Showing 78001 words to 81000 words out of 135036 words

Chapter 27 - Wa Yasan Gobe Compelet Book by Safiya Abdullahi Musa Huguma .pdf

shude a haka ta rasa ya zatayi,tunaninta suna da first aid kit a gidan?to
koda ma akwai din bazai qyaleta ta tashi ta dauko ba don gaba daya a kanainaye yake
ajikinta,dabara ta zo mata da sauri ta miqa hannu ta dauko robar ruwanan da cuo din da dazu
ta shigo da su,ta tsiyaya ruwan sannan ta sa bakinta ta tofa masa ayatush shifa ta hada masa
da _*allahumma rabbin nas,azhibul ba'asi,wash fi antash shafi,la shifa'u illa shifa'uk,shifa'an la
yugadiru saqama*_

Ta dan kalli fuskarsa da tayi ja har yanzu idon ke rufe yana hada gumi "pls can you take it?" Ya
dan motsa kadan tasa masa cup din abaki yasha kuwa fiye da rabi

Cikin ikon Allah da taimakon ayoyin al qur'ani sai mutsu mutsun da yake ya soma raguwa,riqon
tsaurin da yayi mata ya fara sassauta,sai ajiyar zuciya da yakej saki kadan kadan,bata samu
sukuni ba sai da taji numfashinsa ya soma daidaita,a hankali jikinsa yayi weak bacci sosai ya
daukeshi
Ta saki ajiyar zuciya tana kallin irin yanda ya zagayeta da hannunsa,ta tabbatar da a
hayyacinsa yake bazai yi hakan ba,gumin fuskarsa har yanzu da saura,tasa lallausan tafin
hannunta tana share masa kadan kadan gami da bin fuskarsa da kallo ganin yadda tayi ja
alamun wahala,tayi tayi ta janyeshi daga jikinta cikin dabara saidai abun ya faskara yayi mata
nauyi ahaka itama baccin yayi awon gaba da ita

*THIS IS THE BEGINNING OF*............

*mrs muhammad ce*

✍✍
[10/16, 1:59 PM] �Salma�: 
*WA YASAN GOBE?...*


*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*


*PART 2*

4⃣5⃣&4⃣6⃣

Yau kam sun makara sosai suka makara don ko sallar daren babu wanda yayi a cikinsu
sakamakon bacci da basu samu ba jiya,shi ya fara farkawa ganinta cikin jikinsa ya bashi

mamaki,kamar ta san me yake faruwa ta farka itama fuskarsu cikin ta juna,kamar hadin baki da
sauri kowa ya janye jikinsa suka miqe a tare,shi ya fara shigewa toilet ita kuma ta shiga na
parlour

Ta rigashi idarwa tana zaune tana azkar har ya idar,tana zaune har ya kammala nasa
addu'o'insa, tadan waiga kadan tana duben gefansa tace "ina kwana" kamar yadda ta saba ba
tare da neman amsa ba tunda ta sani ba masawar zaiyi ba don bai taba amsawa din ba,saidai
idan yaga dama ya daga mata hannu kawai,saidai yau ga tarin mamakinta karo na farko sai taji
ya amsa da "lafiya",ta sake cewa "ya jiki?" Kai ya daga mata,ta tabe baki ta miqe cikin zuciyarta
tana cewa"hmm an ma yi yau abun arziqi" tana kallonsa ya sake komawa gado ya duqunqune

Bai dade da kwanciya ba wayoyinsa dake gefan gadon suka hau ruri,hannu yasa ya debo su
bai daga kiran ba hakanan ba tare da ya duba mai kiran ba ya kashesu duka sannan ya maida
su kan side drower hadi da jan bargonsa ya sake rufa



Tana kitchen tana hada breakfast tajiyo muryarshi cikin parlour yana amsa waya,saidai muryan
tayi qasa sosai alamun bai cikin jin dadinsa don bata iya jin abinda yake cewa,cikin rarraba
hankalinta da takeyi ne ta yanke hannunta da wuqar da take rarraba kazar da take so tayi
masa pepper chicken ba tare da ta sani ba,wuqar ta shigeta sosai don yankan ba qarami
bane,zafin ya ratsa ta har cikin qwaqwalwarta batasan sanda ta saki razananniyar qara ba,jini
ne sosai ke zuba ta runtse idonta tana jin azabar yankan

Ta bude idonta a hankali suka sauka kansa lokacin da yake shigowa kitchen din cikin
sauri,hannun nata da yake digar jini yake bi da kallo,da sauri taga ya ajjiye wayar saman
freezer,hannun nata dake digar jini ya riqe yana kalla,wani yarrr fadila ke ji har cikin jininta,shi
din ma haka,lallausan tafin hannunta yaso haddasa masa wata sabuwar fitinar cikin jikinsa,yayi
saurin sakin tafin hannun nata ya kama tsintsiyar hannun

Janta yayi zuwa gaban sink ya kunna famfo ya tara hannun sannan ya barta gaban famfon ya
fice da sauri,cikin 'yan sakanni sai gashi dauke da first aid kit,abunda tayi ta tunanin ina yake
jiya,spirit ya fito da shi ya janye hannunta daga famfon ya dangwala a auduga ya soma wanke
mata kan yankar,zafi sosai take ji yana ci gaba da ratsata ta runtse ido � tana dan yin baya
da hannun,cak ya tsaya da wanke matan da yake don spirit din baya samun inda yake
so,fuskarta da idanunta ke rufe ya zubama ido har wani abu yaso shagaltar da shi

Jin shiru ya daina sawa ya sanyata bude ido,idonta ya shiga cikin nasa suka hadu,wani magnet
ya hadu da qamshin turarenta yaso rikita aliyyu ya manta da abinda yake,amma sai yaso nuna
mazantaka ya dake har da qarfin halin kaurara muryarsa "stop it,idan baki buqata zan hada
kayana,kau da kai tayi don bazata iya jurar kallon qwayar idanunsa ba,ya duqar da kai yaci
gaba da wanke mata daga bisani ya rufe mata da bandage don kada datti ya dinga shiga

Yana maida kayan cikin akwati ta dan motsa labbanta tace "thanks" "for what" ya fadi ba tare da
ya dago kai ba bai kuma tsaya da rufe akwatin ba,she became speechless don haka ta zabi yi
masa shiru kawai,haka shima bai sake cewa komai ba har ya kammala rufe akwatin ya dauki
wayarsa ya fice
Da hannu daya ta qarasa aikin don haka kafin ta kammala duk ta jagwalgwale hannun jinin da
ya tsayar mata tuni wani ya soma tsatsatsafowa ta bandejin da ya sa mata,sai da ta gama
serving dinsa sannan ya ankara da girkinta ashe ta ci gaba da yi,ya dago ya dubeta tana ta
faman hurawa yatsan iskar bakinta,baice mata komai ba ya tashi ya sauka a dining din sai
gashi dauke da first aid kit,ta zaro ido cikin tsorata� tana tunanin mai kuma zai mata yanzu

Sosai ya riqe hannunta gam tana qoqarin zamewa saboda azabar yadda yake daye bandage
din da ya sa mata dazun zai canza mata sabo,sai da ya cire tas ya sake wanke mata ya saka
mata sabo sannan ya maida kayansa ya kwashe mai jinin ya sauka da su

Ya dawo ya soma cin abincinsa yana kallonta time to time yadda take ta qwalla "ko da yaushe
kina acting kamar baby" hakanan taji ya fada can qasan maqoshinsa,sai da ya kammala cin
nasa taga ya ja plate ya zuba mata komai ya tura mata gabanta, "oya" yace hadi da yi mata
nuni da plate din da ido fuskarsa a hade,ta dan langabar da kai gefe don bata marmarin cin
komai yanzu sai ta tashi a lecture "am ok,na qoshi" kallon nan nasa ya tsareta da shi cikin tsare
gida,ta fuskanci hukuntata yake sonyin da ido,tayi saurin janye idanun ta hadi da sake jan plate
da cup din gabanta ta soma ci tana yamutsa fuska cikin zuciyarta tana mitar "ya wani tsare
mutane sai sunci abinci sai kace wani abbana lokacin da ina gida"

"Good haka abban ke miki saboda baki jin magana kan cin abinci ko?"ya fadi yana fuska a hade
yana daga girarsa,da sauri ta dago ta kalleshi batasan sanda tea din da ta kurba a bakinta ya
dawo ba,batasan ya akayi yaji abinda take fada ba,anya wannan mutumin ba maye bane?, "am
talking to you kin qwalalomin idanunkin nan masu girman tsiya"(lol aliyyu ) ya fada
cikin dan daga murya,kai kawai take girgizawa don babu bakin cewa wani abu,minti biyu tsakani
yace "shi yasa kullum store da freezer dinki ke acike kenan basuyin qasa ko?good.....to ni a
gidana dole adinga cin abinci.....oya....bismillah ina son naga plate empty"

Daga haka ya maida kansa gun wayarsa dake ruri ya fara amsa wayar mr lien,ci take amma
sam bata so,da zarar kuma ta tsaya suke hada ido dole take ci gaba da ci,sai gashi taci abinci
mai yawa wanda ita kanta ta jima rabon data ci,ta ture plate din tana dan taba cikinta da taji yayi
fam tana yatsina fuska yayi mata wani irin qabe qabe babu dadi, "I think u filled your stomach,let
me see" ya fadi yana qarashe kashe wayar"qwalalo � ido tayi tana tunanin anya kan aliyyu
daya?ciwon cikinsa na jiya kodai ya taba shi?,she dont know why he behaving like dis?,cikin
nata zaya ce ta ta yaye rigarta ta nuna masa?,ta dawo cikin hayyacinta lokacin da ya zare mata
ido yace "aha show me" ba shiri cikin sanyin jiki ta dage rigar sanyin hadi da shirt din dake
ciki,cikinta ya bayyana, ashafe yake tamkar zai hade da bayanta,ya zuba mishi ido,soft skin tata
ta bayyana kanta ko ba'a fada maka,wani irin magnet ke fusgarsa,ya dubeta ta tsira mata ido
duk a rude take,muryarsa can qasan maqoshinta yace "up" yana ci gaba da kallon cikin,a zaton

ta bai gani bane sosai ta dan sake janye masa rigar "up again" ya sake fada,sai ta tsorata don
dukka cikin nata ya fito waje da zarar ta sake janye rigar qirjinta(breast) ne zai bayyana

Ganin bata sake dagewarba yasa ya dauje idanunsa daga kallon cikin ya maida qwayar idanun
nasa cikin nata,ya karanci ta tsargu don haka sai ya waske ya bata rai hadi da janyo warmer
yana budewa gami da cewa "no ni banga yayi full ba,don banga ya daga ba" ta marairaice tuni
qwalla har ta cika mata idanu "I swear idan ka qaramin zanyi amai wlh Allah haka cikina yake"
da mamaki can qasan ransa ya tsaya da abinda yake din,dama akwai mata masu irin
wadannan halittar cikin?,ya riga da ya saba da matansa masu tumbi

Ya koma ya jingina da kujerar da yake kai yana cewa "ok remove dis items,but be careful with
your wound,dama neman mafita taje don haka da rawar jiki ta tashi ta soma gyara gun ,cikin
kitchen kitchen tafi minti biyar tana dafe da qirjinta idanunta a lumshe kafin yanayinta ya
daidaita "me ya sauya shi haka" can qasar zuciyarta take tambayar kanta
*Mrs muhammad ce*

✍✍
[10/16, 2:00 PM] �Salma�: 
*WA YASAN GOBE?...*


*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*


*part 2*

4⃣7⃣&4⃣8⃣

Ta dade kafin ta baro kitchen din har yanzu yana dining area bisa kujera yana danne dannensa
a waya,a falon ta tsaya ta jawl computer din ta ta tafi da gidanka(laptop) ta bude tana shirin
kunnawa "hey stop" taji ya fadi cikin wata iriyar murya mai kama da ta mai jin kasala,kasaqe tayi
tana jira taji mai zaice "shutdown ur system yau ba daukan lecture,kin mance wound dake
fingers dinki ne?" Sai ta rasa mai zata ce tana ganin ai hannunta bazai hanata lecture ba koda
guda daya zata iya yi,amma da yake mutum ce ba mai son jayayya ba don haka ta kashe din ta
koma ta zauna hadi da zubawa sarautar Allah ido

Tana zaune ya shiga ciki yayi wanka ya shiryo cikin kayan sanyi,kan kujerar dining din dai ya
koma ya zauna,babu dadewa kuma door bell ta kada,ya dubeta sannan yace "put your hijab"
mayafine yafe a jikinta bayan kayan sanyi masu kauri da tasa,nan ma dai bata tanka komai ba
ta koma daki ta dauko hijabin,ko da ta dawo su biyu ta tarar shi da doctor yungpho,ta samj kuje
daya ta zauna doctor yungpo mutumin china na gaidata cikin harshen turanci

Suna gefanta doctor ya gama duk hwaje gwaje da tambayoyinsa,ya dago yana duban aliyyu
"sir,sanyin garin mu na son taba ka gashi kana kwanciya a inda zai iya affecting health dinka,ya
kamata ka kula saboda kada yayi maka yawa ya zamarmaka illa" "ok" aliyyun yace, "sannan
ciwon cikinka ciwon marasa aurene me yasa ya taso maka a yanzu bayan kana da aure?...." da
sauri aliyyun ya katseshi yana satar kallonta duk da kanta baya fuskantar gun amma hankalinta
na gurin haka nan kuma ta dago wani abu duk da ya katse doctor din

Magunguna doctor yungpo ya bashi yana shirin hade kayansa aliyyu yace ya bashi pain killers"
ya hada masa duk cikin magungunan,fitarsa babu dadewa aliyyu yasa ta bashi ruwa yasha
magungunansa,tamiqa masa ita kuma ta wuce kitchen da zummar dora abincin rana tunda taga
alamun da qyar idan yau zaya fita
Sai tsintar aliyyun kawai tayi cikin kitchen din ya damqota yayo waje da ita,saman kujera ya
zaunar da ita yana ware mata sexy eyes dinsa kamar wata qaramar yarinya "idan kika sake
jangwale ciwonki I will wash it again budewa zanyi in sake wankewa no pity ok?" Tayi qasa da
kanta tana kallon yatsan nata mai ciwon,muryarta so cool tace "lunch zan hada mana ne" "we
don't need" ya fadi yana juyawa "wo hoho Aliyyu.......Aliyyu...." fadila ke fada cikin zuciyarta,ya
sata hutun dole kenan?....... Babu karatu babu girki?.....fine" ta fadi tare da yin kwanciyarta
saman three sitter

Wunin ranar tana zaune ita dai sai gani tayi an kada qararrawa da rana an kawo musu lunch
hakanan da daddare,coffee kawai ta faki idonsa ta hada,shima tana dire masa ta bar bedroom
din don kada yace zai mata fada,sai da ta kintaci kamar yayi bacci sannan ta koma,cikin sanda
ta salallaba ta hau daya side din tana jan bargon zata rufa taji ance "good" ta zaro ido tana
shirin sake jin mai fada,jin yayi shiru bai sake cewa komai ya sanyata jan bargo ta lulluba tana
addu'o'inta cikin zuciyarta tana yiwa kanta dariya,wato ita mai wayo taqi shigowa ta gudu sai
yayi barci ashe idanunsa biyu,ta saki ajiyar zuciya wadda ba don kwanciyar kai da qafa sukayi
ba da zai iya jiyota

Yafi awa biyu yana yaqi da zuciyarsa,qamshin turarenta ke ban banta masa tunani,ya rasa
wace iriyar masifa ce,sosai ya san yana cikin wani hali amma baisan me yasa ta sanadiyyarta
yake samun kansa cikin wannan halin ba,sunsha zama haka shi da salima idan ta masa laifi
don ya hukuntata,suna daukan tsawon lokaci a haka ba tare da kuma ya damu ba,saidai ita ta
gaji ta hanyar gyara laifin da kuma bashi haquri,ya runtse ido,da qarfi yake son tilastawa kansa
sai yayi bacci,da qyar wani wahalallen bacci mai cike da mafarkai yayi awon gaba da shi



Kwana uku tayi babu cas babu as,duk abinda ta dauka zata yi sai yace "stop it,hatta da shara
kuwa kawai akan dan yatsanta guda daya,saidai ta faki idonsa ta kimtsa inda taga bai dace ace
ana barshi haka ba,da zarar kuwa yazo yaga alamun hakan zai zuba mata ido wanda ta fassara
shi da *eyes punishment*,sai ta sunkui da kanta kawai ta wuce sum-sum-sum ta bar gun,kwana
biyu yana gida yana jinya babu inda ya fita,sai a rana ta ukun ya koma kan ayyukansa

Sosai itama ta rungumi karatunta tana jin dadinshi matuqa ta bashi mahimmanci mai matuqar
tasiri don ta sani zai sake jawo mata qwarewa da kuma daukaka ta fannin aikinta,hakanan tana
sake samun goyon baya da qwarin gwiwa daga gidajen rediyoyin da take mu'amala da su,su
kansu ko yaushe suna fadi mata yadda sukayi missing aikace aikacenta masu cike da inganci
da juriya


_*SANADI*_


Cikin nasarori masu tarin yawa dukkan wani shirye shiryen bikin bude kamfanin suka
kammala,cikin watansu na uku da sati na uku a qasar ta sin,wanda cikin lissafin da fadika keyi
kwanaki goma daka iya zuwa a gaba koma sati guda wato next week zasu iya komowa gida,tun
sati uku da suka gabata ta kammala naga coarse din ta kuma fita da sakamako mafi kyau duk
cikin daliban

Tuni ya sayi injina masu kyau ya aiko da su gida ta container din max air wanda na wasu
kamfanoni ne da yakeson budewa idan ya dawo gida a kano cikin rukunin kamfanoni dake
sharada industrial area



Tsaye take a kitchen sauri sauri take ta kammala girkinta saboda yau tayi late sosai,sanye taje
cikin trouser na mata sai rigar sanyi in and top ta saqa ce irin saqar turawa,yar cikin har gwiwa
take mai gajeran hannu ta saman ce iya qugu mai dogon hannu,wuyan rigar yankan *V* shape
ne,ta taje baqi sidik din gashinta mai sheqi ta sake shi ya sauka gadon bayanta,kanta na saye
da hular sanyi na mata mai wadda a jikinta yaje saqale da teddy's qananu,shigar dark pink tayi
tayi masifar yin kyau kamar wata black American

Hankalinta sosai yayi gaba,ta bada duk wani attention nata kan girkinta don hatta dan siririn
mayafinta da tadan yafa da hular kansu sun zame don haka ko shigowarsa bata ji ba,fresh milk
shi din ma ya shigo dauka hade da ruwa don busy din da tayi yau ya sanya ta mance bata ajjiye
masa ba yadda ta saba,wani strong abu yaja hankalinsa sosai game da ita,sai ya koma jikin
freezer din ya jingina ya harde hannayensa saman qirjinsa kamar yadda ya harde qafafunsa
yana bin duk wani moments nata da kallo

Sosai ta tsorata lokacin da ta juyo zata dauki ragowar markadaddun kayan miyan da ta sanya a
fridge saboda ganin mutum a tsaye unexpected,tsananin tsoro ya kamata tayi baya zata qwalla
qara don rudewa ma bata barta ta kalli fuskarsa ba sai kuma ta taka bawon doya ta zame tana
shirin shan qasa saboda santsin tiles da doyar ga kuma ruwa
Gaba daya taji ya rungumeta tsam cikin jikinsa yayi hada bakinsa da nata don hanata yin

ihun,zaro ido tayi,cikin yan sakanni ya soma kashe mata jiki saboda yadda yake sarrafa bakinsa
cikin nata tamkar ya samu sweet qamshin turarenta na dada ingizashi,cikin lokaci qanqani ya
soma burkice mata har ya fara bata tsoro duk da ita din ma tana cikin shauqin abinda yake
matan,wannan shine karo na farko da ta soma hada jikinta da wani da namiji a rayuwarta
Caraf tayi qarfin halin riqe hannunsa jin yana qoqarin shiga wani fage,sai lokacin da ta hada
hannuntabda nasan sannan ya soma dawowa saitinsa,cak ya tsaya da abinda yake yi din,cikin
sauri ta 6ashi daga jikinsa tana maida botiran rigarta hadi da maida gashinta baya wanda tuni
ya hautsine,kunyan da tsoro suka hanata tsaiwa ina zata boye?,bedroom nasu ne su biyu
duka,kitchen gashi a ciki,gudu gudu sauri sauri ta nufi qofar ventilation da niyyar ficewa

"Hey you" taji aliyyu wanda ke jingine jikin kantar kitchen yana maida numfashi yace "cak ta
tsaya ita bata qarasa ficewa ba hakanan bata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login