Showing 6001 words to 9000 words out of 54507 words
Chapter 3 - ZARRAH BOOK COMPLETE BY OUM HAIRAN .pdf
Zahran yace “Kamar yanda ka fada Sunanta
Asma'u Hussain Babanta Mal Hussain talaka ne na qarshe domin kuwa tunda ya taso aikinsa
Bai wucce dako da faskare ba mahaifiyarta Amina itace babbar Matar Mal Husaini sai sauran
matan babanta su biyu Lamunde da Lantana su Hudune Yaya a gidansu Mudansir sai Zabba'u
sai Dijangala sai ita qarama Asma'u wadda ake Kira da Ma'un Inna ko ace Ma'un Sadiqu autace
a gdansu duk da kasancewar uwarta ba komai bace a gdan Amma hakan bai hanata samun
gata daidai na talaka ba duk da kasancewar Babu abin sisi da Mal Husain yakewa yaran saidai
suyi sana'a da iyayensu suyiwa kansu ita Inna da kake ji macece me qoqari gaya akan yayanta
tayi qosai tayi aikatau gdan masu kudi tayi surfe tayi dakau sannan tayi wankau zamanin
tanada idanunta har abincin siyarwa tayi duk da tanada ya mace Bata Dora Asma'u talla saidai
Mudan da ita su dauka suje su siyar a bakin kasuwa a cewarta ita ya mace kadara ce me tsada
Kuma abar farauta ce idan kayi wasarairai da ita kamar dawisu take inda yafi yalwal bishiyoyi
da Ni'ima nan take fakewa tace zatayi rayuwa a cikinsa idan akayi rashin saa sai asamu
mafarauta su kameta shikenan rayuwarta ta lalace:
Yarinya ce me qwazo tun tana qarama hakan yasa uwarta taci burin sai tayi karatu me zurfi lkcn
da aka makantar da Inna lkcn Asma'u ta gama primary daganan abubuwa sukayita lalacewa
dan abinda ake fita a Nemo na rainawa babu halin fita a nemoshi Nan suka shiga Ni yasu
abinda zasuci ma yakan gagaresu akwai wani yaro Sadiqu da tun tasowar Asma'u yakeyi Mata
wahala shine rakata makaranta shine komanta saiya zamana idan yasai da rake ko ya dauki
tallan yalon bello yaje ya siyar ne yake samu yabasu abinda zasuci.
Ana hakane wata Ladi almajira tayiwa Inna tayin fita bara tunda dai Allah yasani batada
mataimaki da farko Inna taqi abin Amma lkcn da Asma'u ta farayi mata mitar duk qawayenta
sun tafi makarantar secondary ita tana gda saita farabin Ladi bara suna samo na batarwa a
hakadai har suka Tara kudin makarantar lkcn har anci zango daya suka kaita Prime school dake
Inna tun dacan Bata yarda yaranta sunyi makarantar gwamnati ba tace Babu karatu ita Kuma
so take yaranta suyi karatu, daga lkcn da Asma'u ta fara zama budurwa saiya kasance idan
sunje neman taimako mutanenmu sai suka fara nuna maitarsu akan yarinyar itakuma uwar tana
nuna Mata aibin hakan musamman dake Asma'u tana zuwa islamiyyar dare, matsalar Asma'u
daya ita tun tana qarama batada hqr Kuma Bata yafiya indai kayi Mata saita rama so da mutane
suka fara gwada rashin imaninsu akan mahaifiyarta sai ta dauki gabarar duk Wanda yayi Mata
ko waye a duniya saitayi Masa kalmarta daya itace “ka jira ZARRAH ta ranar da zan zama
babbar likita zanyi fada da uban kowa a duniya Kuma zan nuna maka kaiba komai bane" yanzu
haka zancen da nakeyi maka burinta na gab da cika domin kuwa takusa kammala secondary
Wanda Innarta tafi shekara biyar tana adashin gata domin Asma'u ta wucce makarantar da
zatayi karatunta na likitanci"
Murmushi Dr Aseem yayi yace “aikinka yana kyau Kuma meye yanayin ubanta da kudi sannan
a wacce unguwa suke zaune?" Jinjina Kai Zahran yayi yace “wanda yayimin bayanin tarihinsu
yace kirarin mahaifinta Mal Husaini idon cin naira indai kanada kudi to kanada cikakken
mutumci a gurinsa idan kuwa baka dashi to kashinsa yafika daraja anan Tukuntawa gdansu
yake shikuma babanta a sabuwar gandu majalissarsu take gefen rumfar wani me nama suna
zaune idan ansiya suyi sudi aikinsu kenan"
Jinjina Kai Aseem yayi yace “ka gama magana inason kwadayayyen mutum saboda buri yana
saurin cika Asmah ki jirayi zuwana burinki bazai taba cikaba zan rusanki duk wata walwala da
farin ciki zaki rayu da qunci zan massheki baiwa a gdana saikin lashe tafin qafata da
harshenki...... Dafashi Zahran yayi yace “tabani haushi dazu Amma da naji tarihinta sai tabani
tausayi please ka hqr da daukar fansar nan kabarta don Allah akwai quruciya yarinya ce
qarama fah....." Hannu ya Dora Masa a baki yace “karka qara bani hqr wlh bantaba tausayin
wani Abu kamar yanda na tausayawa yarinyar nan ba Amma hakan bazai hanani daukar mataki
akanta ba saita Raina kanta Kuma sai tasan tasa Wasa da Aseem Shaheed"...........
Vote
Comments
Share
*_Oum Hairan_*
[20/06 4:27 pm] Oum Hairan: *ZARRAH*
_Tare da Alƙalamin_
*_Oum Hairan_*
_Bismillahir Rahamanir Rahim_
_Free Page 9-10_
*_Wattpad realfauzahtasiu_*
   Telegram
Â Â Â Â Â Â í ½í±‡
https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7
_____________________________
_____________________________
Tunda Asma'u ta koma gida take zumbure zumbure Matan gdan Babu Wanda ya kulata Inna
kuwa ba ido ba balle tasan matsalar yartata haka tayi wanka tayi sallar azahar da La'asar ta
zauna tsince wake bayan ta gama ta dora musu abinci tana girkin tana qunquni da haka ta
gama ta zuba ta zauna tanaci bayan ta gama ta shirya ta tafi islamiyya sai shidda ta dawo lkcn
uniform dinta ya jiqu ta wankeshi ta shanya sai lkcn ta jirge ta zauna tana bawa Inna lbrn abinda
ya faru.
Sosai Inna ta nuna rashin jin dadinta da abinda yartata tayiwa Aseem tare da rufeta da fada
daga baya ta dawo yimata nasiha to ta danji a lkcn ta miqe tayi sallah ta kwanta, washegari da
wuri ta fice saboda so takeyi yau suje makarantar da wuri cikin saa ta tarar da Jidda ta shirya
suka tafi suna tafe suna Hira Jidda tace. “Nifa jiya kin kullemin Kai Asma'u waike bakida tsoro ne baki tsoron kada mutumin nan ya
sanya yan sanda su kamaki?" Tsaki tayi tace “kuma saboda Ina tsoro saina bari yaci mutumcina
na qyaleshi ko?"
Kada Kai Jiddah tayi tana Shirin yin magana wata mota tazo ta giftasu kawai sai sukaga taci
burki a gabansu hankalin Asma baa kan motar yake ba har zasu gifta taji Jidda tace “mun shiga
uku Asma'u mutumin jiya ne fah" da sauri ta kalli gurin suka hada ido ta galla masa harara ta
qarawa tafiyarta sauri saboda Inna tace idan ta sake kulashi sai taci mutuncinta. Murmushi yayi cike dajin tsanar yarinyar a qasan zuciyarsa yaja motarsa ya qara gaba ta
gefenta ya wucce shuuu taja fasali tace “kaci arziqin Inna ta hanani kulaka wlh yauma dasai
nayi maka rotse sakarai Wawa"
Duk da Aseem baiji abinda ta fada ba Amma ya fahimci dashi take murmushi yayi ya qara bawa
motarsa wuta tabbas sai yayi maganin rashin kunyar yarinyar nan da take ganinta daidai dashi
saiyabi ta kowacce hanya yaga ya koya Mata hankali saiya sanya Mata jin cewa Ashe ita ba
kowa bace a rayuwarta tunaninsa yanzu ta inda zai fara gudanar da aikinsa kisan mummuqe
yakeson yimata batare da wani ya gane qudurinsa ba yakeso ya baje tarihin rashin kunyar
Asma'u,
Yana tuqi yana murmushi Yana maimata sunanta yanayin yanda ta harareshi dazun yana Masa
gizo yanajin wani nishadi da Allah yasa yarinyar ta siyar Masa da qasar wasan dole akwai
badaqala zai ganar da ita kurenta na shiga sharafin daba nataba. Koda yaje asibitin ya fara
duba marasa lfyrsa bayan ya gama ya wucce nasa private hospital nanma yayi abinda zaiyi
sannan ya shige office dinsa ya zauna yana juyi a kujerarsa cike da zumudin ganin yamma tayi
Zahran ya gama aikinsa ya daukeshi suje su nemi mahaifin Asma'u kamar yanda ya tsara
kafinnan Saida ya sake tura wani yaronsa yayi masa binciken tsaf inda anan ne yaron nasa
Uzairu yake sanar dashi ai Mal Husaini yasa gdansa a kasuwa zaiyi auren yaransa uku sukuma
iyayen zasu koma qauye da zama wacce bazataba Kuma tasan inda dare yayi mata.
Fiye da tunani Aseem yaji dadin wannan farin lbr aikuwa hudu da rabi suka fice daga asibitin
suka nufi bakin kasuwar sabuwar gandu inda anan Mal Husaini yake zama Nan suka nemi a
rakasu ofishin dillalan qasa akayi musu jagora sukaje suka gaisa Zahran yana nunawa Aseem
Mal Husaini da yaketa maka hamma da hularsa ko Kari Babu bisa dukkan alamu yunwa yakeji. Caraf kuwa Alh Bala dillali yace “Idon cin naira da alamun dai yau baa sammaka abin sawa a
maqoshi ba ka fito" kamar me jiran kadan ya balle zance kamar Wanda ya qone a tsakiyar ka
cewa yake “yo dama wadannan sakarkarun waye yanzu yake sammin abincin Lantana da
Lamunde sunce sun daina cida qato Wai auren yayansu zasuyi Amina ce me tausayina take
bane to itanma saidai idan wannan ja'irar yarinyar Ma'u batanan amma fir take hanawa tace ai
ba Basu nakeyi ba kuma tana ganin lkcn da nake bawa Lamunde nikuma ganin suna fita bara
nasan na annabi baya qarewa shiyasa bandamu da sammusu ba gashi anma kasa samun me
siyan kangon can nawa bare na Dan murmure kafin bikin nan"
Jinjina Kai Aseem yayi Bala dillali ya dubesu yace “Alh Allah gida ko fili ko kango ko haya ake
buqata?" Cire hularsa yayi ya maida hankalinsa ga Zahran Zahran ya gyara zama ya karkace
yace “gda muke buqata ginin gargajiya anan Tukuntawa zamu zuba shanu da tumaki a ciki...."
Yunqurowa Mal Husaini yayi Mal Bala ya dakatar dashi yace “toh ikon Allah kamar Kuma na
nawa kuke buqata?" Kallon Aseem Zahran yayi Aseem da sai yanzu yaga samar mgn yace “ba
qarami ba ba babba ba duk yanda kasuwa ta Kama munaso idan akwai a nuna Mana abune na
urgent da muke buqatarsa tsakanin yau da sati biyu" duba Mal Bala yakai ga Mal Husaini da
dama yake jiran abashi dama nan yayi kwance kwance yace “yo Alh Allah muje suga nawa
Mana ko Allah zaisa a daidaita tunda qananun masu kudi sun kasa siye sunce zaici kudi wajen
gyaransa
Tunda ya fara mgnr Aseem ya zuba Masa ido har ya gama murmushi Aseem yayi Wanda
shikadai yasan dalilin murmushin nasa yace “ok muje mu gani idan yayi sai muyi ciniki Amma
gsky muna buqatar gurin da wuri zamuyi aiki a ciki ne" Babu tunanin makomar iyalai Mal
Husaini yace “Haba yaro abinda yake kasuwa ai ko yau kakeson abinka baka akayi indai ka
biya nidai fatana Allah yasa gurin yayi maka fitinar zabba'u ta isheni yau ta debo wannan gobe
ta kwaso wancan gara na auraddasu kawai na huta sauran kudin naci tsire dasu hhhh koba
hakaba yaro..."
Sudai murmushi kawai sukayi suka nufi motar Mal Bala da Mal Husaini suka shiga baya Aseem
da Zahran suna gaba a haka Mal Husaini yaketa basu kwatance suna amsawa har suka shiga
unguwar tun daga farkonta suka fara Raina kansu asalin uguwar talakawa ce ko Ina kwatami ne
yake gudu haka sukayita kutsawa lunguna har suka isa qofar wani tsohon gda ginin jar qasa
dako arziqin yabe bai samu ba babu qofa a gidan sai labulan tampol da aka sanya domin
sakaye gdan, tundaga qofar gdan Aseem ya qara Raina matsayin Asma'u tare da tsananin
mamakin izzarta a matsayinta na wadda ta taso a wannan rubabbiyar unguwa a unguwar ma a
gda mafi qasqanci domin shidai iyakar dubansa baiga gdan da yakai nasu Asma'u lalacewa ba
a area.
Mal Husaini ne ya shiga ciki ya sanar da matansa cewa zaa shigo ganin gda me tankade ta
tashi me dakama ta miqe sukayi daki Inna ce dama tana daki a zaune tana lazumi shigowa
sukayi suna duba gdan a zahirin gdan Babu uwar da Aseem zaiyi dashi Amma da suka gama
dubawa sai ya dubi Zahran yace masa “ina ganin kamar gurin zaiyi ai ko?" Sarai Zahran yasan
me yake nufi shikuma sai yace “dadai an nemi Wanda yafi wannan gsky shanun zasu takura"
dafashi yayi yace “kada ka damu fashe dakunan zaayi daki biyun nan kawai zaa bari saboda
me gadi da abincin dabbobi" da wannan suka juya zasu fita suna Shirin fita kyawawan
yammatan na sawo Kai Dijangala ce a gaba sai Zabba'u ita kuwa gwanar ta cake a qofar gda
Laila sarkin soyayya ita da Sadiqun ta suna bawa fure ruwa ai suna fitowa tana dago Kai suka
hada ido ba itaba shima Saida yaji gabansa ya fadi ya kasa dauke ido daga kanta dake dariya
takeyi yanzun sabanin duk haduwar da sukeyi dashi yau saiyaga tayi wani haske tayi kyau
kyawawan haqoranta ya zubawa ido da akayi musu kwalliya da siririyar wushirya.
Ganin fitowarsu daga gdansu yasata saurin tsuke fuska kamar ba itace take dariya ba ta kawar
dakai daga kallon da sukewa juna ita da Aseem din, sosai Sadiqu ya lura da sauyin nata don
haka ya dubeta.
Yace “ya akayine jarumar Mata?" Ajiyar numfashi tayi tace “meye ya kawoshi gdanmu?" Da
rashin fahimta yace “wafa?" Duban Aseem tayi da ya juya baya jikin motarsa yana waya tace
“wancan Mara mutumcin Mana shine fah mutumin da nake baka lbrn na fashewa qafa ko qarata
ya kawo gda gurin Mal tab aikuwa zan daku shikuma zai ragargazu Dan wlh hayar tantiran
hayin qwari zanyi su rugurgujeshi.
Dariya Sadiqu yakeyi Mata domin ya lura gabadayanta a tsorace take tsinkayo muryar Mal tayi
Yana qwala Mata Kira “Ma'ulele ke Ma'u bakijina ne bakiga mutane ba dan qaniyarki irin
tarbiyyar da gyatumarki tayi Miki kenan?" Sumsum ta nufi gurinsu duk a razane take a rusuna
tace “ina yininku" Zahran ne da Mal Bala suka amsa shikuwa gogan kallonta kawai yakeyi Mal
Bala yace “Mal nayi nayi dakai ka bani daya cikin yammatannan naka kaqi da tuni baba nakece
maka ga Ma'u ma ta girma abinta" tsuke fuska Mal Husaini yayi yace “yo Banda abinka yaro ai
sai yaro kaga wancan kafirin yaron da qaton Kai shine ya zamemin alaqaqai nayi nayi na
rabasu sunqi rabuwa harma na hqr basa zanyi suje su qarata"
Dagowa Aseem yayi yace “wai itama wannan din taka ce Baba?" Murmushi yayi yana sosa
qeya yace “wlh kagansu Nan kamar yar maraqan shanu haka akayita jeramin su harsu uku
gasunan kansu daya ita wannan itace qaramarsu shekararta sha shidda sabodasu nema zan
sayar da gdannan" Jinjina Kai yayi cikin jin dadi yana hango nasara yace “a aikuwa ba ayi haka
ba kasai da gda baba kaida kake da Yaya Mata kabar gdanka kawai" da sauri ya dubeshi yace
“inbar gda fah kace Alh waye zaiyimin auren yayan?" Murmushi Aseem yayi ya bude motarsa
ya bude dashboard ya dauka raffers ta dari biyar biyar guda biyu ya bashi yace “karka damu
baba ka riqe wannan gobe insha Allahu zan dawo ai kamarka kanada wadannan kyawawan
yammatan ba abarka ka tozarta ba" sake miqa Masa wata reffer yayi yace a rabawa matan
gdan wannan anan suka qyale Mal Husaini sake da baki da kudi a hannunsa suka dauki Mal
Bala suka tafi a mota Aseem ya dubi Mal Bala yace “yarinyar nan data gaishemu ta fanshi
mahaifinta indai zai bani auranta na rantse zanyi Masa komai da yake buqata na hidimar
aurensu tun daga satin farko har ranar da zaa gama biki ka sameshi ka fada Masa idan ya
amince har gdanma zan gyara Masa"..........
[20/06 4:27 pm] Oum Hairan: *ZARRAH*
_Tare da Alƙalamin_
*_Oum Hairan_*
_Bismillahir Rahamanir Rahim_
_Free Page 11-12_
*_Wattpad realfauzahtasiu_*
   Telegram
Â Â Â Â Â Â í ½í±‡
https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7
______________________________
______________________________
Tunda suka tafi sukabar Asma'u da sakakken baki kallon da Aseem yakeyi Mata ita da Sadiqu
shine yafi Bata mamaki da Kuma dalilin zuwansu gdansu ganin ya damqawa Mal Husaini
kudine yasata sake maida hankalinsu garesu amma sai taga ya dubeta yayi murmushi yaja
motarsa sunbar Mal da kallon kudi cikin mamaki. Mal Husaini na dagowa suka hada ido da Asma'u yayi saurin sanya kudin cikin hularsa tare da
watsa Mata daquwa tayi saurin kawar dakai sukaci gaba da tsinkar furensu ita da Sadiqun ta
Saida aka Kira magariba sukayi sallama ya nufi masallaci ita Kuma ta shiga gda ta dauki buta ta
shige bayi ta Kama ruwa ta fito ta daura alwala daidai lkcn da taji Mal Husaini na cewa “ni Babu
ruwana da inda Zaki Amina gdane saidashi zanyi dole kowacce ta nemi inda zata zauna kafin
ayi bikin yarannan ku koma qauye ba Saida nace kada ku kuskura ku haifi Mata ba ku masu
kunne qashi kuka haifesu ai gashinan basu kawo kudi ba sun kwamushe muku naku" cafkar
kunnen Asma'u yayi yace “ja'ira da kanta tunna zuwa duniya saura naji kince wani Abu baki
kamar gdan tsutsa tana tafe kamar allura" itadai tana samu ya sakar Mata kunne sumsum ta
shige daki ta tayar da sallah tare da jan bakinta ta tsuke Abu daya ta iya tambaya shine meye
ya kawo baqin gdansu? Inna tace Mata. Masu siyan gdansu ne daga haka tayi shiru da bakinta
saboda batason subutar baki tasa tayi wata magana don Bata kuskura ta fadawa Inna tsiyar da
tayiwa Aseem Shaheed ba.
Kwana Asma tayi tana tunanin dalilin da yasa Aseem yakeson siyan gdansu, a daren taci
alwashin indai Allah ya hadasu gobe a hanyar makaranta sai taci mutuncinsa yanda zaiji bama
ya sha'awar siyan gdan nasu, aikuwa tun asuba ta shirya taja ta zauna tana jiran lkc bakwai
daidai ta fice daga gdansu ta nufi gdansu Jiddah suka dunguma suka tafi tana bawa jiddah
labarin abinda ya faru jiya na zuwan Aseem gdansu a matsayin Wanda zaisai gdan zaiyi kiwon
shanu"
Dariya sosai Jiddah tayi tace “kin gamu da qarfen qafa me wuyar kwancewa wato gayen nan ya
shiryawa wasan so yake ya qure malejinki ya wulaqantaki Kinga idan ya siye gdanku ko haya
ya baku ai babanku ya koma qarqashinsa balle ma tashinku zaiyi a wulaqance ya zuba shanu a
gdan Kinga ya nuna Miki rayuwar shanunsa tafi taku muhimmanci. Nifa dama bangano Miki
nasara a buga wasa da wannan mutumin ba da ganinsa kinsan yaci yatada Kai zai iya ramawa
wulaqancin da zakiyi Masa ta duk inda yaso gara dai yan gujaru gujarun da muke tsokana