Showing 1 words to 3000 words out of 54507 words

Chapter 1 - ZARRAH BOOK COMPLETE BY OUM HAIRAN .pdf

[20/06 4:27 pm] Oum Hairan: *ZARRAH*


_Tare da Alƙalamin_

*_Oum Hairan_*



_Bismillahir Rahamanur Rahim_



_Page 3-4_





*_Wattpad-realfauzahtasiu_*


*_Telegram Link_*
            👇🏻
https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7






____________________________
____________________________



Wani matsiyacin kallo yayi Mata ya watsar da ita sosai kalamanta sun Sosa zuciyarsa tunda
yake baitaba katarin haduwa da tsageran daya taba duban tsabar idonsa ya fada Masa
kwatankwacin wadannan tasassun kalaman ba sai wannan kucaka Kuma qazamar yarinyar
almajira lallai ta daukowa kanta bala'in dazai addabi rayuwarta ko mutum me cikakken gata
yace zaija dashi wahala yakesha balle matsiyaciya almajira da ko arziqin yar aikin gdansa
batakai ba.
Juyawa yayi ya fice daidai lkcn da Inna ta bude idanunta ta saukesu akan Asma'u ta yafitota da

hannu ta matsa da sauri ta tsugunna tare da cewa “sannu Inna inane yanzu yakeyi Miki ciwo?"
Girgiza Mata Kai tayi cikin muryar ciwo tace “naji sauqi Asma'ul Husnah meye yasaki kuka"
sunkuyar da kanta tayi tare da saurin goge hawayenta tace “karki damu Inna zaki iya tafiya mu
fita mu samu dan sahu mu tafi wani asibitin?" Zuro qafarta tayi ta miqe tace “zan iya Mana
Asma'u dama sarqewar numfashin ne kawai Kuma yayi sauqi ince dai ba wanine ya sake
farautar mutuncinki ba?" Murmushi ta qaqaro cike da tausayin Innanta tace “aa Inna muje gda
zan baki labari yau na hadu da wani taqadirin dan iska da baisan darajar uwarsa ba bakiga cin
mutuncin da yayi min ba harda Marina kawai don na tareshi ya taimakemu ya kawomu asibiti
qememe dake dan dudun maguzawa ne yaqi harda tukuicin baqaqen maganganu yayi
tafiyarsa sai wanine ya tare Mana dan sahu mukazo nan asibitin ashe Wai na dan bamagujiyar
nanne infadamiki yazo ya duba kowa yana ganina ya juya zai tafi nikuwa na rama maganganun
daya fadamin nace indai bai dubaki ba kika mutu ya jira ZARRAH ta sai nayi shari'a dashi".....




Dariya Inna tayi ta lalubota ta rungumeta tace “ho ma'u na baki barin ta kwana do Allah ki rage
zafin zuciya Kinga ke macece gdan wani zaki ki rinqa hqr da lamarin rayuwa kinji" cuno baki tayi
gaba tace “waike waike Inna saikiyita cewa mutum yayi hqr Kuma mutanen duniya ba mutunci
da hqr suka sani ba Ni kawai in anyimin ramawa zanyi idan mutum ya cika zaqewa nace ya jira
lkcn da zan zama babbar likita wlh idan tsohuwarsa tazo hanuna allurar mutuwa zanyi Mata"
Dariya sosai Inna tayi tace “Ma'ulele ma'un Inna tashi mu tafi kinji kar yazo yaci Mana mutunci"
miqewa tayi ta Kama hannuta suka fito harabar asibitin cikin sa'a kuwa suka samu sahu suka
hau zuwa unguwarsu Asma'u tabashi kudinsa a gurin bada kudin ma saida akaso ayi fada da
dan sahu Saida Inna tasa baki sannan ta hqr suka tafi tanata mitar ita Inna komai akayi tace ayi
hqr kamar wacce akayiwa wankan farko da ruwan alwalar La'asar🤣
Suna shiga gdan taci karo da Dije yar kishiyar Inna ta debo ruwa a bohol tana ganin Inna ta
shige daki ta angije Dijangala ruwan ya tuntsire akan Lamunde dake tsugune gaban murhu tana
hura wuta da bakinta, kafin kace kwabo kokawa ta rincabe tsakanin ita da Dije kiciki kiciki
daqyar Malam Husaini dake shigowa ya raba fadan Dije ta tsaransa karya da gaskiya ya kuwa
hau ya zauna ya dauki sanda ya shiga bugun Ma'u aikuwa ta angajeshi saura kadan ya fadi tayi
waje ta zauna saman dakalin qofar gdan ta rinqa kuka.




Anan Saurayinta Sadiqu yazo ya sameta da qunshin kifinsa ya zauna yayita aikin rarrashinta
daqyar ya samu tayi shiru shima Saida yace idan batayi shiruba mutuwa zaiyi aikuwa dake
dama kukan na iskanci ne sai tayi shiru ta dago ta kalleshi tace “jiyafa a gabanka Dijangala ta
angizani kwata na fasa qwauri sannan ruwana ya zube Amma shi malam babannan saboda
suna bashi abinci baice Mata qalaba harma Kaine ka kaini chemist din Sallau shine yau danna
rama ya Kama dukana Allah duk ranar da nacimma ZARRAH ta duk sai narama cutar da
akayimin

Murmushi Saddiqu yayi yace “to Banda abinki Ma'una waye yake rama laifin mahaifa aisu sha
kundum ne komai sukayi saidai ayi hqr abarwa Allah" harara ta galla masa tace “chabdi lallai
ma Sadiqu Mai raken nan wato so kake kace na yafe makantar min da Innata da Lamunde tayi
da ruwan zafi ko Kuma so kake kace na yafe hanamu abincin da baba yakeyi yake basu a boye
duka Kai bari kaji harma satar kudi fah sukeyima Inna shiyasa na daina barin kudi a dakinmu
nake baka kake ajiye Mana yawwa barima kaji yau da mukaje bara gdan Alh Qasim Dubu goma
sha biyar yabamu kaga nasamu kudin makaranta na sauran musaiwa Inna magani musai kayan
abinci ko?"
Numfashi Sadiqu yaja yace “kayy alhmdllh dama yau da tunanin kudin makarantar nan taki na
yini Kinga yau har aikin gini nayi jiyama haka da ribar raken dana saro da kudin aikin ginin gaba
daya dubu hudu da naira tamanin ne da so nake sukai sha hudu sai a biya kudin makarantar"
Jinjina Kai tayi tace “Allah Sarki dan Sadiquna kaga kasai siminti da kudinka tunda ai kaima
naga gini kakeyi Mana wanda idan munyi aure zamu zauna yawwa nadai fada maka ka ginawa
Inna ta daki qur'anin Allah bazan tafi nabarta anan su kashemin itaba kaga saura wata biyar
yanzu muyi candy Kuma Mal yace da munyi Candy aure zaiyi mana dagani har Dijangala da
Zabba'u, Inna ce mataketa qoqarin ganin ya barni nayi ko Hygiene ce shikuma yace baza'ayi
yahudanci a gdansa ba"




Jinjina Kai Sadiqu yayi ya dauko Mata kifin daya siyo Mata ya miqa Mata tasa hannu biyu ta
karba harda tsugunawarta tace “angode Allah ya dada arziki da wadata yasa wataran kasiye
duk kifin garin nan" 🤔 zaro ido yayi sukayi dariya a tare yasa hannu ya dauki daya tace “ka
qara Mana" girgiza Mata Kai yayi yace “ki shiga gda ki gyarawa Innanmu bari naje gurin musa
na siyo Miki taliya ki dàfa Mana yau gwaggonmu taje qauye Kuma qila sai dare zata dawo"
miqewa tayi ta shiga gdan ta tarar da Inna ta idar da sallar La'asar ta zauna zata farayi Mata
surutu tace “Ma'u zanci qaniyarki akan sallah maza tashi kije kiyi alwala kizo kiyi sallah" dake
tasan batada gsky Bata jaba ta fita ta dauki buta tayi alwala har yanzu fadan be qareba yanzu
ma Saida ta harari Dijangala tace “zamu hadu a filin baja koli wallahi sai nayi qasa qasa nayi
sama sama na dumbuli miya a ludayin uwar yarinya naga ubanda zai tare Mata shegiya me kan
qotar gatari....."
Hadiye guntuwar maganar tayi lkcn da taji saukar ranqwashi a tsakiyar kanta tana dagowa taga
yayansu ne da take masifar jin tsoro don tasan yayi sukuwa a ruwan cikinta ba abune me wuya
a gurinsa ba aikuwa kamar yasa kwado ya datse bakinta haka tayi muqus ta tashi sumsum ta
shige daki ta fara jera sallolinta bayan ta idar yaro ya shigo ya kawo cefanen Inna tace a Ina
tasamo cefane nan tayi Mata bayani dake Sadiqu ba baqo bane a gurin Inna yasa batayi fadaba
tanajinta ta kunna rishow ta dora jallop din qamshi kuwa ya gauraye gidan Asma'u badai iya
girki ba Inna tayi fama Amma tayi saa an iya da taimakon aikatau din da sukayi a gdan masu

kudi ita da innan yaron gdanne ya fara kawowa Asma'u hari dole tasa suka hqr da aikin suka
fara wainar shinkafa da miya kafin iftila'in makanta ya fadawa Innah wadda tasa dole suka hqr
domin Asma ita kadai bazata iyaba.



Lkcn data gama girkin ta zubawa Sadiqu nasa ta zubawa Inna itama ta zuba domin taci harta
zauna zata faraci Inna tace “kin zubawa su Dijangala kuwa?" Turo baki tayi tace “ni gsky Inna
kinayimin katsalandan cikin rayuwata su din bamu sukeyi naga ko yunwa zata kashemu ba
sammana abincinsu sukeyi ba yanzu idan muka ajiye guntuwar da safe ai mayi dumame tunda
ni makaranta zan tafi" murmushi Inna tayi cikin tausayin quruciyar yar tata tason ita duk abinda
akayi Mata saita rama walau alkhairi ko sharri wanda rayuwa ba haka takeba tace,
Na haneki da barin yin ramuwa akan komai Ma'u rayuwa ta zahiri ba haka takeba kada ki zamo
cikin mutane masu son dole sai sunyi qeqe da qeqe tabbas wadannan nau'i na mutane basa
tsintar komai a rayuwarsu sai tarin nadama da danasani mara amfani to bandama quruciya irin
taki Ma'u ai abinda ka bayar shine rabonka do Allah dauki kwano ki zuba musu inada naira dari
biyu da safe sai baki dari kudin mota dari kisai abinda zaki karya kinji Ma'ulelena"
Janyo flat tayi ta zuba abincin kashi biyu ta dauka takai dakinsu Zabba'u ta tarar da Mama
Jummai tana sallah ta dangwarar Mata da kwanon ta fice ta nufi dakinsu Dijangala ko sallama
batayi ba ta dire kwanon tayo waje Lamunde da taya bera bari tace “kekam kin shiga uku da
baqar rowa da nufinki muji qamshi a banza ko ho Ma'u albasa dai batayi halin ruwa ba" har ta
bude baki zatayi raddi taga Yaya Mudan ya bude labule ya fito sumsumsum ta shige daki tana
qwafa ta zauna tanacin abincin tana qunquni takaicinta Yaya Mudan daya hanata rawar gaban
hantsi shigowa yayi dakin ya dokanta harara tayi qasa da kanta yace “Ya Inna Ina abincin nawa
ni?" Tasan halinsa sarai idan tayi wargi yanzu zata gwabzu hakanne yasata samawa kanta
salama tanaji Inna tace masa “duba tukunyar ko ta rage" da sauri Ma'u tace “bari na zuba maka
yaya" miqewa tayi ta dauki flat ta zubansa ta debe sauran a yar qaramar kula ta tura qarqashin
gado ta koma ta zauna.




Yanacin abincin suna taba Hira da mahaifiyar tasu Asma'u najin haushin rashin zuciyar yayan
nata duk matasan gdan sune suke ciyar da iyayensu Mata da qannensu Amma shi ko kudin
omon da zaiyi wanki saiya tambayi Inna gashi da ƙi faɗin masifa"




Shi gani yake dole shi wata tsiyane qwafa tayi yakai Mata naushi ta goce yace “wlh Inna badan
keba da tuni na dade da barar da yarinyar nan batada aiki sai jan maganar masifa shegiya
kullum baqi take qarawa Wai kwananki nawa ma bakiyi wanka ba ne?" Turo baki tayi tana
qunquni ya miqe yayi kanta Inna tayi saurin riqeshi tace “Kaga Mudansir ka kiyayi tabamin auta

qaniyarka zanci uwarme tayi maka da zaka wani zage kwanji kace zaka bugeta bakaganin ba
qwari gareta ba" qwafa yayi yace “yawwa Inna wlh na qara ganinta da Sadiqu sai na kakkaryata
nan Naziru abokina yazo yanasonta tayi masa rashin albarka har tana cewa nima din dana
turoshi menene bare shi. Murmushi tayi tace “to Banda abinka Mudan inakai ina shiga tsakanin Ma'u da Sadiqu Kuma ma
meye laifin Sadiqu yarannan sunason junansu tun suna qananu bakace su rabu ba sai yanzu
da aski yazo gaban goshi to ban yarda karna qaraji matuqar Ina raye saina dauki Ma'u nakaiwa
Sadiqu dakinsa matsayin Mata insha Allahu na lura dagakai har babanku ba son zaman lfy
kukeyi ba shikenan kowanne rashin albarkarku ya tashi akan Asma'u na zai qare yar tawa tilo
bata damu kowa ba Amma kowa ya dameta"




Jinjina Kai yayi ya fice yana cewa “ai dama Mal yace kece kike daure Mata gindi a gdannan to
Allah yasa na qara ganinta da Sadiqun a unguwarnan Kai nama daina zuwa ko Ina a qofar
gidannan zan rinqa zama naga qarshen rashin kunyarki shegiya me idon aljanu" matsawa tayi
ta kwanta jikin Inna tace “nifa Inna bansan me Sadiquna ya tarewa su Mal da Yaya ba dazuma
da Mal yaganmu inaji Sadiqu yana gaisheshi yaqi amsawa nikuwa nace da Sadiqu dama ya
daina wahalar da kansa aure ne dai dole a dauramin da wanda nakeso kamar yanda aka
daurawa kowacce ya a gidannan ehe...."
Buge Mata haba Inna tayi tace “kinci malafar ubanki don qaniyarki bakisan cewa Allah uba
yabawa damar zabawa yarsa budurwa miji ba to shine har kike wata taqama kul na kumaji yar
jaka da qusa kawai tashi ki debi kayan makarantarki ki goge jiya Jiddah ma tazo bakyanan kinje
debo ruwa tace ki taho muku ta tast book dinnan na biology zakuyi tast ranar laraba miqewa
tayi ta fita ta aro dutsen guga ta dawo tana gugar suna Hira da Innanta rabin hirar akan Aseem
Shaheed ne da irin alwashin da taci na yimasa rashin mutunci duk ranar da Allah ya sake
hadasu, Jinjina Kai Inna tayi tace “amma da kin hqr da yafi Miki kinga shi namiji ne ke kuwa
mace ce ko marinki ya sakeyi ya cuceki a sadakinki sai an rage wani abu balle ma ni banga
laifin da yayi miki ba badan dai sakarcinki ba mutum nawa kika nemi taimakonsu sukaqi
taimaka Miki baki qullacesu ba saishi wasu ma mutuncinki suka rinqa farauta Amma duk kin
manta saishi da yayi fada dake da fatar baki Kuma tabakin nasa ai ba kunyar gareki ba qila
abinda kikayi Masa ma yafi Wanda kika fadamin"




Shiru tayi don tasan idan ta cika magana yanzu Inna zata gindaya Mata sharadi ita Kuma tariga
ta qudurta a ranta saidai idan Allah bai sake hadasu da Dr Aseem Shaheed ba Amma saitayi
Masa abinda zai tsaya Masa arai kamar yanda yayi mata ita ba lusarar Æ´a bace dazai zageta
yaci mutuncin Innanta kuma ta ƙyaleshi dama iya ita kaɗai yayiwa da da sauƙi kamar yanda na
bayan sukayi amma shi Innanta fa yacewa tsumma tab ai wlh ya taro march kwararo kwararo
zatake bi don ta ganshi tashin farko rotse zatayiwa motarsa idan yayi yunƙurin yin wani abu ta

kwankwatse masa yatsan ƙafarsa da dutse.
Dariya takeyi ciki ciki Inna tace “dariyar me kikeyi?" Saurin saita kanta tayi tace “tunawa nayi da
wata tsokana da mukayi nida Jiddah a hanyar school ranar mun dawo dukkanmu bamuda kuÉ—in
mota mukaga Mata da miji suna tafiya a qafa matar da tsohon ciki shine Jiddah tacemin lahh
Asmah Kinga wata Mata ta haÉ—iyi wake ya kumbura Mata ciki nikuwa na matsa kusa dasu nace
sannu Mata buhun garin kwaki kikaci ne yayi miki saqeqe a ciki shine mijin ya Kama zaginmu
muka mayar dashi mahaukaci mukayita dariya kawai saiya biyomu da gudu na turansa dutse ya
tungule ya faÉ—i....."




Vote
Comments
Share




*_Oum Hairan_*
[20/06 4:27 pm] Oum Hairan: *ZARRAH*


_Tare da Alƙalamin_

*_Oum Hairan_*



_Bismillahir Rahamanur Rahim_



_Page 5-6_





*_Wattpad-realfauzahtasiu_*


*_Telegram Link_*

            👇🏻
https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7






____________________________
____________________________



Daquwa Inna ta watsa Mata tace “wato dana hanaki tsokanar bakiji ba kenan aikuwa tabbas
zan hadaki da yayanki yacimin qaniyarki ni banason sakarcin banza Shiru tayi saboda tsoran
kada Inna ta fusata ta hadata da Mudan tasan kashinta tsaf zai bushe ta miqe sumsum ta nade
kayan gugarta ta sanya a jakar kayanta ta fice ta dauki bokati ta tafi debo ruwa sawu uku tayi ta
qyale kasancewar dare ya riga ya fara tana shigowa sallar Isha kawai tayi ta shimfida
taburmarta ta kwanta tana addu'a bacci ya dauketa.
Da safe ta riga Inna tashi saboda zumudin kudin makarantar da zaa biya Mata tayi wanka aka
dauki kwalliya aka dau jaka ta fito cikin shirinta tsaf Ma'un Inna idan taga dama yar gayuce ta
gaske komanta qwas-qwas Amma idan taso iskanci tafi kowa iyashi dumamen taliyar data boye
jiya ta dauka taci ta kora da ruwan koko ta miqe tace “inna zan tafi" Fito da kudin Inna tayi ta miqa Mata ta qirga zari sha hudu ta miqawa Inna uku da biyar tace
"saura uku da biyar idan na dawo saimu siyo abinda zamuke ci kafin Allah ya kawo wata
hanyar" Jinjina Kai Inna tayi tayi Mata fatan alkhairi ta fice ta nufi gdansu Jidda dake yafi nasu
kan hanya nan suka dunguma suka tafi sunata hirarsu Asma'u na bata labarin irin wulaqancin
da akeyi musu idan sukaje neman taimako sosai jiddah ke tausayawa qawar tata.




Da wannan hirar suka qarasa suka shiga aji suka fara daukar darasi Saida aka fito break
sannan Asma'u ta nufi Office din Principal tayi sallama ta shiga principal din tanason Asma
sosai saboda yanda malaman bangaren kimiyyar suke yabawa da qwazonta da ace makarantar
tatace ma da tuni ta yafewa Asma kudin makaranta saidai kash batada iko. Rusunawa tayi ta gaisheta ta amsa sannan ta fito da kudin makarantar ta miqa Mata tayi rubuce
rubucenta ta miqanta receipt ta miqe har takai bakin qofa taji a bayanta ance “Asma'u Hussain"
tsayawa tayi adan tsorace tace “yes mAh" murmushi tayi tace “meye yasa duk biyan kudin
makaranta kece qarshe ne meyesa iyayenki sukewa karatunki ruqon sakainar Kashi bayan
Kuma Ubangiji ya Basu dama domin yabasu ke me qwazo da son karatu?" Idanunta ne ya
kawo ruwa tayi saurin daukewa tace “na gode mAh kawai ta juya ta fice daga office din principal
din ta nufi inda sukecin abinci yau batada ko sisi sai kudin motarta don haka ta nemi guri nesa

ta zauna tana kallon daluban wani na siyan wainar fulawa wani na siyan cake kowa dai da
abinda yakeso. Jiddah ta hango ta nufota ta zauna kusa da ita tace “yadai naganki anan"
dubanta tayi tace “to da Ina kikeson ganina?" Share zancen jiddah tayi da cewa akwai wani guy
dana tama a bayan makarantar nan yau indai mun ganshi saina goge Masa hadda"



Zaro idanu Asma tayi tace “kayy Kinga ki rufa Mana asiri Principal tace mu daina kula mazan
bayan makarantar nan yawancinsu duk yan shaye² ne" harararta Jiddah tayi tace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login