Showing 9001 words to 12000 words out of 74861 words

Chapter 4 - mijin malama 1&32 Hausa Novels By Nimcey Sarauta.doc

24 Jan 2026

518

tabbas za a gamo Majeederh zata baka mamaki" Aaliyyah dake kuka sosai ta ce "Abbu don Allah ka bawa Yaa Nura dama ya kawo kuWin aurena, na ga ji da zaman gidan nan na tsani komai dake cikinsa" kai tsaye Mami ta ce "Fitowa za kiyi ki ce kin tsanemu, aure kuma dole sai kin kammala makaranta daman ke Waya ki ka rage cikin gidan.." sai a lokacin Uncle Bello ya ce "Aaliyyah aure ki ke so?" Duk kawaicin Aaliyyah ta shanye ta ce "Eh, Uncle"
"Ki faWawa Nura ya zo ya saman a gida nan da sati mai zuwa In sha Allah zaki bar wannan gidan" yana faWin haka ya mi?e tsaye ya kalli Uncle Isma'il ya kalli Abbu ya ce "Yaya taso muje, Allah ya bada ladan zumunci Sunan family kuma a rubuta a gaban ?oshi ana yawo da shi"
Suka fice tare da barin gidan,Abbu ya nufi part Win sa zuciya babu daWi shi kam Majeederh ta zame masa annoba, Aaliyyah ta shige nata bedroom Win tana zuwa ta Wauki wayarta ta kunna network ta shiga facebook inda labarin Majeederh da Bar Aliyu Sufyan Alhassan yake ta trending a media. Ko photon Majeederh ta gani da gudu take skipping ta shige sbd tsaron zagi da mugun alkaba'in da ake mata, tana cikin dubawa taci karo da wani posting photon Majeederh ne sanye da abaya fara mai kyau fuskarta rufe hannunta ri?e da loudspeaker. An yi rubutu a saman photon tare da saka.

*She's Innocent*
_Malama Majeederh Abdul'aziz Khan babbar malamar musulunci da muke da ita a wannan jiha, wacce ta samu damar zama za?a?ura wajan lashe musaba?ar Alkur'ani ta ?asa, ita kuma ta ?ara jawo kima da martabar jiharmu, wacce take taimakon marayu, marasa gata take nutsuwar da matan aure akan darajar da aure yake da shi, duk da kasancewarta budurwa. Abin tambayar shin ta cancanci haka kowa? Kai da ka ke zaginta ko ki ke zaginta kina da tabbaci akan abinda ya faru, ko kina da hujja? Ko labarin ?azan kurege aka baki har kike Worawa tare da aibatar ?ar jama'a, ta haifi wasun ku da yawa, ta fiki ilimi tunani da sanin ya kamata, ta fika kusanci da mahalicci amma kazo media ko sallar kirki a rana baka yi ka Suge da zagin babbar Malama? Ashe muna rayuwa da dabbobi bamu sani ba? Ko masu aikata zina sai an same su turbi da taSarya tare da shaidu 4 sannan za a Wauki mataki. MALAMA MAJEEDERH ABDUL'AZIZ KHAN SHE'S INNOCENT I STAND BY HER SIDE._

#Mrs No name

Wani murmushin jin daWi Aaliyyah tayi 5 minutes da yin posting Win amma comments wajan 1k hakan ya tabbatar mata da Mrs no name yana da followers kuma babban mutum ne tunda har ya iya Soye sunan shi, kai tsaye profile ta shiga ya rufe komai da komai ko message ba za a iya yi masa ba, dole sai dai tayi magana ta comment section.
Har aka kwana aka tashi Bar Aliyu Sufyan Alhassan bai farka daga suman da ya yi ba, hankalin Hajia ya tashi tana da Papi tare da Almustapha, hatta korar da aka yi masa wajan aiki bai sani ba.
Misalin 8 na dare wahala tayi wahala jikin jaririn ya yi zafi kamar wuta, a yanzu ji take ko jama'ar gari za su kasheta babu abin da zai hanata fita ta nemi ruwan da zata bawa babyn nata, ta mi?e da ?yar kusan gabaWaya kayan jikinta sun Saci tana bin gefen hanya harta isa wani wajan da ake siyar da tsire kanta ?asa tayi sallama, gabaWaya mutanen da wajan suka dubeta wani ya ce "Baiwar Allah lafiya?" Ta jima kafin ta ce "Ruwa nake nema, zan bawa yarona" wani saurayi ya dinga kallonta kafin ya mi?e tsaye ya ce "Mene na rufe fuskar?" Ta Wauke kai cikin sa a ya gano rabin fuskarta da jaririn hannun da ?arfi ya ce "Masi?a la'ananniyya mazinaciyya ku je feta ita ce Malama Majeederh" yana faWin hakan ya sauke mata wani dutse a ?oshinta ji ka ke tauu!! Nan take ya fashe jini ya dinga zuba, kafin ka ce me mutane sun cika kowa ya Wakko duwatsu suka fara jifanta ta ko'ina ta dur?oshe ta rungume jaririn da jikinta, jama'a sunfi ashirin idan wannan ya jefa mata dutse aka sai Wannan ya jefa mata a baya...


Na'ima Sulaiman Shu'aibu
Nimcy sarauta
08119237616
[7/7, 12:25 AM] Aunty Mopol: *

Nimcyluv Sarauta
_*Follow my account=?G? https://www.arewabooks.com/u/nimcyluv

African Queen products
Sabulun matsi
Garin matsi
Humra
Turaren wuta
Maganin Infection
Ga number wayata...08130269641


*5.......*
Ta ko'ina suke jifa mata duwatsun jikin ?aramin lokacin suka farfasa mata jiki. Wani saurayi wanda kana ganinsa kasan criminal ne yana da dakakkiyar zuciya ya Wauki wani dutse tare da faWin. "Fasi?a, mazinaciyya, duk yadda akai kema ba ?ar halak ba ce, shi yasa tsayin shekaru talatin da biyar ki ka sa yin aure kina bin mazan aure da samari" yana faWin haka ya sakar mata dutse a goshinta nan take ya fashe jini ya wanke mata fuska,ta fara gani dishi. Sunayen Allah take kira da neman Waukinsa, tsoro ya kamata jin babyn nata ya daina motsi da kukan da yake fatan Waya Allah ya sanya jifan bai same shi ba, balle ya yi sanadin mutuwarsa.
"To, wai me muke jira ne? daga ita jar jaririn mu sanya musu fetur a ?ona mazinaciyya mai ci da musulunci, a kuma ?one mugun iri!"
Wani wanda yake da Wan hankali ya ce "Amma kana ganin ba muyi kuskure ba? Ai ba jifeta ya dace ayi ba, tunda ba matar aure ba ce, budurwa ce bulala ne ya dace da ita" cewarsa.
Saurayin ya ce "A to mene martabarta da matar aure? Ai auren ne ba tayi niyya ba shi ya sa take ta gantali ta shiga rigar addinin musulunci ta ci zarafin Musulunci da musulmai, ita fa yankata ya dace ayi"
Kafin kowa ya sake magana hasken wata dalleliyyar mota ya haske wajan duk da irin fitilar da suke kan hanya.
GabaWaya suka kalla motar mai ?irar Mercedes-AMG G63 Ash colour, slowly yake driving har ya ?ara su wajan, ta cikin motar yake ?are mata kallo ganinta dur?oshe har yanzu ko motsi ba tayi, ya ja idanunsa ya lumshe wani abu ya daki zuciyarsa zafi da raWaWi yake ji sosai abinda yake ji tsayin shekaru ya ?ara yawa a ?irjinsa. Ya fesar da numfashi tare da sanya hannu ya Wan danne gefen zuciyarsa, gently ya gyara Bluetooth na kunnenshi speaking calmly ya ce.
"Meet me at my house right now" Yana faWa ya Wauki face mars ya sanya tare da Waukan Glasses ya saka a idanunsa, cikin tarin nutsuwarsa da kamewarshi wacce ta riga ta zauna a jikinsa musamman yanzu da izzar mulki ke Wawainiyya da shi. Ya fito daga motar fuskarsa haWe duk da babu wanda ya san waye, bai kula kowa ba ya nufeta tare da sanya hannu zai kama nata a firgice ta Wago idanunta tare da girgiza kai cikin wata murya mai rauni da tausayi ta ce
"Kuyi mini komai, ban taSa jikina" "ji banza shashasha, uwar mene ya yi saura a jikin banda najasa...,"
Marin da aka sauke masa ne ya sanya ya yi shiru da bakinsa domin har tsakiyar kansa ya ji marin shatin yatsun His Excellency ya fito raWau a fuskar.
Ya ?ara kai hannu zai ri?e nata hannun domin taimaka mata tayi saurin Wauke hannu kamar bai son magana murya can ?asa ya ce "Please Hawwa'u, akwai jama'a"
Ta girgiza kai numfashinta na fita da ?yar ya ?ara rusunawa shi kansa kamar wanda ya yi jinya ya ce "Haba Jiddo" ganin da gaske take ya sanya ya tattara ?arfinsa waje guda tare da sunkutar ta gabaWaya har jaririn sai cikin mota, ya kwantar da ita a baya ya sanya hannu ya zare jaririn tare da Waukarsa ya nufi Sangaren diver. Yana shiga ya yi wa motar key da hannu Waya ya fara driving cikin sauri Waya hannun kuma ya rungume jaririn, keSantaccen gidansa ya nufa da ita direct.
Wani tsohuwo ya ce
"To ba ga irinta ba, Waya daga cikin kwarton abokin alfashar nata ya zo ya Wauketa, ai ni duk wani Wan shege na daina tausyainsa tunda ana sane ake haifarsa"
Haka suka dinga surutu, suna faWin duk wata mace mai irin shekarun Majeederh wacce ba tayi aure ba to kawai iskanci take tana aikata zina.
Lokacin da His Excellency Abu-turab ya isa gidansa P.a Winsa na tsaye yana jiran zuwansa, Hammad ya nufi Abu-turab wanda yake Wauke da jaririn yana zuwa ya mi?awa Hammad jaririn shi kuma ya koma wajan motar, lokacin Majeederh ta gama sumewa jikinta ya Wauki zafi sosai a ransa yake istigifari kafin ya tattara ya Wauketa cak, sanin halin Abu-turab yasa tuni Hammad ya shige ciki da jaririn wani Sangare ya nufa da ita ya kwantar kan bed, bai tsaya jan aji ba ya samu ruwan zafi da showel ya danna duk inda aka fasa mata tare da yi mata allurar kashe zafi data barci, ya yi mata dressing yana yi yana Wauke kansa, raunin jikinta bai hana shi ganin asalin kyanta ba, asalin kyawun Fulanin Usul. Zuciyarsa kamar tayi tsalle ta fito ya razana da kyanta sosai shi ya sa ko Hammad bai bawa damar shigowa ba sai da ya gama komai ya sanya mata driving tana ta barcin wahala.
After ya gama ya duba babyn. A hankali ya fito yana dafe kansa sbd ciwon da yake masa yana zuwa ya faWa saman kujera idanunsa rufe. "Amma yana da kyau ka huta Your Excellency" ya ware Idanu tare da tsiyaya black tea a cup sai da ya shanye ya ce
"P.a, kana tsaya iya aikin ka" "Am sorry sir, bayan p.a you're my best friend hak?ina ne na faWa gaskiya kuma na kula da kai, idan kana son hak?in Majeederh tana bawan Allan nan kada ya kama mu yana da kyau a bata wasi?ar ta karanta" Sacin rai wanda Hammad bai taSa gani ba ya bayyana kan fuskar Abu-turab, idanunsa da suke a ri ne ya ware akan P.a cikin kakkausar murya ya ce
"Kasan me hakan ke nufi?" Ya shiga kaWa ?afa a duk sanda ransa ya Saci kafin can ya ce
"She never choice me, ba zata taSa zaSata a matsayin miji ba, she most go back to him ba zata gane shekarun da nayu ina jiranta ba" ya mi?e yana kai kawo
"Sunanta na sanya jinina, sunanta na sakawa ?ata Jiddo, ko sunan mahaifiyata ban sanya ba sai nata, shi kaWai ya isa yasa ka gane, zan iya adalci a mulkina al'ummata, amma ba zan iya adalci akan soyayyar Malama Majeederh Abdul'aziz Khan ba, duk hanyar da zan bi na raba ta da kowa zan yi"
Hammad zai magana Abu-turab ya daka masa tsawa ya ce
"Get out" dole ya fita amma shi a ransa ya san babban kuskure ne su ri?e wasi?ar nan.
"Ya Allah!" Abu-turab ya furta yana Waukan gorar ruwa mai sanyi, sai da ya shanye tas kafin ya yi cilli da Robber.
Babyn daman yana wajan wata maid yana ta barci ya ji ruwan zafi da kaya masu kyau ga madara da aka bashi sai numfashi yake saukewa.
Yadda Majeederh ta kwana kan gado haka ya kwana a parlour, lokaci zuwa lokaci yana zuwa a cikin daren sai da ya sanya mata drip uku kansa cewar ruwan na tafiya da sauri. Kiran sallar Subhi ya sa ya nufi bedroom Winsa farar singlet Win jikinsa ya cire ya sakarwa kansa shower ruwa na saukar masa, alwala ya yi ya shirya cikin ash Win jallabiya masallacin dake gefen gidansa ya shiga lokacin ana kuraye kirayen Assalatu....
Assalatun ya yi daidai da farkawar Bar Aliyu Sufyan Alhassan a gadon asibiti ya motsa a hankali yana dafe kansa dake masa ciwo kamar ya rabe gida biyu, dishi dishi ya fara gani kafin ganinsa ya daidaita idanunsa ya sauka akan Hajia ta ce "Zakina, sannu ka ji" ya yi ta kallonta kafin ya juya ya kalli Papa shi ma ya ce "Sannu Haydar, ya jikin?"
"Ba sau?i Papa" Papa ya ce "Meke maka ciwo?"
Ya mutsa fuska ya yi yana rufe Idanu "Meke damunka? Almustapha kira Dr"
"Babu abinda zai iya"
Almustapha ya ja tsaki ya ce "To ai kun ji, shi fa sam baya tausyain kansa ina can gidana tare da matata ku kirani wai jikinsa ya tashi kamar shi kaWai kuka haifa? Mene abin so a wajan wata Majeederh tsohuwar ko me?" Aliyu kamar zai kuka ya kalli Hajia ya ce
"Kin ganshi ko?" Hajiya ta ce "Ka fita idanuna Almustapha, kabar mini yaro ya ji da abinda ke damunsa" "I love her"
Cewar Aliyu. "Kayi ha?uri zaka sameta idan rabonka ce" Almustapha kamar ya sha?e Aliyu haka yake ji ya ?ara yin tsaki ya ce
"Gashi nan an sallame ka daga court Win da ka ke aiki, sai ka zauna zaman kashe wando kana jiran wata" Zaki ya kwaSe fuska ya ce "In sha Allah sai Allah ya Wora maka son wacce bata son ka" Dariya sosai Almustapha ya yi kafin ya ce
"Ai matata ?ar Aljanna ce ta wada tani da komai na kwanciyar hankali to me zai sanya na fara tunanin yi mata kishiya?"
Sai a lokacin Papa ya shiga dramar ya ce
"Shi ma tashi matar ai ?ar Aljanna ce" "Barshi Papa idan ya cika ya zo ya dauki Latifa ya sata a wuta, matar taka duk raguwar mai"
Yana faWin haka ya juya zuwa ga Hajiya tare da Wora kansa a cinyarta ya ce "Hajia zuciyata babu daWi ki taimaka mini" ta shiga lallashinsa ta ce "Yanzu yana da kyau ka shaidawa duniya baka da haWi da Wan gidan Majeederh, after that sai ka fara shirin nemanta ko?" Ya kalli mahaifiyar tasa sosai sai bai ce komai ba. Misalin 12 na rana lokacin an sallami Aliyu zuwa gida yana zaune ya faWa sosai kamar wanda ya yi jinyar shekara kamar daga sama ta faWo bai kalleta ba, ?amshin turarenta kawai ya ji ya fahimta "Ya jikin?" A gajarce ya ce "lfy" ta zauna ta ce
"Amma ka fasa aurenta?" Ya dubeta ya ce "Ita wa?" Kai tsaye ta ce "Waccar Mazinaciyyar mana" ya yi murmushin kawai bai ce komai ba ta ce "Magana nake kayi shiru" ya juya gabaWaya tare da saka hannu ya ri?e fuskarta ya ce "Kina son rabauta ko Wife? Me ya sa ki kewa mijinki haka?" Ta ce "Idan har zaka ?ara aure zaka iya ganin fiye da haka" ya sake ta yana kwanciya jikin kujera ya ce
"Sai dai idan bana raye, Latifa Omar ke baki tausayina ne? Sai fa Majeederh zata zo gidanki ki ke gyarawa, tsafta zero, kwalliyya zero, girki zero, mu'amalar aure zero, aikin ki kawai ki sani, yanzu mene ribarki don ki aibata mijinki? yaran da zaki haifa sune abin zai zamewa tabo not me or Majeederh" ta mi?e tsaye ta ce "Divorce me"
"Never, ki jira zama tare da sweetheart" ba?in ciki ya cika mata zuciya ya zari key car tabar gidan ya bita da kallo.
Tunda ta farka daga nauyayyen barcin ko tari ba tayi ba, tsoran ta buWe idanu taga su waye akanta take, bata so ta samu Wauki ba ta so ace mutuwa ce ta risketa.
Mama dake zaune ta zabga tagumi ta ce "Baiwar Allah kenan, Allah ya saka miki" ta goge hawayen Idanunta Hammad ya ce
"Kamar ta farka ai" Mama ta ce "Ato gwara ta tashi ai, ga Wan yana ta kuka gwanin tausayi" a hankali ta buWe Idanunta ba tare data kalli kowa ba sai gefe guda, yadda take ji zaka Wauka kuka za tai ta rusawa amma idanunta a ?afe komai na tunaninta ya sabunta hanyar da zata bi ta zama cikakkiyar karuwa kawai take nema.
"Sannu Malama, Sannu kin ji" sai a lokacin ta juya ta kalli Mama tana jinjina kai. Gently ta mayar da Idanunta ta rufe daidai shigowarsa yana gyara zama babbar rigar jikinsa, nutsuwa da haiba tattare da shi.
"Barka da zuwa Your Excellency" Abu-turab ya???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? jinjina kai tare da neman kujera ya zauna idanunsa kwance a kanta,daga nan Mama mi?ewa tayi. Jin shirun ya yi yawa yasa ta juya cikin sa a suka haWa idanu tayi saurin Waukewa. A ransa ya ce "Ma sha Allah, Tubarkallah" a fili kuma ya furta "Jiddo ya jiki?"
Ta haWe rai sosai "akwai ciwo?" Nan ma shiru tayi gani take yanzu kowa ya tsaneta. Sosai ya gane bata san waye a gabanta ba domin ?wayar idanunsa kawai ta kalla. Yana ?o?arin magana ya ji ?arar bindiga na tashi ta karaWe gabaWaya gidan, ya buWe idanu da mamaki yasan akwai securities amma harbin na mene? Hammad ya fice da sauri tsoro ya kama Majeederh ta runtse Idanunta cikin rauni ta ce "Ni za a kashe"
"What? Kisa wake shirman haka" ya ajjiye babyn ta Wauke Wanta da sauri ta duba hijabin dake gefe wanda yake sabo ta Wauka ta saka jikinta jiri na Waukarta ta rungume Wanta tare da nufar wajan domin ta mi?a kanta gare su.
His Excellency Abu-turab Al?asim ya fito yana kallon Hammadala dake Soyewa cikin nutsuwa ya shiga nufar wajan da harbin ke tashi Hammad ya ce "No Your Excellency, kada ka je wani Mahaukaci ne da bindiga yake harbi kawo yanzu ya harbi securities guda uku"
"In my house? Mahaukaci?" Hammad bakinsa na rawa ya ce "Yes Sir, kuma wallahi ri?a??en Mahaukaci ne kayan jikinsa tamkar sun yi shekara Wari a jikinsa, gabaWaya jikinsa zane ne kamar na tattoo gashi ba?i??irin...

Na'ima Sulaiman Sarauta
08119237616
[7/7, 12:25 AM] Aunty Mopol: *

Nimcyluv Sarauta
*_Follow my account=?G? https://www.arewabooks.com/u/nimcyluv


*6......*
His Excellency Abu-turab ya dubi P.a Winsa Hammad ganin yadda jikinsa yake ta rawa kamar wanda aka ce masa ba zasu ?ara samun mulki ba. "Your Excellency abun nan yana neman girmama, mu sanar da securities na Government house" Abu-turab dai bai ce komai a hankali ya ci gaba da takawa har zuwa tsakiyar compound na gidan nasa, ya shiga ware idanunsa akan securities Winsa da aka harba wanda suke kwance a ?asa. Ya Waga kai ya dubi wanda yake tsaye ya juya masa baya, cikin nutsuwa ya shiga ?arewa yaro ko matashin saurayin kallo.
Cikakken namiji ne a tsaye, ya ri?e ?ugunsa da hannu Waya, Waya hannun ri?e da bindiga ga jini yana zuba daga hannun, ba?i ne irin sosai Win nan fatarsa har she?i take gabaWaya wuyansa zanan tattoo ne kamar wanda aka zanawa macizai, sumar kansa a cure take ta wani murmurWe kamar indomie ta sauka har wuya, wani irin crazy

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login