Showing 45001 words to 48000 words out of 135036 words
Chapter 16 - Wa Yasan Gobe Compelet Book by Safiya Abdullahi Musa Huguma .pdf
da ita"tilas kowacce ta waiwayo ta dauki tata tabar sashen
Cikin matsanancin bacin rai ta dago kantasai suka hada ido,wani baqinsa ta gani wanda bata
taba ganin yayi makamancin haka a idanunta ba,kafin ya janye idanunsa ta fara janye nata tayi
azamar juyawa ta bar sashen
Kusan kwanan zaune tayi ,babu abinda ranta bai gaya mata ba,abunda take ta qoqari da fadi
tashin bunneshi ashe ya dade da yin tsiro har yqyi yabanya?tabbasa aliyyu ya cutar da
zuciyarta ya cutar da zuciya da ke cike da qauna gami da begensa cikin kowanne fitar numfashi
na dan adam,tabbas a ayu badon mutum bai da ikon cire son wani daga zuciyarsa ba da itakam
ta ciro har zuciyar ta wurgar ta huta ma gaba daya,ranar idanunta basu ga bacci ba sai tunani
data takurawa.kanta da shi wanda ya haifar mata da da ciwon kai da zazzafan zazzabi,ba ita ta
samu kanta ba sai washegari da la'asar bayan ta takurawa kanta ta cire damuwar ta ajjiyeta
gefe
⚜⚜⚜⚜⚜
Cikin qyanqyami yake shiryawa,gaba daya dakin ya hargitse sun kuma barshi kamar yadfa suka
saba,sai dan yakanji relief idan ya tuna zaije ya dawo ya tarar da komai ya zama neat,da
hanzari ya kammala ya dauki jakarsa ya fice ba tare da ya saurari breakfast da salima ta
hada ba ruwan tea ne fari sol babu citta bare kanunfari sai soyayyen qwai wanda qarninsa ke
hanashi hadiyarsa,shi kuma akwai qyanqyami yayin da su kuma basu maida tsafta
da gyara wani abu mai muhimmanci ba
Sanda ya dawo ya tarar da sashen nasa yadda ya barshi yayi matuqar mamakin hakan,don bai
saba ganin haka ba,yasan ranakun girkinta zai tadda komai a kintse hakanan yaji ransa ya baci
da ganin haka,ya zube anan saman kujera yana fitar da iska mai zafi daga bakinsa,ya dubi
agogon hannunsa qarfe shida da arba'in har da hudu,mintina qalilan suka rage a shiga
masallaci sallar magarib,a kasalance ya duqa yana zare sau cikin qafarsahadi da sabule
safar,wata bahaguwar yunwa ke rarakarsa,yinin yau gaba daya ba abinda yaci banda maltina
mai sanyi da ruwa da yake ta dirka,saoda yana da yaqinin zuwa ya tadda abinci mai kayau,
Kai tsaye ya shige toilet ya dauro alwala ya dawo falon yana goge ruwan jikinsa da
handkerchief,gidan tsit sai hasken fitilu da ya gauraya da duhu suhun magariba da ya soma
kawo kai ,ya dan lumshe idanunsa kewar qanan yara na shigarsa,ya tabbata da yana da su
da zai dinga jin koda hayaniyarsu ce da gilmawarsu ,ya riga ya saba da tsabar qwarewar.matan
gidan wajen iya rashin kula da miji,ya katse tunaninsa sanda ya jiyo kiran salla a masallacin
dake can farkon layinsu ya sanya silifas ya fice yana maìmaita abinda liman ke cewa kamar
yadda annnabi ya horemu idan munji kiran salla
A can ya zauna ya jira sallar isha'i sannan ya dawo gidan,still gidan dai na nan kamar yadda ya
barshi kowa na kulle a sashensa,ya dauki wayarsa ya kira nasiru ya gaya masa inda zaije ya
samo masa masa da miyar ganye,cikin lokaci kadan saiga nasirun ya dawo ya amsa ya koma
ciki yayi wanka ya sauya kayan bacci,ya zuba masar ya ci sai da ya qoshi sannan ya jawo
computer dinsa ya soma shigar da lissafinsa na yau,hankalinsa ya kasu kashi biyu,ko alama
zaman gun ya gundireshi sabo da tsaftar gun bata masa ba,shigowar saluma ce ta saka shi tsai
da abinda yake ,ba laifi salima indai ta bangaren qalqale jiki ne salima ta iya wannnan
kam,yanzun ma ashirye take cikin dinkin lace baqine mai adon ja,ya sauke biron dake
hannunsa
Mrs muhammad ce
✍✍✍
[10/16, 12:42 PM] Salma: 
*wa yasan gobe?*.......


*written by safiyya Abdullahi musa huguma*

▶3⃣6⃣
Ya sauke biron dake hannunsayana dan binta da kallo,tayi masa kyau sosai,fuskar sa ta dan
sassauta daga dauretan da yayi ganin yadda take masa murmushi,gefansa ta zauna cikin
salon kissa take cewa"barkanka da warhaka ranka ya dade"yadan janyota jikinsa yana cewa
"barka kadai......sai yanzu aka ga damar zuwa yimin sannu da zuwan?"ta san tabe baki
tace"girki na ne da zan taho daga dawowarka?" "Ko ba girkin ki bane ni ba mijinki bane?" "To
ayi haquri ko" yace "ya wuce"ya maida kansa kan aikinsa tana tayashi da hira jifa jifa yana
amsa mata
Samira ce ta shigo wannan karan harda sallama,abun arziqin nata yau yana da yawa don
ba'ayi wari da.wari ba riga da zani ta saka na atamfa,kanta tsaye ta zauna daf da shi tana mata
sannu da zuwa ba tare da ta nuna ma ta san da zaman salima ba agun,ya dan saki fuska bayan
ya ja yatsun hannunta da nashi zara zaran yatsun yace"bana amsawa tunda kema sai yanzu"
"bana shishshigi ne sweet kuma bana son maiyi shi yasa"ya dade da haddace wannnan kalma
daga bakin samiran,don haka ya mele baki gefe sannan yace"lallaikam,da kun bani babies ai da
sai nace kusha zamanku ni kuma insha hira da yara na ko?"
"Nikam ai na riga nabada tawa baby din"cewar salima"no she is belongs to momy,u already
know...sabuwa nake so"cikin shagwaba ta dan bata rai sannan tace"haihuwa is not easy
dear"samira sai ta tabe baki hadi da cewa"mukam ai ba yanzu ba,tunda sauran
quruciyata"aliyyu ya jawo ragowar takardunsa yaci gab da rubuce rubucensa ,kowacce
yasan inda tasa gaba dama salima d tasu ai tun shekarun baya,shikam idan da abunda ya rage
masa yanzu shine tara family babba
Cikin kwanakin fadika ta watsar da duk wata harka data danganci aliyun ta koma rayuwarta irin
ta da,idan gari ya waye tayi ayyukanta na gida ta fice office sai ta dawo tan dawowa ta shige to
sai washegari idan ta gaji sai fa kira farida ummi ko anty hafiza su sha hirarsu,ko muhammad
yazo mata su wuni tare abinsu
Gaba dayan bangaren ya fita daga ran aliyyun saboda tsabar kacamewar da yayi,ko ina ba
kyawun gani a hargitse,ranar da salima ta fita daga girki yaga tana shirin kulle sashen ta wuce
nata sashen,cikin takaici ya kalleta ganin bata da niyyar kawar da ko cup din da ta hada masa
tea bare akai ga batun gyara "jimana!" Yace da ita a zafafe ta dawo tace gani"bai ko kalleta ba
ya daga intercom ya kira sashen samira ,sai da ta qara wasu mintina kana ta iso hakan ya sake
hassala shi,ya dubesu cikin bacin rai yace
"Anya kuwa ky mata ne cikakku?ba ko wani jinsin bane ku?"a mamakance suka dago suna
kallonsa,"kamar ya?"inji samira,da hannunsa ya soma yi musu nuni da falon suna binsa su
kuma da kallo,"ku duba....dubi......haka ya kamata ace ya kasance?haka sauran mata suke
barin turakar mazajensu?....abun naku ba ya yi yawa na lira ba hankali a ciki,ba tsafta ba iya
kula da miji?kuma ni kuna son kyautatawa daga gareni?....it cant abun yayi yawa na gaji da
tolerating bad attitude dinku....as from today ya zama dole a kanku kowacce kafin ta bar
nan ta tabbatar ta gyara duk inda ya kamata ba ruwana da qazantarku ruwanku ne ku gyara
naku ko ku barshi haka is not my own business.....
Ya suri briefcase dinsa ya fice,da kanshi yau zaiyi driving kasancewar nasiru baya nan ya tafi
ganin gida ,ya juya kan motar ya danne horn yana jira a bude masa,ta kalli gilashin mudubin
dake gefansa da niyyar gyara zamansa don ganin wanda kebin bayansa sai yaga wata motan
na jira ya fita itama ta fita,ya duba sosai sai ya hangota zaune hannun ta saman sitiyarin
fuskarta tayi fresh cikin safiyar,agogon dake daure a tsintsiyar hannunta take kallo da alama ta
kusa maka rane don sai yatsina fuskarta take,material ne ajikintan yellow mai adon coffee,ba
makeup ko kadan a fuskarta banda powder data shafawa soft chocolate skin dinta,sai lips balm
data shafawa lips dinta sirara masu taushi,tayi lullubinta na mutunci har saman ka,ya dan tabe
baki ya dauke kai itakam bata san ma yana yi ba,duk da ta ganshin
Ayimin afuwa kasancewar yau ina da uziri irin wanda ke kama ko wanne irin dan adam na turo
muku shi late kuma ba yawa amma zamu hadu insha Allah,ina godiya a gareku
Mrs muhammad ce
✍✍✍
[10/16, 12:42 PM] Salma: 
*wa yasan gobe?......*


*written by safiyya Abdullahi musa huguma*

3⃣7⃣~3⃣8⃣
Fisgar motar yayi ya ficee daga gidan sannu sannu take binsa a baya har suka bar cikin layin
suka hau babban titi,yana hangota ta qarawa motar gudu tayi over taking nasa ta wuce shi ba
tara da ta dubi koda sashen sa ba,ya daga idanunsa yabi motar da kallo yana dan gyada kai
cike da mamaki da jin izza shi zata nuna wa iyawa da qwarewar sarrafa mota?,yaushe ma ta
fara kama sitiyarin
Wani girman kai ne ya kamashi,ya qarawa motar shi speed cike da qwarewa da gwaninta shima
ya mata over taking,ta lura sarai da shi amma sai ka rantse da Allah batasan da wanzuwarsa
akan titin ba,ta dan cije lebenta sannan ta dan daki saman sitiyarinta cikin zuciyarta tana dariyar
mugunta,sai da ta barshi ya sakankance sosai ta take motar ta qara maya gudu sai ji yayi fit ta
wuceshi ,cikin zafin nama da mazantaka ya qara wa tashi shima wutar don ya nuna mata bata
isa ba saidai kafin ya qaraso har ta qaraso kwanar freedom ta sanya signal ta shige,ta morrow
din gaba suka hada ido yana wucewa amma sai ya wuni mugun dauke kai kamar ma bata
sanshi ba
Ya girgiza kai ya miqe kasancewar b.u.k zai shiga hanyar ta rabu cikin zuciyarsa yana fadin"zan
koya miki hankaline kin maida ni abokin wasanki kenan
Qarfe biyu ya baro b.u.k din bayan ya kammala abinda ya kaishi,kai tsaye ya tashi motarsa ya
bar makarantar,biyu da rabi ya iso freedom hakanan bai taba zuwanta ba koda hira suke son yi
da shi yana basu appointment ne,ahankali ya gangara layin ya qaraso bakin gidan radio din ya
yiwa mai tsaron bakin qofa horn ua taso don yaji me ke tafe da shi,da ganinsa ya fara fara'a
cikin mutunci suka gaisa ba tare da jiran komai ba ya bude masa qofa yana jira ya shiga,da
hannu aliyu yayi kiransa ya qaraso saitin window ya ranqwafo yana saurarensa,"wata sabuwar
ma'aikaciyar ku nake nema ina fata bata fita ba"cikin tunani yake kalleshi,aliyu ya gyada masa
kai da son tabbatar masa,sai kuma yadan saki murmushi yace "oh ko haj fadila?"aliyu ya
gayada kai yace"yes itace" tana nan ciki kuwa bata fita ba mutuniyar arziqi kuwa ranka ya
dade.....ko kira maka ita za'ayi"aliyu ya dakatar da shi"✋a'ah barshi zan dan jirata ba
matsala"ya tada motar ya shiga security suka nuna masa gun parking"ya daidaita motar qasan
bishiyun dake gun ya kasheta,ya miqar da sit din nasa ya kwantar da shi yadda zai masa dadin
kwanciya,yayi sama gaba daya da glass din motar kasan cewarsu akwai (tinting)jikinsu,yasa
hannu ya qaro qarfin a.c dake jikin motar ta gauraye masa ko ina ya kashe dukkanin wayoyinsa
ya watsa su sit din gefansa,ya maida bayansa ya kwantar jikin kujerar yana fuskantar ginn
gidan idanunsa akan reception,lokaci lokaci kuma yana bude mujalla yana dubawa
Zaman minti ashirin yayi ya ganta ta fito gefanta wata yar matashiyar ce sabe da baby girl a
kafadarta ,ita tayi hanyar waje ita kuma ta nufi inda tayi parking tasa maqullinta ta bude motar
tashiga,ya miqe ya gyara zaman kujerarsa ya jawo belt ya daura,ya kunna motar ya biyo
bayanta sanda take ficewa daga ginin gidan radiyon
Ko kusa fadila bata lura da shi ba don bata kawowa ranta ba,cikin kwanciyar hankali take
tuqinta,wani mahaukacin horn taji ana mata kafin ta ankara motar ta zo daf da ita tana shirin
gogarta a gigice tayi gefe da motar tana ci gaba da kallon motar da ta kasa tantance waye a
ciki?,kafin ta gama wannan tunanin har ya dawo daya side din data koma ya sake matsowa daf
da ita yana shirin gogarta,sai ta tsorata kasancewar titin da ta biyo ba mai yalwar jama'a
bane bugu da qari kuma rana ce babu gilmawar mutane sosai a gun
Cikin lokaci qanqani ya gama rudata gaba daya ta tsorata dama da hugunta ya dinga
komawa,tuni lissafinta ya qwacr tama manta sitiyarin na hannunta ne,sai ta taji motar ta soma
yawo da ita saman titi idanun aliyu na kan motar,ya zubawa motar ido ganin ta soma yawo bisa
kwalta a hankali yana nazari,ya saki ajiuat zuciya sanda yaga ta daidaita ta daina tangal tangal
din da takeyi,ya qaraso saitin window dinta sai ya sauke glass ta juyo idanunta cike da taf da
tsoro suka hada idanu,ya dauke kansa ya qarawa motar speed yayi wucewarsa,wani abu ya
daki zuciyarta sai ta kasa tuqin,ta sauka a hankali ta gangara gefan kwalta ta kashe motar ta
jingina da makarin motar idanunta a runtse zuciyarta na ci gaba da bugawa,sai
hawaye ya biyo rufaffun idanunta ta saki kuka silently,sai da taji don kanta ta samu nutsuwa
sannan ta kunna moyar taci gaba da tafiya slowly a gefan titi don gaskiya ya dauki haqqinta
Tana isa parking space taga motar tayi tsammani ya shge cikin gidan saidai tana gama kulle
motar ta ganshi tsaye jikin motar yana amsa waya,idanunsa suka shiga cikin nata wadanda
suka dan kafa alamar tayi kuka takaici yasa ta sakar masa harara hadi da murguda masa
bakita shige jin alamun taku tayi ana bin bayanta,tana juyawa taga kuwa shi din ne,tasan mai
yasa ya biyota cikin azama ta qarasa shigewa bangaren nata daidai lokacin da yakai hannunsa
zai fincikota,tayi saurin sanya maqulli ta qulle qofar hadi da jingina a jiki,tana kallonsa ya juya ya
koma" kawai"ta fada a hankali
Zaune take tana kallon wani Indian film hum dil de chuke sanam tana ganin son maso wani
tamkar nata da aliyu,ta bada hankalinta kacokam bisa t.v din sai tsintat qamshinsa tayi yana
yawo bisa hancinta,ta dago da sauri yana tsaye bisa kanta hannunsa harde a qirjinsa shima
idanunsa na kan t.v din sai a lokacin ta tuna da abinda ta masa dazu da hanzari ta miqe ta jawo
hijabinta ta zira tana neman guduwa sai alokacin ya dawo da idonsa kanta fuskarsa a dinke
tsaf,da baya da baya ta soma tafiya yana binta har ta dangane fa qofar bedroom dinta ta fafa
ciki tana shirin danno qofar,yasa hannu ya kare ta,yaci gana da binta sai da ta dangane da sif
dinta ,qwalla ta cika idanunta idonta tuni ya raina fata,girgiza kanta ta soma yi tana cewa cikin
tawar murya"donA....Allahh kay......yi...yih.....haquri...."yasa yatsansa ya dalle mata baki,taji zafi
sosai ta sanya hannunta ta dafe bakin,ya zare mata ido sosai yace"wa kika harara? Ni
sa'anki ne?kin raina ni ko?,still tafin hannunta na dafe da bakinta ta girgiza kai tuni hawaye ya
balle mata,ya saka hannunsa ya kama gashinta da ta tufke cikin hijabin har sai da tace
"wayyo Allah na!......,hadi da wani dan guntun hawaye da ya silmiyo mata,ya saketa yana sake
matsota har tana jin hucin numfashinsa,ta runtse idonta gam tana jiran jin hukunci na gaba,ta
yarda aliyyun mugu ne,tasan yau Allah ne kawai zai qwaceta
Shirun da taji yayi yawa ya sata bude idonta,ba kowa a dakin hasalima an ja mata qofar dakin
sai ita kadai dake tsaye jikinya na kakkarwa,ta sake sakin kukan ta kifa kan gadonta
⚜⚜⚜⚜⚜
Cikin kwanakin gaba daya ya gama tsanar bangaren nasa,bedroom sin da suke cikin corridor
din wadanda bai amfani da su duk sai da ya budesu yayi amfani da su ,duk da alokacin su su
samira suna ganin suna qure adaka gun gyaran amma shi sam bai masa ba,don ba wani
qwarewa sukayi ba kamar na fadilan,yakan daure ne kawai ya nuna yabawarsa,ya tabbatar wa
ransa nata yafi wannan kimtsuwa
Kowanne dan adam wani lokacin kakan tsinci kanka cikin rashin jin dadin rai hakanan to haka
yau aliyu ya tashi,alhamis ce wadda aka wuni garin lullube da hadari da iska mai cike da
qamshin qasa,mutane da yawa yanayin yayi musu amma banda shi,biyar saura yama yi
dawowarsa gida,yayi cilli da jakar tasa a falo,gidan dai na nan a yanayinsa na kullum wato
shiru,toilet ya shiga ya watsa ruwa ya fitar jallabiya mai sulbi irin ta maza milk colour mai dogon
hannu ya saka,ya feshe jikinsa da shamsul imarat ya hada da turaren chastity ya dawo parlour
ya fitar da computer dinsa ta tafi da gidanka(laptop)ya jona mata chargy ya jawota har kan
kujerar da zai zauna ya dora ta a saman kujerar,ya daddanata ya bude bayan komai ya gama
daidaituwa ya soma aikin da ya dawo da shi
Munti biyar goma sha biyar sai aikinbya soma gagararshi saboda yunwa,ya dafe kansa da
hannu daya yasa dayan ya lallatsa comouter din ya kasheta,ya zubawa fridge dinsa ido yana
nazarin me zaici a ciki?komai dai na nau'in ciye ciye akwai
aciki Saidai gaba daya sun gundireshi babu abinda yagi buqata sai abinci mai nauyi da gishiri,gaba
daya taste din girkinsu salima bai gamsar da shi bare yasa su dafa masa wani abun,koda ranar
gikinsu ne yana yin kawaici ne kawai yaci don kada suga rashin kyautawarsa
A nutse ya isa gaban freezer din ya bude yana sake kallonta kamar baisan meye da meye a ciki
ba,hannunsa yakai kan madarar fresh yo da tayi sanyi sosai tanata fidda tsatstsafar sanyi yasa
daya hannun ya maida murfin freezer din ya rufe,ya maida kallonsa kan robà dake riqe a
hannunsa yana jujjuyata tamkar mai karanta rubutun dake jikinta
Ya saki tsaki hadi da cillar da robar kana yayi tattakì ya isa bakin window dinsa yajanye
labulayen jiki gefe daya ya dora idonsa a harabar gidan,idanunsa suka sake kaiwa kan
bangaren nata a karo na barkatai,tarwai yake da haske alamun tana nan,ji yayi yà gaji baAi iya
jutewa ba sole ne yazo tayi masa aikin da tasabar masa idan yaci gaba da jurewar yana jin qila
yunwa da tsantsami na iya illatashi,ya juya ya zira slipper dinsa ya fito....
Mrs muhammad ce
✍✍✍✍
[10/16, 1:41 PM] Salma: 
*wa yasan gobe?.....*

*written by safiyya Abdullahi musa huguma*

3⃣9⃣~4⃣0⃣
Ya juyabya zira slippers dinsa ya fito Gaba daya tana ma gida babu inda ta fita saboda ba ba
abinda zatayi a