Showing 27001 words to 30000 words out of 95753 words

Chapter 10 - BABBAN YARO Part 2 By Binta Umar Abbale .pdf

ta shimfid'a masa tana sanye da farin hijab fuska
a sake take amsa sallamarsa.
Cikin ladabi naga ya tsaya bakin kofar ya cire hadd'adan takalimsa karfashi sanye da wata
lafiyayyar safa ya karasa kan tabarmar .

Umma fad'i take"Sannu da zuwa yaron arziki Mara ba lale.
Zama yayi kanshi a kasa yace." Barka da yamma Umma na same Ku Lafiya."?
Umma tace"Lafiya Lou Alhmdullahi ya kokarin ka da fama da jama'a. "?

Yace." Alhmdullahi wallahi ya me jiki kuma."?.Tace" Jiki yayi sauk'i ai bs wani tsanani Yayi ba
Asma'u ta ta soka." Murmushi yayi tare da fadin"Dama yau nayi niyar in shigo mu gaisa sai
kuma take fadamin Momyna babu lafiya."
Umma tace"Wallahi kuwa tari take amma da sauk'i dai tunda Aminu ya siyo mata magani Tasha
ta samu tayi bacci."
Yace." Tou Alhamdullahi Allah ya kara sauk'i. "
Yanda suke hira da Umma sai abun ya bani mamaki kamar Wanda suka shekara da sanin juna
Umma sai shi masa albarka take da fadin"Muna ganin taimakon talakawa da kake yi a garinan
muna jin dad'i Ubangiji Allah ya tsare ka ya kare ka daga sharrin masu sharri. " yaji dadin
adduoin da Umma take masa ga yanayin yanda yake amsawa
Mimi dake kwance a daki tana bacci kamar a mafarkin taji muryar shi firgigt ta tashi ta zauna
k'irjinta yayi mata nauyi sosai rarrafowa tayi ta futo tsakar gida tana dafa bango
Nice na fara ganinta ganin kamar tana kokarin fad'uwa ya sanya naje da sauri na rike ta muka
karasa kusa dasu Umma
Tace." Yauwa ai gata nan ma ta tashi sannu Mimi."
Zaunar da ita nayi kusa da shi, na matsa gefe
Amjad mamaki ramar Mimi yake duk da yake dare ne kuma tsakar gidan babu wadataccan
haske sai da ya fahimci tana jin jiki.
A hankali yace." Momyna ya jikin ki? Ashe haka Abu yayi tsanani. "
Cikin sanyayyr murya tace." Jiki da sauk'i ." gyada kansa yayi tare da kallon Umma yace." Kunje
asibiti da ita kuwa."?
Kafin Umma tace Wani Abu Yaya Aminu ya shigo gidan.
Gabansa ne ya fad'i ganin Mutumin dake zaune ga gidan jininsa Mimi kenan a zaune a kusa
dashi, lokaci guda ya b'ata fuskarsa hade da yin kicin-kicin da ita sama-sama suka gaisa dashi
Yana mamakin me ya kawo shi, zama yayi gefen rijiya yana sauraran maganar da suke yi da
Umma.
Umma tace." Ba muje asibiti ba amma dai gobe in Allah ya kaimu za muje a duba ta sosai."
Gyada kansa yayi shiru na minti biyu yace." Gobe idan Allah ya kaimu zan turo dravar sai a
kaita asibtin malam Aminu a duba ba ta sosai."

Umma tace"Allah yayi albarka ai da ka bari ma, sai muje asibitin Murtala ." Hannu ya zura aljihu
ya futo da kudi masu yawa ya zube gaban Umma ya mike tare da fadin" Zan wuce Allah ya bata
Lafiya ."
Umma tace"Harda wahala kuma ai da ka barshi."
Shiru yayi ya mik'awa Aminu hannu suyi sallama.
Rai babu dad'i Aminu ya mik'a masa nasa hannun sukayi musabaha.
Takalmin shi ya sanya Umma sai godiya take masa futa yayi cikin sauri Umma ta kalleni tare da
fadin" Kije ki raka shi mana kinye tsaye."
Bayansa nabi da sauri..
Yayi nisa sosai don Haka sai da na k'ara sauri.
Na tadda shi.

Yana kokarin bude mota na same shi
Yace." Amma nayi mamakin ramar Mimi,Abunda kika fada gaskiya ne."?
'K'warai kuwa Mimi na sonka sosai kai kuma kana yaudarar ta."
Shiru yayi yana tunani tabbas abunda Asma'u ta fada gaskiya ne baya jin dai-dai da kwayar
zarrah na son Mimi a zuciyar sa, yana yi mata so ne kawai irin na musulunci sai kuma sunan
mahaifiyar sa da take dashi.

Ajiyar zuciya ya sauke tare da fadin"Allah ya bata Lafiya, Nasan ni babu laifina anan gaskiyar
magana ko Yanzu aka ce an bani ita zan aure ta darajar son da data ke min."
[11/10, 8:25 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*



*Mallakar_BINTA UMAR*
*LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN
ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA
KUDIN TA.*




*47*



Shiru nayi masa domin na rasa abunda zance dashi ni kaina al'amarin Mimi yana bani tsoro
Mota ya bude ya shiga tare da fadin"Ni zan tafi zan kira waya insha Allahu. "
Matsawa nayi daga jikin motar ba tare da nace masa komai ba ya ja ya tafi na lura jikinsa duk
yayi sanyi.
Ina koma wa gida na tarar da Ya Aminu ya tasa Umma a gaba sai faman bala'i yake mata
Ina shiga ya hau d'ura min ashar wai me yasa na gayyato Amjadu gida wallahi komai kulafucin
sa ba zai bar mishi Mimi ba.
Masifa yake kamar zai dake ni Umma tace"Kar ka sake ka doke ta Aminu Sam Asma'u bata da
laifi Kaine dai idonka ya rufe, ka ke ganin da laifin ta anan.".
Kan Mimi ya dawo cikin hargowa yace." Wallahi Mimi ko mutuwa zaki baza ki aure shi ba sai dai
idan ki Mutu ni dashi mu rasa amma ina ji ina gani bazan bar masa ke ba."
Yana gama maganar shi ya fuce daga gidan a fusace.!
Mimi ta fashe da kuka tari ya sark'e ta, aikuwa ta dinga yi bubu ji babu gani,
Umma ta jawo ta jikinta ta rungume ta sosai tana danne mata kirjinta hankalinta duk ya tashi
Da sauri tace"Asma'u d'ebo ta murhu a shafa mata ko Allah zai sanya ya Tsaya tari.
Da gudu na nufi kicin na d'ebo toka Umma ta bude rigar Mimi ta shafa mata.
Kamar kara ingizata ake ta cigaba da tari!!! Nace." Ina maganin a dauko a kara bata."
Da kyar Umma tace"Dauko a daki." Dakin na shiga da sauri na dauko maganin, abunda na gani

yayi mutukar gigita ni da bani tsoro wani irin jini bak'ikkirin na gani daga bakin Mimi yana
zubowa jikin Umma,
Da sauri na jefar da kwalbar maganin nayi kanta INA salati.
Umma kuwa kuka ta fashe dashi tana tare jinin da hannunta.
Baki na rawa nace"Umma jini ne ko."? Tace." Asma'u maza duba waje ki gani Aminu nan ki
kirashi mu tafi asibiti abun ya zama babba."
Da gudu na futa ko talkami babu.
Mimi ta galabaita iya galabaita tari take sosai jini na zuba daga bakinta idanunta sunyi jajazur
dashi sai daga hannu take.
Ni da Aminu muka shigo gidan hankalumu ya tashe.
Yana ganin Abunda yake faruwa ya gigice tare da fadin"Innalillahi wainnailahi raji'un. " futa yayi
da sauri ya dauko mota.
D'aukar ta yayi kacokan ya futa da ita da saurin
Nida Muka rufa masa baya zuwa yanzu na fara kuka tukuru ganin yanda Nuffashin Mimi yake
hawa da sauka.
A dai-dai sahu har kofar gidanmu don haka muna futa muka shiga saboda idanun Jama'a
Umma ta rungume Mimi a jikinta hankalinta duk ya tashi mai a dai-dai ya ja mu katafi shi ma
hankalinsa ya tashi da ganin abunda yake faruwa ya tausayawa Mimi sosai.
Murya a sanyaye Umma tace" Ka kira aunty Ku a waya ka fada mata halin da ake ciki, sannan
ka kira Kawunta wato Babansu Munnu."
Wayarsa ya futo da ita da sauri.

Kai tsaye!! Asibitin zana d'an a dai-dai ta ya sauke mu, Aminu ya sallame shi mu kuma muka
taitayi Mimi muka shiga da ita ciki.
Har yanzu tarin take idanunta a rufe gaban rigarta duk ya b'aci da jini
Wani ma'aikacin gurin ne ya k'araso gurunmu da sauri da wani keke dama mun San ka'idar
asubitin Mimi muka Dora kan keken ya ja ta da sauri ya shiga ciki da ita.
Tsayuwa muka yi bakin kofa duk jikinmu a sanyaye.
Umma tace"WANNAN kukan da kike bashi ne zai bata lafiya ba, addu'a zakiyi mata kawai."
Nace"Umma Mimi na bani tausayi haka kurrum zata jawo mana abunda baza mu iya ba."
Tace"Itama ba ita ta dorawa kanta ba Allah ne saboda haka sai dai mu bar masa.
Yaya Aminu kuwa kai wa yake yana kawowa a filin asibitin idan ka kalli fuskarsa sai ka rantse
da bai taba dariya ba tunda uwarshi ta haife shi, shi a ganinsa zuwan guy gidan ne ya dawo da
Mimi ciwon ta sabo ta inda har ya tsananta ta fara zubar fa jini dole ya mike tsaye a kan
al'amarin domin yana ganin Ana so ayi masa tsakiyar da babu ruwa wani irin haushin guy yake
ji da tsanar sa a cikin zuciyarsa

K'arfe goma saura sai ga aunt Hauwa ta shigo asubitin hankalinta a tashe take tambayar
abunda ya sami Mimi Umma ta dinga fada mata tun farkon al'amarin
Jama'ar gidansu Motar Babansu Munnu ce ta shigo asubitin Aminu ya karasa da sauri ya bude
masa motar
Ya futo tare da Ummansu Munnu da ita Munnu duk babu nutsuwa a tartare dasu.
Su k'araso kusa da mu suna gaisawa da Umma jiki duk babu nutsuwa

Yace." Ina Aishatu take." ? Dake da haka yake kiranta
Umma tace." Tana ciki tun d'azu dector yana dubata."
Jin Gina yayi jikin bango yana sauke ajiyar zuciya Mahaifin yarinyar ya tuno da yanda yake
kaunarta da irin amanar da ya bashi kafin ya tafi Wanda har yanzu ba a San a wace duniyar
yake ba, tun bayan rasuwar mahaifiyar Mimi din yaji duniyar ta isheshi ya hada ina sa ina sa,
yayi sallama da 'yan cewar ya tafi Neman kudi tunda ga ranar har yanzu basu sake ganinsa ba
amma labari na zuwan musu cewar yana cikin koshin Lafiya, kuma bashi da zance dai na
d'iyarsa Aishatu.
[11/10, 6:49 AM] Binta U Abbale: Umma da Ummansu Munna zancan suke yi cikin jimami ni da
Munnu kuwa babu abunda muke yi sai aukin kuka

Kusan awar Mimi daya a ciki sannan wata narse ta futo tace"Waye mahaifin yarinyar nan da
aka wo ta yanzu emergency. " Kawu yace." Ganinan." Juyawa tayi tana fadin"Muje dector yana
son ganinka ".
Dukaninmu sai mukaji kamar mu bi Kawu muji me dector zai ce masa.

Kawu da dector ne a ofis a hankali Dr ya cire farin gilashin dake idonsa ya kalli Kawu suka
gaisa a mutumce yace." Kaine mahaifin yarinyar nan ko."?
Jiki a sanyaye Kawu yace." Nine Dr Allah yasa naji alkairi."
Dr ya gyada kansa tare da fadin " I'm sorry to say yarinyar ka tana cikin garari rayuwa domun
zuciyar ta ta Riga ta tab'u sakamakon tunani da damuwa da ta sanya a ranta bayan haka kuma
da akwai a Abunda take mutukar so Wanda aka hanata shi shine mussababbin ciwon nata idan
ba 'ayi gaggawar kwantar mata da hankalin ba, to ana iya rasa ta a ko wane lokaci."

Kawu ya share zufa da take tsatstsafo masa a goshi yace." Dr yanzu wane irin taimako za'ayi
mana."?
Dr ya gyada kansa cikin nazari yace." Taimakon da zan fara yi shine, kuje gida Ku rarrasheta
sosai Ku lallame ta tayi kokarin fada muku abunda take so Wanda ta sanya a ranta ya dame ta,
idan kun San abun to sai kuyi gaggawar bata shi domin samun zaman lafiya da d'orewar lafiyar
ta, bayan haka kuma zan d'aura ta a kan magani insha Allahu mutukar aka bi doka zata samu
lafiya, yanzu dai mun dakatar da zubar jinin insha allahu babu matsala."

Kawu yace." Insha Allahu komai zai zo cikin sauk'i zamu bi doka zamu kuma zauna da yarinyar
domin mu tuntube ta muji meye Matsalar.

Dr ya gyda kansa tare da fadin"all right." rubuce-rubece yayi jikin wata takarda ya mik'a masa
tare da fadin idan ka futa zaka ga pharmacy sai ka shiga ka siyo wad'annan magungunan insha
Allahu, amma ba yau zamu sallame ta ba sai zuwa gobe dole zamu ga dai-dai tuwar
numffashinta." Kawu ya karb'i takardar da sauri ya futa.

Yana futowa muka mike da sauri dukaninmu tambayar sa muke jikin Mimi

"Da sauk'i yake cewa kawai ya nufi dakin magani Aminu ya bishi a baya.
Ofis din Dr suka nufa har Aminu Dr Ya kalli Aminu tare da Kawu yace." Wannan fa."?
Kawu yace." Shine Wanda zai aure ta." Dr yace." Zauna muyi magana da Kai. "
Aminu ya zauna kan kujera jikinsa sanyi k'alau!
Dr yace." Kaine kafi kusanci da sosai Kaine zaka fi sanin abunda yake damunta domin sai ta
fada maka abunda yake damunta bata fadawa Iyayenta ba, saboda haka Kayi kokarin
rarrashinta ta Sanar da kai meye matsalarta domin magance ta kada ka rasa kyakyawar
matarka Cikin lokaci kankani."Ya Aminu yayi shiru yana sauraran Dr da abunda yake fada Ba sai yayi masa dogon sharhi ba, yasan kome ye yake damun Mimi bai wuce soyayyar
Amjadu ba, Wanda yake ganin a kan ya sadaukar masa da ita gwara Mimi ta mutu in yaso kowa
ma yayi asara.
Shiru kawai yayi har Dr ya gama maganar shi suka mike da niyyar futa Aminu ya tsaya tare da
fadin" Dr babu halin ganinta a yanzu."? Dr ya gyda kansa tare da fadin" ta samu bacci yanzu sai
dai gobe insha Allahu da safe sai Ku shiga Ku ganta kafin a sallame Ku."
Jiki babu k'wari ya futa daga ofis din.
Fuskarsa na kalla naga yayi kucin-kicin gabana ya fad'i nayi saurin kallon Fuskar Kawu nan ma
naga babu sauk'i tuni kukana ya tsananta nace"Ku fada mana ko menene k'afafun Babansu
Munnu na rike ina kuka.
Ummansu Munnu ta janye ni tana rarrashinna ni a lokacin sai nake ganin kamar zasu ce Mimi
ta mutu ne Sabuda yanda muka kawo ta a sibitin ta futa daga hayyacin ta.


Can gefe guda suka tsaya suna magana. Kawu yace." Aminu ni a iya fahimta ta nafi tunanin
Mimi ta sanya soyayyar wannan Yaro da zai auri Asma'u a cikin ranta ne Wanda yake kokarin
haifar mata da WANNAN gagarumar Matsalar shine Abunda nake tunani."

Aminu ya gyara tsayuwarsa babu sassauci a muryarsa yace." Dama ni tun kafin muzo gaban
likita ya fada mana meye na gane komai, a gaskiya Baba babu mahalukin da zan iya barwa
Mimi domin nima idan nayi haka zan iya shiga cikin tashin hankali watak'ila ma nawa yafi nata
tunda kowa ya shaida nafi sonta ita bata sona saboda haka ni ina gani kawai daga nan zuwa jini
a d'aura mana aure da ita ba sai an jira lokacin da aka sanya ba, idan taji labarin haka nasan
dole zata hak'ura ta fawwala Allah kasan dama ance kiyyayyar 'ya mace bata tasiri ina ganin
Mimi zata hak'ura ta zauna dani."!

Kawu ya gyada kansa yana Nazarin maganar Aminu Yaro Yaro ne, murmushi yayi yace." Aminu
kenan, kamar ka manta abunda Dr yace akan Aishatu, Jin labarin d'aurin auranku zai iya
sanyawa zucuyarta ta buga gaba daya ta mutu lokaci guda, kaga kuwa wannan sha'awar taka
ba abun dubawa bace."
Aminu ranshi ya b'aci da jin abunda Kawu yake fada murysrshi a kaurare yace." Kai ya kake
ganin za'ayi."
Kawu ya kalleshi cike da mamaki jin yana yi masa magana kazar-kazar babu Wani ladabi.
Yace." Abunda za'ayi shine mu samawa Aishatu abunda take so domun samun ta da

tabbatuwar lafiyar ta.

Aminu ya watsa masa wani kallo tare da fadin"Kawu in na fahimce ka anan shine kana so kace
min in hak'ura da Mimi in yaso Ku bats Wanda take so kome."?

Kai tsaye..... Kawu yace." Shine abunda nake Nufi."
Aminu ya guda kansa yana murmushi me ciwo yace." Impossible, bazai tab'a yiwu wa ba Kawu
Mimi 'yar kace nima inda kara d'an ka ne nasan baza ka bawa Mimi bare ba gani a zaune, ina
so saboda haka yanda aka karb'i kud'in aure na da Mimi to babu mahalukin da ya Isa ya hana
tabbatuwar auramu idan ba Wanda ya hallice mu ba." Cike da d'umbun mamaki Kawu yake kallon Aminu ganin yanda yake wani irin huci!! Yace."
Aminu ka fahimce ni mana ba wai ina k'in ka ban......... Kafin ya karasa Aminu ya daga masa
hannu a fusace.!!! Yace." Kawu ga magana nan ta futo kanunamin bakai ka haife ni b.... Cike da
b'acin rai Kawu yace." Rashin kunya zakayi min Aminu. " Daga kafad'a yayi tare da fadin "Babu maganar rashin kunya anan Kawu gaskiya ce ni nayi
rantsuwar babu Wanda ya Isa ya hanani auran Mimi."

Ganin tsageran cin da Aminu yake masa ne yasa ya fusata shima yace." Aminu indai nine
waliyin Aishatu to baza ka aure ta ba."
Aikuwa sai ya ingiza Aminu ta inda ya shiga sirfa masa rashin kunya wanda ya jawo hankalimu
Kansu dukanimu mu k'araso gurin tare da tambayar ba'asi
Abunda Aminu yake yi yayi bala'in konawa Umma rai ta cire hannunta ta zabga masa mari cikin
tsawa tace"Na kara jin bakinka a gurinan Aminu sai na tsine maka, a tunanin ka wannan
tsagerancin da rashin kunyar da kake yi shine zai sanya a baka auran Mimi ko meye."?

Kawu yace." Kyaleshi ya zage ni son ransa lokacin sa ne."
Wuce mu yayi tafi can bakin get ya zauna tare da masu gadi

Fada sosai Umma take wa Aminu Tace" Haka ake soyayya da hauka Aminu ka futo da son
zuciyarka a fili kana ganin mawuyacin halin da yarinyar nan take ciki shine zakaje gwara ta
mutu a kan ka janye kudirin ka a kanta, me yasa ita lokacin da ka fad'i har ka kwanta a asibiti
tace"Zata aure ka alhalin ga Wanda zuciyar ta take so Mimi yarinya ce me ladabi da gudun
b'acin rain wani ta so ta faranta maka ta faran wa zuciyata ba tare da ta damu da nata farin
cikin ba, shine yanzu tana cikin halin rai da rayuwa kake mummunan magana a kanta Aminu
wannan ba soyayya bace."!!!!
Umma ta karasa maganar ta tana haki! Kana ganinta zaka fahimci tana cikin tsananin b'acin rai
da damuwa
Cikin kuka na futar hayyaci nace"Wallahi tallahi Umma mutukar Ya Aminu bai janye kudirinsa ba
nima bazan aure shi ba, sai dai mu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login