Showing 24001 words to 27000 words out of 54507 words

Chapter 9 - ZARRAH BOOK COMPLETE BY OUM HAIRAN .pdf


Miqewa tayi tana layi ta fada dakinta ta janyo akwatu cikin akwatunanta yau kam kome Aseem
yake bata a duniyar nan zata hqr da zama dashi tagaji da cin mutuncin nan shi yayi mata
uwarsa tayi mata dangin matarsa idan tsautsayi ya hadasu suyi mata dole zatabar musu gidan
su huta idan suka daina ganinta kowa sai hankalinsa ya kwanta. Mayafinta ta dauka ta yafa ta janyo akwatunta ta sauko daga saman tana saukowa yana
shigowa ba qaramar faduwar gaba yajiba ganinta da akwatun yaja ya tsaya a bakin qofar
batako kallesa ba sai hawaye da taketa tsiyayarwa tana isa gabansa yakai hannu ya riqe trolley
din ya mayar da qofar ya rufe, suka tsaya kallon kallo zare mukullin yayi yaja trolley din ya shiga
parlourn ya zauna a kujera yace “idan kin fita ina zaki?" Shiru tayi masa tanaci gaba da
shassheqar kukanta ya taso ya matso bayanta ya rungumota jikinsa ya dora hannunsa saman
hips dinta yace “zakije kice musu meyene nasan bai wucci kice zaki gda ba garama ki zauna
anan din zaifi miki sauqi domin ko Innah ta goyi bayanki Mal saiya dawo dake kasancewar yana
saka ran ta dalilinki hajjin bana dashi zaayi kinsan shi mutum me arziqi yana tutuya da arziqinsa
ne wajen shuka duk abinda yakeso zaifi miki sauqin Rayuwa ki tsaya kici Arziqi kibarshi inda
yake iyayenki bazasu iya riqek......" Dafe kuncinsa yayi saboda saukar yatsunta da yaji a
kuncinsa taja da baya da sauri ta nunasa da yatsa tace “iyakar tsiya kawai kuke iqirarin akwaita

ga iyayena tabbas na yarda Mal Hussain daya dauki aurena ya baka saboda kwadayi shi
matsiyaci ne domin tsiyar ke bibiyarsa tasa ya fansar da mutuncinsa da nawa so inaso ka tsaya
iyashi da yake nema a gurinka kamar abinda na fada maka a farko ne uwata talaka ce amma
tanada wadatar zucci domin bata qyamatar duk wani abin halitta Aseem zan iya jurewa komai a
rayuwa banda taba martabar mahaifiyata domin na hanga na hango banga ta inda taka tafi
tawa quality ba......"



_Comments_
_Share_
_Vote_
_Please_



_*Oum Hairan*_


[20/06 4:32 pm] Oum Hairan: _*Zarrah*_




_*Fauziyyah Tasiu Umar*_



*ELEGANT ONLINE WTITERS*



_*33-34*_



*_Wattpad realfauzahtasiu_*



Tana gama fadin haka ta juya a fusace ta fara jijjiga qofar da dukkan qarfinta a qoqarinta na
ganin ta bude qofar, tsayawa yayi sokoko a mugun mamakance cike da takaicin irin yanda
yarinyar ta iya fidda hannu ta zabgansa mari kuma har ta sami damar gaggaya masa

maganganu haka son rai.
Ganin yanda take jijjiga qofar idan ya qyaleta tsaf zata fashe masa glasses din jikinta yasashi
finciko hannunta da mugun qarfi ya cillata bisa kujera ya nunata da yatsa batasan uwar daya
tuna ba kuma ya juya ya fice daga parlourn ya kulleta ta baya ta yanda babu yanda zatayi ta
bude qofar kukanta taci gaba dayi me gigita tunanin me sauraro ta dade a zanne ganin batada
wata mafita yasata miqewa ta koma saman ta fada gado kanta na juyawa take wani zazzabi me
zafi ya rufeta.




Shikam yana fita motarsa ya shiga ya zauna ya hada kansa da sitiyarin yana tariyo kalaman
yarinyar akansa tabbas ba qarya tayi ba iyaye suna da darajar da bai kamata ace ana maka
wasa da alfarmarsu ba to amma meye laifinsa don yace tayi hqr ta zauna? Numfashi ya furzar
me zafi kalaman da Hajiya ta fada mawa Asman sunayi masa yawo ba itaba shi kansa baiji
dadin kalaman ba yana danganta abin ace shine akace masa maye iyayensa mayu harma aka
nasabta wani abu da zahirinsa ansa bashida alaqa dashi aka dora masa ya zaiji a ransa?
Sake furzar da iska yayi ya tada motar ya fice yana kallon fuskarsa a madubin motar sahun
yatsunta sun fito sun kwanta rada rada a farar fatar tasa yakai hannu ya shafa tare da fusgar
motar ya fice daga gdan lkcn 7:30pm asibitinsa ya nufa ya shige office dinsa ya zauna ya rafsa
uban tagumi gabadaya duniyar tayi masa zafi duk wani tunani ya qwace masa kalaman Asmah
sun kasa gogewa a mind dinsa a hankali kuma ya rinqajin tausayinta yana sauko masa.



Ya rinqa jinjina girman abinda Hajja tayi mata a ransa dole yakamata ace ta samu kalma koda
daya ce me dadi daga gareshi amma sai akasin hakan ta biyo baya yaja ajiyar zuciya ya tashi
ya nufi inda yayi parking ya shiga motar ya fice saida ya biya wani babban mall yayi musu
siyayya samnan ya nufi gdan nasa part din Mimee ya shiga da yake kwana hudu kenan dayi
mata aikin ta dawo gda gdan kuwa cike yake da danginta sunata faman mayar da mgn, shi
dama ba ma'abocin mgn ba haka ya wucce bai saurari kowa ba ya nufi dakinsa ya cire kayansa
yasa marasa nauyi ya sake fitowa ya fice Mimee ta dubi Naja qanwarta tace ta leqa mata taga
ina ya shiga.
Tana leqawa taganshi yasa key yana bude qofar Asmah ya shiga ya mayar ya rufe ta juyo tace
“gurin matarsa ya tafi" zaro ido tayi tace “wato baiji abinda hajiya ta fada masa ba kenan cewa
fah tayi idan ya sake batamin rai sai tasa ya saki yarinyar nan"




Murmushi Naja'ah tayi tace “nifa da nice da wannan yarinyar a matsayin kishiya da tuni ta fice
tabarmin gdana" kallonta tayi tace “ta yaya?" Sake fadada murmushinta tayi tace “ta duk inda
akebi" nan Naja'ah ta rinqa bata shawarwari tana dorata a keken bera ita kuwa ta hau ta zauna

ta suka tafa tare da cewa da ita “muddin zatabar gidannan nikuma nayi alqawarin ko nawa ne
zan kashe akan mijina"

A kwance yaje ya tarar da Asmah kashirban tanata rawar sanyi ya matsa jikin gadon da sauri ya
janye bargon a razane ya zubanta ido bacci takeyi amma na wuya sanye take da qaramar rigar
bacci iya gwiwa yaja fasali ya matsa ya zauna a gefen gadon yakai hannunsa saman goshinta
yajishi zau yayi saurin gangarawa qirjinta yaji yanda zuciyarta ke bugawa da qarfi ya janye
hannunsa a razane ya dagota jikinsa yana jijjigata sai yanzun ya lura ashe bama bacci takeyi ba
suma tayi sake dagota yayi yana jijjigata ganin batamasan yanayi ba ya miqe da sauri da ya fita
har yana tuntube ya nufi part din Mimee ya dauko key din motarsa ya sake fita da sauri yaje ya
ciccibota yasata a mota.




Duk abinda akeyi a kan idon Naja'ah tana fadawa mimee sukayi qwafa tare shikam bai masan
sunayi ba yaja motarsa a guje yana tuqi yana leqenta tsoronsa na nunkuwa yanda yaji zuciyarta
tana bugawa da qarfi dakansa ya sunkuceta har dakin da yake tunanin ya dace yakaita ya fara
dubata ajiyar zuciya ya sauke lkcn daya tabbatar tsabar zafin zazzabin ne yasa bugun zuciyarta
ya qaru, ruwa ya jorner mata yasa mata allurai ya zauna ya zubawa fuskarta ido yanajin
faduwar gaba ya rasa meye yasa duk sanda ya zubawa fuskar Ma'uh ido sai yaji gabansa yana
faduwa sosai kyawunta yake daukar masa ido baya gajiya da kallon fuskarta musamman cikin
watannin nan da tafara zuwa school ta waye tayi wani mayen kyau me daukar hankali jikinta ya
qara murjewa dake tadan qara qiba sai qirjinta ya qara cika hips dinta da bombom dinta suka
qara bajewa abin yana mugun birgeshi gashi nema takeyi tafi qarfinsa da idan zai tafi office
yake fita da ita ya sauketa yanzun kuwa duk sanda zai fita idan yayi mata mgn sai tace batada
lecture dole haka yake qyaleta da abin nata ma ya shahara kawai sai ta daina daga wayarsa ta
daina bashi damar shiga part dinta koda kuwa ya shiga to bazai ganta ba tana dakinta ta kulle
abinta.
Numfashi ya sauke ya dauki alluran ya daga rigarta ya saita inda zaiyi mata ya soka mata
yanajin dumin jikinsa na hauhawa yanajin wani wahalallan yanayi da yake kasancewa a ciki duk
lkcn daya matseta, daqyar ya koma ya zauna ya kifa kansa a saman cinyarsa yanajin yanayin
yana qara zagaya ilahirin jikinsa a hankali ya gane ashe mugun feelings nata ne yake dawainiya
dashi, bai bambamce hakan ba sai tsakanin shekaran jiya zuwa yau da bashi da gurin hutawa
dake a baya da mimee ko banza idan yaso kota qarfi zai karbi haqqinsa to yanzun babu dama
babu lafiya.



Miqewa yayi ya fara zagaya dakin zuciyarsa na ayyana masa abubuwa da dama yaja fasali tare
da qaryata kansa a fili yace “habadai tama isa kenan so nake ta qara rainani ashe ma" da
wannan yaji taja ajiyar zuciya ya matsa gabanta tayi miqa tare da salati yabi qirjinta da kallo
yana hadiye wasu mugun yawu ya zauna da sauri yaci gaba da kallonta idanunsa na rikida, a

hankali ta bude nata idon ta fara kallon dakin kafin ta sauke idanunta akansa, lumshe nasa yayi
ta yunqura zata miqe zaune daidai lkcn daya bude nasa ya sake saukesu akanta.
Tashi yayi ya matsa gabanta ya taimaka mata ta tashi zaune batare da yayi furuci ba ya koma
jikin basket din daya sanya aka kawo ya hado mata tea ya miqa mata ta kawar dakai ya
zubanta idanunsa fuskarsa a daure da alamun babu wasa, kawar da kanta tayi ya zauna ya
diba a cokalin yakai mata bakinta taso qin sha so amma yanda ya dage din yasata dole ta rinqa
karbar tea din tanasha daqyar take hadiyarsa kamar ruwan magani, ta kawar dakai yafi sau
goma yana qara matsanta tasha saboda magungunan da yakeson bata aikuwa daya cika
matsawa wankeshi tayi da amai da sauri ya miqe ya riqota tanata kakarin aman yana dannanta
qirjinta bayan ta gama ya shiga bathroom ya wanke jikinsa ya hadanta ruwa ya dawo sai
yanzun ya samu damar mgn da cewa “kije kiyi wanka zakiji qarfin jikinki" itamma zafi takeji
hakan yasa ta zuro qafafunta yabisu da kallo komanta me kyau ne sai tsabar iskanci da rashin
kunya dake damunta koda yake alamu sun fara ta fara laushi,
Da azamar gaske ya tarota ta fado jikinsa sabida jirin daya debeta ya sunkuceta cak ya nufi
bathroom din da ita ya mayar da qofar ya rufe ya ajeta ya fara qoqarin cirenta kayan ta riqe
hannunsa da sauri a galabaice tace “kaje zanyi...." Bai tsaya saurarenta ba ya kama rigar ya
zare tasa hannu ta rufe qirjinta ya zubanta ido yanajin wani lugudan zucci dana jiki hakanan ta
qarfi yayi mata wankan tana kuka tana komai amma yaqi qyaleta yanayi yana bama idonsa
abinci duk da bai cirenta pant ba amma shatin HQ dinta ya dauki hankalinsa matuqa har
hannusa yakai ya shafa gurin sai kuma ya tuna wani abu kawai ya basar............


_Comments_
_Share_
_Vote_
_Please_



_*Oum Hairan*_
[20/06 4:32 pm] Oum Hairan: _*Zarrah*_



_*Fauziyyah Tasiu Umar*_


*ELEGANT ONLINE WTITERS*




_*Wattpad-Realfauzahtasiu*_

_*35-36*_




Daukota yayi kamar wata bby ya fito da ita ya bude jakkar daya dauki mata ya bata doguwar
riga ta zura ya zubanta ido kamar mai karantar wani abu sai kuma ya share ya juya ya nuhi
waje ya jima ya dawo da magungunan ya dubeta ya debe kayan itadai ko kallon inda yake
batayi tanaji ya sake fita da kayan ya dawo yace “zamu iya tafiya gda Allurai ne guda 12 zaayi
miki daya kullum har zuwa lkcn da zaki warke"
Zaro ido tayi cikin firgici zatayi mgn ya fice yana cewa “ki fito ina jiranki" dole haka taja jiki ta fito
ya budenta motar ta shiga yaja suka tafi, suna tafe yana sauraron wata waqa zahirinsa
hankalinsa ba akan waqar yake ba abubuwa ne da yawa cunkushe a ransa yama rasa ta inane
zai fara, wani guri ya biya ya tsaya ya fita ya siyo musu gasasshen nama ya dawo yaja motar
suka tafi lkcn da suka isa gda 11:30pm yana budewa ta shige dakin.


Dakinta ta barshi tsaye yana binta da kallo jin da yayi ta mayar da qofar ta danna mata key
yasashi jan fasali ya nufi kitchen ya bude freegde ya sanya mata kayan daya siyo a ciki ya nufi
saman ya bude dakinsa da tsayin watanni bakwai din da tayi matsayin matarsa bai taba
shigansa ba, mamaki ya cikashi ganin komai dake dakin tsaf kamar dama ana amfani dashi ya
bude bayin shima ya ganshi tsaf dashi yaja numfashi yace “kowa da irin baiwarsa" komawa yayi
ya zauna hakanan yaji yana sha'awar kwana a part din ya jima a zaune sannan ya tashi ya
shigo bathroom din ya watso ruwa ya fito ya bude wardrobe din ya dauki sabon towel ya 
budeshi a leda ya goge jikinsa.



Ya koma ya kwanta yanata tunanin ta inda zai farawa Asmah tabbas lkc yayi daya kamata ya
fara neman haqqinsa na aure a gurinta itama kamar ko wacce mace zuwa yanzun idan yaci
gaba da kawar mata dakai to cutuwa zai farayi, miqewa yayi kamar wanda aka tsikara ya bude
qofar dakin nasa ya fito parlor harya kama handle din qofar zai murda sai kuma zuciyarsa ta
fara ayyana masa yanzu kamar shi yaje yace zai nemi wani abu gurin wannan yarinyar yar
rainin sense ai kawai gara ya bari ya samawa kansa wata hanyar.
Aminta yayi da shawarar zuciyarsa ya koma dakin nasa ya kwanta yanata matse matsen cinya
feelings na damunsa amma girman kansa na bala'i ya hanashi samawa kansa maslaha,
washegari tun asuba daya fita bai dawo part dinba to itama dake ba daidai takeba bata fitoba
balle tasan meye yake faruwa a daddafe tayi sallah ta sake narkewa a gado tanajin yanayin
zazzabin yana sake sauko mata.

Wajen 8:30am ya shigo cikin shirinsa na tafiya office ya bude dakin ya shiga ya isketa kwance
kamar ruwa ya qarasa ya janye mata blanket din ya  zubanta ido gabadaya hankalinsa yana
kan qirjinta baiyi tunanin idanunta biyu ba saida yaga ta bude idonta ya sosa qeya da yanayi na
borin kunya yace “kinsha magungunan?" Lumshe idonta tayi ya juya ya fita ya hado mata tea ya
dauko mata tarkacen daya siyo mata jiya duka babu wanda ta taba ya dawo ya taimaka mata ta
tashi zanne ya rinqa bata a baki tanaci a hankali tana hawaye gabadaya sai yaji tausayinta ya
qara mamaye zucciyarsa magunginan ya ballo ya bata tasha ya gyaranta kwanciya yace “zan
sake sanya miki drip idan ya qare ki cire sannan kada ki zauna da yunwa kinji" dagowa tayi
idanunta ya shiga cikin nasa yayi ajiyar zuciya shi kansa yanayin da yayi mata mgn dashi ya
sanyashi jin wani yanayi na daban.
Juyawa yayi ya fita ya dauko drip din ya dawo ya sanya mata yanata zuba mata sannu ya fice
tananan kwance bacci har ya fara daukarta taji an shigo part din nata saida gabanta ya fadi tayi
tunanin Hajja ce aka bude qofar aka shigo ta sauke ajiyar zucciya ganin Jiddarh ce zama tayi
kusa da ita tace “na shiga school najiki shiru inata kiran wayarki baa dauka ba qarshe wannan
miskilin mijin naki ya daga yacemin bakida lfy shine hankalina yaqi kwanciya nace bari nazo
naga jikin naki" lumshe idonta tayi batasan sanda hawaye ya zubonta ba tace “ina Innata kwana
biyu idan na kira wayarta bata shiga" kallonta Jiddarh tayi tace “wai kina nufin baki sani ba ai
bama ta qasar tana Saudia zaayi mata aikin ido" zaro ido asmah tayi ta yunqura zata miqe
Jidda ta taimaka mata ta zauna tace “waye ya biya mata?" Harararta tayi tace “kinji ki toda wa
kike tunani bayan mijinki"



Hawaye ne ya zubonta tace “shiyasa kullum yake qara samun damar cimin mutunci duk mgnr
da tazo bakinsa ya fadamin uwarsa ma ta fadamin Jiddarh meye yasa Innah itama takeson
zama irin Mal ne basa tunanin mutunci na da qimata a gdan aure kawai biyan buqatarsu suke
dabbaqawa nikam wannan rayuwar bansonta zanso ace sun hqr da talaucinsu don mutumcinsu
da qimata Jiddarh yaushe ne don Allah rana zatazo? Yaushe ne nima zanyi farin ciki a gdan
mijina Jiddarh yaushe zan zama cikakkiyar mace me yancin zama da mijinta tayi hira tayi dariya
suyi nishadi su bawa juna farin cikine, wlh a baya bana damuwa duk da cewar nasan cewa abin
zai dameni wataran amma banyi tunanin zuwanshi a wannan lkcn ba Jiddarh babu irin kirsar da
banayi domin na samu kan mijina amma na kasa samu harma takai na hqr na qyaleshi amma
duk da haka bana tsira daga rashin albarkarsa na gaji Jiddarh na gaji gara na kauce na samu
salama shima ya samu........"




Shigowar da sukaji anyi dakin ne yasasu dagowa suka kai dubansu inda ake shigowar Hajja ce
take shigowa ita da wata mata gaban Asmah ya fadi taja hijjab da sauri tana shirin sanyawa
tajita a baje a qasa bata gama tantance meye yake faruwa ba taji an rufeta da duka kamar

saqon Allah aikuwa tuni ta fice daga hayyacinta Jiddarh ce tayi kukan kura ta angaje Hajja tace
“kutmar Ubancan wannan wanne irin rashin mutunci ne ubanme tayi miki...?" Daidai lkcn Aseem
ya shigo da mugun gudu ya hawo saman dan ko motarsa bai kashe ba saboda yanda Aunty
Aseemah ta kirashi ta sanar dashi cewa Hajja zata kashe yar mutane Mimee ta shirya mata
qarya da gaskiya"
Lkcn daya shiga ya tarar da Hajja tana zabura zata qara dukan Asmah Aunty Aseema da
Jiddarh sun kakkare asmah dake kwance a qasa kamar gawa da gudu ya qarasa ya turesu ya
dago Asmah da bakinta kanta da hancinta ke fitar da jini ya fara jijjigata fadi yake “Asma'uh!
Asma'uh!! Ke Asma'uh Innanillahi wa inna ilaihirraji'un Hajjah kin kasheta meye wai Asma'uh ta
tare muku ne kukeson ganin bayanta....." Miqewa yayi ya dorata a gado ya haura gadon da
sauri da ruwa a hannunsa ya balle bottle din ya rinqa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login