Showing 24001 words to 27000 words out of 74861 words

Chapter 9 - mijin malama 1&32 Hausa Novels By Nimcey Sarauta.doc

24 Jan 2026

523

ba za a taSa samun matsala daga Hawwa'u ba, ha?urin ta ya shige yadda kuke tunani, tana da zurfin ciki" Dattijon ya numfasa ya ce "Haka Uba na gari ya kamata ya kasance, kuma mun amshi amana zamu ri?e babu abinda zai sameta domin da Wa da dukiya na Allah ne, ?addara kuma kamar riga ce zata iya faWawa kan kowa, kada ka damu zanwa His Excellency magana da zarar jikinsa ya samu"
"To, madallah madallah dai" cewar Uncle Isma'il.
Ya juya zuwa ga P.a Hammad "Hammad kai abokin Abu-turab ne na ?warai, kasan halayyar shi mai kyau da akasin haka, ba ina doubting akan shi ba ne, ina son sanin mene halinsa wanda ya dace ace ko wane Uba ya sani a matsayin wanda zai bada aure?"
Hammad ya yi shiru kai a kai a ?asa. "Ka ji tsoran Allah, a maganar aure ba wasa ba batun kuWi da mulki babu wanda bashi da zuciyar da zata iya kai shi zuwa wani bigirin na sauyin hali, faWa mini gaskiya" Ya Wago kai tare da zubawa Uncle Isma'il idanu kafin ya ce.
"No!, actually no, he's innocent bashi da matsala" Uncle Isma'il ya yi murmushi ya ce "Allhamdulillah" shugaban Jam'iyya da Dattijon su kayi godiya sosai, tare da nuna farin ciki na auren Malama Majeederh Abdul'aziz Khan, da Governor Abu-turab Al?asim. Sai Hammad motoci suka shiga kai tsaye kuma Government house sukai.
Tsaye Ya samu matar shi Hajiya Luba sai masifa take,ya ja ya tsaya tare da yin shiru yana son jin wannan masifar ta mece. "Fisabilillahi duk kin cika kunnen jama'a? Hala ke da Sona ne?"
"A'a, ni da Uban Sona da Jawaad ne, yanzu abinda ku ka aikata ya yi daidai kenan? Kamar kuna neman kai da Majeederh sai a Waura mata aure sama taka without her permission? Meke damunka tana da iko na zaSawa kanta wanda take so take ?auna kuma ai a bari ko yaye yaron tayi?" Uncle Isma'il ya ce "Tab Win, wannan masifar taki bata da gurbi yanzu, zuciyar fulani ta motsa kyaci kanki to" ta yi saurin tarar shi da
"Muci kan mu tare dai, naga alama shi His Excellency Win ka kewa ba?in cikin gyaran Fulanin Gombe, yadda ka susu ce a kaina ka ke takaicin ya ji haka?" Ya hangame baki tare da ri?e haSa ya ce "Haba ko da na ji, cewa zaki Soyayyar da nake miki ba banza ba, to maza maza karya asirin da ki kaiwa zuciyata ina bu?atar ?arin aure" ta maka masa harara irin ta wasan miji da mata sam bata ji daWin hawan ?awarar da su ka yi wa rayuwar Majeederh ba. Tana bu?atar hutu da nutsuwa tana bu?atar sanin waye zai so ta, so na gaskiya waye ba zai gorantawa ?addararta ba. Uncle Isma'il bai tsaya da maganar ba ya ce "Ki ji tsoron Allah Hajiya Luba, ashe shi ya sa kullum ki ke zaune daram a zuciyata, shi ya sa kullum nake ganinki tamkar alawa mai tsinke a leda, Oh! Ni Alhaji Isma'il Khan, Allah na tuba ka yafe mini ina da arzi?in yin mata huWu amma sharrin matan fulanin Gombe ya hana"
Duk yadda Hajiya Luba ta haWe rai bai hanata yin murmushi ba ta ce "Stop kidding me, ban ji daWi ba, ban ji daWi ba kuma still ban ji daWi ba, yarinyata nada gata a bari ayi mata auren gata mana? Kuma batun ta tare yau babu shi" Uncle Isma'il dariya yake sosai he's so friendly
"To me ?a, ai sai dai ayi ha?uri aikin gama ya gama kada ki manta daman ita ba mai son bidi'a ba ce, ki yi ha?uri ko wacce mace darajarta Wakin mijinta, a yanzu babu abinda Hawwa'u take bu?ata irin aure ta zama cikakkiyar matar aure, damar data rasa a baya ita ta samu yanzu, ki dubi Allah ki yafe mini amma ki janye batun cewa sai tayi yaye ai daman ba shayar da shi take ba" Hajiya Luba ta ce "Idan daWin baki ne ba daga nan ba"
"Da shi na siye zuciyar ?ar mutan Gombe" su kai dariya ya bata side hug ta zaro ido waje irin ya haka?. A tsaye ya samu Abraham wanda ya kasa zama har yanzu yana ri?e da Ibrahimul-khalil, haka kawai zuciyarsa ke faWa masa something bad was gonna happen to him, babban damuwar shi yadda a karo na biyu daya hango tashin hankali akan fuskar Maluma Jee. GabaWaya Uncle Isma'il ya mance da Abraham gabansa ya faWi, musamman daya tuna shi Abraham bai san ?addara ba balle ya yarda ya kuma yi Imani da ita, cikakken mabiyin addinin Yesu ne na Injila. Ga Grandpa Win shi cikakken Pasto ne, zuciyar su a gurSace take. Ya nisa tun kafin ya yi magana ya ji saukar muryar Abraham ya ce
"What's going on? Uncle?" "Nothing"
"Malumana, she's crying" "She most" Abraham ya ware idanu yana ?ara rungume babyn a ?irjinsa yana jin tamkar ya tsaga jikinsa ya mayar da shi sbd tsananin son da yake masa. Ganin kallon tuhumar da yake masa ya sa Uncle Isma'il ya haWe rai, ya ce "Ba zamu shirya da kai ba, kuma ita Maminka ba dole tayi kuka ba acikin jama'a akan idanun manyan mutane dana mahaifinta ka sanya hannunka ka Wauke ta? Sbd kai baka jin nauyin aikata abin kunya daman ka saba, ka ji ma da sanin bakwai jituwa da mahaifinta yadda ka mayar masa gida kamar wani muzuru duk sanda kayi niyya sai dai ka haura, to a hir Winka ba zan zuba idanun hakan ba, ko da wasa na sake ganinka inda Majeederh take sai na saSa maka, banda abin kunya ba taci kashi da fitsarinka ta goyaka a bayanta ta yi maka wanka amma sbd....,"
 ..... She's not my mother Unclu ya ce "Ba shakka" Abraham ya zube gaban Uncle kansa a dur?oshe ya ce cikin turanci "Na maka al'?awari sauya, zan zama yadda addininku yake son ya zama"
"It is too late to cry, Abraham" Abraham ya Waga gajiyayyun idanunsa kamar wanda ya sha ya yi tatul da basara ya ce "You're kidding me, right?" Uncle ya yi shiru Abraham ya ?an?ame Ibrahimul-khalil yana jin tamkar shi ya rage masa a rayuwa, daman tuntuni ya ha?ura da mahaifina. Tausayinsa ya kama Uncle Isma'il ya ce "Kawo a kai mata Wan?"
 .... No! Uncle help me kayi saving rayuwata, I love Mulumana, and am ready to convert to Islam ba zan ?ara taSa Jeena ba sai ta zama halak a gareni" ya faWa cikin turanci. GabaWaya ya rasa me zai ce.
"Ok, I'll think about that" zan yi tunani akan hakan. Ya ?ara da "Kai mata babyn, ask her forgiveness sai ka je ka fara tunani idan kana son musulunta da gaske"
Ya mi?e cikin takunsa na isa kai ka ce cikakken Muslim ne yadda yake tafiya, yana tafiya arms Winsa na motsawa yana yin jikinsa har Mmk yake bawa Uncle Isma'il, ya yi kusan ukun Abuturab ba?ar fatar jikinsa irin wacce ake so Win nan, so romantic and classic. Abraham is always stronger when he has Majeederh by his side, knocking ya yi ya daWe kafin ya sanya hannu ya tura cikin kamo kalman da suka rage masa na Hausa ya ce "Salamu... Alayk" tana zaune saman kujera cikin abayar dake cikinta tun safe ta zura hannunta a tsakanin cinyoyinta sai girgiza ?afa take slowly slowly, fuskarta tayi jajir kamar wacce ta ji ciwo haka ke tabbatar da ranta. " I can't believe this" Abraham said quietly. Da sauri ya ajjiye Ibrahimul-khalil ya zube gabanta tayi saurin Wauke kai, girman Abraham tsoro yake bata, musamman idan ta tuna sanda yake yaro yana binta yana Mamina, gashi da son jiki da taurin kai baya jin magana bashi da tsoro. Ya jima da sanin rauninta ya san me sanyata magana ya san abinda zai sanya ta ji sanyi a ranta, but she hate him yana ganin ?iyayyarsa a ?wayar Idanunta. Ya rasa ta ina zai fara sbd sometimes bai wani iya rarrashi ba, One thing daya iya idan zai rarrashi mutum shi ne ya rungume shi, he just give a tight hug Win nan. Gently ya mi?e daga tsugunen da ya ke tare da fara zagaya Wakin yana nutsa hannunsa cikin hargitsatsiyyar sumar kan shi. Da sauri ya yi kamar zai fita sai kuma ya sanya ?afa da ?arfi ya rufe ?ofar bedroom Win Majeederh tare da zura key Win cikin wandon shi....



MIJIN MALAMA na kuWi ki biya ki karanta....If you read for free>?7? @&?>?7? @&?>?7? @&?>?7? @&?08119237616
[7/7, 12:25 AM] Aunty Mopol: Cikin sauri Barrister Aliyu zaki ya shiga mota tare da bin bayan Abraham, His Excellency Abu-turab ya shiga zagayawa a wajan yana sauke numfashi a wahale jiri na neman Waukan shi, ganin yadda yake shirin rasa Jiddo a lokacin na biyu. Al'amarin na neman zame masa tamkar ta le?o ta koma ne, ga ?oshi ga kwanan yunwa. Wanda bashi da mara ba da inuwar giginya na nesa kasha daWi.
Ya fesar da numfashi tare da juyawa ya kalli Uncle Isma'il wanda ya fito tare da tsayawa a harabar gidan nasa, gabaWaya ya shanye mamakin da Abraham ya shayar da shi ta hanyar zubawa bakin gate idanu a tuninsa ko Abraham zai dawo da Malama Majeederh. Amma zaton shi ya saSa tunaninsa.
"Uncle a Waura auren kawai" Uncle Isma'il ya dubi His Excellency, duba na tsanaki.
"Matsayin auren fa?" His Excellency ya ce "Zan sanya a rufe ko wacce tashar mota, data jirgin ?asa, zuwa na sama, dana ruwa, zan zuba jami'an tsaro a kama shi zuwa gidan yari, ita kuma sai a akai mini ita gidana"
"Kada ka tsauwala, gaggawa aikin shaiWan Your Excellency" ya ?ara girgiza kai ya ce "Majeederh ba auren sada?a za mu yi mata ba, tana da daraja sosai ?addara ce kawai ta faWa mata, yadda aka juya mata baya ni ba zan bari ba" cikin girmamawa His Excellency Abu-turab ya dubi Uncle Isma'il kamar zai rusuna ya ce
"Afuwan bana nufin haka, ka fahimci ni, ka dubi halin da nake ciki Uncle"
Mahaifin Aliyu Sufyan ya numfasa ya ce
"Ita mace allura ce a cikin ruwa, mai rabo ka Wauka, ina tunanin abar maganar zuwa sanda wannan Win zai dawo da ita" "Mahaukaci ne fa, zai iya aikata abinda ya furta" cewar Abuturab.
Murmushi kawai Uncle Bello ya yi, domin ya fahimci hutar son Majeederh a cikin idanun His Excellency.
Sun sha bamban da Abraham, shi a fili yake nuna maitar shi wanda yake sawa ayi tunani jikin Majeederh da kyanta ke fisgar shi tare da ingiza shi zuwa tubalin da bashi kenan ba.
Shiru ya biyo bayan maganar ta su ko wanne akwai abinda yake sa?awa a ran shi. Abu-turab ya kasa jurewa hankalinsa yana can kan Jiddo, zuciya ke raya masa yanzu ga su can Wan iska yaron can mai idanu a tsakiyar kai yana yi mata tijara da keta mata haddi, ya samu damar da shi baya tunanin zai samu musamman da bai hango soyayyar shi a zuciyar Malama Majeederh ba.
"No, i can't take it"
"Me za ka yi?" Inji Uncle Isma'il. "Zan nuna masa ni ke mulkarshi, zan yi amfani da ?arfin iko, na manta waye ni, na ajjiya matsayina akan samun Malama Majeederh amma wani na can da ita" "Ba zai cutar da ita ba" cewar Uncle Isma'il.
"Zai aikata abinda ya ce, ai Mahaukaci ne"
"Depression ne"
"Ba su da mara ba, abin da ke gidan ?aura shi ne a Goje, ka bani dama ka kuma share mini fage"
Sai a lokacin Haseenatou ta yi murmushi mai ciwo ta ce "Abin mamaki baya ?arewa, ra?umin dawa ya ga na gida,ko a labaran Hikaya, da film da littafan hausa ban taSa ji ko ganin yadda ake rurrumar auren mace mara tsafta wacce ta haihu ba aure ba sai yanzu" Daga Mama har Abu-turab kallon Haseenatou su ke. "Yes, duk soyayya ta rufe ku,kun makance kun kasa ganin gaskiya na tabbatar da a hayyacinku ku ke ko da kuWi aka haWaku ba zaku taSa sha'awar aurenta ba, to yanzu baku da mara da wanda su ke turo" ta faWa rai Sace domin har ranta bata ?aunar auren Abu-turab da Majeederh.
Ta yi ?wafa ta ce
"Abin da sake an bawa mai kaza kai" Sona da ke tsaye ta ri?e ?ugu ta ce
"Abin nema ya samu, matar dan doka ta haifi Sarawo, ka dai ki ce halin dangin miji ne ya motsa miki?" Kamar Sona na karantar zuciyar Haseenatou, bata da burin daya shige irin Abu-turab ya auri ?ar uwar shi Intisar ta gyara tsaiwa tana kallon Sona ta ce "Aikin banza talaka ya girmi sarki, ina abun yake? Ai da tsohuwar zuma ake magana"
"Hankaka mai da Wan wani naka, na aza cewa kan ki ki kewa farauta, to ai ke kin yi kaWan kuma Anti Jeederh dashen Allah ce, murucin kan dutse bai fito ba sai daya shirya, kuma ?addara bata bar kan kowa ba" har huci Sona ta ke don masifa ta ?ara watsawa Haseenatou harara ta ce
"Hannu Waya baya Waukan jinka, kin yi kaWan a wannan wasan kina iya komawa ki samo nagartattun ?an wasa sai a fafata kuma....,"
"Stop it" Uncle Bello ya faWa yana nunawa Sona hanyar shiga cikin gida ya ce "?ar banza uwar magana,ba ki Wauka a ?asa ba" murmushi kawai Uncle Isma'il ya yi domin surutun ?ar ta shi a yau ya yi rana.
Almustapha shi ma ya ji daWin bayanin Haseenatou, Ubangiji ya sa Aliyu zaki ba zai taSa samun Malama Majeederh ba har abada.
Musty ya kada baki ya ce
"Idan kaga kare yana sunsuna takalmi Wauka zai, ba bu rami mai ya kawo rami Allah dai ya kyauta" Hajia ta watsa masa harara. Duk abinda ake Abbu yana ciki bai fito ba, ba?in ciki kamar zuciyarsa zata fito wai yau ?ar shi ta lalace? Take ?o?arin lalata masa family?.
Ganin yadda duk a kayi shiru kowa yana jimanta al'amarin a ran shi. Uncle Bello ya ce "Ina tunanin mu bar wannan maganar, zamu ?ara zama idan komai ya daidaita"
"Ba zai dawo da ita ba" cewar Abu-turab. Uncle Isma'il ya ce "Zai dawo da ita, da hannun daya Wauketa ka sanya cewa wacce ta haifeka ba zata cutar da kai ba, to Abraham ba zai taSa iya cutar da Maminsa ba"
His Excellency ya dubi Uncle Isma'il, ganin kamar shi ne babba kuma waliyyin Malama Majeederh, ya ce.
"Ka bani dama, ka yi mini alfarma a Waura auren nan" daga ba?in ?ofa Abbu dake fitowa ya ce
"Ni na ce ka auri Majeederh, kuma yanzu na ce kada ka aureta domin zata Sata maka iri, kuma sam bata dace da kai ba" Abu-turab ya ce "Don't say that Abbu, kayiwa mata uzuri, kuma ka nasan ita alheri ce a gareni" murmushi kawai Abbu ya yi kana ya ce
"Allah ya taimaka, ko mene ya faru ka kuka da kan ka" yana faWin haka ya nufi motarshi, Mami na bin bayansa suka shige ya ja ya rufe. Uncle ganin Abu-turab ya kafe ya ce "Ka je, zuwa dare sai ka zo mu yi magana"
"Thank you" "It's my pleasure Your Excellency sauka lafiya" Haseenatou kamar zuciyarta tayi bindiga haka ta shige fuuuu! Ta nufi mota shi na motarshi ya shiga Waya daga cikin motocinsa Chevrolet Silverado. Ash colour, dake tafiyar sirri ce ya sa baya bu?atar motar gidan Gwamnati hatta P.a Winsa Hammad bai taho da shi ba.
Hajia da Papi tare da Almustapha suka ta fi suma gidan ya rage daga Uncle Isma'il sai Uncle Bello da Yaran da suke cikin gidan.
Sosai Abraham ya take giyar motar gudu yake ba tare da ganin abin da yake gabansa ba, idanunsa sun yi jajur ta jikin madubin motar ya hango Aliyu dake biye da su. Ya cije leSe yana girgiza kai a fili ya ce
"Fouk You, zan kashe ka" ya ?ara sanya giyar motar shi ma Aliyu ya ?ara gudu cikin sauri Abraham ya yi reverse kamar zai tsaya hakan ya sanya motar shi ta daki da Aliyu ya ?ara yin baya da motar ta sake hankaWe ta Aliyu kamar zata kifa. Duk yadda ta so share shi ta kame kanta ta kasa ganin da gaske kisan kai ya ke son yi akan Idanunta a gabanta "Meke damunka, zaka kashe shi fa"
"And so f****** what?" Ya faWa yana kallonta, sosai tayi mmkin ganin yadda idanunsa su ka yi bata taSa ganin hakan ba sai ranar da haura cikin gidan su kowa na barci.
Gudu yake sosai tuni ya hankaWe motar Aliyu,ta firgita ba kanta take ji ba Wanta take ji ta runtse Idanunta cikin wata kalar murya ta ce "Stop the car, right there" ya yi mata banza. Hannu Waya ya sanya ya Salle bottle na rigar jininsa da ta yi masa nauyi bai saba saka kaya irin haka ba, yana cire rigar ya cilla ta gidan baya, ya rage sai singlet fara rabin faffaWan ?irjinsa a buWe. Ga Brest Win shi kamar wata ma ce jikinsa duk a murmurWe naman dake arms Win shi sai rawa yake. Ya kai giyar motar ?arshe. "Stop, ka saurara"
Ya yi banza da ita, domin ya fara losing mind Winsa. Da ?arfi tana ?an?ame jikinta ganin sun nufi wani rami ta ce
"Don't, listen to me Little" Cak! Ya tsayar da motar dab da ramin tare da kifa kansa a kan sitiyarin motar ya shiga fitar da numfashi mai zafi yana dafe kansa da yake jin kamar zai rabe biyu.
Yadda zuciyarta ke harbawa haka ta shi take harbawa, ta rasa me zata ce masa, ta san kuma ba zai taSa cewa komai ba. Sun Wauki wasu da?i?o zuwa mintinu ni kafin ya Waga kan shi. ba tare daya kalleta ba cikin turanci ya ce
"Ki shirya mutuwa!"
"Wait!" Ta faWa ya harWe hannu a ?irji girman kai biyu sun haWu, Majeederh ji da kai da nuna isa musamman da take ganin da auren wuri tayi da tuni ta haifi kamar Abraham. Ya sauke numfashi zuciyarsa tayi masa nauyi without looking at her ya ce
"Why!" "Shi ne tsarina"
"Liar" ya furta ya gyara zama sosai tare da juyawa ya kalleta ya ce
"Na ce ki jirani, na jima da bada sa?on haka, mene na cin mutumci haka?" Ta daure ta ce
"Na sha bamban da tsarin ka, You too young"
Kalmar daya tsana ta ce masa wai shi yaro

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login