ba,a yar madaidaiciyar harabar gidan sukayi parking,kai tsaye
suka nufi falon gidan,ba kowa cikin falon da alama matar gidan na ciki don haka suka dinga
kwada sallama,daga kitchen matar gidan ta fito anty hafiza kenan kyakkyawar bafullatana,tana
ganinsu ta saki fara'a cikin barkwanci tace"lallai yau baquntar tamu ce"suka saki
dariyadukkaninsu suka gaidata cikin girmamawa ta amsa musu cikin kulawa tana tana
tambayarsu ummi,suka ce tana lpy tana gaidata,fadila ta zaro packet na chaculet tace gashi
injita a baiwa twince,wai ni ina suke nema anty?""tace yau ai ranar school ne suna can amma
suna hanya don bala ya tafi dauko su,""na manta wlh"ta fada tana qoqarin kwanciya bisa
doguwar kujera"anty hafiza tace"ah ya haka ina murna kuku tazo kuma naga tana neman bin
lafiyar kujer?"fadila ta dan murmusa tace " anty yau saidai amin afuwa yau kasala nake
ji""na miki"inji anty hafiza,farida dake canza tasha a t.v tace"qyaleta anty muje na canjeta yau
tsokano fada tayi sauran kadan taci na jaki badan Allah ya kawoni na ceceta ba""tab wucenan
wlh wa ya isa yayi gangancin taba mana ita?""fada mata dai anty"cewar fadila,suka
shige kitchen nan suka barta a falon Gyara kwanciyarta tayi don taji dadin yin tunaninsa,shi wa?,idan bata manta ba A.S mai tama
binta tace da ita,A.S mai tama ta shiga maimaita sunan ita da zuciyarta,"to me A.S mai tama
take nufi?"A dai duk inda aka zaga farkon sunansa ne,to ahmad ne ko ko abubakar ko
abdul?,oho itama bata sani ba,wani murmushi ne ya subuce mata sai tunaninta ya dawo
kan abinda ya faru tsakaninta dashi dazun,sassanyan muryarsa ta dinga yi mata amsa kuwwa a
kunnenta,kyawawan idanunsa yanayin zubinsa da tsarinsa,sai ta tuna sanda ya fito a fusace
lokacin data murguda masa baki ta harareshi,nan ma dariya ce ta subuce mata,"lafiya kuwa?"ta
tsinci muryar farida na tambayarta,ta hade rai tace"lpy lau me kika gani?"farida ta dan tabe baki
tace"hmmm tun dazunfa kike murmushi har da dariya ke kadai kamar wadda ta fara soyayya"da
sauri fadila ta kalleta tace"lallai yarinyar ni kikewa wannan titsiyen?to gyada na zama na soye
qarewar soyayya"anty hafiza dake zaune saman kujera bata sa baki ba sai yanzu tace"um um
yaya fadila wannan fa sign ne na falling in love"fadila ta miqe daga kwanciyar tana
cewa"kai anty,please kada ki biyewa shirmen farida,ita 'yar sa ido ce komai ta gani idonta na
kai,kuma sai ta sanya ma question mark",ta gyada kai sannan tace " alright idan tayi wari
maji,Allah yasa alkhairi ne""amin amma ba abinda zaiyi wari ma anty",nan gidan suka wuni har
'yan biyu suka dawo suka yini tare da su,suna son yaran sosai ko dan su kadaine jikokin gidan
nasu,sai bayan magariba sukayi sallah sukaci abinci har yaya ahmad ya dawo ya tarar da
su,bayan sunyi shirin tafiya ne ya ahmad ya baiwa ko wacce 4000 anty hafiza kuma ta basu
turarurruka.
to daren ranar sam fadila bata samu bacci ba,kusan kwana tayi tunanin A.S maitama,duk da ta
danji dadi don aqalla tasan yanzun yasan da fuskarta a duniya,koda bazai iya shaidata ba bare
tana tunanin mawuyacine ace yayi saurin manta ta ko dan irin karon da suka yi,har washegari
da taje school bai janye motar tasa ba,sun dauki aqalla sati guda a haka sannan taje ta tarar ya
cire,a gida tace ne kawai tana tana garage ana duba mata ita
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Cikin wannan yanayin suka soma attachment,ranar laraba aka turasu domin tattaunawa da
wani fitaccen dan kasuwa,ita da abokiyar karatunta ne hafsat sai wani ma'aikacin gidan radion
khalid da zasu tafi tare qarfe hudu na ranar larabar.
cikin yellow din atamfa ta shirya mai zanan blue din qananun taurari,skert ne rafa da riganshi
wanda dinkin yayi mata cif a jikinta kamar don ita aka qera atamfar,ta maqala qananun fashion
na dutse masu kalan blue,ta daura dan siririn agogo na fata ,qafanta blue din hill shoes ne mai
madauri sai mayafi data yafashi a kafada bayan ta soka daurinta wanda ya fito da dogon
gashinta ta qasan daurin,jakarta ta dauka 'yar madaidaiciya wadda ake maqaleta a gwiwar
hannu ta feshe jikinta da turaren shamsul imarat,shigar ta haska fatarta sosai ta fito dagwas da
ita,farida dake nade a tsakiyar gadon fadilan tana charting ta dago ta dubeta"gsky yaya fadila
kinyi masifar kyau,tsiyar abun daya da baki kula kowa,sai ance anasonnki kuma ki kama mita
bayan laifinki ne saiki yi shiga ta janye hankali kuma kice ba wanda ya isa ya kalaki"banza tayi
mata ta dauki wayarta dake kan dressing mirror ta fice,farida ta dan daga murya yadda zata
jiyota tace"a dawo lpy antyna Allah ya hadaki da mannau ya biyoki har gida"bata dai ce
mata ci kanki ba ta wuce dakin ummi don tasan a wannan lkc tana daki tana azkar,daga bakin
qofa ta tsaya don ta kusa makara tace"ummi zan tafi""to Allah ya tsare hanya ki kula sosai
kuma kuna kammala abinda kukaje yi ki taho gida kada ki yadda kiyi dare a waje"tace insha
Allah ummi",acan gidan radion suka hadu,bata shiga ba ta yiwa su Hafsa waya su fito su wuce
don a motarta suka tsara za suyi tafiyar,Hafsa na zaune a baya yayin da khalil ya shige
gaba,tsaf fadila ta gama karantar manufarsa saidai tayi banza da shi tamkar bata fuskance shi
ba,tun zuwanta gidan yake rawar qafa a kanta saidai ya kasa furta mata kamar sauran maza da
yawa,tana da wani irin kwarjini ne a idanunsu ita sam baya burgeta,ya fiya surutu shi yasa sam
bata son ko aiki ne a hada ta da shi,kamar yanzun ya takura mata sai zuba yake shi ala dole sai
ya burgeta,Hafsa na baya tana ta tuntsira dariya don tasan halin kayarta sarai,daqa qarshe
c.d plate ta dauka tasa sannan yayi shiru
A hankali suke binkwatancen har suka gano gurin,qaton get din gun aka bude musu gu ne a
tsare ahankali aka dinga nuna mata inda zata bi har taje inda aka tana da don ajiyar motoci tayi
parking suka fito,ta jingina jikin motar tata tana qarewa gun kallo,tamkar ma'aikata gun yake
saidai ya tsaru sosai komai neat,khalil ya qarso gunsu bayan yaje yayi tambaya yace muje can
sunce mu jirashi yana fitowa,wani dan gune da ka qawatashi da flastic din kujeru da teburinsu
kowanne yaja kujera guda ya zauna
sun dan dauki mintina har fadila ta soma qosawa da zaman jiran
Tun daga nesa da ta hangoshi qirjinta ya hau luguden bugawa,ji tayi tamkar ta tashi ta bar
gurinsai kuma taga idan tayi hakan ta bada kanta,don haka sai ta basar ta zarme da bude
jakarta ta soma fiddo da kayan aikin da zasu buqata,qashin mayen tutarensa da taji ya mamaye
gurin shi ya tabbatar mata da qarasowarsa,sallamarsa ta same tabbayr mata da hakan
dukkansu suka amsa saidai ita ta kasa dago ido ta dubeshi ta fake da laluben jaka,ya .iqawa
khalil hannu sukayi musabaha hafsat ta gaidashi,sai a sannan ta dago kanta caraf suka hada
ido saidai ga mamakinta dauke kansa yayi tamkar bai taba ganinta ba,a hankali ta radawa
hafsa"da wa za muyi hirar ne?""gashinan a gabanki a.s maitama "inji hafsat"take taji ta dan rude
amma cikin dabara ta gayyato dakiya da nutsuwa ta yafawa kanta,kasancewar Ita ce mai
tambayoyin jfsat da khalil na tayata da rubutu dolenta ta jawo kujerarta ta sake matsowa daura
da shi ta sanya 'yar qaramar recorder dinta a tsakiyarsu suka sake zama verry close aunyi face
to face sosai,wani yanayi ya dinga shiga zuciyarta da gangar jikinta wanda hakan ya haifar
mata da kasala,tanason tayi.masa tambaya ta farko saidai ta kasa,har sai da hafsat ta dan
dungure sanna tayi ta maza ta dago ta fuskanceshi,saidai ga mamakinta hannauensa na
harfe ne bisa qirjinsa yana mata wannan salon jallon rainin nasa,da fari munason muji
ainihin cikaken sunanka,ta fada yayin da ta mayar da dubanta kan radio dinta taga tana nadar
sautin yadda ya kamata,shiru taji har yayi yawa ta dago ta sake dubansa a karo na biyu,saia
taga ya saki hannunsa ya dauke idonsa daga kanta ya kalli khalil yace"ko zakuyi musayar aiki
ita ta ta karbi rubutun kamar ba zata iya aikin ba"khalil ya dan rusuna yave ranka ya dade zata
iya haka tsarin aikin yazo"ya kalleta cikin gatsali yace"zaki iya?"batayi qasaaqwiwa ba tave aisai
an gwada aknsan na qwarai"ta mayat masa da irin yanayim yadda ya yi mata tambayar,cikin
ransa yake jinjina rashin kunyarta tare da fafin nasan maganinki" a zuciyar sa ya fadi hakan
Ku biyoni muje......
[10/16, 12:21 PM] Salma: 
Wa yasan gobe?
Safiyya Abdullahi musa huguma

✍✍✍✍
▶5⃣
Ya dan gyara zamansa cikin isa ya amsa mata"Aliyyu salim maitama shine cikakken
sunana""sunan ya dace da maishi"ta fadi a ranta,cikin nuna qwarewa da gwaninta ta shiga jefa
masa tambayoyi daya bayan daya,sai da suka kwashi kusan awa guda sannan ta saurara
masa,ta katse abun recording din nata ta jefa a jakarta,ta miqe tayi gaba abinta,saidai can
qasan zuciyarta farinciki ne fal ranta,yau ta zauna daf da shi ta shaqi qamshinsa ta saurari
muryarsa son ranta,shi kam bin ta yayi da kallo cike da mamaki da takaicin raininta don a
gurinsa wannan raini ne.
Zaman ta tayi cikin mota tana dakon zuwansu hafsat
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Dukkaninsu suna gidan alh salim,kasancewar yau ake birthday din iftihal,rabi'ah sumayya farida
da fadila anty hafiza sai anty hauwa'u(babbar yar haj maimuna)duk suna bedroom din
momi,fadila na kwance bisa gadon momin,dakin ya kaure da hayaniya amma banda ita,sam
gun ma baya mata dadi,tun jiya da Abba yayi mata da ya ahmad suka yi masu magana ita da
farida kada su kammala attachment dinau ba tare da sun kawo mijin aure ba,farida kam ko
ajikinta tunda dama irin wannan damar take jira ita da masoyinta mubarak
Ta sake juya kwanciyarta hannun damanta kanta yayi mata gingirin zuciyarta a cunkushe,anty
hafiza ta juyo ta kalleta "fadila ki saki ranki don Allah