Showing 54001 words to 54507 words out of 54507 words

Chapter 19 - ZARRAH BOOK COMPLETE BY OUM HAIRAN .pdf

nutsu ta kama kanta idan yaga wani abu sabanin hankali tabbas zata koma inda ta fito
kwanan Jamal Goma a duniya jirgin Mimee ya sauka da gaske gabadaya tayi sanyi batada wani
katabus ta cire komai ta kama Allah tasan shine kawai yanzub zai iya mata bayin kanta ba.

Yaran ta kama ta riqe tun Asmah bata saki jiki da itaba har ta sake mata suka rungumi junansu
komai ya wucce kamar baayi ba anan Sweeden Asmah taci gaba da karatunta na likitanci
bayan ta gama ya nema mata aiki anan din itakam Mimee tace bazata iya wani karatu ba sai
jari daya bata take kasuwanci itama Asmah tana aikinta tana sarar jakankuna da takalma yan
Sweeden tana turawa 9ja ana siyar mata haka nan rayuwa taci gaba da tafiya lkcn da asmah ta
samu cikin hudu itama Mimee ta samu sosai ansha wahalar cikin nan dake allah yayi me taka
qasa ne ta haifi yaranta biyu mace da namiji sati biyar tsakani Asmah itama ta Haifi nata guda
biyu duk maza itakam Mimee mahaifar ce ta lalace dole aka cireta itakuma Asmah haihuwar ce
tazo da tangarda saida akayi mata Cx aka cire yaran aikam tace itafa ta gama haihuwa a
shekara shidda yara biyar to shima bai zafafa ba aka daure mata mahaifar sukaci gaba da
rayuwarsu suna kula da yaransu idan ka shigo gdansu bazaka taba bambamce wace ta haifi
wane da wane ba saboda shaquwar da suka samu da Mimee kusan ma basu samu da Asmah
ba.
Rayuwa tayi dadi tayi albarka lkcn da Ammi da Anwar suka gama secondary ne suka shiga
Jami'a lkcn ne sukuma suka koma 9ja ya gina musu qaton gda A NSRW G.R.A ita kuma Asmah
ta gina qaton Asibitinta ta mayar da hankalinta akan kula dashi kusan ginin shine yayi mata
kayan aiki kawai ta zuba, itama Mimee ya bude mata shagon saida kayan mata da yara...........




_*Tammat Bi Hamdullah*_


_Nan na kawo qarshen wannan labari Ina fatan kuskuren da yake ciki ubangiji ya shafe
abubuwan amfanin dake ciki Allah yasa Mu amfanesu ya bamu ikon bin daidai da kuma aikata
daidai ubangiji yasa ayyukanmu su zama hujja garemu ba hujja akanmu ba_


_Kada ku manta JUHUD shine littafi na gaba dana fara sakinsa ranar 7/7/2021 duk da
kasancewarsa na kudi ina fatan masoyana zasu karbeshi domin nasan tabbas banako tantama
zai nishadantar daku fiye da tunaninku kuma zai ilimantar daku zaku qaru matuqa a cikinsa._



_Ina roqon duk wanda yakeda shirin bibiyar labarin JUHUD da yayi hqr da yanayin labarin
domin tun a tallansa na fada Romance ne akwai......... sosai a cikinsa duk da cewar insha
Allahu zanyi amfani da hikima wajen kyautata harshe, to nima inason uzuri daga gareku._


_Domin sharhi shawara ko qarin haske zaku iya nemana ta WhatsApp a wannan number

09013718241_


_Taku ta kowa me burin nishadantar daku da kawo muku abubuwan da suka shigenku duhu
koda wasunku zasu kasa fahimta_



_*Oum Hairan*_

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login