Showing 69001 words to 72000 words out of 74861 words

Chapter 24 - mijin malama 1&32 Hausa Novels By Nimcey Sarauta.doc

24 Jan 2026

531

in the garden" Ya nemi waje ya zauna idanunsa akan Majeederh kaWan, Latifa tayi dry ta ce
"Nikam how long ka Wauka ba kaga bestie ba?" A takaice ya ce "I can't remember."
Latifa ta zauna kusa da shi "8yrs going to 9 fa, tunda yanzu muna end of the year ne, gasky yau ya kamata ayi hirar yaushe gamo" Sosai Majeederh ta fahimci daga matar har mijin neman magana suke. Aliyu ya ce
"Bestienmu ina yini?"
A cikin nutsuwa a takaice ta ce "Allhamd, ya jiki?"
"Sai godiyar Ubangiji jiki"
Bata sake cewa komai ba ya juya kan Latifa ya ce "Wife yunwa ina ji sosai, wallahi kamar zan ci babu" Yadda ya langwaSe kai da yanayin daya nuna yunwar yake ji da gaske kuma bashi da ha?uri akanta ya sanya Majeederh lumshe idanunta tunanin Little ya faWo mata, ko yana raye ko ya mutu ko yana wacce duniya? Sai ta ji zuciyarta ta karaya ?afarta tayi sanyi. Latifa Omar ta ce "Bestie taimakawa sweetheart da Superghetti"
"What?" Majeederh ta faWa lokacin da maganar Latifa ya dawo da ita daga tunanin ?anta Little. "Kinga bana jin daWi, warin gas hawar mini ka yake ki taimaka please ki dafawa Sweetheart wani abu" Majeederh ta zare idanu har sai dai Aliyu ya Wan sauke numfashi kamar ba zatai magana ba sai kuma ta ce "Amma kin san am not your maid?"
"Mun sani" Aliyu ya ce
"Don Allah, please Bestie me" Latifa ta faWa a marairaice. Tasan weakness na Majeederh da zarar ka haWata da Allah magana ta ?are, Majeederh ta ja gajeren tsaki kamar wacce akai forcing nata wajan magana ta ce "Kitchen"
A tare suka nufi Kitchen Win, Latifa na nuna mata ta dawo tare da zama kusa da Aliyu ya Wan ja gefe da sauri ta ce "Me kuma?" Ya dubeta yana girgiza kai ya ce "Baki jin kunya?" Ta juya masa idanu alamar "Kunya? Akan me kuma"
Ya taSe baki yana faWin "Rayuwarki abar tausayi ce, ban yi zatonki haka ba gaskiya" Latifa ta ware Idanu akan Aliyu ta ce "Kayi mini bayani, bana fahimtar wannan zancen" Ya ce
 ina nufin ?azantarki"
Latifa ta ce "Sbd ka ganta?" Cikin rashin fahimta ya ce "Wa kenan?" Ta yi masa shiru ya ce "Yanzu ke baki ji kunyar Hawwa'u ba? Riga daban, zani daban, abin kanki daban? ?amshin parlourn daban da warin da yake fitarwa daban? What exlty wrong with you Latifa? Haka zaki haifi yara kina wannan ?azantar su tashi da abinda suke ganin kina yi?" Bakinta cike da yawo ta buWe zatai magana ya yi saurin Wauke kansa zuciyarsa na tashi.
"Oh! Daman fa haka ku maza kuke bazan kasan dalili banda cikin dake jikina har zaka ce haka?" Aliyu ya Sata fuska ya ce "Sbd Allah duk matan da mazan su ke musu ciki haka suke wannan azababbiyar ?azantar? Parlour warin yawo, part Winki haka nikam na shiga uku" Zata buWe baki sai ga wayo zarara Aliyu ya yi saurin tashi ta juya kanta bayan kujera ta zubar da yawo ta ce
"Nikam ina yin iya bakin ?o?arina, baka da godiyar Ubangiji" Aliyu ya kasa cewa komai dan takaici can ya ce "Tun satin aurenmu ai haka kike, matsalolinki nada yawa idan zasu zan yi a zuciyata tsaf zata buga tunda na kawo abokaina suka ci abinci suka dinga amai na sare miki, ciki kuma wannan shi ne na biyu wancan ya zube wannan kuma sai ki kula zan kawo ?ar aiki kawai" Ta yi saurin mi?ewa ta ce "Kan uban nan a wanne gidan zaka kawo ?ar aiki? Ai wallahi baka isa ba, tsohuwo ko yarinya bana mara ba da su, haka kurum a aure mini miji, matan yanzu da basu da mutumci kamar mayu haka suke akan mazajen wasu musamman yanzu da za a saka ?an candy marriage, ina son ka ina Mahaukacin kishinka kai ka sani kuma......," Shiru tayi ganin Majeederh na shigowa cikin parlourn hannunta ri?e da wani kyakkyawan warmer wanda Latifa bata taSa amfani da shi ba, Kullum a warmer Waya take zuba masa abinci idan tayi ma kenan. Latifa ta yi murmushi ta ce "Thank you Bestie sannu da aiki" Majeederh ta Wora warmer Win akan table tana nuna tamkar bata jin Conversation Win su ba, Aliyu ya dinga satar Kallonta Majeederh na ?o?arin mi?ewa Latifa ta ce "Ina zuwa"
Ganin ta nufi part Winta yasa Aliyu shafa cikinsa ya ce "Zuba mini please" Ta cikin li?ab ta harare shi sarai ya gani sai kawai ya shafa kansa yana jan plate tare da zubawa a ciki, sosai Superghgett take tashin ?amshi gashi ta sha sadin, kasancewar kaWan ta dafa kuma gas ne ga komai a zube ya sa cikin ?aramin lokaci ta gama dafawa. Idanunsa ya rufe lokacin da daWin abincin ya ratsa cikin kunnuwansa GabaWaya jijiyoyin da suke amsar sa?o zuwa ?wa?walwar sun Wauka tuni sun kaiwa tasa ziraya, cin abincin kawai yake hannu baka hannu kwarya har ya mance Majeederh ce gabansa, ya daWe bai ci abincin mai daWinsa ba. Ya goge bakinsa da tissue a hankali yana kallonta ya ce.
"Kin ceci rai" Ba tayi magana ba, ya saita murya ya ce "You're the best cooker Hawwa'u thank you" Mi?ewa tayi bata jira zuwan Latifa ba tayi gaba abinta tare da ficewa daga parlour bakiWaya... Shigowarta compound Win ya yi daidai da fitowar Abbu daga cikin mota, har zai tafi sai kuma ya tsaya yana Kallonta har ta ?arasu, Majeederh na zuwa ta zube a ?asa ta ce "Barka da dawowa Abbu, ina yini?" Ya dinga Kallonta kafin ya ce "Lafiya, daga ina?"
"Gidan Latifa..." Ta bashi amsa kanta a ?asa tana wasa da yatsun hannunta ya numfasa ya ce "Ki sameni a part Wina" Yana faWin hakan ya juya cikin gidansa nasa wanda ya zama sai mai hannu da shuni ne kawai iya gina gida kamarsa, iya compound na gidan abin kallo ne balle kuma ciki wanda duk sanadin ?ar cikinsa Majeederh ya same su ta tara masa kuWi na ban mamaki. Lokacin data shiga main parlour tuni Abbu ya shige Sangarensa Mami ce kawai zaune tana kallon shirin Mata a yau, ta shiga da sallama tana cire li?ab Win fuskarta tare da zama, Mami ta kalleta ta ce.
"Sai yanzu?" Ta ce "Eh" Ta ?ara cewa "Zaman me ki kai a gidan ma'aurata?" Kamar zatai shiru sai ta ce "Latifa bata jin daWi shi ne naiwa mijinta girki" Da mamaki sosai Mami ke kallon Majeederh ta rasa ma me zata ce kafin ta ce
"Ba kiji nauyin cewa Aliyu ki kai abinci ba? Ba kiji nauyin furta kalmar nan ba? Mijin Aminiyyarki ki kai girki? Ban taSa jin haka ba ko da wasa na Asabe" Mami ta ?ara tafa hannu ta ce "Sai kika shige madafa kika bar miji da mata a parlour suna jiran abinci" Majeederh kanta a ?asa ita sam ba taga aibun hakan ba, tunda taimako ta yi Mami ta ce "To li?ab kika cire?" Ta girgiza kai ta ce "A'a" Sai a lokacin Mami ta sauke Soyayyiyar ajjiyar zuciya kafin ta ce "Na gode Allah" Mi?ewa ta yi ta nufi part Winta, bayan ta shiga ta nufi toilet tare da yin wanka ta Waura alwala wata jallabiya ruwan toka ta saka mai yafin farin duwarwatsu bayan ta idar da sallar Asr tayi azkar idanunta rufe ta shiga tilawar Alkur'ani ta yi hakan ne sbd rashin abin yi kuma bata son yin baccin Asr, tana nan zaune Mami ta murWa handle Win bedroom Win Majeederh ta shigo daga tsaye ta ce
"Zaki mana dinner" A sanyaye Majeederh ta ce "Mami kai na ciwo yake, tunda na dawo ban yi bacci ba, can ma ba bacci nake ba" Mami ta saki ?ofar ta shigo tare da zama saman gado ta kalli Majeederh ta ce
"Kenan Raihana ko Ruma zan kira daga gidan mazajen su suyi mana ko?"
"Sun tafi ne?" Cewar Majeederh, Mami ta ce "Da ke zasu tsaya su taya zaman gida bayan su Allah yaye musu wannan ?addarar? Majeederh shekarunki nawa yanzu ne?" Kanta a ?asa zuciyarta na bugawa ta ce "28"
Mami ta ce "To da kyau tunda har kina lissafe, Sahar a gabanki aka haifeta yanzu yaranta huWu cif, Widad a gabanki aka haifeta haihuwa ta uku ta biyu za tayi a hakan ma don Allah bai bata da wuri bane, Raihana, Ruma duk akan idanunki aka haife su ita Ruma cikin ne baya zama, ita Raihana Allah ne bai bata ba, duk wannan ba zai sanya kiwa kanki karatun tanatsu ba Hawwa'u? Me kike nema a duniya, kina da kyau, kina da iliminki, kina da kuWi mene ya yi saura?"
Majeederh ta kalli Mami jin ta ce tana da kuWi, bayan ko ?wandala bata da shi da sunan mallakinta, komai data mallaka a Misira ta sallamawa Abbu. Mami ta gyara zama ta ce
"To na fara gajiya nikam, gashi nan jama'ar gari sun fara zagina da ?ana nan gulmace-gulmace akan wai an tura ki neman kuWi ba wani karatu da kike, wasu ma cewa suke neman maza kike gashi nan baki aure ba, kuma bama ta kuraki akan aure kina neman tsofe mana a gida" Tunda ta fara magana Majeederh ta kafe Mami da manyan idanunta wanda gefe Waya ya yi ja sbd ciwo Kallon nata kawai take amma tunaninta yana wani waje guda, kalmar neman maza ta girgiza Majeederh ta kasa fahimtar wake neman mazan? "Kina jina?"
"Wake neman maza?" Majeederh ta faWa muryarta na rawa Mami ta bata amsa da "Ke mana, kuma dai bani da shaida akan ki Wana ne ka haifa baka haifi halinsa ba, tunda gashi sam baki damu da rashin auren naki ba" Kalma  Zina babbar kalma ce wacce a duniya ta tsaneta balle mai aikata yinta amma ita ake ?o?arin la?abawa wannan muguwar kalmar? Bayan data aikata zini gwara ta kashe kanta kawai ta huta, da zina zatai ko yawan bin maza ai tun kafin tabar ?asar zata fara sbd abinda ke damunta, sai yanzu ne da Allah ya ye mata dukkan wani abu da take ji zata fara zina? Bayan shi isn't interested at all! ?igon sha'awa yanzu babu a tare da ita, ta wannan Sangaren har mancewa take ita Wiya macace?... Kai ta Wago ta ce "Allah ne shaidata"
"To Allah ya rufa asiri, kin tabbatar kafin shekarar nan ta ?are kin kawo mijin aure, idan ba haka ba wallahi sai ranki ya Saci kinfiso muna jerawa a gida muna haWa kafaWa? Kuma daga yau duk wani aiki na gidan nan ke zaki nama sallami ?ar aiki, Aaliyah makaranta take zuwa" Tana faWin hakan ta mi?e tare da ficewa daga Wakin tana zuba kumfar baki... Majeederh ta bi bayanta da kallo, to ita yanzu za ta yi da ranta? Tallan kanta za tayi kenan? Ko kuma dai photo nanta zata raba masallatai? Wata zuriyar ta ce mata.
"Kin manta kenan ko Majeederh? Bayan mazan gudunki suke babu wani wanda zai ce yana son ki balle aure" Zuciyarta tayi mata nauyi da ?yar ta samu ta ja numfashi kafin ta mi?e jiki a sanyaye ta nufi part Win Abbu. Yana zaune saman ladduma gabansa cike da kayan marmari hannunsa ri?e da jarida ya dubawa ta yi sallama, bai amsa ba sai gyaran murya da ya yi mata alamar ta shiga. Ta zauna a gefe cike da tsoransa ta ce "Ina yini Abbu? Na sameka lafiya?" Ya ce "Lafiya lou" Ya yi shiru ta Wan Wago kanta ta saci kallon Mahaifin nata, ba zaka ce shi ne ya haifeta ba, sbd ya samu duniya da abinda yake so wato kuWi jikinsa ya murje alamun kwanciyar hankali sun bayyana a tare da shi. Ta sauke ajjiyar zuciya a hankali ta furta "Allhamdulillah na cika burin Abbu" Ta Wauka zai tambayeta kalar rayuwar da tayi a Egypt ba tare da iyaye ko wani nata ba, ta Waukan zai sanya mata albarka bisa namijin ?o?arin da tayi na zama Gwarzuwa a musaba?ar Alkur'ani ta ?asa, ta Wauka zai albarkaci rayuwarta bisa burinsa data cika sai ta ji ya ce "Na haifi ?ar da bata san girma da ?imata ba, na haifi ?ar da take son tuna mini asiri a cikin al'umma, na haifi ?ar da take son saka mini ciwon zuciya...,"
A gigice Majeederh ta dakatar da Abbu da faWin "Me na yi Abbu, me aka ce nayi idan zuwa gidan Latifa ya Sata ranka don Allah ka yafe mini" Jikinta duka rawa da Sari yake sbd tsoran Sacin ran mahaifin nata. Abbu ya dubeta sosai kana ya jawo laptop Winsa ya shiga Gmail ya nuna mata wani sa?o ya ce "Hukumar makarantarku ta ?asar Egypt take ?orafin sun nemi alfarmar ki zauna musu domin zama malama amma ki ka?i bayan sun yaba miki ba za su samu wata Waliba data kai ki ba" Majeederh ta ce
"Ka yi ha?uri Abbu" Ya Waga mata hannu cikin tsawa ya ce "Ha?uri? Kin manta al'?awarinmu dake?" Ta ce
"Ban manta ba" Cikin zafin rai ya ce "Ok isa ce ban ba? Anya zaki albarka kowa Majeederh? Kina son wanyewa lafiya?" A ruWe ta ce
"Ka yi ha?uri Abbu, rayuwata a wata ?asar da bani da kowa akwai hatsari ba zan iya zama ba, na yi ?o?arin cika al'?awarin amma na kasa ka yafe mini, bana da kowa a Misira bana da mai mini faWa, bana da wanda zai kalla a matsayin wani nawa, bana da wanda zan zauna nayi fira da shi" Abbu ya dinga kallon Majeederh cikin tarin tsana da ?onar rai ya ce
"Shi Wan uwanki Alpha ba mutum bane? Da yake tafiya cikin jeji sai ya yi shekara bamu sa shi a idanun ba, ba kuma mu san halin da yake ciki ba, gwara ke mun san inda kike...,"
Ta ce "Abbu taya zaka haWa Wiyarka mace da namiji? Namijin daya kusa tun karar shekaru arba'in? Kuma zai iya kula da kansa?" Ta ?are maganar tana sakin kuka sosai. Abbu ya ce "Ok ke yarinyar goye ce kenan ba zaki iya kula da kanki ba? Kinga tashi maza ki bar mini parlour idan na ci-gaba da ganinki zuciyata bugawa zatai mu zauna mu cinye ?an kuWaWen da suka rage kinga ma dawo gidan jiya talakawa" Zatai magana ya ?ara daka mata tsawa kamar ba Mahaifinta da take mutuwar so kamar rai ba ta mi?e jiki na ?yarma da Sari ko kallon gabanta ba tayi ta nufi waje ga idanunta da suke mata wani masifaffan ?ai?ayi nan da nan sukai jajir ta shiga susawa tana yin main parlour kuka na cin ?arfinta, karo tayi da mutum tsaye wanda shigowarsa kenan cikin garin Kano tana ?o?arin yin compound a tunaninta main parlour ne sbd idanunta rufe yake caraf ya sa hannu ya ri?o nata hannun....

*BOOK 1 PAGE 31*
MIJIN MALAMA
LITTAFIN KU?I NE WANDA YAKE SO YA YI MAGANA 08119237616

Ina godiya bisa ta'aziyyar da akai mini ta babban rashin da na yi na wan mahaifina Alhaji Musa Zakari sheka ( Dagacin sheka) Na gode sosai Allah yabar zumunci marubuta da yawa wasu ma ban san su ba, sun nuna mini kara ?warai makaranta ina alfahari daku kune silar kai ni inda nake kune kuke goya mini baya ta hanyar siyan littafaina, ina fatan ba zaku gajiya ba=?O? [7/7, 12:26 AM] Aunty Mopol: Janta ya yi har tsakiyar main parlour yana zuwa ya saki hannunta yana binta da wani irin kallo kafin ya ce "Baki da hankali?" Ta buWe idanu wanda sukai jajir ta ce "Me na yi?" Da idanu ya dubi shigar dake jikinta da kuma kallon fuskarta dake buWe, itama tayi saurin kallon kanta tana Wan marairaice fuska zuciyarta duk babu daWi ta kasa cewa komai sbd yadda ?irjinta ke Wagawa ga zafin da idanunta suke mata duk ta sushe su. Ya gyara tsaiwa yana harWe hannu a ?irji shi ma nasa idanun sun yi ja sbd abubuwan da suke masa yawo a zuciya can ?asa ya ce "Kuma da gaske fita zaki haka? Tsirara?"
 .... Tsirara!? Ta faWa da sauri cike da tsoro, Alpha ya haWe fuska ya ce "Mene marabar dambe da faWa?" Majeederh ta yi shiru domin ita sam tunaninta baya nan wajan, zuciyarta ta KaWaita da maganganun Abbu, lura da yanayinta ya sa Alpha bai ?ara magana ba ya bi ta gefenta ya shige ya zauna saman kujera yana harWe ?afafuwan. Majeederh ta shige part Winta not too long ta dawo sanye da rolling na vail a kanta, ta nemi waje saman kujera ta zauna, shiru ya biyo baya can ta ce "Ina yini?"
"Lafiya" Ya bata amsa a ta?aice. Majeederh ta yi ?asa da kanta cikin sanyin murya ta ce "Ance an maka ?arin girma congratulations" Alpha ya ce "Uhm" Yana Wan kaWa ?afa kafin babu wasa idanunsa ya kira sunanta ya ce "Majeederh!" Ta yi shiru.
"Zabiya?" Ta kwaSe fuska tunda bata son sunan ya Wan shafa kai daman He just wants to tease her. Ta mi?e zata bar parlourn ya ce
"No, please" Ta zauna kamar zatai kuka ta ce "Tun ina ?arama kake ce mini Zabiya Yaya, ni ban so idan kai ma da Aljanar nake maka kama to"
"Stop it Majeederh!" Ya furta a tsawa ce, domin ji ya yi kamar ta caka masa nashi a ?ahon zuciya, ya girgiza kai ya ce "Sorry"
Ta yi shiru speaking calmly ya ce "Sannu da dawowa ?asa Nigeria, yanzu sai me?" Kanta a ?asa tana wasa da yatsun hannunta ta ce "Sai abin da Abbu ya ce" Alpha ya watsa hannu ya ce "Kina sane da problem Winki, komai zaki ki fara tuna aure first" Kunya ta kama Majeederh sai yanzu take dana sanin sanar masa da matsalarta, kuma yanzu da baya ai ba Waya bane tuni Ubangiji ya ye mata "Kina ji?" Ta ce "Aiki zan nema" Da wani irin sauri ya ce "Aiki?" Ta Waga kai ya ce "Shi ma Abbu ne?" Tayi shiru cike da tausayawa ya ce "Am sorry, zan masa magana ya fara bari kiyi aure" Wani irin abu ne mai Waci ya tsayawa Majeederh a ma?oshi ta runtse Idanunta tuni ta ji rauninta na son bayyana muryarta na rawa amma ta dake domin tayi al'?awarin ko hawan jini zai sameta, ko zuciyarta ce zata buga ta mutu nan take ta daina yin kuka ta sauke ajjiyar zuciya ta ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login