Showing 51001 words to 54000 words out of 54507 words
Chapter 18 - ZARRAH BOOK COMPLETE BY OUM HAIRAN .pdf
sabon sauyi ne kuma ya tunkarota mijin da yake
lallabata da abinda ke jikinta yafi kowa sanin cewa ba koyaushe take iya girki ba idan tayi
wahala takesha shine da kansa ya dauke mata girkin idan ba ganin dama tayi tayi batare daya
sani ba amma yau shine yake bata umarnin dole akan ta sama musu abinda zasuci da matarsa.
Tana cikin wannan tunanin ya shigo kitchen din yaganta tsaye yace “Mimee tace Fatan
cous-cous takeso kiyi mata nikuma ki dafamin coffee kawai ya isheni.........
_*Oum Hairan*_
[07/07 12:24 pm] Oum Hairan: _*Zarrah*_
_*Fauziyya Tasiu Umar*_
_*Elegant Online Writers*_
_*Wattpad-Realfauzahtasiu*_
_*63-64*_
Jinjina kai tayi zuciyarta a karye ta fara duba abinda zata buqata ta hadansu duk abinda suka
buqata ta jeransu a dinning din falon ta shige dakinta ta kwanta zuciyarta na hautsinawa ba
kowanne qamshi take iya dauka ba bata tashi ba sai wajen goma na dare shima amai ne taji
yana taso mata ta nufi bathroom da sauri ta fara sheqashi a wahalce saboda bataci wani
abincin kirki ba, tana tsaka da aman ya shigo ya qarasa bathroom din da sauri yana zuba mata
sannu ta dago ta dubeshi ta kawar dakai ta miqe ta share gurin ta zagayeshi ta fice tanajin
yanayin yana mata babu dadi,
Matsowa yayi gareta ya zauna gefen gadon ya kamo hannunta yace “kin kuwa ci abinci?"
Numfashi ta sauke ta kada masa kai alamun eh yaja fasali yace “amma meye yasaki amai?"
Qasa tayi da kanta ya dagota cikin yanayi na tausayi yace “kiyi hqr bansan meye yasa na
takura miki kiyi girkin ba amma bazan qara ba tashi ki samu wani abun kisa a cikinki taso
yimasa gardama ya narke mata dole ta karbi cake da yourghut din da yazo dasu ta faraci tana
yatsina fuska a haka taci da dama ya taimaka mata tayi brush sannan ya miqe yace “mu kwana
lfy ki kulamin da babyna"
Yana fita ta fada gado taja ajiyar zuciya to ko menene yasashi canza mata dazu? Girgiza kai
tayi tare da cewa “Allah shine mafi sani" da wannan tunanin bacci ya qara dauketa bata farka
ba sai gaf da asuba tayi raka'atainil fajri ta zauna tana lazumi lkcn asubs na qarasawa tayi ta
dauki qur'ani ta fara karatunta ta jima tana karatun kafin ta ida tayi addu'o'inta ta miqe ta gyara
dakinta ta bude dakin ta fito ta tarar da falon kaca² bata jurewa ganin guri da qazanta hakanan
ta zage ta gyara ta nufi kitchen ta dafa Indomie ta fito.
Clear sukayi da Mimee ta fahimci hankalin mimee akan cikinta yake kuma batada niyyar kauce
mata hakan yasa ita ta kauce tare da cemata “barka da safiya" bata amsa ba saima tsaki datayi
murmushi Asmee tayi tace “dadina dake baki gajiya da tsaki kamar tsaka" mgnr ta daki Mimee
ta juyo zatayi bala'i kafin ma ta iso ita ta shige dakinta ta kullo ta zauna tanacin Indomien ta da
qwai tanajin dadinta sosai, koda ta gama bata fito ba ci gaba tayi da chat dinta har azahar ta
miqe zatayi sallah wayarta ta fara ruri takai hannu ta dauka sunan Aseem tagani akai ta daga ta
gaisheshi cikin ladabi yaja numfashi yace “shine kinga na fice da wuri amma ko ki tambayeni ya
na tashi ko Soul?" Murmushi tayi tace “Allah bansan da wuri ka fita ba da nayi sallah bacci na
koma ban tashi ba saida babynka ya tasheni"
Langwabar dakai yayi kamar yana gabanta ya karyar da murya yace “me kike shirya min yau?"
Tace “name ba?" Murmushi yayi yace na tarbar mijinki 2 days baya tare dake yayi kewarki
sosai" ajiyar zuciya tayi cikin salonta me narkar dashi tace “au dan wannan ma me kakeso na
shirya maka?" Cikin jin dadi yace “komai indai daga gareki ne" dariya tayi tace “har dani?"
Shima dariyar yayi yace “kedin nafi buqata dama" haka suka yita shirmensu suna sanya
junansu nishadi sannan sukayi sallama ta kashe wayar yinin sur da ita ya yini a ransa gashi
abubuwa sun riqeshi bai dawo gidan ba sai tara na dare Asmee tayi niyyar qunsawa Mimee yau
dinnan don ta lura itama da shirinta tazo.
Tunda tayi wanka ta dau kwalliyarta ta dawo falo ta harde tana latsa wayarta abin yabawa
Mimee mamaki wato yarinyar ta gama raina ta dariya tayi a ranta tace “a banza kiwon makahon
kare yarinya boka yace karna damu na bari ya kusanceki qaryarki ta qare daga yau" bude qofar
yayi ya shigo idanunsa nakan Asmah ta miqe da sauri ya bude mata hannunsa ta fada qirjinsa
ya rungumeta yana sunsunar wuyarta yaja wani numfashi me qarfi yace “wow miss you my
favorite nayi kewar qamshin nan naki" wani farr tayi da idanunta ta harari Mimee tace “nikuma
nayi Missing sweet lips dinka...."
Bai barta ta gama mgnr ba ya hade bakinsa da nata ya fara tsotsarta da salonsa me mantar da
ita komai
Sun jima a haka suna maqale da juna ba shi da banmasan da Mimee a gurin ma hatta Asmah
da tayi don gayyah ta manta da ita saida sukaji ta saki glass cup a qasa ta fara bala'i fadi takeyi
“au tanan kuma kuka bullo qananun yan iska lallai ma Aseem ka qaro wulaqanci to bari kaji na
fada maka indai iskanci ne wannan bai isheni gani ba saika tubeta a gabana ka zura mata
burarka sannan zan yarda kun tabbata yan iska......"
Daganta hannu Asmah tayi tace “Assha Aunty Mimee kiyi qasa da muryarki kada ki qware nifa
laifin ma da akayi miki banganshi ba mijinki ne mijina ne babu inda akayiwa wani shamaki da
inda zai haska zuciyar mijinsa ni a son raina ma a falon nakeson ayi komi......" Hannu takai zata
dauketa da mari yace “karki soma wlh" idanunta ne ya ciko da qwalla tayi kamar zatayi magana
ta fasa ta shige dakinta sake kwantar dakai asmah tayi a jikinsa ya dagata cak suka shige daki
daqyar ta samu ta bambareshi yayi wanka ta dauko masa abinci yaci sannan suka kwanta ranar
sun gurji juna iyaka sannan sukayi bacci manne da juna.
Tunda suka shiga daki Mimee ke kasa kunnan taji Aseem ya wartako Asmah kamar yanda
Boka yayi mata alqawari amma shiru har asuba har gari ya waye bataji komai ba hankalinta bai
qara tashi ba saida taga sun fito sunata dariyarsu ta rakashi qasa ya fice, data dawo a falo ta
tarar da Mimee ta riqe qugu tanata hucci koda ta shigo bata kalleta ba ta nufi dakinta ta fincikota
da qarfi abin tsautsayi kawai ta kifa a akan cikinta ta saki wata qara daidai lkcn da Aseem din ya
turo qofar yaganta tsaye akan Asmah daketa juyi cikin fitar hayyaci ya matsa kanta a guje ya
bangaje Mimee ya dagota yana kiran sunanta ta bude idonta cikin tsananin azabar ciwo tace
“way....wayyoh cikina Soul zan mut...." Dagawar da zaiyi yaga jini ke binta ya saki wata qara
tare da cewa “Maryam ciki.... Ina kika daketa kashemin su kikazo kiyi dam....." Bai iya qarasa
mgnr ba yayi waje a mugun guje ya nufi asibitin cikin gurin take suka shiga bawa Asmah
taimakon gaggawa sun gama fidda rai da cikin na jikinta saboda daqyar suka samu Ubangiji ya
taimakesu cikin ya tsaya bayan sunyi mata daurin mahaifa saboda budewar da bakin
mahaifarta yayi suka kafa masa sharruda kuwa masu tsauri akanta haka ya rinqa amsawa da
to.
Bayan komai ya lafa ne ya fito ya nufi inda dakinsu yake yariga ya gama yanke mawa Mimee
hukunci dole a wannan karon taje hutu saboda abin nata yayi yawa yasani ita tasa Hajja ta
dakar masa mata sannan ita ta hada mata gobara a part dinta duk ya kawar dakai yanzu kuma
ta fara bibiyar rayuwarta, Dakin Asmah ya shiga yayi wanka ya sanya kayansa ya fito ya nufi fita ta fito da sauri da waya
a hannunta tana rusa ihu tace “don girman Allah kada kayimin haka wlh na daina...." Tureta yayi
yace “wlh saikin koma inda kika fito Maryam na gaji da iskancinki duk da cewa nine na baki qofa
tun farko amma kin zaqe da yawa Banga uwar da yarinyar nan ta tsare miki ba kike neman
rayuwarta bakisan duk wani motsinki kallonki nakeyi ba na dade da gane inda kika dosa,
Maryam kada na dawo na tarar dake a gdannan igiya daya na yanke ki fadawa duk wanda zaki
fadawa saboda dan dake cikin matata da kikayi qoqarin salwantarwa na datse igiyar aurena
daya a kanki idan kuma na dawo naisheki a gdannan labari zai canza zakiba da labarin nace ki
tafi da saki daya kinqi shiyasa na qarasa yanke biyun saboda na fahimci tafiyar zatafi miki dadi"
Yana gama fada ya juya yayi ficewarsa daga gdan ya koma asibitin zubewa tayi a gurin ta rinqa
rusa kuka tana regretting na abun data aikata yanzun gashi tajawa kanta auren da take taqama
dashi ya guntule, tana hada kayanta tana hawaye Naja'at da Hajiyan Aseem sun cuceta sune
sukayita zugata ta biyosa ashe rabon shan duka ne yasata dauko qafa ta taho Boka yace
Asmah zata dawo a hargitse ashe itace zata koma a hargitsen Naja'at takaita ta baro itace ta
rakata gurin bokan ashe reshe ne zai juye da mujiya,
Daqyar taja akwatinta dama dashi kadai ta taho ta fita ta tsari texi ta dauketa zuwa gidan
yayanta dake zaune a qasar koda matarsa ta ganta tasan da damuwa amma dake ba jituwa
sukeba bata tambayeta ba.
Wasa² saida Asmah ta kwana uku a asibiti sannan taji sauqi ya gama shirya musu barin qasar
Dad ya kirashi yace daganan ya wucce Sweeden akwai wata kwangila da zai kula masa da ita
har tsayin 4 months yaji dadin hakan sosai duk da cewa hankalinsa yanakan Asibitinsa amma
ko ba komai zai qara samun shaquwa da matarsa kuma zaiyiwa Hajja nisa yanda bazata takura
masa da mgnr wata Mimee ba.
Hakan kuwa akayi ya dauke matarsa suka lula Sweeden acan ne Asmah taga sabuwat rayuwa
Ashe da Aseem ba komai yakeyi mata ba na kulawa yanzun ne zai fara bata kulawa, babu
abinda yake barinta tayi da kanta komai shine yakeyi mata gashi kullum cikinta qara girma
yakeyi ya dauki so da qaunar duniya ya dorawa cikin nan a cikin lokutan ne kuma Hajjah ta
kirashi take fada masa lallai ya dawo da Asmah gida ta haihu tunda yasan watan haihuwarta ya
kama, yaso yayi mata musu amma yanda ta dage yasa dole badon ransa ya so ba ya dauki
hutun sati uku ya shirya musu tafiya.
Tun suna jirgi takejin mararta na damqawa tana daurewa ai suna isa airport ciwo ya sako kai ta
kasa taka qafarta bayanta ya riqe ta cije lebe tana girgiza kai gumi na keto mata, dagata yayi ya
nufi motar Jabir da ita yana zubanta sannu ciwon ya lafa suka dauki hanyar gida kai tsaye gdan
Hajja suka nufa itadai ga azabar ciwo ga faduwar gaba batasan da wacce siga hajja zata
karbeta ba suna isa bata fito a mota ba ciwo ya dawo sabo maimakon a shiga agaida hajja sai
sune suka fito ita da Nasmah da Aseemah ya dubeta sosai yana sharce gumi yace “Hajjah tun
kwana uku EDD dinta ya qare inajin fah haihuwa zatayi...." Da gudu Hajja ta matso ta cakumeta
tayi mota da ita driver yaja suka nufi asibitinsa suna dubawa kuwa sukaga a matakin qarshe
take allura sukayi mata saboda ta gama jigata shine ya tsaya a kanta tana nishi yana mata
sannu yana duba mintunan da suka rage mata yanajin kamar ya rage tsayinsu aikuwa lkcn na
cika tayi wani nishi ta qanqameshi babyn ta danno kai kuwa qatuwa da ita tana gama fitowa
suka sauke ajiyar zuciya a tare tare dayin hamdala don nuna gdyrsu ga ubangiji.
Tun kafin nurse din ta yankewa Babyn cibiya Hajjah ta danno dakin ana yankewa a cikin jinin ta
karbeta tana hamdala wasu hawaye na zubo mata tabbas taso tayi kuskure data biyewa zuciya
ta salwantar da gudan jinin danta da suka dade suna jiran zuwansa shekara da shekaru, ashe
dai da gaske ne rabo meshi yakebi rabon ba a jikin matar son nata yake ba a jikin wacce ta
dauka a matsayin abokiyar gaba yake yanzu da da take qoqarin rabasu ina zatakai rabon
wannan sankaceciyar budurwar? Tambayace da bata da amsa a sanyaye ta miqawa Asmah
dake kallonta yarinyar cikin tsananin kunyar kai tace “kiyi mata addu'a Asma'u duk abinda kika
roqa mata shine zai bibiyi rayuwarta a daidai wannan lkcn qofar karbar addu'a tsakaninki da ita
dama duk wanda kikasa a addu'arki a bude take"
A kunyace ta karbeta ta zubanta ido ta dago ta kalli Aseem da yaketa sharar qwallar farin ciki
yanaji a ransa Asmah ta gama masa komai tayi masa murmushi ta soma yima yarinyar addu'a
bayan ta gama ta miqa masa ita jikinsa na rawa ya karba ya zauna ya zubanta ido tsananin
kamar yarinyar dashi abin abin masha Allah gabadaya yama manta dame zaiyiwa yarinyar
kawai kallonta yake yana murmushi yana sharar Hawaye saida Asmah tace “Soul takace fah
halak malak kowa tafiya zaiyi yabarka da ita please kayi mata addu'a kaji"......
#Comments
#Shares
#Votes
_*Oum Hairan*_
[08/07 2:21 pm] Oum Hairan: _*Zarrah*_
_*Fauziyya Tasiu Umar*_
_*Elegant Online Writers*_
_*Wattpad-Realfauzahtasiu*_
_*65-66*_
_*End! End!! End!!!*_
Wata ajiyar zuciya yaja me qarfi ya daga yarinyar saitin fuskarsa yayi mata duk abinda ya
cancanci uba yayima yarsa ya rungumeta a jikinsa yanajin qaunarta na ratsa zuciyarsa lallai ya
yarda qaunar da da mahaifi daban take tunda yake baitabajin qaunar wani abu kamar wannan
yarinya ba numfashi ya sauke a ransa yace “yanzu da sakaryar can tayi nasara fah da tuni bai
sameta ba" Asmah ya duba yayi mata murmushi ya miqa mata babyn Hajja tayi maza ta karba
tace “kawota a gyarata mana kun barta tinqi sai zagawa kukeyi da ita" ita da kanta ta wanke
yarinyar ta shiryata tsaf Aseemah da Nasmah na tayata ana gama shiryata ya fara zubanta
hotuna ko kunya babu Inna dake shigowa itakam yar kallo ta zama daqyar Hajja ta qwaceta a
hannunsa ta bawa Inna ita Inna tayi murmushi tace “kamar zare kamar Allura Aseem hankali ya
kwanta ubangiji yabada lfyr tarbiya da nemo Abinci don da ganin wannan bakin zaiyi ci"
Murmushi yayi ya fice daga dakin ya nufi gidansu dashi da masu aikin gdan suka gyare gidan
tsaf sannan ya debar musu kaya ya fita ya koma asibitin sai dare suka dawo gida da rikici aka
taho wai zasu tafi da ita gida yayi tsalle yace shikam baa isaba dole suka qyale sai Inna ce ta
zauna a gurinta wannan yarinya tayi goshi Zulaihat yasa mata sunan Kakarsa Sukece mata
Ammi gatakam Ammi da mamanta sunganshi bayan suna komai ya lafa Badon inna naso ba
haka ta zauna har arba'in sannan ta tafi su Mimee harda zuwa barka taga yarinyar ji takeyi
dama itace ta haifa masa yarinyar sosai take nadamar biyewa zuciya data rinqayi har takaita ta
baro gashi tayi uku babu ba surukar babu Mijin babu Haihuwar.
Gashi wacce takeso taga bayanta din ta zama itace take mulkar gdan wannan abu nayi mata
ciwo, ranar da sukayi arba'in washe gari kuwa ya dauke matarsa suka bar qasar duk yanda
Mimee taso ta shawo kansa abin ya faskara hakanan ta hqr ta zubawa sarautar Allah ido kullum
mahaifiyarta cikin goranta mata take ta kaso aurenta tazo tana sa musu ido a gda itakam
batada bakin mgn saidai idan sun guma mata ta shige daki tayi kuka tayita kiran Aseem baya
dagawa dole ta hqr ta sallama mawa Asmah mijinta donta fahimci yanzu hankalinsa baa kan
kowa yake ba sai matarsa da yarsa tana ganin status dinsa kullum daga matarsa sai Amminsa
sune a status dinsa idan tayi masa mgn ma baya budewa, tafi tafi har shekara guda Aseem yayi
gurin zama A Sweeden yaqi dawowa shekarar Ammi guda ta sakejin labarin Asmah ta qara
haihuwa.
Ta haifi Mukhtar Sunan Mahaifinsa kenan Suna kiransa Anwar tuni ta zubar da makaman
yaqinta ta koma lalubar Asmah tana gaisheta tare da tambayarta yara da farko bata saurarenta
sai daga baya ta saduda take amsa mata suke gaisawa sosai tayi nadama da kanta take bawa
Asmah hqr take roqonta ta taimaka ta bawa Aseem hqr ya daina gaba da ita wlh sharrin zuciya
ne da tsautsayi.
Saida Asmah taji dam a ranta ta saba rayuwarta daga ita sai mijinta yanzu kuma ace wata tazo
ta shiga wannan abu ya girmi tunaninta bazata iyaba, Suna chat da Jiddarh take fada mata
halin da suke ciki nan Jiddarh take bata shawara akan ta manta da komai tayi domin Allah Allan
bazai tabar da itaba nan take fada mata halin da Mimeen ke ciki a gdansu na tsangwama da
wulaqanci kasancewar Qanwar Mimeen Zahra qawarta ce.
Jikinta ne yayi sanyi ta nutsu ta fara tunanin itama hakan zata iya faruwa da ita idan akaqi
taimaka mata bazataso ba kuma duk wanda ya taimaki wani tabbas Allah zai taimakeshi, da
wannan nazarin ta danni zuciyarta ta runkari Aseem din da maganar yakoyi funfurus yace
bayada raayi, Haka ta rinqa binsa da magiya da komai yamaqi sauraronta balle tasaran zai dubeta gajiya tayi
ta yima Inna mgnr itace ta nemesa akan ya dawo da matarsa ai tayi hankali yaso yayi mata
gardama amma mutuncinta da yake gani yasa yace mata shikenan zaiyi nazari.
Lkc yayita tafiya baice mata qala ba har saida aka qara daukar wata shekarar ta qara sunkuto
masa da namiji a wannan karon ne tayi nasara da Inna ta qarasa baki ya amince ta dawo amma
ta