Showing 30001 words to 33000 words out of 74861 words

Chapter 11 - mijin malama 1&32 Hausa Novels By Nimcey Sarauta.doc

24 Jan 2026

541

cikin damuwa ya ce "Ya ya ta sauka ne?" Bilkisu ta girgiza ta ce "Ayya ai sai abin da hali ya yi na?uda tun jiya ana abu Waya sai fama ake, gashi Malam ka ?i a ta fi asibiti" Malam Abdul'aziz ya haWe fuska ya ce
"Yanzu nan zata sauka lafiya, ni ban fiya yarda da aikin nasara ba yadda nayi wannan tofin babu shakka zata rabo da cikin salin alin" "Allah ya sa, amma Fulani na shan wahala" cewar Bilkisu.
Ta amshi maganin tare da Waga labule ta shiga, rawar dai har yanzu bata sauya zani ba. Domin Nishi ake son ta yi amma abu ya gagara. Bilkisu ta ce "Sannu kin ji Fulani" ta bawa wata mata dake zaune gefen Fulanin ta ce "Yanzu Malam ya kawo wannan tofin, taimaka ki Wagata ki bata kin ji Asabe" Asabe ta amsa cikin alhini ta tallo kan Fulani ta shiga mata maganin jikinta duk ya riga ya saki.

"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, na shiga uku me zan gani ni Asabe Yaya Bilkisu ?afa ce ta fito, haihuwar dire za ta yi"
"Wanne irin dire ni ?ar nan matsa muga Asabe" Asabe ta matsa Yaya Bilkisu na dubawa ta ga da gaske ?afa ce guda Waya ta fito harta fara bushewa. Suka rasa yadda za su yi hakan alama ce dake nuna musu ruwa ya ?arewa Wan-kada. Suka yi rufdugu akan Fulani wacce take jin mawuyacin hali salati kawai take yi gefe guda kuma tana kiran sunan Hawwa'u.
Da ga bakin ?ofa Malam Abdul'aziz ya ce "Ya ake ciki? Ta kusa sauka ko?" Yaya Bilkisu ta ce "Wanne sauka za ta yi dire, Malam ka je ka kawo mota mu je asibiti ko na Murtala ko na nasarawa" sai a lokacin Asabe ta ce "Ai bama za su amsheta ba, domin bata taSa zuwa awo ba, ko haihuwar Majeederh a haka ta zo mata"
"Ikon Allah, Ubangiji ga mu gareka" da ?yar suka taimaka mata Waya ?afar ta fito suka dinga yayyafa mata ruwa tare da bata shayi mai zafi cikin sa a nishi mai ?arfi ya zo mata ta haifi Wiya mace a karo na biyu. Murna sosai sukai harda hamdala aka yanke cibiya tare da gyara kyakkyawar yarinyar. Malam na waje Yaya Bilkisu ta fito tare da barin Asabe a Wakin.
"Ga kyautar da Ubangiji ya ?ara yi maka, uban ?a ?a mata" Malam ya yi murmushi ya ce "Hakan ma suttura ce Yaya, kuma ina alfahari da Wiyata Majeederh wacce zata bani abin dana rasa a baya" Yaya Bilkisu ta yi murmushi tana faWin
"A kan Soyayyar Majeederh baka da Wauke ?afa, tana ina ne?"
"Makaranta Yaya Bilkisu, ai tun tana shekaru biyu na sanyata a makaranta gashi yanzu dab take da yin sauka" Yaya Bilkisu ta zare idanu sosai cike da mamaki da al'ajabi ta ce
"Yau na ga abin da ya isheni ni Mai gadon zinare ba bu tausayi shi ya sa gata nan duk a fige saboda tsabar karatu" Wani Uban kira Asabe dage cikin Waki ta shiga ?walawa Yaya Bilkisu jiki na Sari har zaninta na faWowa ta tsuguna zata Wauka domin gyarawa ashe takalmi ta Wauka tana faWin.
"Muhammadur Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama, Wanne irin Waukan alhaki ne haka Asa....," Abin da idanun Yaya Bilkisu ya gane mata ya hanata ?arasa duguwar maganar data Wakko. Fulani ce ke kwance kamar Matacciya sai jijjiga take harshenta ya fito waje ga jinin dake fita a ?asanta kamar an yanka rago.
Yaya Bilkisu dake zuciyarta da rauni tuni ta fara sharSar hawaye tana faWin "Oh, mu mata muna ganin jarrabawa a wajan haihuwa rabu ba a tsira ba" Fulani da numfashinta ke sama fuskarta tayi fari sosai saboda jinin daya ?are a jikinta ta ce "?a ?ana, ?a ?ana Yaya a kira mini Hawwa'u kafin na koma ga mahaliccina"
"Assha, Assha daina faWa mai ha?uri albarkacin ha?urin ki Ubangiji ba zai amshi rayuwarki yanzu ba, ke zaki raini yaranki da kan ki kamar yadda kika haifa" Fulani tayi shiru banda salati babu abin da take ana haka Malam ya shigo jin shirun ya yi yawa. Wani bugawa ?irjinsa ya yi ganin halin da matarsa Fulani ke ciki, tsananin kyan da Ubangiji ya yi mata kasancewar ta Fulanin Gombe Usul gaba-da-baya Fulanin kuma makiyaya masu kiwon shanu wanda nono ya zamr musu jarin su wanda a yanzu shi ake sarrafawa zuwa madarar Rufaider yoghurt. Tun tana shekara goma sha biyar da haihuwa aka Waura mata aure da Malam Abdul'aziz, a lokacin ya ziyarci garin Yobe shi da abokinsa yin dillacin wata saniyya domin kiwo. At first sight soyayya mai ?arfi tayi dirar mikiyya a zuciyar matashin saurayin Abdul'aziz. Har Ubangiji ya tabbatar da auren su, bata sami haihuwa ba sai da tayi shekaru ashirin da biyar a gidan shi, sannan ta haifi ?ar ta Hawwa'u Majeederh Abdul'aziz Khan! Wacce kamar ka ki tayi ta zubar saboda zallar kamannin da su ka yi. A nan ya samu wadata ya ?ara aure Majeederh na da shekara wacce ya aura ta haihu ta samu Wiya mace. Kasancewar kwanika take ta sake haihuwar wata ?ar lokacin Majeederh nada shekara huWu ana haka Fulani ta samu ciki. Har ya isa mizanin zuwa duniya a daidai gaSar da Malam ya bar gidan domin kawo tofi a lokacin na?udar da ta ke tun jiya ta tsanan.

Nishin da Fulani ta yi tare da salati ya dawo da Malam daga tunanin daya lula firgigit ya zube gabanta yana faWin "Fulani kada kiyi magana haka, ba mu shirya zuwan wannan ranar ba" ta ri?e hannunsa sosai tana salati ta ce "Malam ka kira mini Hawwa'u ina son ganinta, ina son faWa mata wani abu mai muhimmanci a rayuwarta" Malam ya fara addu'a tare da cewa "Ki faWa mini ko ma mene, ni ne uban Hawwa'u kuma zan ri?e amana" ta girgiza kai ta ce "Al'amari ne daya shafi uwa da ?arta, da kuma dangina ka je ka dawo mini da Hawwa'u, dole zata Sukaci sani a lokacin da bu?atar hakan ta zo" Ta dinga rufe ido tana salati gabaWaya wajan aka fara salati Yaya Bilkisu ta zari mayafi ta ce "Wacce ?addararriyar makaranta ce har kusan almuru? Wallahi yanzu zan je na dawo da ita, Allah ya baki lafiya Fulani"
Tana faWin haka ta yi waje lokacin yaran duk suna makaranta banda guda Waya.
A hankali Yaran suke tafiya wajan su biyar, uku a gefe guda biyu a can gefe sai. Wacce ta fi ko wacce nutsuwa ta ?ara ?an?ame Alkur'aninta a ?irji tana sauke numfashi, a hankali ta yi kyakkyawan murmushi ta cikin li?ab Win dake ma?ale a fuskarta. Murmushi daya haifar da lomawar dimple Winta guda Waya. Farin ciki yau take ta ?arasa bada haddar Alkur'aninta surar ?arshe kuma shafin ?arshe na Suratul Bakrah. Latifa dake kusa da ita ta ce "Majeederh kina dariya ko?" Ta jin jina kai ta ce "Uhm, Mimana na siyo mata alawa, kuma zan ga babyn da zata haifa na samu ?anwa" Latifa ta ce "Laa Mima haihuwa za ta yi?" Majeederh ta bata fiya hayaniya da surutu ba sai ta ?ara jinjina kan ta cikin siririyar muryarta ta ce "E, ba kiga cikinta ya yi ?ato ba? Zan je na ga baby kuma na ce mata na kammala hadda ta yi mini sada?a inji Ya mu'alim" farin ciki ya kama Latifa sosai ta ce "Ai nima zani na ga baby kuma ni ma zan ce na kusa gama haddata" Murmushi kawai Majeederh ta sake yi har ranta farin ciki take na ganin ta riga kowa kammala haddar Alkur'ani ga Mima zata haifa mata ?anwa. Tuna haka sai ya sa ta lumshe idanu tare da rungume Alkur'an ta na ji tamkar ta yi tsuntsuwa zuwa gida. Amma kamar wacce ake ?ara bayar da ita baya sbd yadda take tafiya a nutse da tarin kamala nutsuwarta ta fi ta wata cikakkiyar budurwar. Tunda kuma ta fara girma Abu ya siya mata Li?ab kamar yadda Ya mu'alim ya bashi shawara sbd kyan da Allah ya yi mata na musamman ne tamkar zara ce a cikin sauran taurari ga sai dai ?ar firit take karatu ya sata gaba Islamiyya da boko ga tarin hadisan da Abu yake ?ara mata idan ta dawo, bata barci sai wajan ?arfe 1 asuba na yi take tashi ta fara karatu.
Sun zo dai-dai wajan wa su matasa wani ya kalleta ya ce "Yarinyar nan daga gani munin ya yi mata yawa, tunda nake ban taSa ganin fuskarta ba" Wani ya ce "Kuma dai gata kamar fara ce"
"Ahhab, waya faWa maka fari kyau ne?" Suka dinga surutu Waya ne ya ce "Ni kuma nutsuwarta ke birgeni, idan ba makaranta ba ko aike bata fitowa mahaifinta ya gwammace ya je da kansa, amma sauran ?an uwanta ga su nan kullum suna fitowa" Latifa za ta yi magana Majeederh ta yi saurin ri?e hannunta tana ?arawa tafiyarta sauri. Burinta bai shige tayi tuzali da Mima ba tana son jin labarin da a kullum take ce mata yana da muhimmanci a rayuwarta. Yau kuma ta yi al?awarin bata wannan labarin. Farin ciki ya danne yunwar da ta ke ji.

Tazarar gida Waya ne tsakanin gidansu Majeederh da na su Latifa, wannan dalilin ya sa ?awancan su ya ?ara ?arfi duk da girmewa Latifa da Majeederh ta yi kuma suka samu nasarar shiga makaranta Waya daga ta boko har Islamiyya akwai bambancin fahimta tsakanin su, wanda ya sa Majeederh ta fi Latifa gane komai. Tun da ga nesa Majeederh ta hango Yaya Bilkisu tana zuba uban sauri tare da share hawayen da ke bin idanunta. Cak! Ta tsaya sbd mummunar faWuwar gaban daya risketa Kur'anin hannunta ya nemi faWuwa ta ri?e sosai fararen Idanunta masu tsari kwance akan fuskar Yaya Bilkisu har zuwa lokacin data riski tsaiwar ta su.
"Allhamdu lillahi, maza zo muje ?ar albarka" Majeederh ta ?urawa Yaya Bilkisu Idanu domin Allah ya yi mata baiwar fahimtar abu dalilin da ya sa Abu ya ce psychologist zata karanta bayan nan sai ta koma Islamic studies. "Haba Kulun Majade mu je mana" Kamar wacce take karantar zuciyar Yaya Bilkisu ta ce "Mimana? Mene ya sameta? Ta ce zata bani labarin abu mai muhimmanci, ta ce kafin na dawo zata kawo baby, ta haihu?" Tsoron ya kama Yaya Bilkisu ganin tafarar Waya Majeederh ta kasance abin da ke shimfiWe a fuskarta lallai tunani da kaifin basirar Majeederh ya shige shekarunta. Ta ce "Eh, yanzu ma cewa tayi muje ta faWa miki wani abu" ta tsorawa mata Idanu sai kuma ta sauke ajjiyar zuciya mai nauyi tana jinjina kai. Sauran ?annenta Ruma da Wayar kana ta kama hannun Yaya Bilkisu suka nufi cikin gidan domin suna gab da ?ofar dama. Malam ya dinga girgiza Fulani yana faWin "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, Fulani faWa mini abinda ki ke son faWawa ?arki Majeederh" Ta ja numfashi da ?yar tana karanta kalmar shahada ta ce "Malam kayi mini wannan alfarmar kamar yadda aka baka ni ina shekara 15, to ka aurar da Hawwa'u a wannan shekarun domin akwai Soyayyiyen abu tare da ita don Allah, don Allah..." Kalamanta suka tsaya sbd ajjiyar zuciya da tayi tana Waga idanu sama daidai shigowar Majeederh ya yi daidai da wa'adinin rasuwar Fulani........ The destiny was just begun!


Duk wata mace yana da kyau ta nutsu ta bi labarin nan.

MIJIN MALAMA
Paid book
1 and 2 pay 1k to join us 08119237616
[7/7, 12:25 AM] Aunty Mopol: She is too young a lokacin da Ubangiji ya amshi ran mahaifiyarta Fulani. Majeederh ba zata iya cewa ta shiga maraici ba sbd Abbu ya Wauke mata dukkan wani nauyin na uwa ya haWa da na shi na uba. Yarinyar da aka haifa lokacin mutuwar Fulani wacce take bin Majeederh ta amsa sunan Aaliyah, motsin kaWan Aaliyyah zata ce Anty Jeederh domin ita ta kewa kallon uwa mahaifiya, Albarkaci kyauttukan da Majeederh ke samu tun lokacin ?uruciya har zuwa matakin girma ya taimakawa Abbu wajan rushe gidan shi tare da gina wani sabo rayuwar ta fara sauya musu, ba sauyi mai yawa ba.
After 20yrs
Shekaru sun ja a lokacin da ta kammala karatun secondary wanda ya yi daidai da ?ara yin saukarta ta uku, lokacin tana da Shekaru Ashirin, Ruma kuma Sha Takwas, Raihana nada shekaru Sha Bakwai. Sai Aaliyyah mai shekara Sha biyar. Filin taron cike yake tab, da manya da ?ana nan mutane, sarakuna da ?an siyasa, sai kuma masu kuWin jiyar da suka ?ara sawa taron ya yi armashi. Zazzafar Musaba?a ake gabatarwa tsakanin makarantar su Majeederh Ahlul Madar, sai Nurul huda, a lokacin ne duk wacce ta lashe zata amsa sunan Gwarzuwar Jiha kuma babbar malama wacce zata dinga wakiltar ?asar jihar bakiWaya.
A hankali ta Wago kanta inda take tsaye tana bin tarin tarin jama'ar da suke wajan da kallo, ta na jin idanunsu a kan ta. Ta samu kanta cikin wani irin faWuwar gaba, wacce bata taSa jin irinta ba. "Malama Majeederh, ke muke saurare" aka ?ara maimaita sunanta a karo na babu adadi. Ta rufe ido tare da mai da kanta ?asa cikin nutsuwa da kamala ta shiga rera karatun Alkur'ani mai tsarki wajan ya Wauki shiru sai sautin muryarta dake ta shi. Wannan shi ne karo na uku da Malama Majeederh ke jan ragamar musaba?ar makarantar su, wacce ta zame abin alfahari wannan gaSar ne kuma idan ta samu nasarar lashe wa zata samu zarafin zama gwarzuwa a garin su, kuma ta zama cikakkiyar Malama.
Kammala karatun na ta mai cike da Tajwid da makarujil-huruf ba tare da gyara ko tini ba ya sanya wajan ya Waukar kabbara. Ta lumshe idanunta hawaye ma su zafi tun bayan rasuwar Fulani ya samu damar fitowa daga cikin kyakkyawan Idanunta. GabaWaya ta cika burikan mahaifiyarta aure kawai ya rage mata a yanzu. Kyaututtuka ta samu hadda kujerar makka Governor dake mulki a lokacin ya amshi sunanta tare da yi mata al'?awarin samar mata da scholarship a ?asar waje. Ba ta yi wata murna ba har suka isa. Mami ce ta riga kowa shiga gida, hakan ya sa ta shiga har ta cire mayafin jikinta ta ajjiye ?ar fos Win tata tare da dawowa parlour ta zauna. Tana zama sassanyar muryar Majeederh mai cike da nutsuwa da kamala babu hayaniya a cikinta ta ratsa kunnen Mami. Sauran ?an-uwanta na biye da ita. Aaliyyah, Ruma, Raihana.
Mami ta dubi Majeederh dake ?o?arin shigewa bedroom Winta ta ce.

"Wai lafiya na ganki ba kuzari? Kamar kazar da ?wai ya fashewa?" Mami ta faWa furta hakan lokacin da take kallon Ruma dake faWin. "Babu mamaki ba?in cikin na samu saurayi take mini a wajan taron candy da musaba?ar su" Mami ta kalli Ruma tana ri?e haSa ta ce "Bana son sharri da rashin ta ido Ruma, Majeederh ba yayarki ba ce? Ina ruwanta da saurayinki?" Ruma ta haWe rai sosai ta ce
"Mami da ruwana mana, salon kawai ta shafa mana ba?in jini duk kyan nan nata fa bata taSa yin saurayi ba, ba a taSa cewa ana son ta ba"
Mami ta ce "Allah Al-hakkamu, akwai abin mamaki ace mace kamar Majeederh shekaru Ashirin amma babu mushinshi ni gaku nan ?annenta shirin kai ku Waki muke" Raihana dake tsaye tana cire mayafi ta ce "A to idan abun ya gagara, kawai sai ta auri Wan da zan haifa"
Wani irin fashewa da dariya Ruma ta yi hadda ri?e ciki ta ce "Amma Raihana kin fi Wan iska iya iskanci, ki ce kawai tsohuwo zaki aura masa" Aaliyyah ta ja tsaki tare da tura baki ta shige domin bata da ikon magana yanzu Anti Jeederh zata mata faWa wai tana rashin kunya bayan su ma rashin kunyar su ke. Zuciyar Majeederh sam babu daWi she's just 20yrs ita ba taga girman da tayi da har za a fara mata surutun bata da saurayi ko ba tayi aure ba. Jiki a sanyaye ta shiga bedroom tare kwanciya akan gado. Wayarta ta fara ringing ganin sunan Latifa Omar ya saka ta amsa kiran.
"Latifa" ta kira sunan bayan ta amsa sallamar ta. Latifa dake zaune kusa da mahaifiyarta ta ce "Malamarmu ya gajiya? I just want to say, congratulations! Kin zama babbar malama kamar yadda Abbu yake muradi" Majeederh ta lumshe Idanu ba tare da ta ce komai ba, ita kaWai ta san wasi?ar jakin da take karantawa a zuciyarta. "Majeederh"
Latifa ta sake kiran sunanta jin ta yi shiru ta ce "Lafiya kike kowa?"
"Allhmdu lillahi"
Cewar Jeederh murya can ?asa domin bata fiya son surutu baz musamman idan bata cikin yanayi me daWi.
"Me damunki? Dole akwai damuwa a tare da zuciyarki Majeederh tun ba yanzu ba na fahimci abin da zuciyarki ke muradi" Majeederh ta ja pillow ta rungume tana buWe manyan Idanunta farare tas da su cikin sauke numfashi tare da nuna yadda abin ke cinta ta ce. "Latifa ba ni da kyau ne?" Mamaki ya kama Latifa ainun domin ko ita da take mace wani lokacin da ?yar take kai zuciyarta nesa wajan Wauke ganinta akan Majeederh. "Duba madubi yanzu? after zan kira na ji result" Ta na faWin hakan ta kashe kiran. Majeederh ta yi shiru tana tana tunanin maganar Latifa Omar ta mance rabon da taga fuskarta a madubi. Ita Win ba ma'abociyar ganin kanta a madubi ba ce. Ta mi?e tsaye tana ajjiye wayarta cikin tafiyarta ta nutsuwa ta ?arasa wajan madubi Idanunta rufe sbd tsoran abin da zata iya ganin wanda zai sanya ya zama dalilin da maza suke gudunta.
Aaliyyah dake tsaye tun Wazo ta yi murmushi tana le?a yayar tata ta ce
"I have never seen a beautiful as someone as you" ta ?ara kallon ta ta ce "Wallahi Anti Jeederh ban taSa ganin macen da take da kyau, kuma take Soye kyan nata ba, da ace Maza na ganin ki kamar yadda muke ganinki da tuntuni kin manta da yin aure, ko sau Waya ne ki cire li?ab Win kema Kiyi saurayi su Anti Ruma su daina miki gori" Majeederh ta buWe ido tana sakin kyakkyawan murmushi akan fuskarta ta dafa kafaWar Aaliyyah ta ce
"Kin damu ne?"
 .& .Sosai Anti Jeederh, ai gori suke miki ni kuma bana jin daWi, ina son ki riga su yin aure..
"Uhm Aaliyyah"
Cewar Majeederh domin asirin ciki sai hanji maganin cuta Allah. Aaliyyah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login