Showing 15001 words to 18000 words out of 54507 words

Chapter 6 - ZARRAH BOOK COMPLETE BY OUM HAIRAN .pdf

da dumama yanayi.



Cikin dabara ta rinqa qoqarin zame jikinta yaqi bata dama har saida yaji ta soma shassheqar
kuka sannan ya fahimci abinda yake shirin aikatawa ya sake ta ta zame a hankali ya kwanta
saman kujerar three sitter din da yake kai tare da harde qafafunsa yana qoqarin aro kwarjini
yasawa Kansa yace “meye ya hanaki zuwa gdan kwalliyar dana kaiki jiya?" Sunkuyar da kanta
tayi har yanzu qirjinta lugude yakeyi itakam ta hadu da masifa wannan mutumin wanne irine me
yake nufi da ita wanne salone wannan yake son zuwar mata dashi da yake Neman zarta
girman kwanyarta a mizanin hankali.......
Ji tayi hannunsa na yawo a fuskarta ta dago da Sauri sukayi ido hudu yasa yatsansa



wasa da ruwan hawayenta yayi murmushin da yasa kuncinsa lomawa sajensa ya hadu da gumi
ya kwanta luf a fuskarsa yace “Asma'uh Ma'un Innah Mara kunya fitsararriya wacce bata barin
kowa idan tsautsayi yasa ya shiga gonarta am don Allah ki daina kuka kuka bai kamaci fuskar
jaruma kamarki wacce ta shiryawa fito na fito da mutum kamata ba ki jira lkcn kuka na gaba lkcn
da zaki gane shayi baikai matsayin ruwa ba domin shi ruwa haka ake buqatarsa shayi ko sai
ansa masa Lipton da suger yake shawuwa, Kalmomin qarshe da nakeson sanar dake banson
jayayya akan abinda yake hurumi na dole ne idan nasaki Abu kiyishi ko bakyaso kina nunamin
jin dadinki kuma komai wahalarsa idan kin gama kiyimin godiya sannan koda wasa kada ki
qara kashemin waya na kira ban sameki ba saboda banson shigowa wannan lungun talakawan
dole ce take biyo dani am akwai sauran dokoki da sharruda na zama dani a matsayinki na
baiwa don baki isa nayi miki kallon mata ba ke kanki kin sani zan baki jadawalin ayyukanki
ranar da kika tare a gdana"
Shiru ce ta ratsa ta tsayin lkc har yanzu hawayen bai daina zuba a idonta ba yayi ajiyar zuciya
ganin yanda ta lumshe manyan idanunta gashin idonta ya sauka saman kuncinta abin ya bashi
nishadi bude bakinsa a saitin kunnenta yace “wannan dogon surutun ma da kika sani kiyimin
gdy"

*_Oum Hairan_*
[20/06 4:32 pm] Oum Hairan: _*Zarrah*_



_*Oum Hairan*_



_*21-22*_



Sake qoqarin shigar  da ita yakeyi jikinsa ta sunkuya  a hankali tanajin quncin abinda yakeyi
mata A ranta tace “don Allah ka kyaleni na tafi jirana akayi...." Sunkuyawa yayi ya dora 
hannunsa a bakinta yace “da hakan ma ni  meye yasa da nabaki umarnin kije kikaqi zuwa?"
Yana mgnr yana dagota ta sake lumshe idonta yayi murmushi yace “ke jaruma ce  kuma mara 
kunya tabbas saurin kuka bai kamaceki ba" Yana fadin haka ya juya ya fice yana cewa dole kibi
abinda na gindaya miki  idan kinqi kuma ki sake shigar da kanki  sawarwarin wahala sakarya
kawai"
Bayan tafiyarsa ta jima tsugune a gurin kafin ta tashi ta fice daga gdan ta nufi gdan hajar tana
zuwa ta kwanta kanta yana juya mata abubuwan da suka faru suna dawo mata nan Hajar tazo
ta sameta tana tambayarta meye yake faruwa ta miqe zaune tare da jan fasali tace “wai zai
aureni ne matsayin baiwa Aunty Hajar wacce irin bauta ke a cikin aure bayan wacce duk wata
mace takeyi a gdanta?" Shiru hajar tayi tana nazarin kalamin kafin tace “to Allah shi dai yasan
karatun Kurma kedai kamar yanda Innah taketa fada miki kiyi hqr kuma kiyi biyayya Allah bazai
barki banza ba zai kawo miki dauki a dukkannin lamuranki yanzun meye ya kawoshi?"


Goge hawayenta tayi tace “akan banje gyaran jiki bane" harararta hajar tayi tace “ai dama saida
aka fada miki baki gaji da zubar da hawaye bane shiyasa kikeqin daukar shawara kije kiyi
abinda kikaga ya dace dake namiji ya aureka ma don qauna yaka qare bare wannan da ya
aureki don gayya kada ki saita zamanki kije kina raba hali kishiyarki ta fahimci baraka tsakaninki
da mijinki kigani in zakikai labari"
Sosai kalaman hajar ya kashe mata jiki tabbas wannan way din data dauka ba mafita bace
gareta miqewa tayi ta zari hijjab dinta ta fice ta hau napep ta nufi gurin kwalliyar cikin saa taje
angamawa kowa kawai aka hau yimata abinka da fata me kyau itan tafi kowa daukan kyau, 
hakanan bayan an gama suka tafi sai zuba qamshi sukeyi suna zuwa suka tarar ankawo kayan
Dijangala da Rabi kayan sun gaji da haduwa kowa sai kodawa yakeyi.

Ko kallo basu isheta ba tayi shigewarta ta kwanta washegari aka shiga hidimar biki gadan²
kowa yanata warkajami banda ita domin kuwa kowa daina kulawa tayi batada abokin hira sai
wayarta itanma da taga zaa dameta take watsarwa tayi kwanciyarta a ranar ma saida sukakai
ruwa rana kana ta yarda sukaje lalle da gyaran gashi yamma liss suka dawo juma'ah da safe
aka kawo mata kayan dinner a wata qaramar akwati kayan sunyi kyau matuqa da yamma Aunty
Aseemah ta turo aka dauketa bayan kwalliyar da sukaje akayi musu ta kuma gyarata tasa akayi
mata shiri na musamman domin ita a ranta yanzun takejin qaninta yana aure domin wancan
auren zabin mahaifiyarsu ne wannan kam duk da yana iqirarin bayaso tasan zabinsa ne.
Daganan aka daukesu qarfe Shidda sai gurin dinner din ashe shima gurin dinner din uku ya
kama nasu shine na musamman tare kuma a lkc daya motansu ya tsaya aka bude masa ya fito
itanma aka bude mata ta fito suka hade a tsakiya sauti me dadi yana tashi itadai banda hawaye
babu abinda takeyi tasan daga gobe shikenan kashinta ya bushe a hannunsa,  tana tafe tana
layi har suka isa mazauni anan akayi kamu da duk wata bidi'a sannan aka fara gabatar da
dinner din suna zaune zaman kurame babu me cewa wani qala tsakaninsu wayarsa tayi ring ya
zaro a aljihunsa ya kara a kunnensa bataji abinda akace ba tadaiji yace “ok ganinan"




Miqewa yayi ya dubeta kamar zaiyi mgn kamar wanda ya tuna wani abu yayi gaba abinsa tabi
bayansa da kallo take MC din ya fara babatun “toh amarya ya haka kika bari ango ya fice wasa
bai qare ba?" Wasu hawayen baqin ciki suka zubo mata ta miqe itama da sauri ta nufi hanyar
fita da sauri Jabir ya riqota yana girgiza mata kai ta watsa masa wani kallo da yasashi sakinta
yace.
“Kiyi hqr kiran gaggawa ya samu a asibiti shiyasa" bata saurareshi ba ta hankadeshi ta fice
wannan abu yabawa kowa haushi a gurin da mamaki kowa nata fadin albarkacin bakinsa
itakam tana fita ta tsari napep ta fada masa inda zai kaita tana zuwa gda ta fada dakin Inna ta
zube a jikinta ta rushe da kuka sosai hankalin Innah ya tashi daqyar ta samu tayi shiru ta
lallabata ta fada mata meye ya faru, murmushi Inna tayi tace “banda abinki Ma'uh lfy ai tafi
komai kada kisa wannan a ranki komai zakiyi kiduba girman Allah ki zauna da mijinki lfy ki
fahimceshi kinji" sake kwanciya tayi jikin Inna tana sauke ajiyar zuciya tace “Innah wlh inajin
tsoron mutumin nan bashida tausayi kuma ni nasan ba domin allah ya nacewa aurena ba"




Ajiyar zuciya Innah tayi taja bakinta ta tsuke tanaci gaba da shafa bayan Asmah, a haka bacci
ya dauketa lkcn goma ta wucce daqyar Innah ta gyaranta kwanciya da taimakon Innah Azeezah
a daren Jabir yake fada masa abinda ya faru baiji haushin kansa ba sai ita yayita kiran wayarta
tasata a silent ya kira yakai sau uku bata dagaba dole ya hqr amma rainin yarinyar yanacin
zuciyarsa ranar kwana yayi yana huci Mimee na kallonsa bata kulashi ba don ta fahimci a yan
kwanakin bashi da fushin daya wucce Asmah sai wajen biyun dare sannan ya kwanta shima

kiran wayar bai daina ba cikin saa kuwa ta daga cikin mayen bacci bai bari tayi mgn ba yace.
“Ke wacce irin mara tarbiyya ce da zaki jizgani a cikin abokaina kinsan su waye a gurin kuma
kinsan dalilin da yasa na tashi nabar gurin ne shashasha sakarya mara tarbiyya....." Qit yaji ta
kashe wayar ya miqe zaune da sauri yana kiran wayar yajita a kashe gabadaya yaja wani huci
tare da cilli da wayar ya miqe kamar wanda aka tsikara ya zari mukulli sai kuma ya kalli agogo
yaga uku saura wata ajiyar zuciya ya sauke ya koma ya zauna yana dafe kai yana mayar da
numfashi a fili yace “saura 7 hours zakiyi bayani duk wani iskanci da kike ji dashi zaki saukeshi
a gidan matsiyatan iyayenki" Komawa yayi ya kwanta




Tunda ta farka taga kiransa ta kasa sake rintsawa wai yar marasa tarbiyya ta jinjina kalmar nan
tafi sau hamsin kafin ta sake kwanciya wannan wanne irin miji Allah ya zaba mata da wannan
tunanin ta tashi kawai tayo alwala ta tayar da sallah ta jima tana roqon Allah ya cire mata jin
ciwon kalaman Aseem a ranta ya sassauta mata zuciyarta ya bata ikon yi masa biyayya koda
zata cutu matuqar bata sabawa shari'ah ba
Da safe kuwa kamar yanda suka tsara hakance ta faru qarfe goma masallacin dake kusa da
gdan Mal Hussaini ya dinke maqil da dandazon al'ummah saida aka fara daura auren Rabi'ah
da angonta Mansur sannan na Dijah da Khamal sai na Asma'uh da Dr Aseem Shaheed nan
gurin ya dauki kabbara maroqa suka rinqa zubawa angwaye kirari a cikin gdan kowacce amarya
murna takeyi amma banda Asmah da tayi laqwas ta lafe jikin gado idanunta na saman silling
hawayenta tun daren jiya yaqi tsayawa dukkan wata kalmarsa babu me dadin da zata tuna
tasata farin ciki a daidai wannan lkcn a ranta tanajin yanzu da bai rabata da Sadiq dinta ba da
yanzu itama tanajin irin Happy din da yan'uwanta sukeji, itadai haka ta yini bata iya tsinanawa
kanta komai ba sai kuka ko kwalliya taqiyi qarfe Hudu kuwa motocin daukanta sukazo lkcn
daqyar Mal Hussaini yasata tayi wanka aikuwa tanajin ance ita akazo tafiya da ita ta rushe da
kuka me dukan zuciya ta qanqame innarta tana mata magiyar kada ta bari a tafi da ita idan aka
tafi da ita waye zaike yiwa Innah aikin gda,




Duk rashin tausayin Mudan ranar saida qanwar tasa tasashi kuka daqyar ya bambareta jikin
Innah yasata a mota ya rufe tana kuka tana kiran sunansa shima hawaye yake sharewa hakan
motocin suka daga suka dauki hanyar Shagari quarters horn sukayi aka bude musu get Aunty
Aseemah ta bude musu bangaren amarya Asmah har zuwa lkcn shassheqar kuka takeyi
sukuwa yan kawo amarya lalacewa sukayi a kallon wannan katafaren falo basu qarewa duniya
kallo ba saida suka haura saman me dauke da madaidaicin falo da dakuna biyu sun bawa ido
abinci sosai.
Dake ba yawane dasu ba kasancewar yace kada a wucce mutum biyar haka suka zaunarta a
saman carpet din dake tsakiyar dakin jikin gadonta suka farayi mata sallama suka fice hatta
Jiddarh ficewa tayi tabisu aka barta ita daya tanata aikin kukanta me ban tausayi, kusan awa

uku tana zaune ita kadai tun biyar har tara sannan taji tsaiwar mota a harabar gidan qirjinta ya
buga da qarfi ta koma ta sake lafewa dukan qirjinta na qaruwa daidai lkcn da taji an bude qofar
an shigo an sake murda ta dakin an shigo qamshin turarensa ya daki hancinta ta sake narkewa
inda shikuma ya tsaya akanta yana qare mata kallo, yafi 5 minutes yana kallonta kafin yayi
wani murmushi yace “waike nan kin yarda amarya ce ke ko? Hmmm yarinya kinyi kuskure
babba da kika yarda kika fado komata tabbas zaki fahimci bambamcin da kika kasa ganewa,
am ba bata lkc nazo ba ga wannan ki taba nasan qila rabonki da nama tun sallah sorry karki
damu da sai kin biya bana buqata kasancewar qyanqyaminki nakeji, abu daya da zan fadanki
shine idan kin tashi kullum da safe kinada aiki a gdannan, ki shiga wancan part din ki gyarashi
sosai sannan ki samawa matata abinda zataci am tanada qaramin ciki ne bata aikin komai
saboda tanada matsalar mahaifa tana buqatar tausa kuma batason ta inji so duk sanda ta
buqaci tausa kiyi mata har sai tace ya isa haka ina fatan kin gane?".................





_*Oum Hairan*_
[20/06 4:32 pm] Oum Hairan: _*Zarrah*_




_*Fauziyyah Tasiu Umar*_





_*23-24*_



Juyawa yayi ya fice daga dakin yaja qofar ya rufe ta miqe ta bude labule tana kallonsa ya bude
dayan bangaren ya shiga ya mayar ya rufe taja fasali tare da ajiyar zuciya ta koma ta bude
ledar gasasshiyar hanta ce da taji kayan lambu sai qamshin takeyi dayar ledar kuma kaza ce
itama ta hadu taja fasali ta zauna da farko kamar kartaci zuciyarta ta raya mata garama taci
rabonta ne idan bataci bama ba gwaninta zatayi ba.
Sake budewa tayi ta dauki hantar takai bakinta saida taci iyakar cinta ta kora da lemon ta miqe
ta cire mayafinta ta shiga bathroom ta bata lkc tana kallon bayin tana mamakin irin tsaruwarsa
kafin ta dauki sabon brush ta bude ta matsi man goge haqori ta wanke ta cire kayanta ta fara
kokawa da shower ta hada ruwa tayi wanka ta fito ta shafa mai ta bude wadroop din ta dauko
doguwar rigar bacci tasa ta karkade gadon ta haye taja bargo tayi kwanciyarta.

Baccinta tayi cikin kwanciyar hankali saboda gajiyar biki bata farka ba sai safiya ta tashi tayi
wanka tayi sallah tana saman sallaya taji an taba qofar ta juya ta kalli qofar jin shiru baa qara
tabawa ba yasata tunanin babu kowa taxi gaba da lazuminta sake taba qofar ne yasata miqewa
tana tambayar “waye" ba ayi mgn ba ta bude qofar taja da baya da sauri Aseem ne tsaye cikin
shirinsa na tafiya aiki da tarkacen laptop da takardu a hannunsa.
Qasa tayi cikin ladabi tace “ina kwana" Idanunsa ya dauke daga kanta ya juya ya fara tafiya
saida ya kusa step din benen sannan yace “Mimee tana jiranki kije ki hada mata break" wani
abune ya caki zuciyarta tana kallonsa ya fice hawaye suka sulalo mata na baqin ciki wannan
baqin qasqanci da mahaifinta ya siya mata Allah wadarai dashi, komawa tayi ciki ta dauki
wayarta da keta ring ganin number ya mudam tasan Innah keson mgn da ita ta kara a kunnenta
a sanyaye, yanayin yanda tayi sallama ya tabbatarwa Innah ba qalau ba taja ajiyar zuciya tace
“ya akayine ma'uh na?" Cikin kuka ta durqushe a qasa ta kwashe duk abinda Aseem din ya
fada mata ta sanar da Innah Sosai Innah ta girgiza dajin wannan qasqanci da rayuwar Asma'uh
ta tsinci kai a ciki amma a fili sai tace “duk a cikin ibada ne kiyi hqr zakiga ribarsa a gaba don
Allah badon niba ki mayar da komi ya zama ba komi ba koda anyi abinda ya kamata ki kalla ki
kawar dakai wataran sai labari"




Cikin mutuwar jiki tace “yanzu Innah yimata zanyi?" Murmushi Innah tayi tace “qwarai kuwa yi
zakiyi domin Allah ai lalura ta kori komai kema wataran zata taimakeki" haka inna ta rinqa
tausar Asmah hardai ta hqr ta saki ranta ta miqe ta dauki hijjab dinta ta nufi part din Mimee ta
qwanqwasa aka bata izinin shiga ta bude ta shiga cikin nutsuwarta me tsayawa a rai tayi
sallama, a qasan maqoshi mimee ta amsa tanajin wani kishi na taso mata duk yanda su
Saimah sukazo suke koda kyawun matar yayan nasu ganin idonta sai taga tafi haka duk da
kasancewar ba fara bace amma a sahun kyawu dole ta karbi lambar yabo.
Rusunawa tayi tace “Ina kwana Aunty...." Numfashi Mimee ta sauke tace “normal ina fatan
Honey ya zayyana miki aikinki a gdannan ko?" Jinjina kai tayi Mimee tayi murmushi tace “ok sai
a tashi a fara ina buqatar kunun tsamiya ne da qosan bread" miqewa tayi ta fara neman kitchen
din ta nuna mata tace “ai basai kin wahala ba da part dinki da wannan duk iri daya ne
bambamcin kawai a matsayi yake " duk da Asmah tasan mgn Mimee ta fada mata bata kula ba
ta nufi kitchen din a hargitse yake gabadaya kayan sunyi qura ta jinjina kai ta lalubi tukunya ta
dora ruwa ta rinqa bude kitchen cabinet din har allah yasa ta samu duk abinda take buqata ta
hada ruwan kununta sannan ta debi surfaffen wake tasa masa ruwan zafi ya tashi ta hada
tattasai da albasa da attaruhu da duk abinda tasan zata buqata ta wanke ta zuba a blander, a
wannan lkcn ilimi ne kawai yake aiki bawai sani ba duk kayan aikin baqine a gurinta hakanan
dai ta ganganda ta gama hada komai ta Jere a dinning din ta koma kitchen din ta fara gyaransa
saida ta gyareshi tsaf ta wanke kayan da sukayi qura ta mayar dasu muhallinsu sannan ta fita
parlor shima ta gyara tayi duk abinda ya dace sannan ta juya zata tafi taji Mimee dake zaune

tana kallo tace “ki hau sama ki gyara masa dakinsa"




Tuni wani riqaqqen baqin ciki ya cika zuciyarta taji kamar tayi tafiyarta kalaman Innah ne kawai
suka sata juyawa ta nufi saman ta bude dakin farko Allah kuwa ya taimaketa shi dinne ta shiga
ta fara gyarawa saida ta gyareshi tsaf kayan da ya cire duk ta ninke tasa a kwandon zuba kayan
wanki ta wanke bathroom ta fesa turare ta janyo ta fito ta rusuna gaban mimee tace “na gama"
daganta kai kawai tayi ta juya tayi tafiyarta ta koma nata part din ta gyara ta nemawa kanta
abinda zataci ta dawo ta zauna a parlor ta kunna kallo tana kallo tana karyawa bayan ta gama
ta haura saman tayi wanka tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login