Showing 90001 words to 93000 words out of 135036 words
Chapter 31 - Wa Yasan Gobe Compelet Book by Safiya Abdullahi Musa Huguma .pdf
hannu ya janyo
wayar da niyyar kasheta,number din uncle abba ya gani,bau damar kashewa kenan,luguden
bugu kawai zuciyarsa ke masa,ya danna ok,ya gama bada amannar cewa fadila taje musu
ne,ba qaramin rudewa yayi ba saboda sanin halin abban nasa sarai bashi da sauqi kan wasu
lamuranYa kara a kunne jiki a sanyaye,tambayar da abban nasa ya masa ta sake sashi cikin
wani halin ha'ula'in"me kake yi haka ne aliyyu?,lafiyarka kuwa qalau?" Cikin rawar murya yace
"abba...wallahikuskure ne....kuskure aka samu kuma....."ya dakatar da shi"ya isa bana son jin
komai maza ka tashi ka shirya,mr lin ne ya kirani ya gaya min komai har mutum ya aiko maka
ka koreshi,damar da ka ka jima kana jira yanzu don ka sameta shine kakeso kayi wasa da
ita?,maza ka ahirya kafin lokacin yayi kamar yadda aka tsara"wata boyayyar ajiyar zuciya ya
saki ya maida bayansa jikin kujera "to abba inshaAllahu" suka qare wayar yana masa addu'ar
samun nasara tare da sanya masa albarkaYa kashe wayar sannan ya zuba mata ido,yana ji a
jikinsa da zuciyarsa bai kyautawa abban nasa ba ma,bai san da qanne ido zai kalleshi ba,cikin
kasalartasa ya miqe ya shiga toilet ya hada ruqan wankanshi da kanshi don cika umarnin abban
nasa,awanni biyu ya dauka ya kammala shiryawa,komai da yakeyi babu walwala a
fuskarsa,dama yaya lafiyar kura bare tayi hauka? Hakanan babu kuzari ko qanqani tattare da
shi,shigarsa ta suit yayi saidia wannan ta musamman ce 'yar ubansu,wadda dama an tanadeta
ne domin wannan rana,maqudan kudade aka kashe gun siyan nata,kai da kanka idan ka kalleta
ba sai angaya maka ta lashi kudi ba zaka baiwa kanka amsa ash ce mai cakude da yarfin baqi
rigar ciki kuma da tie dinsa kuma light pink ne,agogo da ya daura da takalmi na qafarsa ma
kawai abun kallo ne,sumarsa tayi kyau sosai kamar yasa mata relaxer,sosai aliyyun yayi kyau
tamkar balarabe,yaya dama mai kyau yasa abu mai kya?,saidai cikin zuciyarsa sam babu
nutsuwa ko farinciki ko dayaSuna waje suna jiransa cikin dalleliyar sabuwar baqar
mota,sabuwar qira ce don a shekarar aka farahawanta,yana daya daga cikin kutane na farko da
suka mallaketa ko a qasar chinan,mutum uku ne suka miqe ya watsa musu harara don yana
ganin susuka takurashi zuwa gurin tamkar su suka yi laifin,dayan ya bude masa inda zai zauna
yayin da ragowar biyun suka bishi da gaisuwa,baiko kallesu ba sun san ba lafiya son haka basu
sake cewa komai ba suka shiga mai tuqi ya tafa motarTafkeken dakin taro ne dake cikin ginin
kamfanin*maitama factory*,hall ne da yaci sunan hajiya*maimunatu ibrahim muhammad*
mahaifiya gareshikenan,cike yake da al'umma mahalarta taron,sosai aka qawata
gun,decoration aka masa mai azabar kyau da tsari,kowanne table kujeru hudu ne suka
zagayeshi,kusandukka mahalarta taron sunyi shiga ne ta baqaqen coat kamar masu
ashobi,maza ne damata jinsin yarw da qabila daban daban,kowanne zaune gurinsa a nutse
cikin tsari suna sauraran bayanai daga bakin mai gabatarwa duk cikin dakon isowar aliyyu,babu
wata hayaniya kai sai ka rantse babu mai numfashi cikin hall dinShigowar tasa ya sanya duk
wani dake dakin taron miqewa tsaye cikin girmamawa,tafi ya cika hall din raf raf raf,tamkar ya
zura da gudu ya bar hall din haka yake ji don tafin nasu wani kuda yake masa akunne,sai da ya
hau step din da ka tanadar musu don zama gefan hannun hagunsa mr lin kusa da shi miss
sisineo ce hannun damansa kuma ramzan ne kusa da ramzan kuma mukhtar ne,sai da auka
kmmla zama sanna kowa ya koma.mazauninsaya zaunaDakin taron ya sake yin shiru,mai
gabatarwa ya yi wa aliyyi barka da isowa,sannu a hankali aka ci gaba da gabatar da taron
yadda aka tsara daki daki,duk anun nan da kae maganar minti biyu aka ritsa aliyyi da bindiga
aka ce ya maimaita saidai a harbeshin don baya gurin *gangar jikinsa* ce kawai
zaune,hankalinsa na kan fadila da agogo,duk bayanminti guda sai ya duba lokaci,jawabai masu
muhimmanci da ka tsara shi zai gabatar babu ko daya da ya iya yi,sai ya bada uzirin baijin dadi
sosai,drinks da kayan ciye ciye da ka cika gaban kowa da shi babu qanda ya iya kalla balle ya
tantance yana sha'awarsu ko baya yi bare akai ga batun zai ci ko zai shaAwanni biyu aka dauka
sannan aka zo gangara,su mukhtar suka tilastashi kan dole ya karba yayi jawabin godiya ga
dimbin al'ummar da suka.tako gari ya gari suka zo masa,yana ture lasifiqar yana komai haka
mukhtar ya manna masa ,idanu da sukamasa ca yasa ya sa hannu cikin kasala da rashin sanin
a halin da yake ciki ya amsa"Fadeelah!" Abinda ya soma mabata kenan cikin bututun
maganar,tsit suka yi fiye da wanda sukai dazun tamkar wanda yayi calling attention nasu,ido
kowa kr binsa da shi don dai sun san suna.ya ambata "fadeelah ta soni matuqa cikin
rayuwarta.....na zauna da ita cikin boyayyen nuni gairin tawa kalar soyayyar gareta",ya danyi jim
sannn ya shaqi numfashi ya dora "fadeelah ta barni a lokacin da ya bayyana gareni na dade
nima ina sonta ba tare da nawa sanin ba....ta barni a lokacin da nake da buqatar yi mata
mafificiyar soyayyar da ba'a taba gwadawa wata 'ya mace irinta ba......ta barni da wani nauyi
mai azabar nauyi cikim zuciyata ba tare da na samu na sauke mun raba tare ba......fadeelah ta
zama ruhina da gangar jikina"dora hannun sa yayi saman qirjinsa saitin zuciyarsa "fadeelah ta
mallaki nan ba tare da saninta ba,ya dade da zama mallakinta ba tare da sanin ku mu duka
biyun ba""Na tsinkayi fushi fusata da rashin fahimta masu tarin yawa qunahe cikin
kalamanta,qunshe cikin takardar da ta zamo baqa aguna,cikin saqon dake bayyana bankwana
da abinda zuciya ke so,cikin shafin takarda qwaya daya tal saidai sun yimin nauyi fiye da
littattafai dari masu shafuka dari dari"ya hade tafukan hannayensa guri guda yana yinsa ya
sauya soaai da alamun abinda yake fadi din na taba zciyarsa sosai,da alama zancan daga
ainihin zuciyarsa yake fita ba daga harshensaa yakeba "ku yimin alfarmar sani a
addu'o'inku....ku yimin alfarmar roqa min Allah ya huci zuciyarta,na gode muku baki daya...."ya
fadi yana qoqarin komawa ya zauna,gaba daya suka.miqe suna tafi,yanayin salin ne ya
burgesu,fuskarsu da zuciyarsu cike da tausayinsa,abunka da mai jajayen kunnuwa akwai
girmama soyayya komai tsufanta,miss sisineo ce tabude 'yar jakarta ta fiddo da bangles na
gwal guda biyu danqara danqara ta ajjiye gaban aliyyu tace ga kyautar ta a isar da ita ga
fadilaSosai abun burgeshi ta yima fadilansa kyauta duk da yana da arziqin da zai siya mata
ninkin wanann amma ayi kyauta wa masoyinka ma abun faranta ranka ne,yasa hannu ya dauke
yayi masu kyakkyawar ajiya..........*mrs muhammad ce*✍✍✍✍?
*PART 3*
3⃣&4⃣
Bayan ciye ciye da akayi a gun suka soka fita gun ainihin ginin kamfanin wanda aka zagaye shi
da wani yadi mai kyau aka daure bakin qofar shigar da shi,aliyyun ne a gaba a tsaye andi ya
miqo masa qaramin almakashi ya amsa ya dora saman yadin ya datse,tafi aka saki sannan
suka dunguma gaba daya sukayi ciki,guri guri suka dinga shiga daya bayan daya cikin
kamfanin,sosai ginin ya tsaru yayi kyau matuqa da gaske,komai cikin fasali gwanin sha'awa
Ba qaramin qaguwa yayi ba,duk bayan minti daya idanunsa na kan agogo,gani yake kamar
yanga lokacin yake masa,binsu kawai yake ba tare da fahimtar abinda suke yi ba,sam
hankalinsa bai tare da su,cikin dabara ya zame jikinsa ya koma office dinsa wanda aka tanadar
masa ko da zai zo wani lokacin,yasa key ya bude ya shiga sannan ya koma ya kulle ya koma
saman kujera ya zube,awoyi uku ya rage jirgin nasu ya tashi,baya tsammanin zai iya zaman
jira,ya zaro wayarsa cikin hanzari ya kira jumong da mukhtar
Tare sukayi knocking ya tashi ya bude musu,kan kujera mukhtar ya qarasa ya zauna yayin da
jumong ya rusuna yana jiran jin umarni,"ka shirya mota zan fito yanzu zaka kaini airport" "ok sir"
ya fadi hadi da juyawa cikin hanzari ya fice,yayin da mukhtar ke kallonsa yana son tambayarsa
me zaya yi a airport?,bai bashi wannan damar ba ya soma masa bayani da kansa ba tare da ya
tambayeshi ba "nijeria zan wuce mukhtar nan da awa uku,ina son na bar komai a hannunka
kayi handling dinsa,bazan yi sallama da kowa ba its urgent,ka wakilceni please"cikin rashin
fahimta yake dubansa "like how aliyyu baqin naka zaka bari ka wuce nijeria?" "Pls mukhtar if u
cannot help just tell me directly" yasan halin kayan sa sarai saboda haka ya gyada kai "is ok,is
ok I will" ya miqe tsaye ya sake duba passport nashi da ticket dake cikin jakan sa,yaga komai
na nan yadda zai buqace shi,ya dauka gami da zaro master card platinum ya ajjiyewa mukhtar
din sukayi hand shake "thanks" aliyyun ya fada a gaggauce sannan ya bude qofar ya
fice,mukhtar da mamaki ya cika shi yabi aliyyun da kallo galala,gaba daya aliyyun ya fita daga
hayyacinsa sam ya fice daga nutsuwarsa
Ta get din baya ya fice don baison kowa ya tsaidashi,don kuwa baiga abinda zai tsaida shi daga
tafiya nijeria ayau din nan ba saidai ikon Allah,ko cikin motar ma gani yake jumong baya sauri
laqaqai laqaqai kawai yake,gaza haquri yayi har sai da ya soma masa maaifa kan ya qara gudu
"sorry sir ida mukayi gudu ya wuce qa'ida camera na kallon mu za'a iya kama mu" sai a lokacin
ya tuna ba'a nijeria yake ba dole ya haqura a haka har suka isa airport din,ko jirgin ma gani
yake ba sauri yake ba shirme yake(hhhhhh),da suka sauka ko a ethopia aka basu dakunan
kwana kan sai gobe zasu qarasa nijeria jinsa yayi kamar a saka shi a kurkuku,masifa kawai
yake yana fadin dole ya sayi private jet nashi,dole yana ji yana gani ya haqura har sai
washegarin
Qarfe goma na safe a garin kano tayi masa,tuni nasiru yazo da mota don daukarshi,gidansu
yace ya wuce da shi kundila maiduguri road,yana shirin fitowadaga cikin motar saiga sumayya
ta fito cikin shirin tafiya school,da sauri ta sauya akalar tafiyar tata ta nufo gurin motar fuskarta
qunshe da fara'a"sannu da zuwa ya aliyyu" ta fadi tana leqa cikin motar cikin neman
fadila,"yauwa" yace yana sanyo qafarsa waje,ya dubeta cikin dakiyar nan tasa "ke,me kika bani
ajiya kikemin leqe leqe cikin mota" sai ta dawo ta tsaya dai dai cikin fara'a "anty fadila nake leqe
ko zan gani yaya,surprising din mu kuka so yi shi yasa ko a waya bata gaya mana ba,kwananta
biyu ma bata kira mu ba ashe kuna hanya"da sauri ta juya tana shirin komawa ciki tace "bari na
fara yi mawa momi albishir"sosai jikinsa ya mutu basu da labarin ma ta dawo to me yake faruwa
ne?"maida qafar tasa yayi cikin motar ya rufe ya bawa nasiru umarnin ya kunnata su wuce sani
mai nagge(unguwar su fadila)
Har cikin gidan malam ya bude musu suka shiga,ya fito ya ningina jikin motar bakinshi fal
addu'a,yana tunanin yadda zai shiga gidan ne,sai ga muhammad ya fito daga inda suke ajiyar
motocinsu hannunsa dauke da qaton almakashi irin na yankan shuka,nasiru ne ya qwala masa
kira,da sauri ya juya ganinsu yasa shi nufo gurin yana fara'ar ganin aliyyun,"sannu da zuwa
yaya"muhammad ya gaida shi ya amsa masa "kai da anty ne yaushe kuka dawo amma bata
gayama ummi zaku dawo ba"ya fadi yana washe baki da son jin amsar inda yayarsa
take,innalillahi wa inna ilaihi raji'un"aliyu ke fada cikin wani irin hali,muhammad ya juya yana
fadin "bari nakira abba bai fita ba"aliyu na shirin hana shi saiga abban ya fito ummi na riqe da
jakarsa
Sosai abban ya nuna jin dadin ganin aliyun,yasa muhammad ya bude sitting room suka
shiga,maganar da abban ya qara fadi ita ta sake tabbatarwa da aliyyu fadilan bata zo gidan
ba"ina mai kukan tafiya yanzu dai ai kuka ya qare ko tunda gashinan anje lafiya an dawo
lpy"aliyun ya sunkuyar da kai wata fargaba na shigarsa "tana lafiya abba" abinda ya iya fada
kenan,to shima abban bai takura masa da wata doguwar hira ba ya sallameshi shima ya fice
kasuwa
Gidansa kawai yasa nasirun ya kai shi don bai san kuma me ya rage masa ba,tunaninsa ya
tsaya cak,a harabar gidan ma'aikata ne kowa na masa barka da dawowa,baijin ma me suke
fada hannu kawai yake daga musu,ya sallami nasiru ya fito daga cikin motar yana shirin
shigewa ciki aka sake dage gate din gidan,tsayawa yayi hadi da juyowa don hajin wanda aka
bude mawar,motar samirah ce wadda ta sake cin ubanta,su hudu ne cikin motar,wata dabance
ke driving din samirah na gefanta sai wasu su biyun a baya,dariya suke ta sheqawa sam basu
ma kula da wani aliyyu ba har suka yo parking,har ta fito tana sheqa dariyarta kamar wadda aka
yiwa albishir din ba zata mutu ba,cak ta tsaya tana kallonsa kamar yadda shima ya zuba mata
ido,suma qawayen dariyarce ta tsaya cak,sun san halinsa sarai baya da kyau,sum sum daya
bayan daya suka fice daga gidan,kai kawai ya gayada ba tare da yace mata komai ko ya sake
kallonta ba ya shiga bangaransa
Yafi mintin talatin a zaune kafin ya miqe yaje yayi wanka,kafin ya kammala shiryawa anyi kiran
sallar azahar,duk wani motsi da zaiyi tana manne cikin ransa,duk wani tunaninsa na ina zai
sameta?ina zai ganta?ina kuma yanzu zaije nemanta?,cikin yadin tissue fari tas ya shirya,yayi
kyau sosai duk da kana kallonsa zaka karanci bai cikin walwala duk da kusan hakan yanayin
fuskarsa yake amma wannan karon ya ninka yadda yake da,ficewa yayi kansa tsaye ba tare da
ya nemi kowa ba da kansa ya ja motar ya bar gidan
Sai da ya fara tsayawa a masallacin bakin layinsu ya bada faralin sallar azahar dinsa sannan ya
wuce,kai tsaye yahaya gusau ya wuce gidan farida,ya dan jima a tsaye a qofar gidan baiga
gilmawar kowa ba har yana shirin komawa sai ga dahiru almajirin faridan,da sauri dahirun ya
qara so inda aliyyun ke tsaye don ya ganeshi,cikin girmamawa ya gaida aliyyun,ya amsa masa
yana tambayarsa matar gidan na ciki?,ya amsa masa da "eh alhaji ko a kira maka ita za'ayi?"
"A'ah tambayarka dai nake so nayi"aliyu ya fda yana gyara tsaiwarsa "to..Allah yasa na sani"
"tayi wata baquwa tsakanin jiya da shekaran jiya da yau?" "Kai gaskiya a'ah,don suma jiya suka
dawo daga lagos ita da mai gidan"ya fada masa cikin bashi tabbaci
Idanunsa ya rufe yana jin wani abu sannan ya bude,ya saki qaramar ajiyr zuciya sannan ya ciro
kudi ya bama dahirun ,cikin murna ya amshe yana zuba godiya,bai bi ta kan godiyarsa ba ya
shige motar ya tasheta ya bar layin
Har la'asar aliyyu salim na bulayi bisa titunan kano,shiga wancan fita wancan,ko manshi da
yake qonawa bai damu ba,ya rasa inda zai zauna bare yayi tunanin mafita,gaba daya feeling
kansa yake a matsayin guilty,cikin rudanin inda ta tafi yake,ina ta boye kanta haka?,duk da yana
ji daga can cikin wani sashe na zuciyarsa na gaya masa she is safe and she is in safety place
Sai da ya soma ganin gurare daban daban na ta alwalar sallar la'asar sannan ya samu ya
kashe motar a bakin wani masallaci ,ya daura alwalar ya bi jam'i,sai bayan da ua idar ne yaji
cikinsa na qugi sannan ya tuna rabonsa da abinci har ya mance,ya miqe ya koma cikin motar
tasa ba tare da yabi ta kan yunwar dake sakadarshi ba,sai da akayi sallar magariba yana bilayin
yawon titina sannan ya gano cewa wannan fa ba mafita bace,tunanin matsalar itace zata samar
masa mafita da gano masa inda fadilan ta boye,ya juya akalar motarsa ya nufi gidansu dake
kundila. .......
*mrs muhammad ce*
✍✍

[10/16, 2:09 PM] Salma: 
*WA YASAN GOBE?...*


*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

*PART 3*
5⃣&6⃣
Yana shiga ya tadda rabi'ah kan dining area ita da iftihal momy na kitchen,da alamu su din ma
zaman na cin abinci ne,da gudu iftihal ta gangaro tana ihu "yeyyyyyy daddyyyy"kamar yadda ta
saba ta duqa ta gaidashi,ya amsa mata maimakon ya dauketa ya shilla sama yadda suka saba
wannan karon sai taga kawai ya shafa saman kanta yayi hanyar kitchen din,ta tabe baki kamar
zata saki kuka
Tana kiciniyar rufe warmer taji an rufe freezer,ta dago kai da sauri aliyyun na tsaye yana
daddakar ruwan mai azabar sanyi,sai da ya shanye robar guda momin na kallonsa ta zuba mai
ido,ganinsa take a wani birkice duk da jikinsa fes yake kuma ya yi kyau da 'yar cika(sakamakon
kulawar da ya dinga samu a china)amma abunka da mahaifiya kallo daya tayi masa t gano
akwai damuwa a ransa
Yana qare shanyewar suka hada ido da momin,sai ya kautar da kai ya sanya robar cikin dust
bin yana cewa "momi barka da dare ina wuni"bata dai daina kallon nasa ba tace "lafiya lau Ali
kun dawo lafiya?" "Lafiya qalau ha fada yana jan kujerar plastic dake kitchen din zai zauna
"mun sameku lafiya?" Ya sake tambayar momin yana dauke kai don baya son irin kallon nan na
momi,nan da nan take naqaltar mutum,itama sai ta dauke kan tana ci gaba da rufe warmer din
tace"lafiya lau,tun safe sumayya tace min gaka,shiru shiru baka shigo ba ko da aka leqo kuma
ba kai a gun"ta qarashe maganar idanunta a kansa kamar tana son jin amsa kenan
Ya basar da zancan ta hanyar cewa"rabu da wannan shirmammiyar yarinyar momi,makaramta
fa zata tafi amma don gulma ta koma,gida muka qarasa kawai"ta dire warmer din tana cewa"ina
'yata fadila" gabansa sai da ya buga "lafiya"kawai ya iya furtawa tare da miqewa don kada ta
sunkuto masa wata tambayar da zai gagara kubutar da kansa,ta waiwayo tana cewa "a'ah ina
zuwa kuma?" "Zan wuce gida ne momi" "baku gaisa da abban naka ba,yana gida fa,kuma ma
na zaci tare zamuyi dinner ko?" Abinda momi bata sank ba bazai iya jiran abban nasa ba don
gani yake kallo daya zai masa ya karanto abinda ke faruwa,karo na farko da aliyyun yayi ma
momin qarya a rayuwarsa
"Zani gida ne momi za muyi magana da mukhtar,na baroshi ne da mutane a can wadanda ban
sallamesu ba na taho" to da yake ma