Showing 57001 words to 60000 words out of 74861 words

Chapter 20 - mijin malama 1&32 Hausa Novels By Nimcey Sarauta.doc

24 Jan 2026

533

kawai a ciki" Latifa Omar tayi kamar karta shiga haka kurum jininta bai zo Waya dana Alpha Bello khan ba, baya kulata ko gaishesa ta yi, sai kuma ta mi?e tsaye daman tuni Aliyu ya mi?e tayi gaba ya bi bayanta a hankali ta murWa handle Win ?ofar tare da shiga bakinta Wauke da sallama, ta matsa gefe Aliyu ya shigo idanunsa ya sauka akan Majeederh da kanta ke cinyar Alpha sai kuka take rusa masa mara sauti wanda ya fi ko wanne cin rai, yadda idanun Alpha ya yi jajir zai baka tabbacin kukan na Majeederh yana taSa masa zuciya. Aliyu ya dinga kallon yadda Majeederh kewa Alpha kuka kana gani kasan kukan data jima tana tarawa a zuciyarta ne, ya rasa kukan na mene? Hannunsa ya sauka akan hannun Alpha da yake Wan shafa kan Majeederh da sauri Aliyu ya juya har yana birgewa da ?ofa jiri na Waukarsa ya fice daga room Win, Latifa ta biyo bayansa, Uncle Isma'il dake tsaye shi da Dr ya dubi Barrister Aliyu ya ce "Badai har kun gaisa ba?" Ya daure murya can ?asa ya ce "No, zan dawo" Yana faWin hakan ya nufi harabar asibitin tare da shiga mota ko Latifa dake kiransa bai saurara ba yaja motar da gudu yabar asibitin...
Alpha ya Wago Majeederh ya kasa cewa komai can ya sauke numfashi ya ce "It's okay, stop crying" Ta kasa daina kukan harda shasshe?a daman kuma Alpha ne kawai ke iya jin zurfin cikin na Majeederh tun tana yarinya, ya sa hannu ya ri?o fuskarta ya kalleta ya ce "What again? Kina so ni ma na shiga damuwa ne?" Ta girgiza kai ya ce "Gashi kina ta kuka, 20 yrs kamar yarinyar goye" Ya sa hannu ya share hawayen fuskarta a hankali ya cire hannunsa ya yi shiru, Majeederh ta ce "Kada ka faWawa kowa abinda nace please" Ya kalleta kawai ta ?ara marairaice fuska ta ce "please" A hankali ya ce "Ok" kasa ci-gaba da ganinta haka ya yi a hankali ya fice daga room Win yana jinta tana wani kukan. Anti ta tsare Alpha da idanu ta ce "Har yanzu bata ce maka komai ba? Na yi mmki" Maman Alpha dai kallonsu kawai take da idanu dake magana bai dameta ba, Uncle Isma'il ya ce "Lallai al'amarin babba ne tunda har ta kasa cewa Alpha komai" Alpha bai tsaya ba ya nufi wajan Dr ya biya bills na komai kana ya dawo ya ce "Uncle zamu iya tafiya" Anti ce da kanta ta shiga wajan Majeederh ta bata hijabi ta zura kanta a ?asa suka shiga motar Alpha kai tsaye kuma Gidan Abbu ya nufa, lokacin Abbu yana zaune saman kujera yana duba littafi Anti ta yi sallama hannunta ri?e dana Majeederh sai Maman Alpha, Uncle Isma'il da Aaliyyah da sauran napep suka shiga shiyasa tafiyar bata yi daidai ba. Bayan sun gaisa da Abbu suka nufi ciki har kan gado Anti ta kwantar da Majeederh ta ce "Ki kwanta ki huta sosai, Kinga ace 7 jirgin naku zai ta ce" Ta juya ta kalli Wakin ta ce "Kin dai gama haWa komai?" Majeederh ta ce "Na ji sau?i fa, na gama" Ta ce "To Allah ya ?ara afuwa, bari ni ma duk na gaji kwana biyun nan" Mami ta yi musu godiya suka samu Alpha zaune da Abbu Maman Alpha ta ce "Kai fa?" Ya Wan yatsuna fuska ya ce "Momi kuje kawai, ga kuWin napep" Ya zaro dubu biyu ya bawa kowa duba Waya suka tafi, Abbu da Alpha suka ci-gaba da magana har aka kira Magriba suka nufi masallaci a tare. Mami na haWa abincin dare Alpha ya yi sallama ya shigo parlourn Mami ta ce "Soja mazan fama, sai da ranka akan na wasu" Ya shafa kai kawai bai ce komai ba ta ce "Ga abincin dare zauna ka ci" ya ware idanu ya ce "No thank you, am full" Mami ta haWe fuska ta ce "You're always full dama" Ta ?ara cewa "Tana ciki ai" Ya nufi Wakin Majeederh ya sameta zaune saman ladduma tayi wanka ta sauya kaya kanta a ?asa, shi kuma ya tsareta da idanu kamar zai magana sai kuma ya ajjiye takeaway Win hannunsa tare da fita.
Har aka kira sallar Issha Majeederh na zaune tana azkar, turo ?ofar Wakin aka yi Mami ce ta shigo ta kalli Majeederh ta ce "Kizo inji Abbu" Tana faWin hakan ta juya tabar Wakin, sosai gaban Majeederh ya faWi ko sunan Abbu aka kira sai ta ji faWuwar gaba, gudun kada ta yi laifi ya sa ta ajjiye azkar Win ta nufi waje ta samu su Raihana a parlour suka dinga yi mata sannu, ta samesa a zaune yana wanke hannu zai ci tuwo ta yi sallama ya amsata ta nemi waje ta zauna. Cikin Sacin rai ya ce "Ni mahaifinki Majeederh zaki tuzarta? Sbd ki nunawa duniya forcing naki nayi zuwa Misira kika kwanta ciwo? Na haifi yarinyar da zata haWa da ?an-uwana Majeederh ni zaki saka ciwon zuciya? Sbd na nemi alfarma a wajanki? Ko ri?onki nake ban cancanci ki wula?anta ni ba irin wula?antawar da ki kai mini yanzu ba, babu komai ki je na soke tafiya Masar Win" Majeederh ta zube akan ?afafuwanta ta shiga girgiza kai idanunta cike da hawaye ta ce "Ka yafe mini Abbu, na tuba na bi Allah na bika, wallahi ban san na faWi ba gani na kawai nayi a gadon asibiti, kuma bance bani da lafiya ba, bance kai kace naje karatu ba, ni nake son karatu nina zaSi tafiya Egypt ba kai ba, na shiga uku idan kalamanka su ka yi tasiri a gareni, ka yafe mini na tuba na bi Allah na bika Mahaifina, ka yi mini komai yanzu ya kamata na baka farin ciki gwargwadon yadda zan iya" Abbu ya haWe rai ya ce "You surprised me, as your father you will humiliate me, ni Majeederh? Har kin yi girma hakan? Ba zaki iya sacrifice akaina ba?" Jikinta duk rawa yake ta gigice da kalamansa wani irin kuka take kamar zata haWiye zuciya ta ce "Ka yafe mini don Allah, ni mai laifi ce na yi alkawarin zan yi karatu zan yi aiki duk acan ?asar, har sai mutuwa ta riskeni ko ka bani umarnin dawowa?" Abbu ya sauke numfashi ya ce "Kin yi mini al?awarin zaki aiki a can?" Ya jinjina masa kai sbd kuka ya ci ?arfinta ya ce "Allahamdu lillahi, idan ki kai hakan kin gama mini komai Allah ya yi miki Albarka maza jeki kwanta kada ki makara" Ajjiyar zuciya ta sauke tare da mi?ewa tabar Wakin ta nufi nata tana jin kamar zuciyarta ce zata faWo......
A can Darmanawa a rikice Aliyu ya shiga cikin haWWen gidansu lokacin Hajia da Almustapha da Papa suna zaune a parlour Almustapha ya ce "Papa amma Gwamnati mai ci a yanzu tana ?o?ari, na ji Walibai wajan Wari biyar aka Wauka scholarship shi, hadda allowances every month" Papa ya ajjiye remote Win hannunsa ya ce "sosai ga hukumar jakadanci ta jiha ta saka hannu, haka na tsaro, hukumomin fikira, da tawaga ta musamman duk an zuba idanu akan Waliban gudun samun matsalar rikicin ?abilanci, ko wani abu" Almustapha na ?o?arin yin magana Aliyu ya shigo babu ko sallama hannunsa ri?e da kansa, Hajia ta mi?e da sauri ta ce "Zakina Lafiya? Baka da Lafiya ne? Meke damunka?" Aliyu ya kasa cewa komai sbd parlourn dake juya masa a hankali ya ce "Hajia lulluSeni san yi nake ji" Hajia da bata jure rashin lafiyar yaran nata gabaWaya ta rikice ta ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Aliyuna mene ya sameka yanzu ka fita lafiya lafiya fa?" Papa ya kalli Almustapha ya ce "Kira Dr" Almustapha ya juya da sauri zuwa Wakko waya, Papa ya kama Aliyu ya kwantar saman duguwar kujera sai rawar sanyi yake idanunsa rufe jijiyoyin kansa duk sun fito, Hajia ta fashe da kuka ta ce "Na shiga uku mayu sun kama mini yaro, yarana kwaya biyu kacal a duniya shi ne za a ga bayan Wayan?" Papa ya dinga kallon Aliyu shi kansa ciwon ya bashi mamaki, Aliyu dake cikin ciwo ya kama hannun Hajia ya ri?e ya ce "Ki danna mini ?irjina Hajia, zuciyata zata fito waje" Hajia ta ?ara saka kuka, daidai nan Almustapha ya dawo babu jimawa Dr ya zo allura ya yi masa tambayar duniya ya faWi meke damunsa amma ya?i. Suna zaune har bacci ya Wauke shi a cinyarsa Hajia yana sauke numfashi a wahale..
Har gari ya waye bacci baiga idanun Majeederh ba, ana kiran sallah ta tashi tayi wanka tare da yin Sallah ta jima tana addu'a sosai kafin ta shirya cikin wata duguwar riga Maroon tayi rolling kanta. Tana tsaye Latifa Omar ta shigo idanunta ya yi jaa taci kuka son ranta ta ce "Wai ki fito ba lokaci" Murmushi Majeederh ta yi ta ce "Haka aka damu dani? Irin wannan kuka" Latifa ta sake fashewa da kuka, bata hanata ba don dai itama taiwa kanta al'?awarin daina kuka ne, da babu shakka sai tayi nata kafin ta tafi, safiya ce amma ?an-uwa sun cika gidan Abbu kowa yana son ganin tafiyar Majeederh, tafiya ce wacce ba lallai a sake ganin juna ba, inma ita ta mutu inma su, kanta a ?asa ta fito daga nan suka rankaya airport, anan sukai ta ganin Walibai masa da mata, kasancewar a makare suka ?arasu wajan yasa ta shiga sallama da mutane ta ?arasa wajan Abbu ta ce "Abbu na tafi ka yafe mini don Allah" Ya ce "Babu komai, Allah ya bada sa a" haka ta dinga bin mutanen wajan tana zuwa wajan Aaliyah ta rungumeta, a can gefe ta hango Alpha yana tsaye rungume da hannunsa, uniform Win sojoji ne a cikinsa amy colour ta nufi inda yake ya kalleta bai ce komai a hankali ta ce "Na tafi" Ya gyara tsaiwa ya ce "All The best, ki kula" Za ta yi magana ya yi saurin shigewa mota, sai a lokacin hawaye ya taro a Idanunta ta nufi cikin wajan har tayi nesa da su kai tsaye jirgin ta shiga sai da ta zo matattakalar ?arshe ta Wago kanta ta kalli ?an-uwanta kamar ance ta kalli gefe idanunta ya sauka akan Aliyu hannunsa ma?ale da carnoner...


MIJIN MALAMA
08119237616
Uhm get ready...... Yanzu zamu fara>?y?
[7/7, 12:26 AM] Aunty Mopol: Alhaji Bashir ya gyara tsaiwa yana shu'umin murmushi ya ce "Bana Waukan asara ba kuma zan fara akan ka ba, ka yarda zaka bani auren yarinyarka Majeederh? Ni kuma na baka dukkan abin da ka ke so?" Abbu bai dugun tunanina ba ya ce "Na baka aurenta ?ata Majeederh halak makal, ko bayan bana raye" Alhji Bashir ya ce "Baka raye to waye zai tashi matsayin shaida?" Ya yi jim kafin ya ce "Allah da Manzonsa su ne shaidar hakan?" Alhaji Bashir ya haWe fuska ya ce "Na san da haka, amma mutane huWu shaidu nake so" Abbu ya shiga nazari idan ya ce a'a ya san tabbas zai dauma cikin wannan gidan nasa da baya samun ci-gaba, mafarkinsa na zama wani a duniya ba zai tabbata ba, hanya Waya ce wacce ta kasance madafar shi shi ne  Majeederh Abbu ya ce "Zuwa dare sai ka dawo ni kuma zan haWa maka shaidun" Alhji Bashir ya ce "Never mind, Allah ya kaimu" Su kai sallama Alhji Bashir ya shiga mota ya tafi, Abbu kuma ya koma gida. Yana shiga ya samu Mami zaune ya nemi waje ya zauna tare da yin shiru yana mamakin abin da ya hana Majeederh kiransa gashi har anyi kwana biyu.
"Lafiya?" Ya sauke numfashi ya ce "Ina yaran? Aaliyyah, Raihana, Ruma?" Mami ta ce "Ruma ta tafi raka Imran, Aaliyyah da Raihana sun je gidan Widad" Abbu ya numfasa ya ce "Rumana ta dinga janye jikinta daga yaron nan"
"Wanne yaron?" Abbu ya tsareta da idanu babu alamar wasa ta yi saurin cewa "Naga aurenta zai yi shiyasa bana damuwa" Abbu ya ce "Kina da tabbacin haka? Baki san meke Soye ba" Mami ta yi saurin cewa "Me ka ke nufi? Bayan shi ya ce yana son ta zai aureta?" Bai ce mata komai ya mi?e ya shiga duba gidansa lungu da sa?o deep down na zuciyarsa yana tunanin wa zai kira matsayin shaidu?...
Da daddare misalin ?arfe tara Latifa Omar na kwance idanunta a sama kewar rashin Aminiyyarta na damunta, ga rashin kiran Aliyu wayarsa ma gabaWaya a kashe take, she so much loves you ya yi tasiri a zuciyarta sosai. Ta ?ara juyawa idanunta rufe a hankali ta sake jawo wayarta tare da danna kira a number da tayi saving da  Heart choice Cikin sa a kiran farko ta ji an Waga a marairaice cikin damuwa ta ce "Sweetheart" Almustapha ya yi shiru yana gyara zaman wayar a kunnenshi tare da juyawa ya kalli Aliyu dake kwance saman gadon asibiti ya yi mahaukacin ramewa "Hello"
Muryar Latifa ta sake dawo da shi hayyacinsa ya ce "Majeederh Abdul'aziz Khan, right?" Latifa ta zaro idanunta waje zuciyarta na bugawa, mene haWin Aliyu da Majeederh? Ta yi shiru tuna muryar da ta ji kamar bata Aliyu ba, a hankali ta ce "No, Latifa Omar ke magana, Aliyu fa?" Ta yi saurin tambayar hakan cike da bin umarnin zuciya. Almustapha ya ce "Ok, mai wayar yana kwance asibiti" A ruWe cikin tashin hankali idanunta har ya ciko da hawaye ta ce "Subuhanallahi! Wanne asibiti" Musty ya ce "Aminu Kano"
"Am on my way" kafin ta ajjiye wayar ya ce "Amma kamar dare ya yi, da kin bari zuwa safiya" Ta girgiza kai kamar yana ganinta ta ce "I can't, ba zan iya bacci bangan shi please" Musty ya ce "Ok, daman daya farka ke ya kira, so na kira ki wayar a kashe shi ne ya ce a nemi Malama Majeederh kuna tare" Ya faWi hakan yana gyara Sarnar da ya yi a baya. Daga haka ya yi hanging off.
Papa dake jin duka maganganun Musty da Latifa ya ce "Me ya sa kayi mata ?arya Almustapha Sufyan Alhassan?" Almustapha ya shafa kansa ya ce "Shi ne mafita Papa, zan so a Waura auren shi da Latifa in prioud time. "He doesn't like her" cewar Papa. Almustapha ya ce "Yanzu mene amfanin haka Papa? Duk jiya yake kira mana suna Waya Majeederh, Hawwy, Hawwa'u, na tambaye shi me ya sa yake son Latifa bayan Majeederh ce a bakinsa?"
"Me ya ce?" In ji Papa.
"He refused to answers my question" Hajia ta juya kan Aliyu dake jin duk abin da suke faWa amma idan ka ganshi zaka Wauka bacci yake, hannunsu dake danne da ?irjinsa kawai ke motsawa dalili bugawar da zuciyarsa ke yi.
"Me ya sa Zaki?" Ya buWe gajiyayyun idanunsa da sukai jajur kamar ba zai magana ba har Hajia ta ?ara cewa "Meke faruwa ne?" Ya yi saurin ri?e hannun Hajia ya ce "Ban sani ba, Amma ina sonta a gefena" "Aurenta za ka yi?" Hajia ta tambaya tana ri?e nasa hannun.
"A duk sanda na ji ina son aurenta sai na ji na tsaneta, amma idan na cire batun auren sai na ji babu wacce nake son gani sai Majeederh, i want to see by my side, ko sunanta na ji zuciyata bugawa take don Allah ki taimaka mini Hajia please" Papa ya yi zuru yana ganin ikon Allah, wani abu mai kama da almara. Bai taSa ganin hakan ba, ko a film na hausa, Indian movie ko series balle novels, ace wacce mutum ke son aura daban wacce kuma take zuciyarsa daban "Ikon Allah" Cewar Papa Hajia ta ce "Ikon gaske, Yanzu me ka keso" Cikin sauri Aliyu ya ce "Majeederh na keson gani Hajia please" Hajia ta zabga tagumi Idanunta jajur alama ta jima tana kuka domin tun jiya Aliyu bai san inda kansa yake ba sai yanzu, Papa ya sauke numfashi cike da jimamin al'amarin da kuma tausayin Wan nasa ya ce "Zan nema maka auren ita Majeederh a wajan Mahaifinta idan ka amince, kada ka sanwaltar da rayuwarka akan ta" Aliyu ya girgiza kai ya ce "Ba aurenta zan ba" Almustapha dake tsaye harWe da hannu ya ce "Ok ita Teddy ce da za a ajjiye maka ita kai ta Kallonta? Me ya sa ka ke son kan ka har haka? Kana ganinta, But you don't want to marry her? what kind of nonsense and stupidity is that??" Aliyu ya marairaice ya ce "Ka tausaya mini Yaya, ni kaWai na san halin da nake ciki idan kai baka rarrashi su Hajia ba waye zai taimaka mini?" Jikin Almustapha ya yi sanyi ya ce "Papa Hajiya help him don Allah kada wani abu ya same shi" Papa da ran shi ya fara Saci ya ce "Ok kai ma da kake da hankali kenan ko? To ba zan Wauki wannan haukan ba, zan je na nema masa auren Latifa Omar ?ilan hakan zai sanya ya manta da batun Majeederh" Wani irin rikitaccen kuka Aliyu ya saka jikinsa sai rawa yake ya ri?e Hajia da ?arfi numfashinsa na sar?ewa yana ri?e ?irjinsa, Almustapha ya shiga faWin "Dr... Dr... Dr.." Likitoci suka haWu akan Aliyu da ?yar suka dawo da numfashinsa tare da yi masa allurar bacci dake jininsa mai ?arfi ne sai bacci ya gagari idanunsa ya dinga surutai. Dr ya kalli su Papa ya ce "Alhaji zaku tafka babban kuskure idan zaku dinga yin abin da zai Sata masa ran shi" Papa ya kasa magana sai kan shi da yake jinjinawa. Suna haka wayar hannun Almustapha ta fara ringing ganin sunan  Latifa Omar ya sanya ya Waga kiran "Ok" ya furta yana barin cikin Wakin, not too long suka dawo tare da Latifa da kanta ke ?asa sanye da hijabi ta yi sallama tare da dur?osawa ta ce "Ina yini ya mai jiki?" Hajia ta dinga kallon Latifa Omar frm head to toe a ta?aice ta ce "Alhmd" kana ta mi?e ta bar Wakin, Papa ma ya fita Almustapha ya ajjiye wayar Aliyu ya fice wajan ya rage daga Latifa Omar sai Aliyu dake kwance. A hankali ta mi?e ta zauna a gefen gadon ta ce "Nasan ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login