Showing 3001 words to 6000 words out of 54507 words
Chapter 2 - ZARRAH BOOK COMPLETE BY OUM HAIRAN .pdf
“kefa wani
lkcn farar kura ce me suka Isa suyi Mana basai mu gudu ba mu jasu har area mu hadasu dasu
Sadiqu suci ubansu" Shiru tayi tana nazarin kalamanta kafin ta dago tace “nidai Babu ruwana
bazanje garin goge musu hadda su su gogemin tawa ba" dariya Jidda tayi tace “bansan yaushe
kika zama matsoraciya ba wlh Ma'u Allah ya shiryeki" bata Kuma cewa komai ba har suka koma
aji Basu suka tashi a makaranta ba sai uku Wanda a qa'ida biyu suke tashi wani mugun
malaminsu ne yabasu assignment me wahala shine suka bata lkc haka gashi yace a lkcn
yakeso dukkan fuskokin daluban daka gansu kasan sun jigata da yunwa musamma Ma'u da
batayi karyawar kirki ba gashi babu kudin break sun riga kowa something suka fito duk ta
galabaita suka nufi get megadi ya Kuma taresu akan cewa principal tace kada su fita da daidai
su bari su tashi gabadaya,
Neman guri sukayi suka zauna kawai Jidda taga qawar tata na kuka Asma'u babu juriyar yunwa
ko kadan tasan dalilin kukan don haka ta miqe da sauri ta nufi shagon me gadi ta siyo musu
biscuits pure blues dan saba'in ta siyo musu lemo jarka daya sukaci Saida sukaji dama dama
asmai ta dubeta tace “dama kinada kudi shine kikaqi ki siya Mana break?" Harararta Jiddah tayi
tace “wanne kudi ke gareni kudin motarmu ne naga zaki mushe na taimaka na siyo Mana muka
taba Kinga malama an gama fitowa kawai miqe mu yanki burtali"
Takaici ne ya hana Asma'u magana saboda tana cika magana zuciyarta fadowa zatayi haka
suka rinqa dabawa a qafa gashi da nisa tsakanin unguwarsu da makarantar sosai suna tafe
Jiddah nayi Mata hirar tura haushi taqi kulata sunzo daidai wani guri da ruwa yake taruwa
kawai basuyi aune ba sukaji ruwan dagwalon kwata ya fallatso musu ya bata musu jiki
musamman Asma'u da ruwan yafi batawa ta sunkuyar dakai ta kalli kanta tun daga sama har
qasa ta dago kanta ta sauke akan motar da aka tayar ana Shirin tafiya zuciyarta na azalzala
taga me motar yaja zai qara gaba ai batayi wata wata ba ta dauki wani dutse qato dake gefensu
ta jefi motar akwaita da mahaukacin saiti kuwa ji kake taratsatsa glass din bayan 4matic din ya
tarwatse hakan yasa me motar cin uban birki a fusace na kujerar me zaman banza ne ya fara
fitowa daidai lkcn data nufo gurin itama tana fadin “ba iyanan naso ya tsaya ba sonayi ya ishe
kan daqiqin dakejan motar yayi masa Ramin da jini zai hade da qwaqwalwar shege muga ta
gadara da dagawa...." Sauke tafin hannunta tayi a fuskarta jin shu'umin Marin da aka dauketa
dashi ta Jima dafe da kuncinta kafin tayi qarfin halin dagowa tana tuna Marin da Aseem
Shaheed yayi Mata jiya kwatankwacin azabar da taji kenan aikuwa tabbas saita rama wannan
koma uban waye ya daga hannu ya Mari fuskarta me daraja,
Idanunta ta rintse ta dage ta daukeshi da Marin da shima Saida ya dafe gurin kafin ya dago ta
sake sauke Masa wani ta daga hannu zatayi na uku Wanda ya fara fitowar ya riqe hannunta da
sauri jikinta na bari ta bude idonta daidai lkcn da Dr Aseem ya bude nasa shima tar a kanta
lebensa datse da haqoransa ya saita injin idonsa akanta tare da sanya hannunsa ya zame
hannun Zahran daga nata ya riqe na yan sakonni sannan ya saki Yana qara kallonta itama shi
take kallo cike da mamaki da Kuma tsana.
Kafin yayi mgn tayi da cewa “au dama Kaine shaidanin daya batamin uniform dina lusari kawai
kagani dai kaga irin aikina dama Saida na fada maka zamu sake haduwa gashi kuwa mun hadu
ko banza zuciyata ta dan sauka daga radadin
Daka Bata sauna kawai ka dauka ana tabani aci bulus ne jiya kaci mutumcin mahaifiyata da tafi
taka uwar don alamu sun nuna kaikam taka jefar dakai tayi wata me tsautsayin ta tsinta.
Sannan yauma ka batani da ruwan kwata Kuma kayi tunanin wuccewa salin alin haba yaro kayi
kadan ka taba ma'un Sadiqu ma'un Inna ka zauna lfy gashinan kayi ta glass din motarka Kuma
dole aje akaiwa me gyara yaci kudi nidai nasan ko kaina ka siyar bazai gyara maka ba......
Tana maganar tana qasa qasa da hannunta ta sake daukan wani dutsen me nauyi tayi kamar
zata wucce kawai ta sakar masa a babban yatsansa yakuwa yi qasa da sauri tare da sakin
wata siririyar qara kafin Zahran ya Ankara ma'u takai a dari da sittin ba Zahran ba hatta Aseem
da jini yake ambaliya a qafarsa Saida ya dago ya dubeta lkcn da take cewa su Corona virus aje
ayi treating kafin mu sake haduwa na daujeta Wawa da kace bakaji.........
Vote
Comments
Share
*_Oum Hairan_*
[20/06 4:27 pm] Oum Hairan: *ZARRAH*
_Tare da Alƙalamin_
*_Oum Hairan_*
_Bismillahir Rahamanur Rahim_
_Page 1-2_
*_Wattpad-realfauzahtasiu_*
*_Telegram Link_*
https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7
____________________________
____________________________
_Farkon labari_
_1/3/2007_
Harabar gdan attajirin cike yake da mabarata maza da Mata yara da manya kowannensu yayi
jungum jumgum Yana tsumayin fitowar Alhaji Qasim Wanda ya kasance shine mamallakin gdan
Wanda ya kasance baya goya marayu jarumi Kuma adali me taimako da taimakon Allah da'ira
da'ira almajiran sukayi kowa yana tattaunawa da abokin shawararsa inda a can nesa kadan da
mutanen na hangi wata dattijuwar makauniya da wata yar kyakkyawar budurwa da shekarunta
bazasu haura 17 ba sanye take da hijjab ruwan qasa Wanda dadewa da kodewa tasashi dole
ya koma toka toka rigarta da zaninta ma gambal habaru ne ma'ana wari da wari tanada
matsakaicin tsayi duk da kasancewarta a jigace Kuma a wahalce kallo daya zakayi Mata kasan
alamu sun nuna tana tsananin ji da wannan mahaifiya tata fiye da tunanin Mai tunani.
Ba fara bace kallon farko zakace Mata baqa saboda dauda da rashin samun nutsuwar kula da
Kai saidai idan ka qura Mata ido zaka gano cewa ba baqar bace kamar yanda idanu ya nuna a
farko saboda roɗi roɗin hasken da zakake hangowa ta wasu bangarori na jikinta, tana da fasali
da diri na bam mamaki Wanda a qananun shekarunta zakayi al'ajabin qirar da ilahi qadiran ala
mayyasha'u yayi Mata so dake lamarin Allah yafi gaban misali da mamaki dole ka aje tunaninka
ka Kama abinda ke gabanka.
“Asma'u! Asma'u!! key Asma'u!!! Tunanin me kikeyi ne dalla malama tun dazu Alh sai miqa Miki
kudi yakeyi...." Abinda ya dawo da ita hayyacinta kenan ta durqusa har qasa ta karba ta bude
baki cikin siririyar muryarta tace “mun gode baya goya marayu Allah ya tsare gabanka da
bayanka ya hana maqiyanka ganinka sai bayan ka wucce Allah ya tare maka zafin hassadar
maqiya da mahassada ta koma kansu....." hakanan ta rinqa jero addu'ar kamar yanda takanji
Ummah tanayiwa duk wanda yayi musu ihsani.
Dadin addu'ar da Alh Qasim yaji tasashi qara zarar naira dubu goma ya sake miqa Mata kawai
saita fashe da kuka bayan ta karba tayi masa godiya da fatan alkhairi, ya wucce ita Kuma ta
dugungune kudaden ta tura a bra dinta ta Kama hannun Ummah tace “Ummah yau Allah ya
dubemu ya amsa addu'ar ki ta jiya ya kawo Mana dauki dama tunda muka fito nake tunanin
idan bamu samu sadakar Nan ba yau Ina muka Kama bamuda abinda zamuci ko na garin
kwakin yau babu gashi gobe ance kar naje makaranta idan ban kawo kudin tearm ba, nikam
Ummah badon kince na daina roqonki ba da sai nace kiyi hqr ki mayar dani makarantar
gwabnati tunda na samu horon farko a ta kudin Ummah kudin sunyi yawa 14 thausand per team
gashi babu mataimaki a gareki sai Allah da bayinsa zababbu...."
Lalubo bakin yar tata tayi tace “Asma'u komai kikaga ya faru da sanin Allah kada ki damu ba
wayonmu ko dabararmu ke rayamu ba burina ko bana raye kiyi karatun bokon nan me zurfi
kema kamar yanda kikekan na addini Asma'u burina ki zama likitan ciwona saboda na fara
gajiya da wulaqancin da likitawa sukeyi Mana duk lkcn da ciwona ya tashi muka rasa mataimaki
Asmah bani da tabbacin amfanar karatunki Amma inaso ki amfanar da al'ummah don Allah
kada rudin duniya yasa kema kibi wancan sahun kinji?"
Jinjina Kai tayi cikin qoqarin sanyawa kanta dakiya da juriya nason cikawa mahaifiyarta burin
data rayu dashi taqici taqi sha dominta ita kadai ta hana kanta sukuni dominta, da wannan
tunanin ta Kama hannun Ummah ta miqar da ita suka fara fita daga harabar gdan suna tafe
suna taba yar hirarsu tsakanin gdansu da gdan Alh Qasim tafiyace miqaqqa Amma haka
ummah tace su tafi a qafa kawai don tsoron kada tayiwa kudin makarantar yar tata gibi ta shiga
wani yanayi suna tafe suna Hira har sukaci Rabin tafiyar sannan suka tsaya saboda nishin da
Asma'u taji mahaifiyar ta ta fara ta riqota da sauri ta zauna ta kwantar da ita a jikinta tace
“Ummah kingani ko abinda nake gudu kenan shiyasa nace mu hau dan sahu naira dari zasu
kaimu kikaqi....."
Mgnr ce ta maqale cikin tashin hankali ta rinqa jijjigata tana Kiran sunanta Amma Ina ta Suma
nan fah Asma ta dora hannu aka ta kurma ihu tana cewa wayyoh Jama'a a taimakeni Ummana
zata mutu don Allah kada ki bari ta mut...." Nandanan saiga mutane sun taru a gurin masu fifita
nayi masu surutu nayi, itakuwa titi ta bazama ta fara tsayar da motoci da yawansu basa
tsayawa wata mota tazo zata wucce tayi tsalle ta dira gabanta tare da rintse idonta take me
motar yaci wani uban birki ji kake qiyyyyyy, abinda yaja hankalin kowa dake gurin kenan suka
juyo domin ganin meye yake faruwa Asma da take tunanin ba a wannan duniyar take ba ta
bude idonta daidai lkcn da taji an dauketa da wani gigitaccen mari daya sanyata durqushewa a
qasa yace “banza mahaukaya zakizo kijamin masifa a banza......" Riqe qafarsa tayi da sauri
tace “don girman Allah kada ka tafi ka taimakamin kada Ummah na ta mutu a titi kakaimu
asibiti....." Dagota yayi kamar abin arziki ya qare Mata kallo sannan yayi watsi da ita tare da jan
tsaki ya nufi inda Ummah take kwance ya leqa,
Tunaninta ya gama bata taimakonta zaiyi taga ya nuna Umman da yatsa yace “dama akan
wannan tsumman kikeson kiyi asarar taki rayuwar sakarya kawai to meye yayiwa wannan
yamusasshiyar tsohuwar saura ai bazata warke ba qarama ki lallaba taki rayuwar qila tayi Miki
amfani a gaba farin magi duk ya kashe tsohuwa" durqushewa ta kumayi a qasa tana qoqarin
yimasa magiya ya fincike qafarsa yace “stupid girl banida lkcn batawa akan wannan gawar...."
Da wannan kalmar ya fada motarsa ta miqe tana me binsa da kallo tare da Jinjina Kai daidai
lkcn Allah yakawo wani dan sahu wani mutum ya tareshi suka tarairayi Ummah suka sakata a
ciki suka nufi Asibiti mafi kusa dasu da niyyar abata taimakon gaggawa kafin su tafi gda.
Suna zuwa aka tura Ummah aka shiga da ita ciki suka sanya mata ruwa kafin fitowar babban
likita, bayan kamar shudewar awa guda sai gashinan dauke da files a hannunsa ya nufo dakin
ta zuba Masa ido cike da wata muguwar tsana shima yana ganinta yaji gabansa ya fadi yayi
saurin mazewa tare da juyawa ga daya gadon Yana duba mara lafiyar ya dauki file din yayi
rubuce rubucensa ya juya zai fita tabisa da sauri tace “Dr Aseem wannan karon ba alfarma
nake nema ba da kudina na kawo mahaifiyata asibitin nan domin a dubamin lfyrta qila taka uwar
bata sallama farin cikinta domin nakaba shiyasa kake kallon iyaye Mata a banza koma dai
menene kada ka manta ta haifeka ta raineka har zuwa yanzun Bata daina baka shawara ba
inhar tana raye just aikin kudi kakeyi a biyaka kazo ka dubamin uwata nasan bakada ikon canza
qaddarar Ubangiji Amma kayi wani Abu da zaisa naji a Raina bakada hannu wajen rushewar
rayuwata wlh idan ka bari sakacinka ya kashemin mahaifiya sainayi shari'a dakai duk ranar da
ZARRAH ta takai inda mahaifiyata ta bata darenta da ranarta domin ganin takai.........."
Wani murmushi yayi me kama dana rainin hankali ya matso gabanta ta matsa ya tsaya a inda
yake yace “au kenan har jiran ranar ZARRAR ki kikeyi Kuma kinaji a ranki zaki sameta okay
almajira kin birgeni da kika taro wasan dani saidai inaso ki sani bakikai na farashi dakeba ki bari
ZARRAR taki takai tukun samu fara takun dake am bari kiji wani Abu daga kallonki naji na
tsaneki saboda idanunki sun nuna bakida tarbiyya wannan dalilin yasa naji bazan taimakeki ba
bazan taba taimakonki ba yarinya wannan asibitin nawane saboda haka na baki 10 minutes ki
debe tsummar tsohuwarki a qara gaba kar a zubamin qwarqwata" hannu yasa aljihunsa ya zaro
raffers ta dari biyar biyar ya jefa Mata yace “ga wannan idan ta mutu a sai geron sadaka"
cafewa tayi ta saita tsaiwarta har ya juya zai tafi ta daga murya tace “Aseem Shaheed" juyowa
yayi da sauri jin ta ambaci cikakken sunansa ta matsa gabansa ta keta raffers din gda hudu ta
watsa masa tayi murmushi me hade da kuka tace “Sunana Asma'u Hussain ka rubutani cikin
qaddarorin da zasu addabi rayuwarka wlh saina baka mamaki matsiyaci me taqama da kayan
aro shashasha Wawa kada ka damu zamu sake haduwa a gaba wasan baa faraba"........
_Hmmmm Wasan baa fara ba correct Asma'u Dr Aseem a sake shiri_
*_Oum Hairan_*
[20/06 4:27 pm] Oum Hairan: *ZARRAH*
_Tare da Alƙalamin_
*_Oum Hairan_*
_Bismillahir Rahamanir Rahim_
_Page 7-8_
*_Wattpad realfauzahtasiu_*
Telegram
https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7
_____________________________
_____________________________
Wata zazzafar ajiyar zuciya ya sauke lkcn da yasa tisue yake tsane jinin tare da rufe ciwon
sosai dutsen ya shigeshi hakance tasa Bai iya jan motar ba sai Zahran ne yaja Kai tsaye suka
nufi Asibiti anan Zahran yayi masa dressing na ciwon.
Duk dagowar da Zahran zaiyi sai yaga shi yake kallo har ya gama Masa yace “angama Dr yau
ka gamu da sharrin yayan talakawa narasa me muka tare musu sukejin haushinmu nasan da
zaa Basu dama zasu iya kashemu su hut....” daga Masa hannu yayi a fusace jikinsa na yace
“ka nemomin gdansu yarinyar nan a duk inda take a fadin garin Kano" da sauri Zahran ya Mike
yace “in kasan gdansu me zakayi Mata" ya dade yana kallon Zahran kafin yayi murmushi ya
miqe yace ya fara tafiya yana dingisa qafa yace.
“Nasan ba kowa bace ita face almajira mabaraciya yar jagoran makauniya so inason sanin
asalinta need saboda nayi ramuwar gayya da hujja tabbas ko Ina yafe komai bazan yafe laifin
fitarmin da jini a jikina ba hannun daya dauki dutse ya fasamin yatsa ya ciremin farce saiya
goge takalmina" ficewa yayi ya shiga motarsa ya fuzgeta da mugun gudu ya nufi unguwarsu
dake Shagari quarters yana parking ko rufe qofar baiyi ba ya nufi cikin gdan ya bude parlourn
ya shiga Mimee matarsa dake zaune da cup a hannunta ta miqe da sauri da niyyar taroshi
ganin Yana dingisa qafa yasata dafe qirji tace “Na shiga uku Life meye ya sameka a qafa?"
Kallonta kawai yayi ya wucce dakinsa ya fada gado yana huci kamar yaci Babu tunda yake
Babu mahaluqin daya taba karambanin daga hannu ya mareshi har mari biyu a lkc daya da
sauri ya miqe tare da kallon qafarsa cikin wani mugun quncin zuciya yake furta “Wacece ce ita
meye take taqama dashi wacece ita!?" Yana mgnr ne da qaraji abinda yasa Mimee shigowa da
sauri tace “lfy Life?" Iska ya furzar tare da cewa da ita “Asma'u Hussain wacece Asma da ta iya
daga hannu ta mareni wacece ita data fitarmin da wani bangare na jikina?"
Duban qafarsa yayi tare da cewa “wlh saita gane kurenta saina koya Mata hankali saina
wulaqantata ita da danginta gabadaya saina rusa Mata burikan rayuwarta" fuuuu ya shige
bathroom Sarai Mimee tasan halinsa idan yanakan tsini bajin rarrashi yakeyi ba shiyasa batayi
yunqurin rarrashinsa ba ta nemi guri ta zauna da tunanin meye ya hadosa da mace shida
magana ma ko da maza ba damunsa tayi ba da har takaisu ga wannan tsamar tabbas bayan
tiya akwai wata caca banza batakai zomo kasuwa.
Miqewa tayi ta fita ta hado masa abinci don tasan ba fitowa zaiyi ba yau an taba mazan fama
Aseem rikici ne gabadayansa tunda ya dauki ragamar ramuwar Nan to gara tayi masa fatan
nasara don idan ta cika mgn kanta fadan zai dawo. Zama yayi yana tsane jikinsa yace “meye
wannan din?" Murmushi tayi tace “bansan zaka dawo da wuri ba jallop din taliya ce" zuba masa
ta farayi ya karba Yana tauna abincin kamar Yana tauna magani ajiye flat din yayi ya miqe a
gado tana kallonsa yanata qwafa ganin bazata iya ba ta miqe ta debe kayan ta fice dasu ta
hada me aikinta dasu ita Kuma ta shige dakinta itama ta kwanta.
Wayarsa ya janyo ya kashe don yasan zaayita kiransa a hospital Kuma ba iya zuwa zaiyi ba
yau gabadaya Asma'u ta Bata Masa lissafin ranar dole haka zata tafi a banza. Haka ya yini
kwance saidai daganan ya juya nan sallah kadai ke tashinsa hudu da rabi na yamma Zahran ya
kirashi yace “ya fito yanada lbr game da aikin daya sanyashi" miqewa yayi ya dauki rigarsa yasa
ya dora hula ya fito a harabar gdan ya ishe Zahran ya qarasa fuskarsa kamar ta sa tsabar
damuwa mota ya bude ya shiga suka dubi juna