Showing 75001 words to 78000 words out of 95753 words

Chapter 26 - BABBAN YARO Part 2 By Binta Umar Abbale .pdf

bukata tana
zaune daram! Cikin Mimi gashi cibiyar ta ta nade mata wuyan ta, amma tana rayuwa a haka
Cikin hukuncin Allah, lafiyarta lau, cikin ya nuna wata shida da kwana takwas wato ya shiga
wata na bakwai duk wasu hallitu ubangiji ya gama abun shi, wahudun kahar Dole ya kwantar
da Mimi a asibiti domin kula da cikin ta da ranar haihuwa, domin kar hankalin su ya tashi ya
sanya yak'i fada musu abunda yake faruwa ganin yanda duk suka saki jikinsu har shi Amjad din
da ya dakatar da komai na rayuwar sa, yanzu ta lafiyar matar sa yake.

Ko da ya fada musu maganar bata gado basu kawo komai ba, har shi Amjad din ya yarda
saboda Jahid din yace masa yana so Mimi ta samu cikkakiyar kulawa har ta haihu, shiyasa ya
yarda da hakan.

Kwananmu bakwai a sibitin Mimi ta warware sosai babu inda bata zuwa, domiin Jahid cewa
yayi muna futowa da ita tana zurga zurga saboda shi yana gani kafin lokacin haihuwar tata
kwanciyar baby ya dawo dai-dai kamar yanda ake so.
Ganin ta warware sosai ya sanya na tafi gida saboda makaranta Mimi bata so tafiya ta ba
amma da na rarrashe ta na kawo mata misalai sai ta hak'ura.

Umma da Granny ne suke jiyyar ta sai Ummansu Munnu dake zuwa kullum tana kawo musu
abunci bayan an sha ruwa, duk da cewa Amjadu yana iya bakin kokari su akan su, komai sai ya
sanya an kawo musu na ci da bukatar rayuwa.

Ni ma ina zuwa amma ba kullum ba, watarana idan muka taso daga makaranta ni da Munnu sai
mu wuce aikuwa Mimi tayi ta murna, ranar yini muke ni da Munnu muna sanya ta motsa jikin ta,
kamar yanda Jahid ya fada.

Yau sati na guda da barin asibiti Wanda yayi dai-dai da satin Mimi biyu a asibitin kuma yau
sallahr saura kwana bakwai sati daya kenan. Ranar juma'a ne na tashi da wani irin mutuwar jiki.
Naji bana son zuwa skull din, cikin sauri na shirya jikina na bar gidan, kai tsaye asibitin
nasarawa na nufa, duk sunyi mamakin ganina lokacin makaranta nace musu yau baza ni ba,
muna tsaka da hira Mimi ta mike ta shiga toilet din dake cikin dakin. Minti biyu naji ta kwalamin
kira, da sauri na bude band'akin na shiga ina fadin"Menen..... Kafin in karasa naga jini jazur
nabin kasan gurin gata a tsugune ta rike kan famfo na toliet din tana cije bakinta cikin azaba ta
rike Cikin nata tana ynukurin tashi tsaye amma ta kasa
[11/25, 7:38 AM] BintuUmarAbbale: Hannun ta na rike ina kokarin mikar da ita tsaye abun ya

gagara, babban abunda ya bani tsoro da ita shine yanda naga jini na zuba da sauri na fita na
kira Umma ta shigo taga halin da ake ciki, itama hankalin ta ya tashi tace"Maza ki karawo Jahid
din zubar jini na da matsala futa nayi da sauri kafafuna na rawa, Granny tana tambaya ta
menene? Ko juyowa banyi ba, Ina kokarin shiga ofis din ne shi kuma yana kokarin futowa muka
buga karo dashi, dauke kaina nayi daga kanshi ina kokarin shigewa, tunda ya ganta a d'amauce
ya tabbatar akwai matsala da sauri ya fada dakin da Mimi take, dama zuwan shi kenan asibiti
ya tsaya ofis din Jahid domin su gaisa, yana shiga yaga granny tsaye kofar toilet tana
fadin"Kama ta Ku futo a hankali, kai amma dai jinin yayi yawa likita yazo ya duba ta." Granny
yake kokarin bugewa yana kutsa kai ban dakin inda Umma take kokarin mikar da Mimi ta kasa
ko da d'aga k'afarta guda d'aya, da sauri ya mik'awa granny wayoyin shi ya tartare hannun rigar
shi, ba tare da damuwar komai ba ya d'auki Mimi hankalin sa duk a tashe ya futo da ita jikinsa
duk jini hakanan itama doguwar rigar dake jikinta sharkaf take da jini. Hannunta ta mik'a ta
kamo wuyansa tana lumshe ido dishi-dishi take gani. Ya kwantar da ita da sauri ya futa daga
dakin, Jahid da Asma'u ya ci karo dasu, sai yayi saurin koma wa dakin, shi kuwa Jahid ganin
jikin Amjad din da jini ya tabbatar masa da akwai matsala, aikuwa suna shiga dakin suka tadda
Mimi tana wani irin buge-buge kan bed din tana wani cije bakin ta ga idanunta sunyi sama sun
k'afe fari tas!! Da su. Innalillahi wa'ina ilahi raji'un " Shine Abunda Jahid ya fad'a ya futa daga
dakin da saurin tsiya, mu kuwa rifuwa mukayi kanta Umma addu'a kawai take tofa mata, ni kam
baki na ya kulle a lokacin kallon ta nake kurrum tana buge-buge na rasa wane taimako zanyi
mata, a takaice ma da naji ina Neman fad'uwa sai na zube a gurin ina fad'in "Innalillahi wa'ina
ilahi raji'un." Amjad hannunta yake kokarin rikewa abun ya faskara domin yau duk k'arfin sa
Mimi yafi shi, kokarin fadowa take daga bed din yayi saurin tare ta ta fad'i jikin shi, har ila yau ba
daina cije-cije da take ba.

Likitoci kusan biyar ne suka rufu a kan Mimi domin ceto rayuwar ta suma sun tsorata da
al'amarin kuma yayi musu bazata lallai ubangji Shahidi ne kuma shine yasan gaibu kana taka
Allah na tashi, duk iya bunkicen su a kan Mimi bai nuna musu wata alamar na cewa zata yi
jijjiga ba, amma dake Allah Allah ne ya saukar da hukuncin sa kan baiwar shi, a war su biyu a
kanta suna kokarin shawo kan Matsalar da tsayar da jinin da yake zuba Abu ya fassakara,
Wanda a wannan lokacin Mimi ta amsa kiran Ubangji dukanin su sun tsorata mutuka duk da
suke likitoci suna ganin irin wannan tashin hankali amma al'amarin Mimi ya girgiza su, Dr Faruk
ya lura cikin na na motsi take suka shirya yi mata CS domin a Ciro abunda yake Cikin tunda
da ran shi.
Jahid daure wa yake akeyin aikin dashi, zuciyar sa nacan tunanin ya za'ayi ya Sanar da Amjadu
wannan mummunan labarin. Cikin hukuncin Allah suka samu nasarar ciro baby girl 'yar wattani
bakwai ba sati d'aya, yarinyar 'yar mitsitsya da ita, tana cikin koshin lafiya take suka sanya ta
Cikin kwalabar su, da aka tana da domin irin su, suka kimtsa gawar Mimi , cike da alhini da
tausayi suka futo
Da Amjad suka yi karo tsaye a kofar dakin dasu ke, Jahid yaji gaban shi na fad'uwa, hannunsa
yaja suka shiga ofis din sa.
Amajad yace." Jikina na bani bazan ji alkairi ba daga gare ka, kawai ka fad'a min menene?
Domin fuskar ka ta nuna alamun damuwa." Babu wani kwane-kwane da b'oye-b'oye domin dole
ya Sanar dashi hakkin shi, yace." Allah yayi wa Mimi rasuw..... Kafin ya karasa ya d'aga masa

hannu da saurin! Yace." Kar ka k'arasa min naji."!!!!!!! Jahid ya mike daga inda yake ya zauna
kusa dashi da kalamai masu taushi yace." Ubangji shine ya hallice ta a sanda yaso babu
tsammani kuma a karb'i abunsa a sanda yaso kar ka manta dani da kai duk zamu je inda Mimi
taje komai daran dad'ewa mutuwa riga CE, aya ce ga dukanin wani musulmi Mimi tayi sha hada
ta mutu ta farkin haihuwa addu'a zaka yi mata."!!
Hannun Jahid ya rike tamau! Leb'anshi na rawa haka zalika jikin shi na wani irin tsuma yace."
Innalillahi wa'ina ilahi raji'un. "!!!!!!!!! Jahid ya dinga dukan kafad'un shi alamun rarrashin yana
tausar zuciyarsa da kalamai masu sanyi, d'ago idonsa yayi Wanda suka zama kamar Jan gauta
bakin shi na rawa yace." Muje a shirya min gawar Momyna ayi mata suttura."!! Jahid ya mike tare da shi suka futa kai tsaye dakin dasu ke aje gawarwaki suka nufa, tuni an
daure Mimi guri guda tana kwance sambal kan wani siririn gado an lullub'e ta da wani farin zani,
fuskar ta ya bude, yaga tayi kyau sai murmushi take kamar yayi mata magana ta amsa, zubewa
yayi jikin gado yana sakin wani irin kuka. Tare da fad'in"Momyna Allah ya jikan ki, halin ki nagari
ya biki, Momyna na hafe miki insha Allahu kece Uwar gida na a aljannar Fiddausi."!

Jahid na tsaye yana kallon shi cike da tausayi da alhini, mik'ewa yayi hade da sanya tafukan
hannayen shi ya shafe fuskar shi, ya kalli Jahid din a dake yace." Muje." Jahid ya bishi a baya
suka futa.
Ko da ya shigo dakin da muke bai yadda ya had'a ido da kowa ba yace." Zamu je gida yanzu
Jahid ya bamu sallama."
Granny da Umma ba yara bane balle maganar sa ta shige su Granny tace"Kai k'ato bana son
kumbiya-kumbiya kawai ka fad'a ma kome yi mu 'yan Adam ne zamu dauki kaddara rufewar
bata da amfani, shin ya jikin Aishatu ne."? Yana kokarin futa yace." Allah ya amshi ta." Wani irin
ihu! Na kurma had'e da bin bayan sa a guje, ina kokarin taddashi tafiyar mu ba d'aya bace ina
kuka nake fad'in"Karya kake mugu azzalimi sai dai idan Kaine ka kashe mana ita, idan hakan ta
kasance sai na dauki fansa."!!!!!!! Ko juyowa bai ba, ya shiga wani daki, kokarin binsa nake
wasu nurses suka rirrike ni suna bani hakuri, wani k'arfi ne ya zo min a lokacin na fuzge daga
jikin su sai kace wata mai iskokai na afka dakin a guje! Abunda na gani ya sani jin wani irin jiri
tuni na fad'i a gurin ina kallonsu dishi-dishi inda suke kokarin Dora mimi kan wani gado Duk an
dad'adaure mata k'afafunta da hannaye ta babu Wanda yabi ta kaina harshi kanshi Jahid din
suka tura Mimi dake kwance kan Wani k'arfe suka futa.
Silalewa nayi na fad'i a gurin ba tare dana San a wace duniyar nake ciki ba.
Tuni Umma da Granny sun futa sun tsaitsaya aka futo da gawar Mimi tare da sanya ta a motar
asibiti Umma sai share hawaye take yi, suka shiga, dravar yaja motar, lokacin kowa ya manta
dani sai Jahid din da ya dawo ta kaina shine duk yayi min taimakon su na likitoci na dawo
hayyacina kuka sosai nake yi had'e da dukan shi kamar mahaukaci nake cewa an hada baki
dashi an kashe min Mimi, ganin kamar bata cikin hankalin ta ya sanya yayi mata allura take
bacci me nauyi yayi gaba da ni.

Wasu nurses ya sanya suka shigar masa da ita mota, ya bar asibitin cikin halin damuwa da
tashin hankali, Kamar gawa a ka shiga dani cikin gidan Amjadu inda ya cika da Jama'a maza da
mata lokacin tuni an shirya gawar Mimi an futo da ita, saboda haka Jahid kawai ya tsaya nan
aka sallace shi da ita, shine a gefe Amjad din a gafe suka dauki makarar dukanin su zuciyoyin

su babu dad'i amma dai komai ubangji ya saukar kan bawan shi ne dai-dai.







*25/11/2019*
[11/26, 9:20 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*


*MALLAKAR_ BINTA UMAR*



*LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA
CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO
MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA
SAI TA CI SHI*




*63*




Mutuwar Mimi ta girgiza zuk'atan Al'umma bamu kad'ai ba hatta da masu gadin gidan sai da
suka ji a mutuwar a jikin su, Jama'a kuwa daga ko ina b'arkowa suke yi ta'aziyya wasu kuma
gulma ce take kawo su, domin 'yan jarida sun ruga sun gama wa tsawa duniya cewa mutuwar
mayar Young millionaire tana da nasaba ne da harin da jama'ar gari suka kai masa, wa 'yanda
basu San yayi aure ba suka dinga mamaki shine suke zuwa zaman makoki, mai girma governor
Sarkin kano duk dasu akai sadakar uku, su mai citta ma duk dasu babu tsoron Allah ko na
kwabo a tare dasu, a fili sun nunawa Amjadu kara a zuciyarsu kuwa murna suke yi sosai, shi
kuwa governor abun ne ya soma bashi tsoro ganin yanda yazo zaman sa na k'arshe jama'ar
gari na raka shi da dutsina suna fadin "Ba mayi."!!! Kuma tunda ga mutuwar Mimi jama'a suka
fara gane cewa harda sa hannun governor akan sharrin da akai wa Amjdin, ranar a tsorace ya
bar kofar gidan Amjad ganin yanda matasa suke jifansa kamar ba governor ba, sai da jami'an
tsaro suka fara sakin harbi sannan kowa yq shifa taitayin sa, Umma kuwa jin irin zantukan da
jama'ar gari suke yi kan mutuwar Mimi yasa tace" Suyi hakuri kar su bata wa Mimi gawa kawai

Allah ya amshi abunsa lokacin da yaso.

*****
Yau kwanan Mimi bakwai a karkashin k'asa, na fige na tsigale sai Umma tayi da gaske nake cin
abinci kullum ina zaune zukud'inm! Ko kuma in tafi dakin ta in kwanta kam bed dinta hade da
rungume wani k'aramin hoton mu, dake cikin frem a kan drowr gefan gado ta aje shi, kuka nake
yi sosai, Umma granny dashi kanshi Uban gayya naga duk sun saki jikinsu har hira suke yi suci
abunci hankali kwance kuma suyi dariya, ni kadai ce nake cikin halin damuwa da bakin cikin
rashin Mimi, tsakanina dashi kallone domun tunda Mimi ta mutum magana ta fatar baki bata
hada mu dashi yau kwanakinmu bakwai kenan a cikin gidan shi, ya sake sosai yayi wanka ya
shirya harda fesa turare sai abun yayi ta bani mamaki ina zargin sa, dama ya fi son Mimi ta
mutu ya cigaba da tsula tsiyarsa take wata irin tsanar sa ta cika min zuciya ta.

Jahid kullum yana kirana a waya sai dai Sam bana sakewa dashi domin gani nake yi kamar
bakin su da daya da Amjad din, matar shi Hafsa me kirki da ita duk a gama zaman makokin INA
lura da ita da yanda take satar kallona a fakaice.

Babu kuzari a jikina na futo daga dakin Mimi hannuna rike da k'aramin hoton mu, kusa da
Umma na zaune a hankali nace"Umma zaman me muke yi a gidan nan? Wallahi nagaji gani
nake kamar Mimi zata dawo gwara mu tafi." Umma tace"Eh dama yau kam zamu tafi tunda an
share makoki, muna jira maigidan ya futo ne zamu je duba baby insha Allah daga asibitin sai
mu wuce gida." Granny tace"Habadai Ku kuwa ai sai kace Wanda ake kora kwabari kuyi sati
biyu mana in baza Ku bari ayi ar'bain ba, har yanzu fa ana zuwa gaisuwa." Umma tace"Tafiyar
tamu ta dole CE Hajiya ni kaina a takure nake a gidanan wallahi, kiyi hakuri duk Wanda zai mun
gaisuwa ya same ni a gida." Granny tace"To Allah dai ya gafartawa wannan yarinya.
Tsaf ya futo Cikin dogayen kaya,na lura tunda akayi mutuwar nan bai sanya k'ananun kaya ba,
k'amshin sa ne ya cika parlor ya tsaya bakin kofar shi yana gyara links dinshi, saurin kauda
kaina nayi daga kanshi ina jan tsaki kasa-kasa wallahi wani mugun haushin sa nake ji. Umma
tace"Ka futo kenan."? A hankali yace." Eh Umma Ku tashi muje yanzu, amma naji kuna wata
magana ko." ? Umma tace"Eh kam yau zamu tafi gida." Yace." Umma kuyi hakuri ayi sadakar
ar'abain mana." Umma tace"Bazai yiwu ba, INA da uziri Asma'u kuma makaranta zamana a
gidanan bashi zai dawo da Mimi ba." Yace." Hakane Umma shikkenan Allah yasa ka da alkairi. "
mik'e wa Nayi da sauri na bar gurin, hijab dina na dauko dama tunda nazo kayan Mimi nake
amfani dasu, Umma ko granny ce ta dauko mata wasu sabbin atampopi super take sanya wa
yanzu daya daga cikinsu a jikin ta, Granny ta mike tana fadin "Baza Ku barni a baya ba, muje
inga 'yar yarinya cikin kwalba."


Aikuwa ko da sukaje Asibitin fafur likitoci suka hana su shiga ganin baby Aisha yarinyar da
Ubanta yayi mata huduba da sunan mahaifiyar ta, shi kam ai dactors din sun San shi farin sani
dolen su suke kyaleshi ya shiga yaga babynshi kullum baya iya bacci sai yaje ya ganta haka
kazalika kullum kara kaunar yarinyar yake Cikin zuciyar sa, yarinyar kamar su daya da uwarta
sai dai ta kwaso hasken fatar shi, fara ce sosai, Amjad kam yafi Mimi haske nesa ba kusa ba,

Alhmdullahi tana samun kulawa sosai daga gurin dactors ta fara k'wari da girma jikinta ya fara
murjewa tana rayuwa cikin kwalba cikin hukunci ubangji.
Babu yanda muka iya haka muka hakura amma naji babu dad'i a zuciya ta domin naso inga
baby nan wallahi ga yanda naji ubanta na fadin kamar si daya da Mimi, Jahid nayi ta kira a
waya yak'i dauka saboda yasan zancan dokar asibitin CE, yana ganin kan Asma'u ba zai sanya
ya karya ba. Amjad har gida ya kaimu Cikin motarsa, zuciya babu dad'i na futo daga motar ba tare da na jira
su Umma da aunt Hauwa ba, barin su nayi tare dashi suna sallama, Ya Aminu ne kawai a gidan
dama yasan da dawowar mu tunda aunt Hauwa tayi masa waya tsaf muka tadda gidan, rumfa
na zube kan leda na fara kuka. Suka shigo suka same ni a haka aunt tace"Wannan wane irin shirme ne." ? Cikin kuka
nace"Aunt don baki San yanda nake ji bane a zuciya wallahi Ashe duk gujewa mutuwa da muke
yi akan Mimi tana jika aunt Mimi tasha wahala a rayuwar ta wallahi" aunt tace"Sai hakuri
dukanin mai rai mamaci ne addu'a kawai zamu yi mata." Ya Aminu ya shigo dakin yana fadin"Wannan kukan da kike yi kina kara mata azaba ne idan ta
fado miki a rai kiyi mata addu'a. " shiru kawai nayi musu.

Ko da na koma makaranta ba wani sake ba, kullum muna tare da Munnu muna zancan Mimi da
halayen ta na hakuri da ban dariyar ta da saurin kukan ta wani lokacin idan na tuno hae sai na
share hawaye sai kawai inyi mata addu'a samun rahamar Allah.

Kullum kuwa sai na damu Umma da zancan babyn Mimi nace ta nemi alfarma gurin Amjad ta
dauko ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login