Showing 72001 words to 75000 words out of 135036 words
Chapter 25 - Wa Yasan Gobe Compelet Book by Safiya Abdullahi Musa Huguma .pdf
ban barakwai,ta ajjiye cup din hannun nata a hankali ta qarasa
dining din,ya sake kurbar tea din idanunsa na kan ruwan tea din da yake sha "sit" yace da ita,ta
ja kujerar gami da kasa kunne tana sauraran mai zaya ce mata
Bai ce komai ba har ya kammala breakfast dinsa,qamshin da yake ji ne ke rudashi ya rasa
wanne irin mayen turare take amfani da shi ya zaro tissue daga cikin tissue dice box yana dan
goge hannunsa inda ya bacin "as from today kada ki sake kawomin abinci ki bar gun har sai na
kammala understand?"(nikam cewa nayi hmmmmm,fadi gaskiyarka na daure.......) "mutum sai
shegen mulkin tsiya ba haka nake masa ba a nijeria wani lokacin bai taba cewa don me ba sai
yanzu?wato zai fara fidda sabon salo don yaga ba'a gida muke ba"cewar fadila ita da
zuciyarta,a fili kuwa gyada kai tayikata na a qasa "hey" ya sake cewa ta dago ta dubesa ta sake
sadda kai "open ur mouth u r not a bruise" to tace masa cikin qosawa da zaman
Har ya ja kujerarsa baya yana niyyar tashi don ya tabbata ya sake qara wasu mintina a gaba
bai bar gun ba tabbas bazai iya mallakar kansa ba,abunda yake ji a cikin gangar jikinsa is very
strong feeling,yana so yace ta daina amfani da perfume nata amma girman kai ya hana, yana
ganin idan ya fadi mata zatayi tsammani ya damu ne da wani abu nata,he feel he can sustain
whatever zaici gaba da ji,wayarsa da ta soma kadawa cikin tattausan ringing ita ta dakatar da
shi daga tashin da yayi niyya
Mrs muhammad ce 
✍✍
[10/16, 1:57 PM] Salma: 
*WA YASAN GOBE?..*


*written by safiyya Abdullahi musa huguma*

*part 2*
3⃣5⃣&3⃣6⃣
Ya ciro wayar ya duba mai kiran ya dan saki ajiyar zuciya kadan sannan yayi pressing ok,sunan
da taji ya ambata ya sata gane da wadda ya ke wayar,salima ce,hira take yi masa sosai yana
dan biye mata,hirar da tasa fadila kasa jure zaman gurin ,satar kallonsa take ta qasan ido gaba
daya launin idanunsa sun canza muryarsa ta sake zama so cool
Idanunsa na kan fadila lokacin da ta miqe don basu guri don zuciyarta ta samu salama daga
mugun kishin dake taso mata,ya dan daki table din da hannunsa wanda yasa fadila daje shirin
sauka juyowa suka hada ido da shi,fararen idanun nan nasa da sukayi returning zuwa ja ya
lumshe su sannan yayi mata alama ta koma ta zauna,kamar ta zura da gudu tabar gurin haka
taji saidai ba yadda ta iya ta koma din
Minti biyu tsakani yayi sallama hadi da kissing wayar sau uku,lumshe nata idanun tayi tanajin
wata dalmar kishi na digar mata cikin zuciyarta,bata bari shaidan ya kitsa mata komai ba ta
soma karanta *hasbunallahu wani'imal wakil*,wani gumi ta gani yana tsatstsafo masa ya maida
jikinsa ya jingina sosai da makarin kujerar idanunsa a rufe wani weakness yake ji sosai cikin
jikinsa
ya dauki aqalla minti goma sha biyar a haka kafin mood dinsa ya dan saisaita ya dinga sakin
'yar qaramar ajiyar zuciya a jajjere,har a lokacin fadila na satar kallonsa tana mamakin meke
damunsa haka mood dinshi yayi bala'in canzawa within few minutes,ya sauke doguwar ajiyar
zuciya lokacin da yake bude idanun sa,caraf ya kamata tana kallonsa sai yayi wani kicin kicin
da rai yana ganin kamar tasan meke damun sa,sunkuyar da kai tayi shi kuma ya zark
handkerchief ya share ragowar zufar fuskarsa
Sauka yayi a ahankali daga dining area din ya shige bedroom,tana zaune a gun ya sake fitowa
wannan karon yellow and coffe din suit ne ajikinsa da alama kaya ya canza koma wanka yayi ne
oho wa yasan masa,hannunsa riqe da brief case yana amsa wayar mr lien a
hanzarce yake tafiya ya sanya hannu ya bude pocket din sa ya zaro yuan dari ya ajjiye
mata(five thousand kudin naija) kana ya dago suka sake hada ido dukkaninsu sunji jiki ita ta
sunkui da kai shi kuma ya fice a hanzarce,ta kalli kudin ta tabe baki "ne me zanyu da kudin
qasarsu?tabdijan" ta fada a fili amma qasa qasa kamar mai gunguni
Yana fita lukas da andi na qofar gida cikin motar kamfaninsa da yake shirye shiryen budeshin
*maitama group of companies* haka yake kowa yasan da su,da fitowarsa suka sara masa
kamar wani soja sukayi handshake kamar yadda yake a al'adar sa don dabbaqa value ba
addininsa a ko ina yake,lukas ya bude masa qofar zungureriyar motar ya shiga suka rufa masa
baya
Driver din ya bawa umarnin yabi ta lujing road huangtian street zasu fara shiga yueyang hotel
yana son ganin ramzan dan india ne wanda yana daya daga cikin wadanda ya bawa contract
na ginin factory din nasa,factory ne babba na qashin kan aliyyu wanda ya narkar da maqudan
kudade gurin samar da shi,factory ne da zai dinga manufacturing kayan babies blouses na
maza da mata
Wunin ranar cikin zirga zirga mai yawa yayi ta ahiga can fita nan,hakan ya taimaka masa sosai
gurin rage masa abinda yake ji cikin jikinsa,yayin da a daya bangaren fadila ta wuni kwanciya
sai bayan ta idar da sallar la'asar sannan ta shiga kitchen,pepe chicken couse couse da miyar
qwai sai mutuminta lemon kwakwa da ya wadatu da madara da flavour wannan shine jadawalin
abincinta na dare
Nan da nan ta gama kasancewar gas din nata mai hudu ne,ta turare gidan nata da turaren
wutanta bayan ta zuge duk wani glass da window dake gidan,sai gidan yayi wani dumi mai dadi
daya gauraye da qamshi,cikin ruwa mai zafi sosai tayi wanka saboda sanyin dake damunta na
garin,riga da wando tayi shirya kanta ciki wandon dogone har qas pencil rigar kuma da kadan ta
rufe cikinta jacket ta saka mai kauri ta mata wanda ta sauko har qasan gwiwarta tana da dogon
hannu sai manyan maballai guda shida masu fadi da aka jera daga gaban rigar kusan sune
kadai adonta,rigace da yawanci a turai matansu ke amfani da ita musamman lokacin sanyi
Gashinta ta gyara sosai ta kamashi da band ta saya socks qafa da hannu ko zata samu sauqin
sanyin,da turarenta ta shafe jikinta ko ina ciki da waje,ta maida ta tattare abinda ya dan
yamutse a dakin ta gyara shi sannan ta ciro jakar laptop dinta da sam ta manta da ita ta cirota
tasan saqonnin email na nan na jiranta jingim ta dauki wayarta ta dawo falo
Sai da ta zauna sannan ta duba agogo don ganin ko lakacin sallah yayi don bata tsammanin
akwai masallaci anan inda suke tun da tazo bata ji kira ba da agogo kawai take amfani ko
dazun ma sauran kadan sallar azahar ta qwace mata,lokaci kadan ya rage lokacin sallar ya
shiga don haka sai ta jona chargy na laptop din nata sannan ta zira hijabi ta shimfida dadduma
ta tada salla
Bayan ta kammala ne ta ninke hijabin hadi da daddumar ta maida daki sannan ta dawo kan
computer din tata,aikam ta tarar da saqonni masu yawa anty hafiza sumayya rabi'ah na sister
farida ne akan gaba harda pictures din baby humaira masu yawa har da na ya ahmad ragowar
kuma duka na masoya ne na gari dake qaunarta ,na 'yan uwanta ta soma dubawa kowanne na
tambayarta ne sun iso lafiya? Da makamantansu,dai sai taji kewarsu ta cikata take ta shiga
maida masu amsa lallai duk wanda yabar gida gida ya barshi,sai data gama da su sannan ta
soma duba na sauran jama'a wanda ke da muhimmanci ta maida masa amsa mara amfani ta
goge shi
A hankali ta daga kai karo na farko ta duba agogo,tara da mintina goma sha biyar,duk da cewa
unguwar da haske ta dan soma duhu alamun dare ya soma kenan wasu sun kashe
qwayayensu "me ya tsaida shi tun safe har yanzu?" Fadika kewa kanta wannan tambayar da ita
kanta bata san amsarta ba,fargaba ta dan soma shigarta da tsoro lokacin da idanunta ke ganin
kamar ana gilmawa ta cikin balcony dinsu,ta miqe a dan tsorace ta maida hijabinta bayan ta
zare computer din daga jikin socket ta maida daki ta dawo falon ta tayar da isha'i
Har ta idar babu aliyyu ba alamunsa,zama tayi kan daddumar jiki a takure,kewa ce sosai ta
kamata,ita ba layin qasar cikin wayarta bare tayi kira,a gogon ta sake kalla ya nuna mata qarfe
goma da minti biyu,tsoro ya sake shigarta musamman da taji unguwar ya sake yin shiru ba
komai ke tashi sai haushin karnukada keta kai kawo
Dif wutar gidan ta dauke gaba daya,gabanta yayi wani matsanancin bugu yadda duhu ya
mamaye gidan ko tafin hannunta bata iya gani,tuni jikinta ya soma rawa ta dunqule guri guda
tsoro ya mamayeta haushin karnukan sai take jinsa kamar a qofar gidan
Bata san sanda ta wuntsila tayi bayan kujera ba jin haushin karen a bakin qofar falon hadi da
tsaiwar mota wadda aka yiwa full light aka dallare gidan gaba daya daga baya aka kashe,ai
bata san sanda ta saki kukan tsoro ba dumin hawayen kawai itama taji,cewa take shikenan na
banu,kusan minti biyar sannan ta daina jin motsin karen,zama tayi dabas a qasa hadi da dafe
goshinta da tafin hannunta,kuka sosai ta saka,tana bala'in tsoron kare arayuwarta,don duk
gidan da zata matuqar suna da kare to komai mutuncin da kuke tafa bar zuwarmuku kenan
daman yaya lafiyar kura,yana daya daga cikin abinda yasa bata saba da gidansu aliyyu ba bata
zuwa kenan da can suna da karnuka har biyu kafin daga bisani uncle abba yasa aka fita da su
Sam bataji shigowa ba sai takun sawaye ta ji,a guje ta miqe tana neman mafaka a rude ,ji tayi
an cafkota cikin duhun,ihu ta bude bakinta da niyyar yi ko da wanda Allah zai sa ya kawo mata
dauki sai taji ansa hannu an toshe mata baki dai dai lokacin wutar ta dawo,fuskarsa cikin tata
yake kallonta ya zuba mata qwayoyin idanunsa,fuskarta tuni tayi jage jage da hawaye jikinta sai
bari yake don sai da wutar ta dawo ta gane ashe tuni har hular kanta ma ta cire saboda tsabar
rudewa
Ita ta fara janye idanunta hadi da kawar da kanya gefe ganin shi bashi da niyyar janye nasa
sexy eyes din da ya zuba mata,qoqarin zame hannunta take har a lokacin kanta na gefe tana
kuka mara sauti don iya tsorata ta tsorata,jikinsa a mace yake murus ga gajiyar zirga zirga da
ya wuni yana yi tuni rigarshi ma ta saman ya cireta a hannu ya shigo da ita,yaqi sakin hannun
nata yayin da yake qara zuba mata wani dafin mai illa ga ruhinta har cikin qwaqwalwarta don
baisan me riqe mata hannun ya jawo mata ba,ta kuma rasa me yake yi a tsayen har lokacin don
qeya ta juya masa idanunta bai kansa ta kuma qi kallonsa
Gashinta yake kallo dake ta sheqi shigar ta karbeta sosai kamar yasa hannunsa ya shafa
gashin saboda sha'awar da ya bashi sai kuma wata zuciyar ta gargadeshi "zaka jawowa kanka
raini" a hankali qamshin turarenta ya ci gaba da sakar masa da gabobi da qyar ya Iya dauke
idanunsa yana jan tsaki cikin ransa yana jin haushin kansa
Mrs muhammad ce
✍✍
[10/16, 1:58 PM] Salma: 
*WA YASAN GOBE?..*


*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

*PART 2*
3⃣7⃣&3⃣8⃣
Ji tayi an janyota baya an zaunar da ita saman kujera ta dago kai suka hada ido fuskarnan tasa
kamar dai koda yaushe,ta sunkui da kai hawaye naci gaba da zuba,tana jin tausayin kanta ne
cikin zuciyarta soyayyar aliyu ta gama yi mata illa,yana tsayen dai yayin da ya sauke dukka
qwayoyin idanun nasa a kanta yana kallonta ita kuma kukanta take haiqan mara sauti lokaci
lokaci tana sa tafin hannunta tan rage ruwan hawayen ta hanyar sharesu hadi da jan majina
Kusan minti biyar sannan taga ya dora mata handkerchief saman cinyarta qamshin turarensa
da yake jikin handkerchief din ya daki hancinta,briefcase dinsa ya dauka ya wuce daki,saman
gadon ya fada yayi rigingine yayin da qafafunsa ke qasa hadi da cewa *"ya Allah"*
Lokaci sosai ya bata yana maida numfashi tukun kafin ya miqe ya cire kayan jikinsa ya sanya
rigar wanka ya wuce bandaki,ko cikin toilet din ma haka ya dade cikin bathtub kafin ya cude
jijinsa ya fito,jallabiyya ya gani saka da short nikker gefan gadon a ajjiye bai kawo komai cikin
ransa ba bayan ya tsane jikinsa ya shafa lotion dinsa sannan ta taje soft sumarshi ya feshe
jikinsa da designers turarukansa ya jawo kayan ya sanya
Har yanzun tana bisa kujerar saidai yanzu har jingina tayi lokaci lokaci ta na dan saki ajiyar
zuciya irin na wanda ya sha kuka,kallo daya yayi mata ya dauke idanunsa ita kam dama ko
sashin da yake bata kalla ba don haushinsa take ji,sai da ya fara zuwa gun makunnin t.v ya
kunna ya dauki remote ya qaro volume gidan talabijin dun qasar ne ke labarai ya maida remote
din ya wuce dining,da kansa wannan karon yayi serving din kanshi sannan ya soma cin
abincin,yaci abincin sosai ba tare d shi kanshi ya san yaci haka ba
Tuni bacci ya dauke ya dauketa kafin ya kammala,ta takure kan kujerar kamar kwanciyar jariri
cikin mamansa,ajiyar zuciya take saki kadan kadan cikin baccin,a hankali ya qaraso gabanta ya
tsaya bayan ya kammala duk abunda zaiyi,ya zuba hannayensa cikin aljihun short nikker dinsa
ya zuba mata ido "sleeping beauty" yaji zuciyarsa na fada,wata sha'awa matsananciya ta taso
masa har wani yarrr yaje ji cikin jikinsa,ya tabbata da da salima yazo kai ko samira ce da tuni an
wuce gun
Itama ita gani yake kamar bada kaine ya tunkareta tunda dukkansu sun fita shekaru,ta sake jan
wata doguwar ajiyar zuciya cikin baccin nata harda juyawa,ya kalli hannunta handkerchief din
da ya bata ne duqunqune tsakiyar dogayen yatsunta,karo na farko wani abu mai kama da
tausayinta ya ratsa zuciyarsa,ya tuna yadda ta tsorata dazun ya tabbata rashin dawowarsa ne
da baiyi da wuri ba da kuma dauke wuta da akayi wanda qarewar kudin wutar su ne daga can
company din ya jawo haka,yasa hannunsa ya danyi mata baya da gashinta da keson shigar
mata ido
Da sauri ya janye hannunsa kamar wanda wuta ta ja,ya daga kai ya kalli lokaci sha biyu na dare
saura minti shida,yasa hannu a ahankali kamar jiya ya zare filon nata,a tsorace kuwa ta tashi
don har sai da yasa hannayensa ya tareta don kada ta fado,sai bayan ta nutsune suka hada ido
ya janye hannunsa tayi qasa da kanta,tana jin takunsa sanda ya shige bedroom,sai da ta tsaya
ta tattare kwanukan ta mada kitchen dare ya riga yayi ga dan Karen tsoro wanda ya hanata
gyare gun kamar yadda ta saba
Tamkar jiya yauma kwance yake saman center saidai yau lullube yake da wani qaton lallausan
farin bargo ba irin na kan gadon ba,saidai ya debe gaba daya filallukan kamar jiyan blanket din
kawai ya bar mata
Again yauma dai sallar ta tarar da shi yana yi saidai ita bayan sallar asuba bata koma bacci ba
breakfast ta hada masa don taji da yana waya kamar yana cewa zai fito da wuri zasu Beijing
⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Washegari maqociyar ta ta hannun hagu mr lin ta shigo mata 'yar asalin qasar china dince tana
da yara uku,sosai fadila taji dadin kulawar da ta nuna mata sun dan jima suna taba hira har
daya mqociyar tata ta shigo,sunanta nadiyya 'yar asalin alqahira ce sai fadila tafi farinciki da
nadiyya fiye da mr lin saboda addini da suka hada duk da cewar itama mai kirki ce,saidai ita
nadiya yaronta daya mashkur sai mai gidanta abdul-basid karatu ne ya rabosu da qasarsu,sunyi
hirarsu da ita sosai cikin harshen larabci don ta nan bangaren ma ba'abar fadilan a baya ba
Rayuwa aqasar da baka da kowa ba wanda ka sani bata fiya dadi ba ba kamar idan kana
qasarka ta gado ba,to hakanne ya kasance ga fadila da zarar aliyyu ya fita ta kammala aikace
aikacenta sai ta koma kan waya ko computer ta duba saqonni,idan ta gaji sai ta sanya hijabinta
ta dawo balcony ta zauna tana kallon masu shige da fice,duk da cewa unguwa ce da bata da
yalwar jama'a amma ba'a rasa masu wucewa jefi-jefi har wasunsu kan tsaya suyi mata magana
ganinta baqar fata mutanen qasar mutane ne masu so da girmama baqo hadi da mutunta shi
A irin wannan ne ranar bayan ta kammla aikinta da wuri ta hau social media dinta ta gaji ta
dawo balcony kamar yadda ta saba,saidai yau da gobe sai Allah sai zaman nan din ma ya
gundireta,wasu 'yammata su uku ta gani sunzo wucewa dukkaninsu akan kekuna suna tafe
ajere suna hirarsu abinsu,sai taji tana da sha'awar zaga koda layin sune zuwa qarshensa
Cikin zumudin tunanin da tayi ta zqro wayarta ta dan yima aliyyu text, _*please zan dan fita
qarshen layi*_
Mrs muhammad ce
✍✍
*WA YASAN GOBE?..*
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*PART 2*
3⃣9⃣&4⃣0⃣
Ta kalmashe wayar a hannunta bayan ta tabbatar saqon ya je,ta miqe ta saya qofar don bata
damu da sai ta kulle ba ta san qasa ce mai cike da tsaro
A hankali take ratsa layukan duk da dan banzan sanyin dake bugarta amma yanayin yayi mata
dadi sosai,tana tafiya tana cilla hannayenta gaba da baya fuskarta qunshe da murmushi
,unguwar ta burgeta matuqa babu yawan jama'a tunda dama can ita bata son hayaniya,sai yara
jefi jefi dake wasa wasu cikin balcony dinsu wasu kuma a qogar gida duk wasannin nasu baya
wuce tseran keke da buga qwallo(football)
Abinda ta lura da shi shine su kamar ma sanyin bai damesu ba ba mamki ko don qasarau ce
sun saba,har ta fita daga layin da shiga second street bata sani ba,yara ta gani su hudu babbar
ciki ba zata wuce shekaru tara ba ma bi mata ba zata wuce takwas ba ta