Showing 9001 words to 12000 words out of 54507 words

Chapter 4 - ZARRAH BOOK COMPLETE BY OUM HAIRAN .pdf


Basu da yanda zasuyi damu sai tsaki sai harara"



Har sukaje makarantar Allah be hadasu dashi ba haka ta rinqa Allah Allah a tashi nanma Basu
gamu ba taji haushi sosai so batada yanda zatayi dole ta hqr tana zuwa suka nufi islamiyya sai
yamma suka dawo liqis dake laraba ce sunyi hadda a dakin zaure suka tarar da Mal Husaini da
Mal Bala suna tattaunawa Mal Husaini sai dariya yakesu suka durqushe suka gaishesu da
fara'a Mal Bala ya amsa inda Mal Husaini yace “Ina Ma'ulelena zonan dan qaniyarki" gabanta
ya fadi tunda dama a tsorace take tana jiran abinda zaije ya dawo.
Matsawa tayi a darare ta zauna tana barin jiki don tasan ba wuya bane Mal ya maketa ba
gyaran murya yayi yace “Ina kike Asma'ul Husnah?" Ajiyar zuciya tayi tace “gani Mal" Jinjina Kai
yayi yace “yawwa Masha Allah dama wani umarnin gaggawa zan baki Kinga dai a yanda kuka
taso a wahale a talauce to ke ki godewa Allah yasoki da arziqi yayi miki ludufi da ludufin da
yakewa duk Wanda yaso cikin bayinsa jiya anzo ganin gida Ashe rabon aganki ne dan farin
yaron nan Alhajin Birni eh wlh tallahi shine dai bayan sunga gda kinje kin gaishesu yagani
yakeso harma yayimin alqawarin idan na bashi aurenki zai barmin gdana Kuma zaiyimin komai
na auren Dijangala da Zabba'u keko yace ki cokali bashi buqata, kinji fah inda arziqi yake"




Tunda ya fara mgnr ta kafesa da ido cikin mugun tsoro da kaduwa ta gane waye yake nufi
domin Zahran ba fari bane Aseem ne fari Anna sai tace “wa...waikace Mal Sadiqun fah?" Wata
uwar harara ya buga Mata yace “Sadiqun0 ubanki yo ko Laminu ne uban Sadiqu ya dawo
duniya ai bazai hanani cin wannan arziqin ba ke nifa bama shawara nake daku ba dagake har
uwarki dama na dauka ke dake kin shafi zamani zakiba da hadin Kai to kema naga qwalluwar
yar baqin ciki ce saboda haka tashi ware kauce karna makeki sauna kawai wadda arziqi ke
binta tsiya ke dawo da ita baya"
Yana fadin haka ya miqe abinda yasata miqewa itama da gudu tayi cikin gdan tana rushewa da

kuka tana cewa “wlh baa isaba bazaa taba cutata a hadani da wannan shegen azzalumin
mutumin ba ai bani kadai aka Haifa a gdanba abashi wata Mana saini saboda an rainamin
hankali...." Jin takun sawayen Mal Husaini yasata shigewa qarqashin gadon qarfen Inna tana
kuka ya shigo dakin yana huci Yana cewa “kajimin mutane yan baqin ciki arziqi yazomin har gda
Allah ya amsa addu'a ta Nima nakusa hutawa shine zakuyimin baqin ciki tabdi ai wlh baku isaba
wannan aure me hanashi saidai mutuwa idan ma mutuwa zakiyi saidai ki mutu ja'irar yarinya
kina tafe kamar ki karye saboda rama yo kika sake kika auri Wannan Dan gadon talaucin da
ubansa tunda nasanshi da tàgiya daya nasanshi basai kin qwammace wannan makauniyar
uwar taki barinki tayi ba"





Harya gama sababinsa ya fita Inna batace komai ba sai bayan ya fitane Asma'u ta fito tanata
shassheqar kuka Inna tace “wai waye wannan ne daga zuwa Mal ya aminta dashi Babu binkice
Babu komi?" Nan Asma'u ta yiwa Inna bayani Inna ta saki salati da sallalami tare da yiwa Allah
kirari tace “naga takaina ni aminatu dama akan wannan kwasasshen mutumin Mal yacimin
mutunci har Yana cimin alwashin aure Babu fashi aikuwa da fashi don baza'ayi wannan son
zuciyar dani ba yaro shekara da shekaru Yana wahala Rana tsaka saboda son abin duniya Mal
ya rufe ido yana cima mutane mutumci ai bake kadai ya haifaba yabasa wata Amma bake ba"




Dayin magariba kuwa saiga Kiran Sadiqu a qofar gdansu idanun Ma'u sun kumbura sunyi luhu²
saboda kuka ta yafa mayafinta ta fito shima duk a hargitse yake yana ganinta ya riqo hannunta
yace “Asma'u meye ne ke Shirin faruwa dazu Baffana yayimin kiran gaggawa naje yake
fadamin Wai saqone daga Mal babuni Babu ke yayi miki miji hakanne da gaske Ma'u rabani
zaayi dake?"
Kafin ta gama shassheqarta ta dago sukaji daga bayansu muryar Mal Yana cewa “eh hakanne
babu Wai a ciki nama rabaku har abada indai nine mahaifin Asma'u to babukai Babu ita nayi
Mata miji daidai da ita kaima kaje ka samu daidai dakai dama ai a rashin uwa ake uwar daki
tunda uwa tazo kuwa dole uwar daki ta kauce soko kawai me hatimin talauci a goshi"



A sanyaye Sadiqu ya tsugunna gaban Mal Husaini yace “Kada kayimin haka Mal wlh idan ka
hanani Asma'u kamar ka datsemin farin cikin rayuwa ne ka taimakeni kabarni da Asma'u nayi
maka alqawarin Bata farin ciki fiye da Wanda kake hango Mata a Wanda kake Shirin aura Mata
Mal baisan darajarta ba kamar yanda na San...." Tsawa Mal Husaini ya buga Masa yace “kajimin yaro sakarai Shashasha aiyo wato Nima kana

nufin kafini sanin darajar Asma'u ko to kaji in fada maka ba daraja ba ko alqabba ne Kai
qarewar daraja Asma'u ba rabonka bace, kekuma munafuka na dawo kanki daga yau sai yau
idan na qara ganinki da wannan faqirin yaron me riga daya saina Saba miki. Zaki shige gda
kosai na karya qafafunki" a guje Asma'u ta fada gda tana kuka inda ta ishe Inna tana sallah
fadawa tayi saman gadon qarfen Inna Mal Husaini ya biyota Yana cewa “wato Ni akeson a
tozarta a garin nan a mayar dani sakaran uba da Bai Isa da gdansa ba ko to wlh baa isaba dole
ne nasa doka abi ke Aminatu kin rainani Ina fada da babbar murya duk ranar dana qara ganin
Ma'u da wani a Aseem ba sainaci mutuncinki wlh saikin gwammace baki sanni ba domin ranar
ne zaki gane Nima namiji ne talauci ne yasani zama mace wawaye kawai masu qashin tsiya
[20/06 4:30 pm] Oum Hairan: *_ZARRAH_*



*_Oum Hairan_*


*_13-14_*





Tunda Asmah ta taji wannan hadi da mahaifinta ya shirya yi mata ta shiga  dimuwa da tashin
hankali abubuwa suka jagule mata ta shiga  tsananin damuwa abubuwa duk suka rikice mata ta
kasa gane ta Inda aka samu asalin barakar sosai take cikin qunci,
A bangaren Dr Aseem Shaheed jinsa yake  cikin walwala sabida ya samu yanda yakeso
mahaifin  Asma'u sai ladabi yakeyi masa shima kuwa ya sakar masa kudi tunda ya fahimci
kwadayi ne dabi'arsa tuni yasa aka fara gyarawa Mal Husaini gidansa tunma kafin a gama
daidaita tsakaninsa da yartasa. Itakuwa Innah tsallle tayi ta dire tace bada itaba bazaa taba yaudarar Sadiqu da itaba yaron tun
asmah batasan kanta ba yakeyi mata wahala sai yanzu rana a tsaka wani yazo a dauki aure  a
bashi wannan ai  rashin adalci ne, sosai Asmah ta samu goyon baya gurin Innah hakan ya dan 
kwantar mata da hankali kadan.

Karatunta ta mayar da hankali tare da cin alwashin duk ranar da Dr Aseem ya kuskura yazo
qofar gdansu saita tata masa asalin rashin mutunci, sati guda da zuwansu na farko tana
kwance a dakin Innah abin duniya yayi mata zafi qarfi da yaji Yaya Mudam ya hana Sadiqu
zuwa gurinta  saidai  su hadu dashi a burtsatse su tsaya suyi yar  hirarsu babban tashin 
hankakinta yanda masoyin ya rame  yayi duhu da sun hadu sai ya fara yimata magiyar karta
yarda a rabasu  a mafi yawan lokuta suna kuka suke  rabuwa duk da cewa Asmah bata gama
gasqata mgnr auren ba,
Hakanan aketa gyaran gdansu ita  kuma tanaci gaba da zuwa makarantarta har tsayin watanni

biyu sosai rayuwa ta fara canzawa a gdansu mal Husaini har buhun shinkafa yake  ajiyewa
inda  itakuma a haukanta ta fara mantawa da aikin dake  tunkarota. Kwatsam ranar Wata
alhamis sun dawo daga  tahfiz ita da Jiddarh Jiddarh ta biyo zata karbi wani text book.



Tun daga  nesa  ta hangi  wasu  manyan motocin alfarma a qofar gdansu guda hudu hakanan
gabanta ya yanke ya fadi suka kalli  juna cikin sanyin jiki daidai lkcn da wasu  fararen dattijai
suke fitowa daga  soron gdan nasu ta zubansu ido tanason ganesu amma ta kasa sai ajiyar
zuciya kawai data suke ta rabasu ta wucce sudinma binta  sukayi da kallo. Itadai ko arziqin gaisuwa basu samu ba tayi shigewarta gdan garama Jiddarh ta gaishesu suka
shiga tabata abinda zata bata ta fito ita kuma ta dauko  buta  ta fito, mamakine ya cikata ganin
matan  gdan nasu da yaransu Dijangala da Lantana a tsaye  cirko cirko to dake  ba shiri suka
cika ba hakanan tayi shigewarta bandaki tanajinsu sunaja mata tsaki bata ko kallesu ba, fitowa
tayi ta shige dakin Innah ta ishesu ita da mudam da Mal Husaini suna tattaunawa,
Kallonta mal Husaini yayi yace “nemi guri ki zauna duk na gama mgn da yan'uwanki kece
kikeson ki bani matsala  kuma ke  dinma baki  isaba"


A gajiye ta nemi guri ta zauna Yaya mudam ya zabga mata harara ta sunkuyar da kanta Mal
yaci gaba da cewa “dazu iyayen Aseem sunzo akan batun aurenki sun kawo kudin aurensu da
sadaki sannan  sun nemi alfarmar ayi biki nan da Wata biyu dadai  nace  Wata biyar  nasa so
munyi mgn dashi Aseem din yacemin babu komi zai dauki nauyin komai wannan tasa  da naga
sauqi yazo na amince...."
Dagowa tayi da Sauri tace “Baffa Sadiqun fah...." Jitayi an buge mata baki ta dago da idanunta
daya  kawo ruwa take ta fara tsiyayar da hawaye Mudam ya nunata da yatsa  yace “shegiya me
qashin tsiya arziqi na kiranki tsiya na cewa nice taki  ana mgnr arziqi kina mgnr talauci ubanme
Sadiqu zaici bare ya baki gayyar tsiya gayyar wahala....."

Dagansa hannu Baffa yayi yace “yo miye na bata bakinka abuda babu fashi  sai anyi  kawai kije
ki fara shiri nanda watanni biyu zan daura muku aure kowa ta kama gabanta" miqewa sukayi
zasu fita  cikin gunjin kuka  Asmah tace “Innah bazakice komai ba don  Allah kiyi wani abu...."
Janyota Innah tayi jikinta tana Shafa bayanta sukayi ficewarsu sannan ne Innah tasamu  damar 
mgn tace “to me zance Ma'un Innah kinji irin  diban  albarkar da Mal yayimin yau har yana cewa
nice nake  zugaki kiqiyi masa biyayya, Asma'uh wannan lamari son zuciya ne saidai kawai Allah
ya sakawa wanda  aka zalumta kiyi hqr kiyi biyayya insha Allah zakiga Ribar hakan a gaba"
Kwantar da kanta tayi a jikin Innah tace “wlh Innah badon  Allah Aseem yakeyin duk abinda
yakeyi ba akwai manufa cikin lamarin nan Innah kada  kibari son zuciyar su Baffa ya salwantar
min da rayuwarta......"

Rufe  mata baki tayi tace “Asmah kiyi hqr kuma kisa  kyakkyawar niyya a ranki  insha Allah
Ribar abin zaki gani" sosai Innah ta rinqa yima Asmah nasiha hardai ta daina kukan ta koma  ta
kwanta  lamo akan gadon Innah tanajin zafin abinda Baffa yayi mata shi bayama  jiye mata
wulaqanci? Ranar ko diban ruwa kasa zuwa tayi saboda zazzabin da yake  damunta




Washegari juma'a duk da batajin dadin jikinta haka ta shirya ta fita domin zuwa makarantar
daga  yanayin takunta Indai kasanta zakasan akwai  abinda yake damunta, cikin saa tana zuwa
gdansu Jiddarh ta ishe  ta shirya suka nufi makarantar a qafa suka tafi  domin dukkansu babu
mai kudin Mota suna tafe ne tafiya irinta kurame babu me cewa wani, sunci rabin  tafiyar sukaji
Mota a bayansu tanayi musu horn basu  tsayaba saidai kaucewa da sukayi suka bawa mai
motar  hanya, zartasu yayi sannan  ya tsaya tare da kashe motar ya fito cikin shigarsa ta likitoci
fuskarsa dauke da murmushin da shi daya  yasan ma'anarsa ya tako  inda  taja  ta tsaya tana
qare  masa kallo batayi aune ba kawai saiji tayi ya sanya  hannunsa ya dago fuskarta ya dora 
bakinsa saman kuncinta ya janye a hankali yana murmushi  yace “to ya kikaga salon wasan 
namu?"



Takaici ne yasa batasan sanda  wasu  hawaye masu  zafi suka zubo mata ba murmushin
fuskarsa ya fadada yace “tun yanzu? Haba  karki karaya da wuri mana aike jaruma ce  kin iya 
rashin kunya zaki qwaci kanki dadin dadawa gashi kinyi saa  gyatumai kwadayayyu Allah ya
baki kada  ki matsawa zuciyarki wajen tunanin abinda ya dace duk wani Abu da yake ya dace
nayishi bayan iyaye shima masoyin na bogine  tunda ya siyarmin da soyayyar a farashi me arha
dubu dari  da hamsin kacal kinga ko yanzu zaki iya  bambamce tazarar dake tsakaninmu koda
yake banson  ma ki gane  yanzu ki bari sai can gaba saiki gane  lkcn da hakan zaibada show na
gaske a lkcn ne wasan zai fara nanda 2 months yanzu sharar fage ce"..........

_Gareku yan'uwanmu na Niger kuma fah kuna  da damar  samun wannan littafan guda biyu
idan kinaso kiyimin mgn ta WhatsApp akan wannan number,09013718241 sai najiku_


*_Oum Hairan_*
[20/06 4:32 pm] Oum Hairan: *_Zarrah_*




*_Fauziyya Tasiu Umar_*
*_Oum Hairan_*

Littafin _*_ZARRAH* na kudine idan kinason zaki biya 200 ta _account dina_
__0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTBank_ _ko kati MTN ta whattsAp a wannan number
09013718241 ko VTU ta wannan number 09031307566._


_Gareku yan'uwanmu na Niger kuma fah kuna da damar samun wannan littafan guda biyu
idan kinaso kiyimin mgn ta WhatsApp akan wannan number,09013718241 sai najiku_



*_15-16_*



*_Last Free page_*




Sosai hawaye kibin kuncinta tana qara saita injin idonta akan Aseem kallo takeyi masa da yake
bayyana tsantsar tsana dajin haushi da kuma tausayin kai tasan duk duniya ba kowane yaja
mata wannan wulaqancin ba face Mal, numfashi ta sauke kawai ganin wankin hula na neman
kaita dare ta juya ta canza hanya ta tafi tabarsa tsaye yana bin bayanta da kallo yana
murmushin mugunta shikadai tasan abinda yake saqawa a zuciyarsa yarinyar ta gama lalacewa
idan ta zama mallakinsa zai nuna mata iyakarta zai nuna mata duniya da bambamci.
Komawa yayi yatada motarsa ya tafi sai lkcn Jiddarh ta lura da cewa ashe Asmah ta jima dayi
mata nisa tabita da sauri tana qwala mata kira bata tsaya ta saurareta ba sai a cikin makaranta
suka hadu bayan an gama assembly suka tafi ajinsu Jiddarh ta dubi asmah tace “wato Allah
idan yana sonka da arziqi sai ka zagi sarki a gaban fadawa yace gaisheshi kayi wlh Asmah a
rayuwata na dade banga kyakkyawan namiji irin Aseem Ba kayy gsky kin dace, amma fah da
alamun dan izzar masifa ne zakisha fama...."



Wani naushi da Asmah ta kaiwa Jiddarh a baki yasata gocewa tare da cewa “daga fadar gsky
kuma Allah mijinki dan kyakkyawa dashi" malaminsu ne ya shigo hakan ya tilastawa Jiddah yin
shiru ita dama Asmah bakinta ya kulle kalaman Aseem ne kawai sukeyi mata yawo a kwanya
iyayenta matsiyata idan ta tuna wannan kalmar sai taji hawaye ya zubo mata to amma komai ya

samu shamuwa watan bakwai yaja mata da mahaifinta baibi son zuciya ba da yanzu tana tare
da masoyinta, da taji haka a ranta saita tuna yace da quarter million ya siye Sadiqunta.
Gabadaya duniya tayi mata zafi ji takeyi kamar tayita rusa kuka hakadai a dafe aka tashi suka
tafi gda daqyar takai gidan saboda azabar masifar zazzabi da yake dirar mata tana zuwa ko
uniform bata cire ba ta fara kwara amai bayan ta gama ta shige dakin innah ta kwanta tana
mayar da numfashi



A kwance take amma duniyar juya mata takeyi itadai bata qara sanin komai da yake faruwa ba
sai farkawa tayi ta ganta daure da robar ruwa a hannunta ta rinqa bin dakin da kallo daya da
daya tanason tunano ko a ina take a hakan taji an turo qofar an shigo ta juyo da kanta idanunsa
na kanta yana wani lumshesu kamar me jin bacci. Guri ya samu ya zauna ya bude takardar hannunsa yayi rubuce rubucensa ya rufe ya sake
dagowa yanzun kanta yana saman silling fasali yaja ya miqe daidai lkcn da Inna Azeezah
qanwar Innah take shigowa suka gaisa har yana wani rusunawa tace “ya me jikin?" Kallon
Asmah yayi yace “gatanan da sauqi yanzu ta farka da alamun jikin dakyau insha Allahu gobe
ma zamu koma gida yasu Innah?"



“Alhmdllh" ta furta koma ta zauna tana hade kaya shikuma ya fice bai jima ba ya dawo da
tarkacen ciye ciye ya ajiye Innah Azeeza nata godiya yayi murmushi yace “babu komai Innah
yiwa kaine fatanmu dai ta samu lfy ai taji jiki sati biyu a kwance ga hidimar biki sai matsowa
takeyi yanzu fah saura sati biyar" jinjina kai tayi tace “Allah yasadai ayi lfy a gama lfy"


Amsawa yayi da amin sannan yasa kai ya fice zuciyarsa najin haske yanajin nishadi yasan
yagama saita saarsa Asmah zata gane kurenta tabbas zatasan ta shigo gonarsa da wannan
tunanin ya tashi mota ya nufi gdansa yajima a mota kafin yayi qarfin halin fitowa yana ayyana ta
yanda zai tunkari Mime da mgnr auren nasa bayan shi da kansa yayi mata alqawarin bazai taba
hada matsayinta da wata ba balle aje ga batun aure.
Shahada yayi daya haura ya tunkari saman a kwance a parlourn saman ya isheta tana duba
jarida ya nemi guri ya zauna ta ajiye jaridar tare da dagowa ta dubeshi sukayiwa juna murmushi
ya shafa kansa yace “ya gda?" Miqewa tayi zaune tana yatsina tace “gashinan babu dadi
kadaici ya dameni kaikuma ka daina samun lkc na na rasa meye yake daukenka hankali gareni"
kawar dakai yayi ya shafa sumarsa yace “abubuwa ne sukayimin yawa 2 days dinnan inason
samun zama dakema nakasa samun lkc” shiru tadan ratsa na dogon lkc can ya dago yace
“Maryam Aure zanyi....." Wata zabura tayi ta miqe da sauri tace “me....me kace Aseem".......

[20/06 4:32 pm] Oum Hairan: *_Zarrah_*

*_Fauziyya Tasiu Umar_*
*_Oum Hairan_*





Littafin _*_ZARRAH* na kudine idan kinason zaki biya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login