Showing 93001 words to 96000 words out of 135036 words
Chapter 32 - Wa Yasan Gobe Compelet Book by Safiya Abdullahi Musa Huguma .pdf
qaryar bata karbeshi ba sai ya jada harda subul da baka
ba tare da ya ankara ba "ya zaka dawo bayan baka sallami baqi ba ali?,wai meke damunka ne
haka?,a kunnena fa abbanka ya tursasaka zuwa bikin bude kamfani,yanzu kuma ka taho ka bar
jama'a acan,baqonka annabinka fa ali"yayi saurin dosar qofar fita yana cewa"momi ai ba
matsala mukhtar zaiyi komai kamar ina nan,sai da safe momi idan abban ya sauko ki gaida shi
ina hanya goben"baki sake ta bishi da kallo tana ayyanawa tabbas akwai abinda ke damun
yaron nan,gashi da shegen zurfin ciki kamar mace,idan kaji cikinsa to ya ciyoshi ne,ta dan daga
murya tana cewa"ka gaida mutan gidan" "zasu ji momi" ya fadi yana barin falon cikin sauri don
kada suci karo da iftihal ta tsaida shi
Har ya koma ya bude sashensa ya shiga yayi wanka ba wadda ya gani,shi yama fi son haka din
ma,yasa koda sunzo babu abinda.zai samu sai qarin tension,shi kuma yanzu abinda ke
damunsa yasha kansa fiye da komai,sai da dibi kusan awa daya da wani abu sai ga
salima,fuskarsa ta zubawa ido tana murmushi saboda sosai aliyyu ya canza,ya qara ja sumarsa
ta sake baqi sidik,gargasar jikinsa kamar an dada mata baqi laushi da yawa,ya sake
kyau,badon fadila da ta hargitsa masa lissafinsa ba da abun yafi haka,hakanan shima ya sakar
muta fuska don ya zama dole haqqinsu ne don bazaya yiwu haqqin wani ya danne na wani
ba,kuma matsalarsa yasan ba tasu bace indai ta wannan bangaren ne
Da sauri ta qaraso ta zube ajikinsa tana fadin "oyoyo welcome my dear"yadan karata ajikinsa
yace "thank you ya muka sameku?" "We are fine but I miss you" yadan saki fara'a "ok,to ai
yanzu gani mai zan samu?" Ta tabe baki sannan tace "ba komai tunda ai ba yau kace zaka
dawo ba ganinka kawai mukayi tsakar rana,ni ta window ma na hageka ka fice" "ni din ma haka
dawowar ta zo min" cikin son bin qwaqwafi tace "ko fadilan ce ta takura sai andawo?" "Eh"kawai
yace mata cikin som kashe maganar don tamkar allura ce akan qurji idan aka tada masa da
zancan fadila, "but ban gata ba kuma ma bangaren ta akle yake" "eh"ya kuma cewa dai bai
buqatar taci gaba da yin maganar
Shiru ya dan ratsa dakin kanta na jingine a kafadarsa,kishin fadilan duk ya cikata gani take
kamar wani gun ya kuma kaita don ta huta,samira ta danno kai harda sallamarta kamar gaske
kai a sunkuye,duk da haka saboda tsabar neman bala'i sai da ta gasawa salima hara ra,ai kuwa
itama bata yi qasa agwiwa ba ta rama don ba qaramin adashen tsiya suka dinga shukawa ba
sanda baya nan,kullum sai an raba gari a gidan saidai idan garin Allah bai waye ba,amma
kwana suke su wuni suna abu guda kamar karnuka,suna hada ido da aliyyu ya bata tasa
hararar tayi saurin sadda kai qasa,gefansa ta zauna cikin tausasa murya tace masa "sannu da
zuwa an dawo lafiya?" "Lafiya"yace mata a taqaice,duk sai taji ta muzanta,tafi kowa sanin
laifinta,gargadi mai zafi babu irin wanda bai musu ba kafin ya tafi kan fice fice,duk da yau ma
tsautsayine amma ta kwan biyu bata saci fita din ba,wannan ne satar fitarta ta hudu salima tayi
biyu tana tsammanin tayi na qarshe tunda ya kusa dawowa qasar bata san yau ya dawo ba
Shiru ya gauraye falon kowa da abinda yake saqawa cikin zuciyarsa,aliyyu yafi kowa nisan kiwo
cikin duniyar tunani,"dear ya kamata muje ku kwanta ko?"salima ta fada tana kashe masa
idanu,da sauri samira ta dago "kamar yaya?"cikin daga murya samira ta tambayeta,itama ta
dubeta ta mayar mata "kamar yadda kika kunnuwanki suka ji nace"da sauri ta nunata da yatsa
"baki isa ba wallahi kinyi kadan don yadda kike buqatarsa nima hakan take.....ke bari ma nayi
miki dalla dalla...yadda kike a matse ni nama fiki matsuwa"ta fada tana wani gayara zama,sai
kuwa cece kuce ya barke dama kadan kowacce take jira 'yar uwarta ta tabo ta,sak yayi yana
kallonsu,sai ya zama kamar wani mutum mutumi,babu wadda tayi masa wani abu na azo a gani
a matsayinsa na matafiyin da yayi wata judu bai cikin iyalinsa yanzu ya dawo musu,shegiya
shinkafa fara sol da yaji babu wadda ta turo masa tace gashi,amma aqalla ai ko tsakar dare ya
dawo idan da tunani sa tashi su sama masa wani abu ko drink ne,to amma ga drink din ma
jibge a freezer dinsa su dauko ma su hada masa da cup suce masa gashi babu wadda ta iya
yin hakan,babu wani welcoming na arziqi,amma ko wacce burinta ya kwanta da ita ya biya mata
buqata kamar wani inji
Ganin abun nasu ma shirin wuce makadi da rawa don har an fara 'yar lakace lakacen hanci
yasa ya dakatar da su ta hanyar daka musu tsawa don idan ba tsawar ya musu ba yadda suka
kacame babu wadda zata iya jiyo shi"bana buqatar kowa cikinku,duk ku tashi ku bani
waje,tunda ku baku iya kwantarwa da mutum hankali ba saidai ku tayar masa,ko kwana daya
banyi ba cikin gidana amma kun fara samin bacin rai?" Tuni samira ta miqe,salima ta rausayar
da kai tana cewa "amma aliyu ......." "amma me?Please stay away" ya fada yana nuna mata
hanya,samira ta sheqe da dariya tana cewa "ato saiki taso ai mu daye,ki daina naci haka kowa
sai ya riqe kwadayinsa tunda yace bai yi" wani banzan kallo alin ya watsawa samiran yana
cewa "kin sanni,kada ki bari muyi arangama dake bani da kyau!"tasan hakan kuwa tuni tayi
gaba salima ta bita a baya,yan jiyo kici kicin kokawarsu a bakim part din nasa,yayi banza da su
_*12 PM*_
Sha biyu na dare ya dinga gwada maqullan hannunsa a qofar har ya samu na qofar tata,ya tura
ya shiga ya haska makunnin fitila ya danna dukka qwayayen suka kama bangaren ya cika da
haske,qamshi falon yake tamkar tana nan,kamar bata yi tafiya ba na tsawon watanni hudu
ba,hakanan komai akillacensa,kai tsaye ya shige bedroom dinta,shima dai kamar falon cikin
qamshi yake da tsafta,gadonta a dame yake komai ajere,pant da brassier dinta ne kawai a
gefan pillow,ya qarasa ahankali ya haye gadon hadi da kwanciya pillow din ya janyo hadi da
rungumeahi tsam tsam a qirjinsa,qamshi pillow din yake kamar a shafa masa turare ne,ya sake
miqa hannu ya dago pant and brassier din farare qal ya zuba musu ido,a hankali ya mannaau a
hancinsa yana sheqar qamahin turarenta na shamsul imaraat
A hankali ya shiga sosai cikin zurfin tunani,yanayinta,halayenta,dabi'unta,haquri irin nata
kawaici da yakanah,bai taba ganin ta tana fada irin nasu samira ba,bai taba ganinta tana koda
sa'insa da daya daga cikinsu ba,duk wata sabga tasu bata ciki,shi da kansa alokutan baya har
haushi yake ji idan yaga bata damu da fadan kishi ba,ashe so ne?,ashe haushi yake ji yana
ganin kamar bata sonshi ne?
Juyi kawai yake samar gadon,jinsa yake tamkar wani maraya,wani irin kewa yakeji mai zafi da
radadi tana kamashi,ya riga da ya saba da kwana jikinsu na gogayya da na juna,ya saba da
sheqar qamshinta,sosai ya sake rungume pillow yana sakin numfaahi sama sama,yafi awa biyu
kafin wani wahalallen bacci awon gaba da shi ,ko cikin baccin ma bata qyaleshi ya huta ba sai
da ta jawo masa yin wanka,ya dawo bakin gadon yq zauna yana tsane jikinsa da towel
dinta,idanunsa ya sauka kan wani dan kyakkyawan madaidaicin frame da yake zaune dirshan
bisa side bed,yasa hannu a hankali ya dauki hoton ya zuba masa ido yana kallonta,murmushi
take yi sosai,fararen haqoranta jerarru reras sun bayyan,yar lobawar dake tsakiyar habarta ta
fito sosai,ya sanya bakinshi saitin lips nata yayi kissing,murya qasa qasa yace "I love you"ya
dan manna hoton a qirjinshi
Sai da yayi sallar asuba sannanya baro bangaren har ya fito ya manta bai dauko hoton ba ya
koma ya dauko abinsa,kan side drower dinshi ya kafa sa,yana shiryawa yana kallon hoton har
ya kammala shirinsa tsaf cikin shadda fara tas mai asalin tsadar sai maiqo take da daukan
idanu,yayi masifar kyau saidai fuskarnan na kirtibe,qarfe bakwai ga fito ya soma da sashen
samira don itace a damansa,yana tura qofar ta bude alamuna bude ta kwana,kai tsaye ya zarce
bedroom din ta don yasan tana ciki,yana tafiya yana bin falon da kallo tamkar dakin ajiyar shirgi
haka ta maidashi
Dai dai ya sameta saman gado hannu can qafa can,gajeran gashinta maras tsawo wanda bai
hadu da mace mai gyara ba duk ya hautsine ya tashi yayi cako cako kamar bishiyar qaya(don
ko baki da tsawon gashi matuqar ke mai gyara ce to zai bada sha'awa,amma komai tsawonsa
indai ba gyara abin qyamata zai zama),sosai iyyu ya tsani irin wannan kwanciyar tata,don kuwa
insha Allahu kuka hada gado daya da samira to ranar fa ka shieya zaka daku da hannu da
qafa,haka kullum yake fama da ita,shi yasa ya gwammace ya matseta a jikinsa ayi baccin haka
Ya dan taba qafarta yana kiran sunanta,saidai kamar gawa ko motsi bata yi ba bare yasa ran
zata tashi jan minsharinta kawai take,yasan hali dama bata motsa din ba kuwa har sai da ya
dage ya daki daki qafar da hannu sannan ta miqe a zabure tana cono baki gami da mutsitstsika
ido,sai da ta gama mutstsike idanun sannan ta dubeshi,ganin aliyyu a tsaye ya sata shiga
taitayinta,addu'a take cikin ranta Allah yasa maganar laifinta yazo yayi mata,don tasan halinshi
shirunsa ba abu mai dadi yake haifarwa ba,fuska a murtuke yace "hala ko sallar asuba bakiyi
ba?" Nan ta hau kame kame "zan....zanyi....yanzu ne na tashi ai..." "good" yace da ita cikin
takaici yana gayada kai,ya juya zai fita "zan fita sai na dawo" "to" tace kaar wadda aka tilasta ta
sai ta fadi hakan,Allah Allah take ya fitan taja bargo ta koma barcinta,bata sani ba shi din ma
Allah Allah yake ya bar dakin,don zarnin bandakinta dake cikin bedroom din shi ke busowa har
cikin dakin gadon,sai taga kuma ya juyo hadi da cewa "bani key din motarki da wayarki" cikin
marairaita tace "don Allah kayi haquri bazan sake ba" a zafafe ya kalleta "will you keep quiet or
not? Da baki iya bada haqurin ba kenan sai yanzu?common bani key da phone nace"nuni tayi
masa kan hargitsatstsen dressing mirror dinta,ya juya ya kalli kan madubin saboda
hargitsewarsa ma shi bai hango wata waya ba ballantana maqulli "ok...ni zanje ma na dauko
miki ko?" Dolenta ta sauka daga kan gadon ta dauko ta miqa masa tamakar zata yi ihu,ya amsa
ya fice da sauri ba tare da yace mata qala ba don zarnin sake busowa yake,kuma ko yace ta
gyara ba zata yi din ba don sau nawa yana fama da ita kan hakan sai tave masa yau fa sati
daya kacal da wanke shi ba wani dadewa yayi ba
Salima ma na bisa gadon a nade bacci na dibarta sama sama,ita din ma sai lokacin bakwai da
wani abu ta yi tata sallar,saidai yana sallamar ta amsa gami da miqewa zaune kan
gadon,murmushi take masa wanda hakan ya sanyashi rage daurin fuskarsa"kar daiace har ka
fito" ta soma cewa,ya kalleta yace "eh"yana mamakin yadda basu iya gaisuwa wa mijinsu
ba,babu wadda ta fado masa sai fadilan,duk safiya sai ya gaidashi kamar yadda ya zame mata
qajibi sannu da zuwa da adawo lafiya duk da sai yaso yake amsawa amma hakan bai dameta
ba haqqinta take saukewa, "amma yaci ace yau a gida zaka wuni ko" ta sake shigowa da wani
qorafin "a hakan kuna batan ran babu wani caring bare a faranta maka"yayi zancqn cikin
zuciyarsa,a fili sai yace "maiduguri zani zuwa anjima zan dawo insha Allah"cikin tuhuma tace
"maiduguri?gurin wa?...." "stop your suspicion,sai na dawo" ya katseta, "madalla"tave tana
binsa da cike da kishi har ya fice
Cikin motarsa qirar 4matics fara ya zabi yin tafiyar shi kadai,bayan yin addu'o'in matafiyi ya
kunna motar ya fice daga gidan cikin tsammani mai yawa da fata na gari akan kanshi
*mrs muhammad ce*
✍✍
[10/16, 2:10 PM] Salma: 
*WA YASAN GOBE?...*


*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

*PART 3*
7⃣&8⃣
Cikin kwankin kullum cikin kuka take kwana take wuni,a haka ma an samu sauqi saboda takan
kaucewa idon anty hauwa don kada ta dinga jin ba dadi,damuwa sosai ta yiwa zuciyarta
yawa,tana jimantawa kanta yadda soyayyar aliyu ta gama illata ta,saidai bata barin damuwar ta
tsawaita mata da yawa ba ta tsananta yin addu'o'i,da taimakon hakan ta soma samun
kyakkyawar nutsuwa cikin ranta,koda yaushe cikin kula da ita anty hauwa take bata barinta ta
zauna ita daya bare ta damu sosai,sau da yawa anty hauwan idan tana bata haquri kunya
fadilan keji "nifa babu wanda yayimin laifi don Allah anty ki daina bani haquri,kunya hakan yake
bani wallahi"
Yara kam murna suke anty fadila ta dawo gidansu sunata tsalle,idan akace babu makaranta to
suna liqe da ita wani lokacin har sai anty hauwan ta kore mata su tace su barta ta huta,ita kam
dadi take ji idan tana tare da yaran saboda dama can mai son yarance ita,sosai mamansu taja
kunnensu da kada su sake su gayawa kowa cewa anty fadilan tana nan gidan saboda yadda
taga suna rawar qafa zasu iya subul da baka
Ita kanta tayi mamaki qwarai yadda ta soma ragewa kanta damuwa kan aliyun duk da yake ba
abun mamaki bane addu'a ai tafi qarfin wasa,sosai tayi yaqi da zuciyarta,bata bari bacin rai ya
rusata ba,da zarar ta soma tunane tunane zata datseshi ta hanyar daukan qur'ani ta
karanta,idan ta gama kuma ta shiga shafukanta na sada zumunta,komai anty hauwa ta hanata
yi,duk da hakan fadilan taqi yarda don kullum tare suke shiga kitchen yin lunch ko dinner,wani
lokaci kuma ta shirya mata yaran da safe
Gudu sosai ya dinga yi shi daya cikin motar,cikin ikon Allah ya sauka lafiya,saidai tun daga
yadda su ya gana ke faman tambayar fadilan ya sare da al'amarin ya tabbatar bata garin ma
baki daya bare gidan,sallah kawai yayi ya baro garin,bai damu da yawan tafiyar da yasha ba
bare ya nemi hutawa har yaci abinci,juyin duniya ya gana tayi ya tsaya yaci abinci amma qeme
me yaqi,ya bata haquri bayan ya ajjiye musu kudade masu dama yace yana da abubuwan yi
masu yawa a kano,haka ya kamo hanya ya taho,gudu na ban mamaki ya dinga shararawa ba
qaqqautawa,sai da yaji tuqin na neman gagararsa sannan ya samu wani shago kam hanya ya
siyi yoghurt yasha,bai fasa gudun nasa ba wanda ikon Allah ne kawai ya kawoshi garin kano
lafiya
Kwana hudu bai cikin daidanshi,matansa mata ne marasa kulawa,tabbas sunga canji sosai
tattare da shi amma babu wadda ta damu da tambayarsa mene damuwarshi,momi kam ganin
baice komai ba yasa ta tsuke bakinta ta qyaleshi don ta sani ida dai ya soma zurfin cikin nan
nasa bai gayawa kowa komai sai lokacin da yaga dama
*G*idan anty hauwa shine gida na qarshe da hankalinsa ya kai kai,anan ya tattara dukkanin fata
da tsammaninsa,duk da wata zuciyar na tantamar mai zaya kaita can bayan ko gidansu bata je
ba?,qarfe biyar da shirin na yamma ya gama shirinsa cikin qananun kaya da sukayi matuqar yi
masa kyau
Suna kitchen ita da fadilan suna hada abincin dare sunayi suna hirarsu,yara suka jiyo wadanda
suka bari a falo suna kallo da yake alhamis ce suna cewa "ina wuni uncle....ina wuni uncle"
gaban fadila yayi mummunar faduwa ta saki mirfin hannunta da take shirin rufe miya da
shi,"shikenan yau zan amshi takardar rabuwa da shi" abunda zuciyarta ke gaya mata kenan
"anty aliyu ne"ta fada tana kallon anty hauwa dake tace shinkafa "aliyu?" Ta fada tana kallon
fadilan cikin kasa kunne,"ina zuwa" anty hauwa fada bayan ta ajjiye tukunyar hannunta ta fice
da sauri,komawa fadila tayi jikin drawer ta jingina bayan ta hatde hannayenta a qirjinta tana jiyo
sweet voice din sa,batasan me yasa take jin qunci a qirjinta dalilin gaya mata da zuciyarta ke yi
takardar sakinta aliyun ya biyota da ita
Ruwa aliyun yace ma anty hauwa ta bashi,duk ruwan dake freezer din falonsu ya qare sai
lemo,da hanzari anty hauwa ta miqe ta hau sama ta dauko masa a parlour din abban kausar
don bata son ya shiga kitchen din,ji yayi bazai iya jiranta ba don haka ya miqe ya shige kitchen
din,a hankali fadila ta bude idanunta da a da ke a lumshe,cikin jikinta take jin tahowar tasa,nan
da nan tayi wuri wuri da ido tana neman maboya,a asukwane ta shige bayan qofar wadda a
kusa da ita freezer din take
Kai tsaye ya qaraso ya dage freezer din ya sunkuya yasa hannunsa ciki,cak ya tsaya da
qoqarin ciro ruwan da yake yi,sai yake jin qamshinta cikin hancinsa,irin qamshin da ya ji cikin
bargo pillow da undies dinta,sakun murfin yayi ya soma kallen kallen kitchen din yana neman ta
inda qamshin ke fitowa,ko ina ya kai idanunsa sai yaga babu kowa,tuni fadila tayi surrender
bayan qofa numfashinta kamar zai dauke musamman da taji ua jingina a bayan qofar ya kuma
qin barin gurin,yafi minti uku cikim kitchen din yaqi fita din qamshin turarenta na ahlamul arab
kawai yake ji,hat sai da anty hauwa ta shigo hankalinta a tashe tana tsammanin ya ga
fadilan,sai ta tadda shi a tsaye kawai jingine jikin qofar hannayensa harde a qirjinsa,"ina ka
shiga ga euwan can na kaimaka" "ok" kawai yace ya gewayeta ta fice daga kitchen din itama ta
rufa masa baya
Ta maida yara dakinsu daga ita sai shi a falon,zuba masa ido tayi sosai tana kallonsa canji qara
ta hango tattare da alin,fara'arsa ta sake qaranci sosai,tsiyayar lemon kawai yake yi yana
dirkawa cikinsa,yadda bai tanka ba itama bata ce kamzil ba har sai da ya tashi da roba biyu ta
ruwa da lemo,ya dago kai ya kalli antin hadi da sakin ajiyar zuciya "ni wai uncle meke
damunka?tunda kazo naga kamar a hargitse kake?"wata ajiyar zuciyar ya kuma saki "fadeelah
nake nema mummyn kausar" kamar gaske ta nuna alamun rashin fahimta sosai "kamar
yaya?fadilan da kuke tare,yaushe dududu sumayya ta ke gayamin kun dawo daga china zaka
ce ita kake nema kamar wadda ta bata" "bata tayi....bacemin tayi"ya fadi