Showing 18001 words to 21000 words out of 54507 words

Chapter 7 - ZARRAH BOOK COMPLETE BY OUM HAIRAN .pdf

kwanciyarta




Wayar tace ta dauki ruri ta daukota ta duba taja ajiyar zuciya Dijanta ce ta kara a kunnenta tayi
sallama dijah ta amsa da sanyin murya tace “inanan inata tausayinki ance mazan da sukasan
dadin mace sunfi rashin tausayi a daren farko Ma'uh nikam naci wuya ji nake kamar kar a qara"
sarai ta gane inda ta dosa tayi dariya me qarfi tace “lallai inayi murna kice har Ali yaga Ali?"
Ajiyar zuciya Dijah tayi tace “yanzu ke haka kuka kwana yana kallonki kina kallonsa duk irin
maqudan kudadan daya kashe Allah bai fanshe ba?"



Numfashi taja tace “nifa banson gulmarki nan ina ruwanki tunda kedai anyi miki abinda kikeso"
sanin hali yasa Dijah cewa “kekam kin fiya masifa daga na kiraki mu jajantawa juna zaki kama
yimin fada to ai shikenan sai kiyita yi nidai nazama cikakkiyar mace yarinya ko iyanan alamu
sun nuna nafiki" murmushi tayi tace “to meye na gorin abinnan da ba dambe ba kowacce mace
ma tana zuwa gurin lkc dai igiya uku ke gareki nima itace dani saboda haka banga bambamcin
ba".........
Kashe wayarta tayi ta gyara kwanciyarta tasha bacci sosai har wajen daya sannan ta tashi tayi
sallah ta gyara gadonta ta nufi part din Mimee har yanzu tana kwance inda ta barta mamaki ya
cika Asmah tayi mata sannu da gda ta dago ta kalleta saida gabanta ya fadi ganin irin kwalliyar
da Asmah ta caba cikin wani tsadadden less dake cikin lefenta, sarai take kallon Asmah tun
daga sama har qasa ta zubawa hips dinta ido tuni Asmah ta fahimci kallon qurillar da takeyi
mata tayi qaramin murmushi a ranta tace “jira dai madam ba damuwata mijinki ba amma dole
ne kisan nafi qarfin matsayin da kuka ajeni"
Dagowa tayi tace “me kike buqata?" Iska Mimee ta furzar ta qanqance ido tace “kewai bakisan
matsayinki bane a gdannan? Waye ya baki damar kwalliya?" Dagowa tayi ta dubi mimee tace
“wai dake naji sunanmu daya a duniya Matan Dr Aseem Shaheed shiyasa nabawa kaina yancin
kwalliya a gdan mijina....."

Wata muguwar tsawa mimee ta daka mata tace “Ubanwa yace miki matsayinmu daya dake yar
matsiyata? Ke mece a mata da har zaki hada kanki dani??" Abinda Asmah takeso kenan ta juya
cikin salonta na iskanci tana kada mata mazaunai tace “In kinga dama ma ki kirani da tafi haka
nidai inajin kaina matsayin matar Mijinki bawai isar ki ce tasa na qudurta yi miki wannan aikin da
kuka bani ba not sister tausayinki ne a matsayinki na patient kuma naji mijina yace cikine dake
zaki haifa mana sanyin idaniya" tsayawa tayi ta juyo tace.
“Bari kiji wani abu ko Maryam naso ko bataso Asma'uh ta Aseem Shaheed ce zabinsa ce
sannan inayi ne don farin cikinsa tabbas zanyi komai indai zaisa mijina abin alfaharina Happy
domin nasan zamusha mango harda gwanda ke har water milon zan yanka nabashi a baki....."
Dafe kuncinta tayi da sauri ta dago sukayi ido hudu da Aseem dake tsaye, ya hade rai sai huci
yakeyi maimakon tayi qoqarin yin wani abu sai kawai ta shammaceshi ta fada jikinsa ta
qanqameshi ta rushe da kuka, raunin Aseem kenan A duniya baya qaunar kuka a cikin
kukanma ya rasa masifar da tasa indai Asmah zatayi kuka sai yafi dagansa hankali fiye da
yanda kukan kowa yake dagansa.
Sake qanqameshi tayi tana tura masa nononta a qirjinsa tuni baisan sanda ya dagata ba cak ya
nufi saman da ita Mimee na tsaye sake da baki tana kallon ikon Allah suna shiga ya ajiyeta
saman resting chair ya fada bathroom ya sakarwa kansa ruwa a ransa yanajin zafin kukan da ta
zauna tanata rerawa har wani qara sauti takeyi, badan ya gaji da wankan ba ya dauro towel ya
fito yace “oh gud ki daina wannan kukan haka na fada miki banso ko?" Ajiyar zuciya ta rinqa
jerawa ya tsugunna gabanta ya kamo hannunta yace “ki daina yi mata rashin kunya duk abinda
zakiyi ya tsaya iyakar ni dana daukoki" miqewa tayi zata fice ya fincikota da qarfi ya hadata da
bango ta saki qarawa hawayenta qarfi tanajin sanda yasa hannu ya shafa shatin inda ya
maretan yace “kinga gurin har ya tashi" tureshi tayi ya sake ruqota ya hadata da qirjinsa ya
murdawa qofar key ya matseta sosai a sanyaye yace “me kika bawa Mimee taci da safe?...."
Bai gama rufe bakinsa ba yaji an turo qofar an shigo, ya saketa d sauri Idanun mimee akansu
wani murmushi Asmah tayi tace “Insha Allahu bazan qaraba kayi hqr kaji mijina" tana fadin haka
ta juya ta fice tana yiwa Mimee Murmushin qeta, kitchen ta wucce zuciyarta tas ta fara hada
abinda zata girka lkcn uku har da rabi tayi tuwon shinkafa ta dora ta rage gas din ta fice ta nufi
part dinta tayi sallah da gayyah ta sake wanka ta canza kaya ta fito ta koma taci gaba da aikinta
miyar zogale tayi musu ta sake yi musu jallop din taliya ta jere musu a dinning ta zuba a nata a
collar ta bude qofar baya tayi ficewarta tanajinsu sunata bala'i itadai ko a jikinta an qudurta tayi
ko zai rinqa zagin iyayenta bazata sake Mimee ta fahimta ba gara idan sun kebe sucinye
iyayensu ma.....



_Comments_
_Share_
_Vote_
_Please_

_*Oum Hairan*_
[20/06 4:32 pm] Oum Hairan: https://chat.whatsapp.com/IJkh1cP8h62Avsz2Zrcr2x




_*Zarrah*_




_*Fauziyyah Tasiu Umar*_



*ELEGANT ONLINE WTITERS*



_*25-26*_



Tana shiga part din nata ta dauki wayarta tana latse latsenta tana murmushi hirar manyan mata
na bata nishadi a group din DOMINKI YAR GATA na Oum Hairan wanda Aunty Hajar ta biya
mata tasata a ciki tunda ta shiga batace komai ba saidai murmushi da takeyi wata matace a
group din tace _“wato Jiya naji dadin lectures din da Malama Ummi tayi mana a gidannan
nabawa kafura kuka kwana sukayi suna bala'i inajinsu dake baa dakina yake ba na kulle
qofata"_ stikers wata ta turo ta dariya Asmah ta sauke ajiyar zuciya kafin tayi mgn taji wata tace
_“ ai koni da nake ni kadai jiya Munji Happy nida Abban Salim har kyautar kudi yayimin unguwar
da na dade ina tambayarsa sai gashi ya daukeni ya kaini, Mukam sai gdy Oum Hairan group
din dominki yar gata 2 yana taimaka mana wajen samawa kanmu yanci gurin riqaqqun mazajen
nan na zamani babu boka babu mallam"_



Suna taka da wannan tattaunawa taga ansawa group din mukulli bayan kamar mintuna biyar
alamun rubutu suka bayyana a saman group din sallama ce ta fara shigowa kafin me rubutun ta
fara da cewa _"kamar yanda kuka sani yau Oum Hairan ke gabatar da shirin zuciyar masoyi ba
Aunty Mamee ce saboda haka zan koma gefe Nima nayi sauraro aunty mamee bismillah

dalubanki na sauraronki💃🏻"_
Tasa alamun rawa tayi dif abinta shudewar yan mintuna aka fara gabatar da lecturer me taken
*ZUCIYAR MASOYI* matan sunji nayi duk sunyi zukudun suna saurare" jinjina kai kawai Asmah
takeyi taji manyan wada wadai tuni ta shiga hankalinta wani abin idan Aunty mamee ta fada har
daukewa numfashinta yakeyi saboda kunya, ta jima a zaune ko sallah ta kasa tashi tayi bayan
an gama lectures ne kuma aka tafi bangaren gyara Hajjiya mandiya hamshaqiya Oum Hairan
ce ta karbi filin da cewa _“Da yawan iyayenmu mata suna damun kansu Idan zasu auradda
yayansu da nemo musu maganin mata wanda a zahiri ba abinda ya kamata ba kenan abu mafi
muhimmaci shine dauki yarki ki kaita asibiti ayi mata gwajin sanyi ayi mata hoton maranta idan
ta tsallake batada sanyi fine idan kuma akwai sanyi to aiki ya sameki ke uwa dole ne kiyi aiki da
hikima wajen nemawa yarki lfy domin kuwa indai da sanyi a jikinta ba namiji ba macema yar
uwarta bazatayi qima a gurinta ba"_

Numfashi Asmah taja cikin tsoro tace "munshiga uku sanyi kuma? Tab to muda ko ararrabi baa
jiqa manaba ya kenan?" Wawurar wayar tagumi
a kashe datar ta kira number Aunty Hajar ta daga tace “Aunty ki hau online oum hairan nayi
lecture akan ciwon sanyi a group din DOMINKI YAR GATA nifa kaina ya kulle" kashewa tayi ta
sake kunna datar ta rinqa bin bayanan a hankali tana nazarinsu tunawa tayi batayi sallah ba ta
miqe ta dauro alwala tayi sallah bata qara hawa ba saida tayi wanka tasa kayan baccinta ta
kulle part dinta ta haye gado taja bargo sannan ta kunna tanabin bayanan wanda bata ganeba
tana tambayar Aunty Hajar saboda anriga angama lectures din taji bayanai sosai har ta dauki
na aikatawa gobe da safe.





Washegari tun asuba data tashi bata koma ba ta gama gyaran part dinta ta sanya wasu yan
iskan riga da wando rigar airmles ce wandon three quarter ta bude cikin akwatunanta ta dauki
takalmi sawu ciki tasa ta hade gashinta tayi donnut dashi ta sauko daga saman da dan gudu
gudunta ta bude qofar ta fice ta nufi gurin training din gdan tana yan guje²nta da tsalle tsallenta
Aseem da ya dawo daga masallaci ya zauna a wani bangare na gurin ya zuba mata ido yana
kallon yanda take sarrafa jikinta kamar babu qashi abin yayi bala'in burgeshi baisan sanda ya
aje jaridar ya zubanta ido yana sauke ajiyar zuciya, dakatawa tayi tana duba agogonta tana
share gumi.
Bakwai saura juyawa tayi ta nufi part dinta ta sake wanka ta sake kaya ta dauko wayarta ta nufi
bangaren nasu bata tarar da kowa a parlour ba ta tabe baki ta fara hade kayan dake parloun
bayan ta gama ta dafansu tea ta zubansu a flast ta soyansu doya da qwai ta jere musu tayi
ficewarta tana fita suka fito qamshi ya cika gdan suka sauke ajiyar zuciya Mimee tace “wannan
yarinyar ta shigo ne?"
Kallon falon yayi yace “idan haka kikabar parlounki to qila bata shigo ba" tabe baki tayi ta zauna
a dinning din ta bude kayan abincin ta fara zubawa yayi murmushi yasakai ya fice a ya nufi
inda yake parking motarsa har ya bude zai shiga yaji kamar ana kallonsa ya dagakai sama

Asmah ya hango tsaye a corridor din samanta tana cilla teddy sama tana cafewa.





Jingina yayi jikin motar ya zubanta ido a fili yace “komanta shirme ne ita" qwafa yayi ya juya ya
shige motarsa ya tayar ya fice daga gdan tayi murmushi ta koma ciki tace “ nagama wannan
aikin" ita kanta ta gaji tana shiga bajewa tayi a gado ta kama bacci sai biyu ta tashi bata wani
damu ba ta miqe tayi wanka ta sanya rigarta iya gwiwa ta daure gashinta ta sakeshi tasa hular
rigar ta fito ta nufi part din na Mimee tana tafe da Bluetooth a kunnenta lkcn hudu harta gota
tana rangaji kamar itaciyar mangoro ta shiga part din na mimee tana jibge a kujera daganta
hannu tayi tace “Hi baby how per" bata jira amsar ba tace “sai hqr yau mijina yace na kwanta na
huta zai shigo da abinda zaaci....." Mgnr ce ta maqale lkcn da yake shigowa ta hadiye yawun
tsoro lkcn da suka hada ido qasa tayi da kanta tace “your are wlcm My qalb....." Kallon mimee
yayi da sauri itama shi take kallo Matsawa Asmah tayi kusa dashi ta karbi kayan hannunsa ta
Dora a center table tana tafe ne tana wani kadansa jiki ta sake juyowa ta wani kashe masa ido
cikin matsiyaciyar kwarkwasarta ta qarasa gabansa ta shige jikinsa tayi dage ta sauke masa
kiss a kuncinsa da yasashi rintse idonsa zuciyarsa na bugawa da qarfi.




Matsawa tayi ta fara bude ledojin kamar yasata yaja wata ajiyar zuciya ya zube a kujera wani
tsalle ta saki ta fada jikinsa ta sake saukensa hot kiss a lips dinsa harda wani zura harshenta
gabadaya yar banzar yarinyar ta kashe masa jiki ya kasa hassalawa kansa komai Mimee ta
hadiya har wuya kadan take jira ta fashe ta tsinkayo muryar Asmah tana cewa “ni nasani mijina
shine gwarzon mazan duniya bayamin alqawari ya saba inasonka har cikin ruhina......."



_Wannan group shine group din zarrah pls idan kinsan kina daya daga cikin groups dina kada ki
shiga ina post a kowanne group sannan idan kinsan bazaki comments ba kema karki shigo
yawwa don Allah yasani ban buqatar yan labe da yan tanks_





_Comments_
_Share_
_Vote_
_Please_

_*Oum Hairan*_

_*Zarrah*_




_*Fauziyyah Tasiu Umar*_



*ELEGANT ONLINE WTITERS*



_*27-28*_



Miqewa Asmah ta sakeyi ta nufi freegde harda dan gudunta na iskanci ta dauko lemo da ruwa
ta ajiye masa a side table din kusa dashi ta qara matso masa dashi ta nufi kitchen ta dauko cup
na glass ta dauki lemon ta tsiyaya masa ta miqa masa shiko maloho banda kallonta babu
abinda yakeyi, kashensa ido tayi tace “inason sanyaya zuciyar duk wanda ya sanyaya tawa
musamman ma kai mijina" sake miqa masa tayi ya karba ta juya tace “ni natafi na sake wanka"
ashar taji Mimee ta saki ta miqe tace “ashe kawai karuwa ka dauko mana wlh baku isa kuyimin
karuwancin nan a gdannan ba kutmar ubancan......"
Tabe baki Asmah tayi tayi ficewarta ta nufi part dinta tayi wanka tayi sallah ta dawo parlour ta
kshingide abinta ta dauki wayarta ta fara dannawa bayan Sallar Isha ta haye sama ta cire
kayanta tasa na bacci ta haye gado har bacci ya fara daukarta taji ana taba qofar miqewa tayi
da magagin bacci ta bude taja baya da sauri ganin fuskarsa babu annuri yasata shiga
hankalinta ya tako ya shigo dakin yana qare mata kallo tare da ajiye ledar hannunsa ya farabin
dakin da kallo bayan ya gama ya mayar da dubansa kanta ta wani rakuye jikin wadrobe har
yanzu fuskarsa a daure take ya taka gabanta batayi aune ba taji ya cafki kunnenta





Qara ta saki ya dora hannunsa a bakinta yace “karki kuskura ki sani ciwon kai dan ubanki ni
sa'anki ne da zaki rinqa yimin wannan iskancin da karuwancin naki?" Sunkuyar da kanta tayi

tana matsar hawaye ya saki kunnenta ta dauka sauqi ta samu kawai taji ya damqi gashinta da
qarfi ai batasan sanda ta saki qara ba ya sake toshenta baki ya hadata da bango ya matse ya
dago kanta da qarfi ya matse bakinta ta rinqa turjiyar qwacewa yaqi sakinta sai hawaye da
takeyi har saida yaga jan lips dinta ya tsage ya fara zubar da jini sannan ya saketa ya cillata
gadon yace “shashasha kawai kalleki kamar 1 kenan harji kike kin isa mace zakike hadani fada
da matata sabida makirci irin naku na yayan matsiyata idan suka samu guri" numfashi ya sauke
yace “kuma duk ranar da kika qara yimin abinda kikayimin yau wlh saikin gane kurenki saina
goge miki hadda zaki gane ni ba abokin wasanki bane idan kinsan bazakiyi aikin dana baki ba
saina canza miki tunda kin zama yar iska"
Zama tayi a gurin da take tsaye ta Dora hannu akanta ta rusa wani ihu yaja baya da sauri tare
da dakanta tsawa yace “kewai mahaukaciyace ne?" Miqewa tayi baya tace “eh din ina ruwanka
dani kuma bazaa daina aikinba aiba donkai nakeyi ba kasan badan tsoronka nakeyi ba arziqin
uwata da kake tsiyatawa kakeci banda haka kai ka isa nayi maka biyayya man....."



Cafka yakai mata ta qwace da sauri ta fada bandaki ta datse tace “bakin nakama da babu zaqi
yawun naka qarni yakeyi ko sweet bakasha kuma ka ficemin daga dakina kazo kallon bulus to
yaro garama ka tafi kafin nayi maka Ehun kwarto" Takaici ne yasashi murmushi wato tunda
yake baitaba ganin mutumin da yakeci masa mutunci ido biyu irin Asmah ba bata tsoronsa ko
kadan wai yawunsa qarni😅
Wani takaici ne yasashi juyawa ya fice ya rufenta qofar da qarfi ta sauke ajiyar zuciya ta bude
bathroom din ta leqo ganin bayanan yasata fitowa ta murdawa qofar key da sauri ta tsaya jikin
qofar tana mayar da numfashi har yanzu kuka takeyi tana baqin cikin zagin cin mutuncin da
yakewa iyayenta da tanada iko da tace ya dena amma tasan nuna masa damuwarta ma qara
ingizashi zatayi kukanta tasha sosai ta share hawayenta ta sake watsa ruwa ta kwanta baccinta
tayi me dadi batabi takan ledar da ya ajiye ba saida asuba da taji yunwa ta isheta ashe ganima
ya kawo mata tayi murmushi ta miqe ta nufi kitchen ta dumama naman taci tayi hani'an ta kora
da lemonta me sanyi ta sanya hijjab dinta ta fice saida taje training space din sannan ta cire
hijjab din ta rataye jikin ragan qwallo ta fara motsa jikinta duk abinda takeyi Aseem na sama
jikin window na dakinsa yana kallonta ya kasa dauke idonsa akanta komanta baisan meye yasa
baya gajiya da kallonta ba ajiyar zuciya yayi lkcn da yaga ta miqe ta dauki hijjab dinta tasa ta
nufo part din nasu komawa yayi ya kwanta kasancewar yau bazai fita ba sai yamma miqewa
yayi ya sake leqawa yaga bata a gurin yasan ta shigo yayi murmushi ya bude qofar ya fita dakin
Mimee ya bude ya shiga ya zubanta ido tana kwance saman gado tanata baccinta cikin
kwanciyar hankali.




Rufe mata qofar yayi ya juya ya sauka qasan ya zauna a dinning din yanajin qamshin girkin
nata ya cika gdan yaja fasali qamshin gwanin dadi ya miqe ya nufi kitchen din ya tsaya jikin qofa

ya zuba mata ido ta cire hijjab din taci dammara dashi tanata suyar dankalin turawa kunnenta
Manne da bluetooth tanabin waqar qwanja ta Mamar tana rawa abinta zame masa kamar TV
tayi ita ko nauyin jikinta bataji koda yake ba jikinne da itaba dama uban hips ne da duwaiwaka
kawai ke janta, Dif ta dauke wuta saboda wani baqon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login