Showing 6001 words to 9000 words out of 74861 words

Chapter 3 - mijin malama 1&32 Hausa Novels By Nimcey Sarauta.doc

24 Jan 2026

519

kuma zargin da ake a kanta ya tabbata?" Abbu ya yi dariya sosai yana kallon ?an jaridan ya ce.
"Ina da ?a Majeederh, amma tawa yarinyar ta zama gawa tun tuni bata raye, ban kuma san yarinyar dake amfani da sunana da kuma sunan familyna ba, zan yi amfani da wannan damar wajan yi mata Allah ya isa har abada, zan kuma shaidawa duniya duk inda suka samu yarinyar nan mai amfani da sunana su jefe ta ko kuma suyi mata bulala akan laifin aikata zina, su kuma Wauki mataki akan amfani da rigar Muslunci tana aikata alfasha"
?an jaridar ya kalli Abbu sosai, da alama ya firgita da maganganun shi ya ce. "Kenan Malama Majeederh ba ?arka ba ce wacce muke tunani?"
Cikin tsawa Abbu ya ce
"Yara biyar ne kaf duniya, tawa Majeederh ta zama gawa tun da jimawa bana son wata tambaya bayan wannan" a firgice Majeederh ta dafe ?irjinta da yake wani bugawa jajirin ya nemi suSucewa ta shiga kokawa da numfashinta, wani abu mai nauyi ya tsaya mata a ?irji Idanunta suka tsaya ?am akan fuskar mahaifinta tunani take ko dai da gaske bashi ya haifeta ba? Mai shagon ya girgiza kai ya ce.
"Kai duniya, kai duniya wai yanzu aikata zina ya zama ruwan dare? Matan aure su aikata zina, ?an mata su aikata zina, zawarawa su aikata zina, mijin aure ya nemi matar wani, matar aure ta nemi mijin wani? ga FyaWe daya ya waita, ga matsalar tsadar abin duniya, ga rashin nefa ga rashin ruwan sha, albashi wannan sai a shige wata ba a biya, wani lokacin ma a rage albashin, ga yawan aibata Musulunci yanzu Fisabilillahi a kaf garin nan waye bai san Malama Majeederh Abdul'aziz Khan babbar malamar musulunci ba ce? waye bai san irin tallafin da take bawa Muslunci ba, waye bai san wa'azin da ta kewa masu aikata alfasha ba, sai gashi ana zaton wuta ma?era sai gata a masa?a, shi ya sa ake cewa kayi amfani da faWar Malam kada kayi amfani da abin da yake aikatawa, wallahi ko ki aka bani dama sai na jefe wannan shaiWaniyyar" Lawan ya girgiza kai ya ce "A'a Bala, amma dai Allah ya kyauta!" Bala ya ce "Amin, shi ya sa ta?i aure tana ta zuba alfasha, kasan daman duk wani mai aikata zina aure bai dame shi ba, kuma ko ya yi aure ba zai daina yin abinda ya saba ba"
Malama Majeederh bata tsaya neman ruwan ba, ta juya da sauri tare da barin wajan a lokacin ji take kamar ta shiga duniya, kamar ta zama ?aruwar da suke danganta ta da ita, ji take kamar ta zama sanadin lalata sunan mahaifinta dana familyn da yake nesa ta da shi gudun kada ya Saci, zuciyarta ta ?e ?ashe duk damuwarta ta tsaya, lokaci zuwa lokaci take jan numfashi ta sauke sbd abinda ya tsaya mata a saitin zuciya da ma?o shinta. Tayi tafiya mai nisa sosai kafin ta samu wani waje kusa da wata bola ta zauna ta rungume yaron wanda ya yi shiru, jikinsa ya Wauki zafi. Ji take kamar ta rataye kanta, ga jinin haihuwa daya gaba Sata mata jiki a haka barci ya Wauketa.
Tsaye suke gabaWaya a parlour Hajia ta girgiza kai ta ce "Me kayi haka Zaki? Me ka aikatawa kan ka haka Aliyu?"
Almustapha ya kalli news paper Win ya ?ara ware idanunsa akan photon Bar Aliyu Sufyan Alhassan da kuma photon Malama Majeederh Abdul'aziz Khan dake zaune fuskarta rufe da li?ab. Almustapha ya shiga karanta headline Win jaridar. "Bar Aliyu Sufyan Alhassan shi ne ya aikata zina da Malama Majeederh Abdul'aziz Khan, tare da saninta domin su wula?anta matar Aliyu wato Latifa Omar kasancewarta aminiyar Jeederh" ya karanta a fili cikin zafin nama da faWa Almustapha ya ce "Wanne shirme da hauka ne haka Aliyu? Zina? ?an shege?" Aliyu ya kalli yayan nasa ya ce..
"Ba shege bane" "To uban mene? Aurenta kayi?" Aliyu ya ce "Ko Waya, ina son ta am ready to marry her, Wa kuma ba shege ba ne" Almustapha ya Wauke Aliyu da mari ya ce
"Mahaukaci, to kayi gaggawar zuwa gidan jaridar nan ka ?aryata rubutun su, ina da tabbacin kuma matarka Latifa Omar ce tayi wannan aikin ai a gidan jaridar take aiki"
"Tayi dubun su, ba zai sauya mini ra'ayi ba"
Cewar Aliyu. Almustapha ya ?ara Waga hannu zai mari Aliyu,cikin sauri Aliyu ya ri?e hannu ya ce
"Kasan Allah ka ?ara marina zan karya hannunka,ka bar ganin kai yaya na ne, idan kun shirya korata kamar yadda Mahaifin Majeederh ya koreta fine I'll leave the house" abu kamar wasa dambe ya sar?e tsakanin wa da ?ani cikin Sacin rai Hajia ta zabgawa Aliyu mari ta ?ara zabga masa mari ta ce "Ka nutsu Zaki, ka nutsu" Aliyu ya fashe da kuka ya rungume Mahaifiyarshi ya ce
"What should I do Hajia? Dame zan ji ne? Wallahi idan kuka matsa mini zan iya aikata komai, Hajia I love Majeederh don Allah ki nemo mini ita, hajia hajia....,"
Da Hajia da Almustapha su kayi kan Bar Aliyu Sufyan Alhassan wanda ya faWi a ?asa sumamme...

Government House
Labarai ake ta ko'ina gabaWaya kuma akan Malama Majeederh Abdul'aziz Khan ne, Human rights sun shiga maganar, ?ungiyar mata ta shiga maganar, shugaban ?an hisba. Ya sauke Soyayyiyan numfashin tare da juyawa kaWan ya kalli tulin jaridun da aka wallafa, gefe guda kuma yana mamakin gidan Jaridar Hausa lastest News, domin sun fi ko wanne gidan jarida Waukan zafi da kuma aibata Malama Majeederh. Sama sama yake kallon photon ta, bai taSa ganinta ba amma muryarta kullum tana yi masa amsa kuwwa a kunne. "Ham...mad" Hammad ya yi sauri ya rusuna ya ce
"Your excellency" "Waye me wannan Shirman?" Hammad ya ?ara yin ?asa ya ce "Wata ?ar Jarida ce, Latifa Omar"
Abu-turab ya ce.
"A dakatar da gidan jaridar" with so much respect Hammad ya ce
"With pleasure Your excellency" ya jinjina kai kawai, Hammad ya juya cikin sauri. Kai tsaye akai sanarwar da yawun Gwamna tare da bada umarnin rufe gidan Jaridar. Abu-turab ya kasa komawa gida, tun safiyar yake jiran ya ji ance an samu Malama Majeederh Abdul'aziz Khan amma shiru har biyar na yamma ya yi. Tajju ne ke driving hannunsa ri?e da Envelope yana ta yawo amma bai samu Majeederh ba, gashi har an kwana wani daren na shirin yi kamar ance masa ya juya idanunsa ya sauka akanta tana nan zaune bakin bolar ta ?an?ame jaririn kamar za a kwace mata shi, ta fita hayyacinta duk jini ya Sata jikinta, cikin sauri Tajju ya gangara gefen titi tare da yin parking yana Hammadala a ransa ya fito,bai san mene a envelope Win ba amma yasan dole yana da ala?a da wannan jaririn babu ko tabbata musamman yanzu daya tuna wata rana. Yazo daidai tsakiyar titin yana ?o?arin tsallakawa wata ?atuwar tifa tayi awon gaba da shi....


#Bar Aliyu Sufyan Alhassan
#Dr Jamal
#Abu-turab


Na'ima Sulaiman Shu'aibu
08119237616
Not editing
[7/7, 12:25 AM] Aunty Mopol: *

Nimcyluv Sarauta

*_Please kuyi following Acct Wina a arewabooks>??? https://www.arewabooks.com/u/nimcyluv


*AN SAMU MISTAKE, WANNAN SHI NE FULL PAGE NA 4 KUYI SHARING, A GOGE WANCAN=?O?
*4......*
Mummunan hatsarin ya ja hankalin mutane da yawa, hatsari ne wanda za a iya cewa tsautsayi ne da kuma gangan cin driver da yake driving yana waya. Da gudu babbar mota tayi gaba bayan tayi wurgi da Tajju zuwa gefe guda, nan take kan Tajju ya fashe jini ya fara zuba hannunsa guda Waya ya fita fit daga jikinsa ko shurawa bai ba rai ya yi halinsa. Motar dake bin bayan babbar motar data buge Tajju ce ta tsaya, cikin sauri driver da wanda yake gefen mai zaman banza suka fito bakinsu Wauke da sallati "General kira mana Ambulance" cikin sauri General ya Wakko wayarsa tare searching asibiti mafi kusa da kuma motar asibitin. Hammad ya ce "Allah sarki, haka rayuwa take Allah ya ji?ansa ya yi masa rahama" General ya amsa da "Amin" da sauran jama'ar wajan suka amsa.
Har Hammad zai juya idanunsa ya sauka akan Envelope dake can gefe guda iska na kaWata a hankali ya ?arasa tare da Wauka, a ransa yana tunanin maybe a samu wani bayanai akan mamacin. Ya ware Envelope Win first abin da ya gani shi ne ring irin na al'?awarin nan, ya juya ring Win sosai sai kuma ya zura acikin aljihu, gently idanunsa ya sauka akan headline na wasi?ar kamar haka.
*_BAD MAN, THE STUBBORN BOY, CRIMINAL, GANG BOY, THE LEADER_*

Daga wannan rubutun idanun Hammad ya sauka ?asan headline Win inda aka rubuta  The memories, was going on my mind, har abad, nasan ni mahaukaci ne da gaske kamar yadda ki ke faWa Jee jikin Hammad ya shiga rawa ganin General na ?ara suwa ya tura wasi?ar Aljihu "Lafiya?"
"Actually, good"
Kafin suyi magana Ambulance ta ?ara su aka Wauki gawar Tajju tare da sanyata ciki, Hammad ya buWe ya Wauki wata number da yaga ana ta kira anyi saving da "Bad boy"
"His phone" cewar Hammad bayan kammala komai Ambulance suka tafi asibiti da shi. Suma su Hammad mota suka shiga driving kawai yake amma tuni ya yi losing mind Winsa, fatan sa kawai ya isa Gov. Abu-turab Al?asim, ya san cewa yanzu ya koma gida kasa jurewa ya yi ya Wauki Wayarsa tare da kiran keSantacciyar number Abu-turab kusan kira uku kafin ya Wauka cikin nutsuwa ya ce.
"Uhm" Hammad ya ce
"Your Excellency, akwai damuwa" a ta?aice ya ce
"Kace komai, banda rasa Majee" cikin ladabi ya ce "Am very sorry for that, amma bamu sameta ba, amma mun sami maganin matsalarta, Wan waye, cikin waye, yadda aka samu cikin duk yana ciki" Abu-turab ya mi?e daga zaunan da yake ya shiga zagaye haWaWWan parlourn nashi fuskarsa tayi jajir. "Ok, meet me at my house" yana faWin haka ya kashe kiran. Tafiya kaWan ce ta ?ara su da su cikin gidan Abu-turab wanda yake zaune tare da iyayensa, sojoji birjik ta ko'ina daka nuna rashin gaskiya zaka ji maza akan ka. Girman gidan ya zarce tunani, motoci kala-kala na kamfani daban-daban.
Ko a jerin masu kuWi ba kowa zaka samu da wannan haWaWWan gidan ba, gida ne 200by 200 iya compound na gidan zai ja hankalinka balle ciki. Kasancewar ba wanda bai san Hammad ya sa ba wani wahala ya nufi cikin gidan, a Main parlour ya samu Mama na sakkowa daga bene ya yi murmushi ya ce
"Sannu da gida Mama" kallonsa kawai take fuskarta kwance da annuri amma kana ganin sanyin jikinta kasan akwai damuwa, kyakkyawar dattijowa mai nutsuwa da sanin ya kamata,ga ilimi na iya zama da ko wanne mutum ga kyakkyawar mu'amala. "Na Wauka mun yi laifi yau ne" cewar Mama bayan ta zauna.
"Laifi kuma Mama?" Ta dubesa kafin ta Wauke kai ta ce "Naga babu ko mai kama da kai, hala wani aikin ka ke" ya shafa kai yana rusunawa ya ce.
"Haka ne kam, ina Yake?"
Ta Waga kai zuwa part Win dama da yake upstairs ta ce. "Ina son tambayarka dama, meke damun shi? Tunda ya shiga part Win sa bayan ya dawo bai fito ba, hatta wajan art Win da yake shiga yau shiru, lunch ma bai ci ba na kira phohe number sa na gida a kashe" ta tsare shi da idanu ya ce "Akwai wata tattaunawar sirri da yake da ita, maybe shi ne yake duba muhimman abu kasancewar tattaunawar sai 12 na dare"
Ta jinjina kai tare da faWin "Allah ya taimaka, kasan ?ar rigimarsa ta hanani sakat ita dai Abbi" Hammad ya yi dariya sosai ya ce "Jiddatul-khairi ai ya saba mata ne" kafin Mama tayi magana sai gata ta fito da gudu ta faWa jikin Hammad ta ce "Uncle, Abbina" ya Wauketa ya shiga hawa upstairs yana faWin
"Daughter me, bari muje muga Abbi sai muje siyan chocolate ko?" Tayi murmushi dimples Winta soka loma tana ta masa surutu har suka isa haWaWWan part Win da kana ganinsa kasan Gov. Abu-turab Al?asim ne a ciki. Hannu Hammad ya saka cikin wani screen dake ?ofar nan take ta fito da bayanan Hammad a hankali kuma ?ofar ta buWe.
Jidda ta ?wace daga hannun Hammad tayi cikin parlourn da gudu tana kiran sunan Abbi, yana zaune saman kujera daman alrdy ya san da zuwan Hammad Win, kayan shan iska ne a jikinsa fara Armless da black Win 3 gauter.
Hannunsa Waya ri?e da Black tea wanda aka sanya masa zuma a ciki, news yake kallo har Jidda ta faWa jikinsa hankalinsa baya tare da shi. "Abbina"
Ya ware idanunsa idanunsa da suke a Wan lumshe ya dubeta "First love" sunan da yake faWa mata kenan, duk da kasancewarta ?ar shi guda Waya. "Abbi"
Ya juya bayan ya gyara mata zama a cinyarsa tare da kallon Hammad yana son ya ji wanne labari ne da shi wanda yake da ala?a da Majeederh.
"Your Excellency barka da yammaci" jinjina kai kawai Abu-turab ya yi.
"Ga wannan wasi?ar, idan ka karanta sai ka Wauki matakin daya kamata akai, ita kuma zamu nemota In sha Allah" hannu ya sa ya amshi wasi?ar tare da warewa zuciyarsa na harbawa, bai san mene ya sanya duk abinda ya shafi Malama Majeederh ya ke jinsa har ?asan zuciyarsa ba, barci ya ?auracewa idanunsa, ga ciwon kan dake ?o?arin kwantar da shi.
Duk Yadda ya so ya daure da ri?e kansa ya kasa ya mi?e tsaye da sauri yana ware idanunsa akan paper Win, tsoro,fargaba damuwa da kuma firgicin rashin sanin makomarsa wajan Majeederh ya taro ya haWe masa waje guda.
Ya sanya hannu ya share zufar daya yanko masa, lokaci Waya ya hargitse wani zazzaSi na neman kawo masa farmaki.
"Your Excellency, lafiya dai?" Ba tare daya kalli Hammad ba ya ce
"Ham...mad" "Yes, Your Excellency"
Ya juya gabaWaya fuska a haWe ya ce "Tun yaushe nake baka labarinta?"
Kai tsaye ya ce "Shekaru wajan biyar, tun ranar daka halarci musaba?ar da aka yi ta ?asa"
Abu-turab ya jinjina kai, Elxty 5yrs kenan, a wannan musaSar ya ji muryar Majeederh, muryar data sanya masa dafin so a zuciya ta zautar da duk wani tunaninsa, ya wanzu cikin muradinta a zuciyarsa, shi kansa ba zai iya sanin abinda ya sanya bai tun kare ta da wannan maganar ba, samun Majeederh Abdul'aziz Khan a garin nan ba wahala zai masa ba. "Har abada Majeederh kada ta san da wannan wasi?ar" da mamaki fal fuskar Hammad ya ce "Your Excellency amma kamar ba a kyauta mata ba, wannan wasi?ar ita zata fitar da ita daga zargi, kuma ita ce zata gane waye ya aikata mata haka" Abu-turab ya koma ya zauna kawo yanzu yasan Bp nasa tuni ya hau cikin kamilalliyyar muryarsa mai tsafta ya ce "Me ka ke nufi?"
"Ba mu yi mata adalci ba" cewar Hammad.
"So baya bu?atar adalci, kansa kawai ya sani, ayi hakkan ya tsaya ni da kai" Hammad ya kalli Abu-turab yana girmama yadda yaso kansa a fili sbd soyayya,idan har son gaskiya ne ba zai taSa bari Majeederh taci gaba da zama da zargi akanta ba. "Shikenan, Your Excellency. Maganar meeting naka an gama shirya tattaunawar a guest house Winka, da kai da Deputy Governor, Secretary to the state of Government, Chief of staff" hannu bibbiyu Abu-turab ya ri?e kansa kana ya jinjinawa Hammad kai ganin yanayinsa ya sa Hammad cewa "yana da kyau ka huta haka, Jidda zo muje" ta ma?ale ka faWa jikin Abu-turab.
"Abbi baya jin daWi" Abu-turab ya ware idanuna ya ce "Go"
Ta kwaSe fuska cikin zafin zuciya ya ce "I said Go Hawwa'u Abu-turab Al?asim!" Tsawar ta gigita mata lissafi ta fashe da kuka tana ?an?ame Hammad ta ce
"Uncle" ya Wauketa yana girgiza yana mamakin sauyawar Abu-turab lokaci Waya.
Dukkan abinda ya faru akan idanun Malama Majeederh Abdul'aziz Khan ya wakana, kasancewar bata fahimta kusan tunaninta duk ya jirkice ?wa?walwarta na gab da fara daina aiki yasa bata fahimci su waye ba, motsi kaWan zata ?an?ame jaririnta kamar zata bayar da shi ciki, wani zubin kuma tayi ta surutu ita Waya sbd tarin abubuwan da suka cunkushe mata, yunwa ba a maganarta jikinta ya fara tashi sbd jini da rashin wanka.. bata shagala azkar, istigifari da addu'ar neman samun sau?i wajan Ubangiji bai bar bakinta ba.
Washe gari Abbu ne zaune a parlour da Mami sai Ruma da Raihana wanda aka kira su daga gidan mazajen su, sai kuma Aaliyyah dake zaune tamkar marainiyya Idanunta a kumbure ko gani ba tayi sosai, sai Uncle Isma'il da Uncle Bello. "Yanzu har a ranka kana jin kayi daidai?" Abbu ya dubi yayan nasa ya ce "Majeederh dai ni na haifeta, ni na samar da cikinta na kuma raineta, kuma na dawo na ce bani da haWi da ita don haka a bar wannan maganar" Uncle Isma'il ya ce "An barta, amma ka bani mamaki a matsayinka na Uba kuma dattijon ?warai har ka iya shafawa idanunka toka ka ce wai ka sallamawa duniya Majeederh, sbd kawai kada sunan family da naka ya Saci? Familyn bazan sunanka Win banza, da rayuwar mace kamar Majeederh ta Saci ba gwara duka sunayenmu su Saci ba, wata rana dalilinta sunan namu ya samu Waukakar damu kanmu ba muyi zato ba, mai ya sanya mu iyaye idanunmu ya kan rufe idan tsautsayi ya samu yaranmu? Yanzu Majeederh ko tana sane wannan abun ya faru ba zaka iya yi mata uzurin akan rashin auren da take da shi ya ja mata wannan ?adsarar ba? Ita Wiya macace duk runtsi duk jimawa dole ta Sukaci Wa namiji wata rana" Uncle Isma'il ya girgiza kai sbd tsabar takaici ya ce "taya ?asa zata gyaru bayan mu da kanmu bamu gyara zamantakewar data yaranmu ba, fine ka kori Majeederh zan nemota na ri?eta a wajena....,"
"Yin hakan zai ja mana babban kuskure yaya, duk wanda zai so ta bayana yake bi, don haka a barni kawai" Abbu ya tari numfashi Uncle Isma'il da faWin hakan. Uncle Isma'il da ransa ya fara Saci ya ce "Zan taimaketa kamar yadda take taimakon addinin Musulunci, bawai sbd data kasance ?arka ba Abdul'aziz Khan" Abbu rai Sace shi ma ya ce "Kana iya yin haka amma daga ranar babu ni ba kai, ka cire ni matsayin ?aninka, ka yanke mu'amala ta dakai" murmushi sosai Uncle Isma'il ya yi wanda ya fi kuka ciwo yana girgiza kai ya ce "In sha Allah, idan kero na yawo zabo na yawo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login