Showing 42001 words to 45000 words out of 95753 words

Chapter 15 - BABBAN YARO Part 2 By Binta Umar Abbale .pdf

musu bakin ciki suga samu suga
rashi,babun bad'ulahu kenan abunda bazai yiwu ba wallahi ko gawar Asma'u ce sai an kaita
Gidan Amjadu sai dai idan shine yace ya fasa auran.


A fusace ! Yace." Duk wani iya shege da zakuyi ke da uwarki a tafin hannuna kuke, kuma ku
rubuta Ku aje, jibi I war haka kin zama matar Amjadu kin zama Mallakin sa, in dai nine wakilin
ki." Ya futa a fusace. !!



Umma naje na rungume da kyau! Ina kuka ina share mata hawaye nace"Umma ki kwantar da
hankalin ki duk yanda kike so haka za'ayi ki zab'a min miji Wanda kike so Amjadu na bar wa

Mimi ."


Umma tace." Asma'u kina jin abunda Kawun Ku yake fada ko akan ki kina jin irin cin mutumcin
da yake min ko.? Nace" Umma duk naji kiyi hakuri ki kyalesu dama ba yau suka saba miki cin
mutum ci. Ni nasan yanda zanyi insha Allahu Mimi bata da miji sai Amjadu ki kwantar da
hankalin ki."
Hannun d'iyar tata ta rike tare da fad'in"Ubangiji Allah yayi miki albarka Asma'u Yanda kike min
biyyaya Allah ya baki 'yaya masu biyayya kema, yanda kike ceci rai ubangiji Allah yasa Annabi
ya cece ki kema." Wasu zafafan hawaye na hau sharewa lokaci guda tausayin kaina ya kama
ni, wani irin hali na shiga a lokacin ta inda naji gwara min mutuwa da rayuwa Allah-Allah nake
naga Mimi a gidan Amjadu ko ma samu hankalin mu ya kwanta, Alluma ajirin fi musibati wa
aklifni kairan minha itace addu'ar Dana ke ta maimatawa a zuciyata tare da Innalillahi wa inna
ilahi raji'un, lokaci guda naji zuciyata tayi sanyi na kalli Umma tare da fadin"Don Allah Umma kar
a kara tayar da maganar nan domin I Dan Mimi taji to wani tashin hankalin ne, Umma kija
kunnen Ya Aminu a kan hakan." Umma tace"Nima abun ya soma damuna Asma'u Insha Allah
zan ja kunnen sa, ke dai Allah yayi miki albarka insha Allahu yanda kika sanya ni farin ciki kema
'yayan ki zasu sanya ki."




Bacci ne ya soma fizgar sa kad'an-kad'an yaji ringing din wayar sa, cikin kunnen sa, dalili
airpic din dake manne a kunnen sa, a hankali ya dauki wayar dake saman k'irjinsa yana
dubawa. Mik'ewa yayi da sauri ganin numbar da ta kirashi.



Ba tare da ya cire airpix din ba ya latsa wayar tare da fadin"Salamu alaikum." Murya Asma'u
yaji sama-sama ta amsa da wa'alaikasalm. " gabansa ya fad'i sosai lumshe idonsa yayi hade da
cije leb'anshi fargabar abunda zaiji daga bakin ta yake."



Kai tsaye yaji tace"Barka da yamma." A hankali yace." Barka ya kike Husnah."!!
"Lafiya.'! Tafad'a babu wani sassauci ta cigaba da cewa " Yanzu Kawu Yunusa ya bar gidanmu
bayan ya Sanar damu sak'on ka."

"Owk" shine abunda Yace yaja bakinsa yayi shiru yana sauraran ta. Ta cigaba da cewa" Allah
ya kadddara ni ba matar ka bace, ina yi maka fatan alkairi idan son da kake min na gaskiya ne,
to a madadina da aka zab'a akan Mimi ni na hak'ura ka mai da maganar auranmu kan 'yar
Uwata domin ceto rayuwar ta.".

Wani irin gumi ne yake tsayaya daga jikinsa bakinsa yayi wani irin daci ya soma Jin zazzab'i
na shigar shi, jin abunda take cewa, amma da yake NAMIJIN duniya ne, muryarsa a tsaye
yace." Meye hujjar ki ta fad'ar haka, shin nine bakya so ko kuma akwai wata manufa taki."? Cike
da dakiyar zuciya tace." Eh duk biyun ne bawai bana sonka ba ne, Mimi tafi ni sonka bayan
haka kuma kayi mata alk'awarin aure ka yaudare ta da kalaman ka hade da zakin bakin ka, kayi
kwance kwance ka lasa mata Zuma a baki daga baya kuma kace ka fasa auran ta, shin baka
tunanin halin da zata shifa ko kuma kana so mu rasa ta, son da Mimi take maka zai iya kashe
ta."!



Wani irin yammm!! Yake ji a jikinsa tsigar jikinsa tana Mik'ewa jin abunda yarinyar take fada, a
kausashe yace." Shine Hujjar ki."! ?
"Eh shine Hujja ta." Ta fada babu wasa a cikin maganar ta."

Ajiyar zuciya ya sauke minti uku tsakani yace."Shikkenan tunda haka kika Zab'a mana ni dake
muyi rayuwa na karb'i Mimi a matsayin mata kamar yanda kika bukata, Allah ya sa haka shi yafi
alkairi.".
Da sauri nace"Ameen auran Mimi alkairi ne a gare ka insha Allahu." Kashe wayarsa yayi ba tare
da yace min komai ba.



Lokacin naji damuwar da ke cikin raina ta ragu burina kawai inga Mimi gidan Amjadu mu huta
da wannan masifar, duk abunda ya faru tsakanina dashi na Sanar da Umma ita ma taji dadin
yanda ya amunce lokaci guda.




Hannusa ya sanya ya dafe kansa dashi lokaci guda kansa ya shiga Sara masa wani irin bakin
ciki da damuwa sun taro sun tsaya masa a mak'ogwaro da kyar yake had'iyar yau!! Sosai yake
jin bakin ciki da takaicin zafafen maganganun da yarinyar ta watsa masa lallai inda ranka kasha
kallo wai shine yau 'ya mace take furta cewa bata son sa baki da baki yarinyar ma k'arama irin
Asma'u.

*14/November/2019*
[11/15, 10:20 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*


*MALLAKAR_ BINTA UMAR*



*LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA
CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO
MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA
SAI TA CI SHI*




*52*




Yana zaune a gurin hannunsa saman goshin sa granny da Iyami me aikinta suka shigo parlor
Iyami ta nufi daining tana gyara gurin, ita kuma Granny ta k'araso kusa dashi da sauri ganin
yanda yake cije bakinsa yasa ta dafa kafadar sa, tare da fadin"Kar ka sake ka sanya damuwa
cikin zuciyar ka har ta haifar maka da wani ciwon ni dai a ra'ayi na nafi so ka auri 'yar bak'ar
yarinyar a cikin su biyun naga kamar tana da kunya da hankali." Ta k'arashe maganar ta a
tausashe.


Da kyar ya iya bude bakinsa yace." Tace bata sona Granny. " Zama tayi kusa dashi cike da
mamaki tace" Amma Wannan anyi 'yar banza ta samu namiji me zafi da kwarjini kamar tace
bata so, in banda ma Matsalar ka nasan ko mata dozin aka aje maka zaka iya dasu, amma
wannan yarinyar ta bani haushi wallahi. " Kwanciya ya gyara hade da lumshe idonsa shi kadai
yasan abunda yake damun zuciyar sa. Granny kuwa mita take tayi tace"Tun farko sai da nace
maka kaje ka nemi auran Hafsatu ka kiji kaga ni ai abunda nake guje maka."

A hankali yace." Granny magana ta wuce a halin yanzu insha Allah jibi za'a d'aura min aure da
Ma ko wacece na yadda haka Allah ya shirya min." Tace"Tunda dai kayi niyyar auran mata biyu
mai zai hana ka hada da Hafsatu nasan in kayi magana baza su ki ba."

Jajayen idonsa ya bude ya sauke su a kanta, fuskar shi a murtuke yace." Ki k'yaleni da wani
zance Inji da guda d'ayan ma ni da ba cikkakiyar Lafiya ba."

Hararasa tayi tace"Au! Ashe munafurci ne yasa kace zaka hada mata biyu hummm! Kai dai ka
sani ma kanka."


Shiru yayi cikin zuciyar sa Yace ." Granny in batayi wasa ba zai sauke fushinsa akan ta yanzu
juya mata baya yayi ta gaji da mitar ta tashi daga gurin.
Wayoyinsa duk kashe su Yayi domin baya bukatar damu a halin da yake ciki ji yake zuciyarsa
tana iya bugawa ta tarwatse.

Sai daf da magari ba ya tashi daga kwanciyar da Yayi kai tsaye masjid ya nufa yayi sallolinshi
tare da addu'ar Neman zabin Allah ya futo daga massalaci Jama'a na ta mik'o masa gaisuwa
Amjadu bashi da wulakanci sosai ya tsaya ya gaisa da mutane, cikin ikon Allah yana shiga
gidan yaji zuciyar sa tayi masa sanyi, sakamakon karatun alk'uranin dake tashi a parlor Granny
ta kamo tashar Saudiya tv Jama'a na ta kewaye dakin Allah *(Ka'aba)* zama yayi kusa da ita da
carbi a hannunta sai da ta kammala tukkuna ta kalleshi cike da kulawa tace." Iyami ta girki
dafaduka shinkafa da daddawa nasan kana son shi, tayi amfani da bussasan kifi yayi dad'i
sosai. " Murmushi yayi yace."naji dad'i kuwa domin rabo na da cin abunci me nauyi har na
manta. Granny ta mike hade da aje carbin NATA a kan kujera tace." Naga alama kazo kaci ka
koshi naga alamun yunwa a tare da kai."
Mik'ewa yayi yabi bayan ta, yana 'yar Dariya domin ya kwantar mata da hankali shi kam a irin
halin da yake ciki yanzu kome za'a bashi bazai faran ta masa ba Idan ba Asma'u aka bashi ba."


*****
Shirye shiryen aure ya kammala duk wani Abu da ake bukata akwai shi a aje idan da kud'in ka
ka wuce Matsalar komai, Tun safe su Kawu Yunusa suka yo gayya 'yaya da jikoki suka zo suka
kare mana zagi ni da Umma munji bakin ciki da ciwo Abunda suka zo suka yi mana a unguwa
amma daga k'arshe muka hak'ura muka cigaba da sabgar mu. Duk Abunda. Amarya take yi
nida aunt Hauwa mun sanya Mimi tayi domin me lallai har gida tazo tayi mata ja da baki, aunt
ce ta sanya mata man shamfo a kanta, ta had'a kayan gyaran jiki na sanya Mimi a gaba na
dinga mulka mata a jiki ina gogewa yinin ranar abunda muka yini kenan, lokaci guda Mimi tayi
Wani uban kyau jikinta sai shek'i yake,murmushi kawai take yi ga lallan ta ya futo radau abunka
da farar fata.

Bayan mun idar da sallahr La'asar ne, muka tafi can yakasai gurin dinki kayamu kala uku duk iri
daya dinki iri daya komai iri daya muka karbo a dai-dai muka shiga muka dawo gida sai murna
nake Mimi ta saki ranta, Muna Isa gida muka tadda Munnu tazo dakinmu muka shige muka
cigaba da tsara yadda zamu gudanar da walima domin lokaci yazo a kurace gobe daurin aure
jibi kuma walima kuma a ranar za'a kai Mimi.

*****

K'arfe biyar da kwata na ranar alahamis yana zaune a harabar gidan shi jikinsa sanye da kayan
motsa jiki Rambo ya shigo cikin gida a mota ya gyara parking ya futo hannunsa rike da ledoji
manya manya masu dauke da tambari na sunan company nin sa, karasowa yayi kusa da shi
tare da fadin"Sir barka da yamma." Dago kanshi yayi yana kallonsa kana ya amsa, Rambo
yace." Komai ya kammala kamar yanda ka Umarta naje har gidansu na kai kayan. " Fuskarsa
babu wasa yace." Alhmdullahi ina bunkice da na sanya kayi min." Rbow yace." Mahaifin
yarinyar dai kamar yanda aka fad'a talaka ne sosai Dan duk 'yan uwansa sun fi shi rufin asiri
yana aikine karkashin company madara ta cowbell bayan rasuwar sa, haka naji daga bakin
abokan sana'ar shi ya rasu sanadiyar hatsari a titin sharada mota ta take shi."

A hankali yace." Wane company yake wa aiki a lokacin."? Rambo yace." Cowbell ne Sir. Kuma
na samu labarin durkushewar company shekaru biyu da suka wuce."

Gyada kansa yayi shi bai taba jin sunan company madara wani cowbell ba Niko nace dama
yaushe zaka ji tunda k'aramin company k'ananun madara yake kawowa irin ta Leda ta yaku bayi
irin 'yar Hamsin a shirin da biyar.

Yace." Rambo kasa yara su gyara Wannan gidan nawa na Badawa nasan dai yayi kura sosai a
wanke ko ina a tsaftace ka duna kaga inda akwai abunda aje bukata a ciki kayi magana sai a
sanya musu, bayan d'aurin aure sai ka kai musu key din gidan."


Rambo yace." Insha Allahu za'ayi yanda kace Yallab'ai yanzu za'a sanya yara su fara aiki."
Girgiza kansa yayi hade daga masa hannu Rambo ya nufi mota da sauri, shiko Doh! Na bayan
shi a tsaye sai zare ido yake.

Rambo na kokarin futa da mota ne sai ga motar Hibbah tana kokarin shigowa ciki, Amjad na
gane ta ya mike da sauri ya shige cikin gidan domin yana gudun tayi masa shirme gaban ya
ransa.

Hibbah bata cikin nutsuwar ta tun lokacin da ta samu labarin auran sa take kuka kamar ranta
zai futa ta kira wayarsa yafi curin masaki yak'i dauka wani lokacin ma sai taji wayar a kashe,
kuka sosai ta sanyawa mahaifin ta, dole ta sanya babu shiri Mai citta ya dinga kiran Amjadu din
a waya bai same shi ba, lallaba ta yayi yace." Tayi hakuri insha Allah bata da miji sai Amjad
tunda tana sonsa. Gani tayi baza ta iya hak'ura ba ya sanya ta biyo shi har gida.


Yana kokarin shiga bedroom d'insa ta fad'o parlor da gudun tsiya taje ta rungume bayansa tana
wani irin kuka me shiga zuciya, tace." My Apple Yanzu aure zaka yi ka barni auran ma ka rasa
wadda zaka aura sai Mara tushe da Asali wacce ake zargin shegiya ce." Tana kuka take

maganar.

Fuskar shi a daure ya sanya hannunshi ya jawo ta gaban shi ido ya tsira mata tare da
fadin"Waye yace miki matar da zan aura Shegiya CE." Hibbah na kuka tace"A gurin jama'ar gari
da gidanan redio."
Kara hade fuskar sa yayi yace." Kar in kara jin Kim fad'i haka matar da zan aura tana da asali
duk sharrin jama'ar gari ne., cikin kuka Hibbah tace." Nasan duk irin Asalin ta da nasabar ta na
fita, ni ya kamata k aura ko don son da nake maka."

Zama yayi da ita cikin kujera muryar shi a cunkushe yace."Hibbah bana son wata damuwa a
halin da nake ciki, ina me tabbatar miki da cewar duk son da kike min tafi ki nima zan aure tane
domin sadaukar wa."

Tana kuka tace." Don Allah ka auremu tare, nayi maka alk'awarin zan jiyar dakai dad'i zan kula
da kai kamar kwai zan tarairaye ka fiye da tsammani ka, ka taimaka ka aurmu tare."
Kallonta yake da rinannun idanunsa yace."Kije ki tambayi Asma'u idan ta amunce shikkenan ko
bayan d'aurin auramu da Mimi ne sai mu shirya aure dake." D'ago kanta tayi dake kafadarsa ta
rike hannunsa tana murzawa tare da fadin wacece Asma'u." Idanunsa ya lumshe a hankali yac"
Tsohuwar budurwa ta CE." Hibbah taji gabanta ya buga daram!!!! Yana nufin tsohuwar budurwar
sa zata roka ta sanya shi ya aure ta, lallai da sake shi ko wane irin so yake mata haka, ranta
nayi mata suya tace." Shin kana nufin kace da ita itace ta sanya ka auri Wannan din."? Daga
kansa yayi alamar Eh.
Hibbah ta sunkuyar da kanta tana wani tunani sannan Tace. " zan tambayeta kuma in roketa
domin durkusawa wada ba gajiyawa bane indai akan Kane babu abunda bazan yi ba, ka bani
numbar ta." Tafad'a tana mik'a masa wayar ta.

Karba yayi ya sanya mata numbar Asma'u. Ta maida wayar cikin jakar ta bayan tayi serving
numbar. Fuskarsa ta kurawa ido tana kallon dan k'aramin bakinsa idanunsa a lumshe suke yaji
kamar ana kallonshi yana bude idonsa ya sauke kan Hibbah ta kura masa ido kamar tsohuwar
mayya, mai da idanunsa yayi ya rufe yana jin takaicin ta, a hankali Hibbah ta matsa jikinsa sosai
ta rungume shi hade da hayewa jikinshi ta tallafo kanshi ta Dora a k'irjinsa kamar mai bawa
YARO mama haka tayi masa, kawai sai ya tsinci kansa da gogo fuskarsa tsakanin k'irjinta
Hibbah ta saki wata zazzafar ajiyar zuciya ta cigaba da sha sumar kansa da take bala'in so,
murya a sark'e tace." Inayi maka wani irin so da ban San iya adadin sa, ba, zan iya shiga wani
hali mutukar ban same ka ba ka tallafi rayuwa ta. Amjadu da duk irin bakin ciki da damuwar da
yake ci baya hanashi fitinar sa Idan ta motsa Yanzu ma mantawa yayi da damuwar sa zuciyarsa
ta kwadaitu da son kasancewa da Hibbah ko banza ta iya salo kuma ta iya romcing sosai yake
jin dadin ta, d'aukar ta yayi ya shige bedroom d'insa da ita ya jefa ta akan gado, Hibbah ta mike
da sauri hade da cire d'ankwalin kanta, kafin ta Ankara runi ya danneta hade da ciccusa
hannunsa biyu cikin matsatstsiyar rigar ta, nishi ta saki ta zura hannuta ta baya ta zage zif din
rigar da hannunta ta cire masa, jiki na karkawara ya balle briziyar ya cafko manyan breast dinta
yana murzawa duk jikinsa ya rikice.
Muna zaune a tsakar gida muna duba kayamu babu laifi gidan ya soma cika da baki,

k'awayenmu Wanda suka samu labari sun soma zuwa, Kawai muka ji Sallama gabana ne ya
fad'i lokacin da naji muryar me sallamar irin ta Rambo, gudun abun kunya yasa na mike da
sauri hade da zura hijab dina na leka soron aikuwa Rambo ne tsaye gaban shi wasu manya
manya ledoji ne guda hudu.

Fuskata na hade sosai nace" Lafiya ko.."? Kamar me jin tsorona yace." Yallab'ai ne ya aiko ni."
Ledojin dake gaban shi nake kallo yace." Gashi yace.",A kawo muku kuyi amfani da wannan
bayan d'aurin aure zai hada mata lefan ta." Nace"Babu laifi ai kace mungode kaji." Rbow yace."
Akwai kayan abunci mota guda yace a kawo." Shiru nayi na minti biyu daga bisani nace" Ka
sanya yara su shigo dasu." Da sauri yace." Shikkenan ." futa yayi da sauri ni kuma na fara
d'aukar kayan ina shiga dasu gida d'aya bayan d'aya.


Buhunan shin kafa ne da taliya ledojin maggi da jarkokin mai, kai duk wani Abu da za'a bukata
gashinan har da nama da kifi ciki wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login