Showing 48001 words to 51000 words out of 135036 words

Chapter 17 - Wa Yasan Gobe Compelet Book by Safiya Abdullahi Musa Huguma .pdf

gidan radiyon shi yasa bata shiga ba,zamanta tayi ta dinga bacci abunta sallar
azahar kawai ta tashi tayi ta dan sha yoghurt ta koma baccinta

Qarfe hudu da rabi ta farka tayi wanka,tq gabatar da sallar la'asar din da ake binta,riga da skert
ta saka hade da mayafinsu sannan tayi kitchen da azama saboda wata hadaddiyar yunwa dake

sakadarta

A tsaitsaye ta hada jallop din taliya� da tasha kifi ta watsa mata carrot piece da grean
beans,da zaman jiran dahuwar abincin da zata yi sai taga gwara ta hada lemo,cikin lokaci
kadan ta hada lemon kwakwa da yasha madara ta bude freezer din kitchen din ta sanya ta a
ciki,bayan ta kammala ta juye a plate ta kalli plate din tana murmushi hadi ya tsina fuska don ita
kanta tasan ba iya cinyeta zata yi ba ta mata yawa"let me try"ta fada tana gyada kai ta hado da
lemonta dake cikin jug din ta taho dashi parlour ta zabi kujerar da zata zauna akai don haka ta
jawo centre table ta dora su a samansa

Ta juya ta koma daki don daukar wayarta ta tashi ne ta tarar da missed call din fauziyya
colleague dinta ta barshi da niyyar idan ta gama abinda take ta kirata

Ya kama handle din ya murda hadi da tura qofar ta bude ya shiga,qamshin freshner din parlour
hadi da qamshin jallop din ya dunqule ya daki hancinsa wanda hakan ya sake haddasa masa
yunqurowar wata matsananciyar yunwa,idanunsa suka kai kan plate din dake dauke da jallop
din��dake ta tururi da qamshi,
Fadila ta fito hannunta dauke da wayar tana duba missed calls din data tarar ciki harda na
rumasa'u da farida,,sam bata lura da shi ba agun sai da yayi gyaran murya,adan furgice ta dago
don bata zaceshi ba,a dinke fuskarsa take kamar kullum ya cillo mata muqullai suka sauka a
kusa da qafafunta,yayi gefe da kansa sannan cike da ginshira yace"ki gyara min bangarena
sannan ki sama min abinda zanci yanzun nan tunda sai an koya muku abinda ya dace" ya nemi
kujera ya zauna hadi da jawo wani dan qaramin table din na glass ya miqe qafarsa akai

A hankali ta sunkuya ta dauki muqullan,cikin zuciyarta tace"ka gama qunbiya qunbiyarka ka
ma,mutum sai shegen jin kai ka fito kawai kace kazo neman taimako guna,ki banza dai ina da
muhimmanci tunda.duk cikinsu babu mai iya maka haka sai ni duk da dan banzan jin kanka"ta
shiga daki ta canza mayafin zuwa hijabi sannan tazo ta wuce shi yana zaune yadda ta barshi
Kamar jira yake ta fita din ya jawo abincin gabansa,ya dauki cokali mai yatsu yana jujjuyata
yana qare mata kallo,a zahiri shi taliya bata dameshi ba don haka ya ture plate din gefe sai
kuma qamshin ya addabeshi don haka dole ya jawo yakai loma daya bakinsa�

Lumshe ido yayi dadin na zagaya kunnensa,ya tabbatar wannan ne taste� din da yayi
missing kwana da yawa kuma shi yake nema wasa wasa saiga gashi ya tashi da plate din gaba
daya,ya shafa cikinsa take yaji yana buqatar qari bai qoshi ba, ya miqe ya nufi kitchen
kasancewar tsarin ginin nasu daya ne shi yasa ya fahimci inda yake,ya daga tukunyar gaba
daya ya juye ta ciki ya cinye ya dawo falon dauke da ruwan roba na faro a hannunsa ,sai yaji ya
samu nutsuwa ba shakka yunwa bata da hankali inji dan almajiri

Ya miqe a kan three sittersaboda yanaji har cikin zuciyarsa yanayin qamshi da tsaftar falon
sunyi.masa,idanunsa a lumshe yana tunane tunane har aka fara kiraye kirayen sallar magariba

sannan ya miqe ya bar sashen,kafin ya qarasa nasa suka ci karo da samirah na shigowa da
motarta,ya tsaya qam yana dakon qarasowarta hannunsa zube cikin aljihun wandonsa,tunda ta
hangoshi tace da qawarta sa suka shigo tare "na shiga uku kubra mai gidan nan ya dawo"kubra
da hankalinta ke kan waya ta ja tsaki tace"mtswee to sai me?ni wlh samira mamaki kike bani
tunda.kika yi auren nan duk kin canza komai adarare duba fa dazu da zamu fita fitted gown fa
kawai nace ki saka amma kika qi bayan kinsan gun manyan mutane zamu ji,tsoron mutumin
nan kike ji kamar wani Allahn ki ke yadda ma kike tsoronsa baki tsoron Allahn naki ma,nidai
gwara ma dai yau naga wanne dan mulkin nan ne wannan da.kike masa biyayya haka kamar
shi ya tsuguna ya haifoki

Cike da gadara da rashin kunya kubra ta fito yayin da samira keta.rabe rabe don kuwa riga da
skert ne a jikinta na shadda kana kallon shaddar kasan an kashe mata naira mai tsada ce saidai
anci mutuncinta ta wajen kacalcalata da yi mata matsatstsen dinki,ga mayafin jiki ta sai kace
wadda aka yiwa gorin lullubi
Kallo daya ya yiwa kubra da ta tsareshi da ido duk wata rashin.kunya da ta fito da ita tayi nata
gun,hakanan aliyu yake Allah ya bashi baiwar kwarjini masifa,ta sake kallonsa karo na
biyu"wow"ta fadi a hankali don gaba daya ya tafi da tunaninta,sai ta mance mission din ta fito da
shi,ta zuba masa ido gaba daya,sai a lokacin idonsa ya kai kanta bayan ya dauke kansa daga
samira,takaici ya kama Aliyu ganin irin kallon qurillar da take masa ya sake dinke fuska
tamau,sai lokacin ta kula da ta bada kanta fa ashe,

Ta dauke kai cike da duniyanci da niyyar bin bayan samira dake ta zuba sauri jiki na rawa,tsawa
ya daka mata� hadi da nuna mata qofar get sannan yace"get out of my house idiot kada na
kuma ganin wadannan lalatattun qafa fun naki a gidana"murmushi ma ta saki ta juya ta fice cikin
karairaya wai ko zata janyo hankalinsa, bata san wani takaicin ne ya sake qumeshi ba yaja wani
dogon tsaki ya juya ya nufi sashen samira

Mrs muhammad�

✍✍✍

3:37 pm 8/11/1437



*wa yasan gobe?.....*

4⃣1⃣~4⃣2⃣

Kubra ta tsaya a bakin get din tana jinjina kai ita daya take sumbatu"kut lallai yarinyarnan dole
ta matowa gayen nan shi yasa take ta faman rawar qafa?ai kuwa wlh baza'ayi bani ba"tayi
qwafa sannan ta ja qafa tayi gaba,

samira ta kasa zaune ta kasa tsaye tasan halinshi sarai yarjejeniya kuma suka qulla tun kan
aurensu kan shi baison wadannan kwashen qawayen nata gashi yau ta saba yarjejeniyar,tana
shirin guduwa dakin gadonta ya damqota ya maidata kan kujera,ya kalleta sosai sannan ya jefo
mata tambaya"ina kika samo waccar shedaniyar?"ta dake duk da tsoro ne fal cikin idanunta
tace"qawata ce fa"ya gane mai takeson yi duniyancin nata data saba don haka ya shirya nuna
mata nasa salon,don haka sai ya saketa daga riqon da yayi mata,ya saki fuskarsa ya daga
kafadarsa hadi da watsa hannayensa na nuna alamun rashin damuwa da abu kana
yace"good....verry good tunda qawarki ce kinga abun zai zo min da sauqi kenan ko?,dama gani
nayi tamun inason aurenta aikinga zaman naku zai miki dadi tunda kun fuskanci juna, bata san
sanda tayi zumbur ta miqe ba tana zazzare idanu ba baki na rawa tace"iyi...mme...me kace"ya
daga mata gira sannan yace"abinda kunnen ki suka ji shi nace"ya juya yana niyyar barin
dakin,hankalinta a tashe ta riqoshi kasancewar tasan halinshi *fada da cikawa*ya dubeta fuska
a turbune yace"meye haka"don Allah ka rufamin asiri wlh bazan qara ba kasan wace kubra
kuwa?"ya sake dage kafada hadi da cewa"ni ina ruwana da koma wace ce tunda kin kawo min
ita har gida ni kuma na gani kuma ta yimin"ya zare hannunsa yayi ficewarsa,yana jiyo
kururuwarta sai ya tuna haukan da tayi masa sanda zai dawo da salima,murmushi ya subuce
masa ba tare da yayi niyya ba,yasan cewa shikenan yayi abinda zai rabasu kenan har abada ba
tare da ya wahal da bakinsa ba,(samira irin mai rawar kan tara qawayace ko wa qawarta ce
kare da doki ga son birga da burgesu ita dole sai an san mijinta wani ne,kaya komai tsadarsa
suka gani a gunta tofa take zata basu ko nawa aka siya musu ko na aliyyun ne kuwa,indai zata
burge tofa magana ta qare,gata da saurin daukar maganarsu don yadda take jin zancansu nata
jin na mahifanta haka ne yayi silar lalacewarta,wannan ne yasa aliyu ya rabata da kowacce
qawa amma da yake akwaita da kafiya taurin kai da naci sai ta sake wasu sababbi wadanda
aliyyun bai sansu ba)

Kai tsaye ya wuce sashen sa tun daga falin ya ga canji komai fes ya koma
hayyacinsa,daddadan qamshin girki ya cika falon nasa,bedroom ya zarce ya daura alwala ya
nufi masallaci,kan ta kammala aikin ta gama gajiya tubus don kuwa aikine ya gama taruwa ya
cakude ita kanta wani gun cike da qyanqyami ta daure ta gyarashi to ina kuma ga aliyyu
Take tasha alwashin zata yiwa tufkar hanci don badaqalar data tarar a bedroom din tasa ta
isa,tuni ta gane cewa fushinta bashi da amfani don yadda komai ya qazance ta sani cewa da
duniya zata gani ba iya su samira kawai za'a zaga ba harda ita,don ba wanda yasan mekw
gudana tsakaninsu,ta sake gayawa zuciyarta lallai ibada tazo yi ibada kuma mai wahala wadda
itace tafarkin shiga aljannarta kuma ta dade da sani aljanna bata samuwa daga zaune ba tare
da ka tashi kayi aiki tuquru ba kuma dole ka ninka haqurinka(wannan sune daya daga cikin
lafuzan umminsu garesu ko yaushe,uwa ta gari kenan)

Aliyu bai shigo ba har sai da yayi sallar isha'i don haka tuni ta gama komai har ta jere a dining
taje tayi wankanta ta shirya tsaf cikin dark blue din shadda doguwar riga wadda aka mata
surfani mai kyau tun daga sama har qasanta ,hankalinta dai na kan taliyarta don haka ta nufi
table din saidai wayam don ko plate din babu,ta juya ta shiga kitchen acan ma a bude ta tadda

tukunyar wayam

Ta san babu wanda ya cinye abincin sai shi don ba wanda ya shigo din,wata dariya� ta
subuce mata data tuno yadda ya shigo dazun rai a hade yayi wani kicin kicin da shi� ashe
harda yunwa itama ta taimaka wajen dinkewar fuskar tasa,ta hade kwanunkan ta dauraye ta
maida su muhallinsu cikin ranta tana cewa"babu rabona nasha ice cream�
Tana bisa carfet ta bude babbar robar ice cream din tana diba a hankali tana kaiwa bakinta
lumshe ido take don babu abinda take jin dadin shansa kamarshi din,wayarta ta duba jin qarar
shigowar text _kizo ki bawa mutane abinci_"haka taga an saka,ta duba sunan Aliyyu salim
maitama kamar yadda yayi mata serving din ta ranar da bata da lafiya"ta miqe hadi da dauke
ragowar ice cream din ta maida cikin fridge ta koma daki ta fesa turarenta na blue lady ta hada
da asaal brush perform ta nade kanta da da farin hijabi ta zari wayarta ta fito hadi da kulle gun
ta,a hanya suka hadu da salima ta rako baquwa suna tsaye da alama magana suke ganin
fitowarta duk sai sukayi shiru suka bita da kallo ganin haka yasa tace musu salamu alaikum
sanda zata giftasun,baquwarce kawai ta iya amsawa itama can xiki kamar wadda akayiwa
dole,suka ci gaba da kallon nata har ta shige bangaran aliyun

sai a sannan suka dauke idonsu baquwar ta saki ajiyar zuciya tace "tab gaskiya salima tahir na
janjanta miki don wannan kam banga ta inda zaki ci nasara akanta ba,saidai ban sani ba ko ta
bangaren farar fata"salila ta kai mata duka hadi da cewa"banason iskanci sadiya kota farar fatar
ai sai na yi yaqi da itan ,dadin abun ma miskilancin mai gidan bai bari ki gane wa yafi so cikinku
ai da tuni inaga na dade da kamuwa da ciwo yanda nake bala'in a son my dear "ta fadi tana
dafe qirjinta"(abunda bata sani ba aliyyun irin mazan nan ne wadanda ke nunawa mace qauna
wadda kan bawa mutane mamaki har adinga zaton kunya ce basu da ita ko mallakesu akai
sunyi sake da damar da ya basu tun farko har ta subuce musu)sadiya ta dafa kafadarta tace"to
Allah ya bada sa'a don ko nice a matsayinki gaskiya bazanyi wasa da aliyyu ba"salima ta juya
ido tace "ashe kin fara gano gaskiyata "

Mrs muhammad ce

✍✍✍
[10/16, 1:42 PM] �Salma�: 
*wa yasan gobe?....*

*written by safiyya Abdullahi musa huguma*


4⃣3⃣~4⃣4⃣

�
''
|� |

/ \
 

Ku tayani duba jama'a na taho da sauri na ina neman littafina na *wa yasan gobe*zan muku
typing na nemeshi na rasa

�
Just for fun ga wadanda suka ji haushina

*wa yasan gobe?....*
Loading..........





*WA YASAN GOBE?....*

*PART 2*


1⃣~2⃣




Sadiya ta dafa kadar salima tace to Allah ya bada sa'a don ko nice a matsayinki gaskiya
bazanyi wasa da aliyyu ba"salima ta juya ido tace ashe dai kin fara gano gaskiya ta"


Sanda ta shiga yana zaune gaban na'urar tafi da gidanka yana qarasa aikin sa da dazun yunwa
ta hana shi yi,sallama tayi ya amsa kansa na kan allon computer din,kujerar dake gefansa ta
samu ta zauna,kusan mintina sama da ashirin bai ce mata kanzil ba don haka itama ta bude
wayarta ta soma register din watsapp saboda yanzu as journalists tana buqatar wadannan
kafofin sadarwar,


duk da basu dameta ba don ba yadda farida batayi da ita tun a gida ta bude koda watsapp ne
kawai ba amma taqi tafi ganewa karance karancen magazines da wasu rubuce rubucen


Cikin yan mintoci qalilan ta kammala da account dinta na watsapp ta soma qoqarin hada na
facebook,falon yayi tsit kowa ya sanya na'ura a gaba,lokaci lokaci takan daga ido ta saci

kallonsa,qayatacciyyar fuskarsa da hasken screen ya sake hasketa tayi fresh,ta zubawa
hannayensa ido yadda yake sarrafa computer din cikin qwarewa da da gwanancewa typing
yake cikin sauri tamkar shi ya qera computer din yasan madannin kowanne abu abun sai ya
burgeta sosai

Wayarsa ta soma ringing ya dauke kai daga kallon fuskar computer din ya maidaa idonsa kan
wayar ba tare da ya daga ba,baquwar numbace kuma bai dagawa,kira aka ci gabaa da yi akai
akai har ya gaji ya danna ok ya dora ta bisa computer ya sanya ta a hands free


Muryar mace ce "hello ranka ya dade" "salamu alaikum wake magana?"ya fada hannayensa na
saman laptop dinsa yana aikinsa,"daga daya bangaren aka sake maqe.murya"suna na nadiya
ina kiranka ne daga unguwar rijiyar zaki kano"bai maida hankalinsa ba kan wannan yace"me
kike nema?"aka danyi jim har yana shirin kashewa sannan akace "don Allah ka rufawa zuciyata
asiri kada ka kashemin waya domin kashe wayar tamkar kashe ni ne"ya tsayar da abinda yake
sannan yace "uhm go on" aka saki ajiyar zuciya sanna tace "maitama Allah ya jarabceni da
tsananin qaunarka wadda tasa na kasa jure hakan cikin zuciyata har sai bakina ya furta
maka,ina roqonka don Allah ka taimakeni ka so........" "hey!"ya daka.mata tsawa "stop
that,rubbish!"tsit tayi,ya ware idonsa kamar tana gabansa yace"ke baki da ajine irin na mata?"
Shiru ba amsa don haka ya dora "let me tell you baki da shi,and inason gargadinki wannan ya
zama na qarshe da zaki kira numberta,I hope kin fahimta ko"ya katse kiran hadi da jan
tsaki,fadila tayi saurin dauke kanta lokacin da ya dago kansa taga tamkar ita zai kalla zuciyarta
na wani irin bugu,kishi ya tokare mata qirji,ta lumshe ido bugun zuciyarta na qara sauri.......


Mrs muhammad dinku ce�
[8/25, 3:44 PM] +234 812 673 9684: 5:55 pm 16/8/2016

*wa yasan gobe?...*


*written by safiyya Abdullahi musa huguma*






*PART 2*

3⃣~4⃣

Kusan kimanin minti biyar idanun nata na lumshe ta kasa budesu saboda wani abu da takeji a
jikinta wanda tasan baya rasa nasaba da tsan tsar kishi,ta sauke boyayyar ajiyar zuciya sannan
ta bude idonta ta dora su bisa screen din wayarta tana ci gaba da qoqarin kammala bude
account nata na Facebook duk da wani bari na zuciyarta na ci gaba da mintsininta,cikin zuciya
lallai ta godema Allah da bai qaddara ta zubda ajinta ta bayyana abinda ke zuciyarta ba har ta
kai aliyyu ya fuskanta bare ta samu nata kason cin zarafin kwatankwacin wannan wanda it may
break her heart


Tabbas ta sake yarda cewa so masifa ne musamman son da hausawa kema laqabi da son
maso wani,babu irin baiwar da tabbas bata da ita iya kyau Allah ya mallaka mata shi ilimi
hankali da nutsuwa,tasha jin mata yan uwanta da yawa na yaba ta bare tarin maza dake kara
kaina a kanta

Ta sake satar kallon nasa wannan karon maimakon ta tadda shi yana aiki kamar dazun yanzun
takardun na watse ne a gabansa ya jingina kansa harda bayansa a jikin kujera dukkanin tafin
hannunsa ya tallafe bayan kansa da su idanunsa na rufe,gashin idonsa yayi ma idon rumfa
tamkar an jera su

"Bani abinci"ya fada idonsa na a rufen,ta miqe ta shirya masa komai still dai idanunsa na arufen
har ta gama ta koma ta zauna,a hankali ya bude idonsa ya kalli warmers din"u mean ni zan
zuba kenan da kaina?" ta girgiza kai sannan ta taso ta zuba masa white rice ce da miyan
kaza sai hadin coleslaw tana kammalawa ta miqe da niyyar fita "ina zaki je?"ya tambayeta cikin
izza,ta kawar da kanta sannan tace "sashina zan koma" yaci gaba da cin abincinsa sai da ya
mula don kansa sannan yace "ban baki izini ba"cike da haushi da takaicin irin mulkin da yake
mata ta koma da baya ta zauna kanta a qas


Cin abincinsa yake with calmness ba abunda ya dameshi ya shanyata abunsa,har ya kammala

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login