Showing 72001 words to 75000 words out of 95753 words

Chapter 25 - BABBAN YARO Part 2 By Binta Umar Abbale .pdf

baya ni daga bakin ka, shin zargin da ake maka cewar ka
had'a baki da yahudawa domin Ku tuzarta Allah da manzon shin hakane."?
Amjadu yaji wani k'aton bakin ciki ya tokare masa a mak'ogwaro shiru yayi bai ce musu komai
ba, kallonsu kawai yake kamar zautacce.! D'ayan da bai yi magana ba shine yace." Ranka ya
dade jama'ar gari sun ci alwashin sai sun kashe ka kan abunda ka aikata sai sun k'one gidan ka
sai sun k'one company ka, sai sun kona ka, yanzu dai sun samu nasarar k'one company ka
kurmus! Ta inda babu wani Abu da zaka Mora a cikinsa, abun mamaki da daure kai kuma sunyi
zanga-zanga sun je har inda kake sun kasa aikata Abunda suka yi niyya, gashi kuma yanzu
mungan ka a hospital cikin halin damuwa da d'imuwa ran ka ya Dade muna bukatar garin haske
a gurin ka.

A jiyar zuciya ya sauke ya mike tsaye da sauri! Suka fara kara masa lasifikar su a bakin sa,
Sunkuyar da kansa yayi kasa hade da soka hannunwan shi duk biyun cikin aljihun wandon dake
jikinshi yace." Alhmdullahi Allah ne abun godiya a halin yanzu." Shiru ya rasa gurin, ga 'yan
kallo duk sun nutsu
Ya cigaba da cewa"Ban yi niyyar magana daku ba amma dole tasa zan fad'i Abu guda akan
wannan k'azafi da akai min, cewar ni *Amjadu Abul Abbas* zan tsaurara bunkice akan mutanan
da suka shirya min wannan sharrin, mutukar na kama su, babu shakka dani dasu za muyi kare
buri jini dasu, domin sai dai a dauki gawarsu ko a dauki tawa, ni *Amjadu* bana had'a Allah da
ma'aiki da kowa, Wallahi wallahi sai dai idan na kashe su hukuma ta kashe ni, duk Wanda zai yi
wasa da Allah da manzo to tabbata barin sa a ban duniya shirka CE,idan ban kashe su ba, I
promise Sai na raunatasu! Sai na jikkatasu! Sai na sassab'a musu kamannii!!!!!, wannan shine
magana ta."!!!
Ya fada yayin da yake wata irin zabura!!!!
Dan jarida d'aya yace." Ranka ya Dade shin baka jin ciwo da bakin ciki akan b'arnar da akai
maka, gashi duka duka company ka ko shekara guda bai yi ba shin yake jin zuciyar ka a
wannan lokacin."?

Girgiza kansa yayi ba tare da wata damuwa ba yace." Company na da suka k'ona bai min ciwo
ba, da sun barshi ma ni da kaina zan zazzaga masa fetur in kona shi, saboda bashi da amfani a
gurina, company da ya tara miyagu marasa tsoran Allah a ciki barinsa babban hadari ne, naji
dad'i mutuka da suka kona shi. " ya k'arasa maganar sa yana futo da hankici daga aljihunsa ya
goge fuskarsa.

Daya Dan jarida ne yace." Ranka ya Dade sai tambaya ta k'arshe kayi hakuri muna son muji me
ya kawo ka asibiti gashi dai a zahiri jikinka babu ko kwarzane babu jini balle ace ko daga gurij
mutanan da suka kai maka har....... Kafin ya karasa maganar shi ya katse shi ta hanyar
fadin"My wife dina tana ciki cikin halin rai da rayuwa duk ta dalilin wannan ibtila'in babu abunda
zan ce sai dai Allah Ubangji ya saka mata ga dukkanin mutanan da suka shirya faruwan
hakan.""""""Yana gama maganar shi ya maida hannun sa fuskar sa ya rufe ruf! Yana kukan
zuciya
Duk wani mai imani da tausayi a lokacin zai tausaya masa mata masu rauni tuni sun soma
zubar da hawaye, jiki a sanyaye 'yan jaridar suka masa sallama suka futa.

Dukanin abunda yake faruwa bamu da labari mun dai ji labarin yanda mutanan gari suka k'one
company ya Aminu ya kawo mana video mun gani a wayar abokinsa garba har yanzu Umma
kuka take yi tana tunanin wane irin hali Mimi take ciki dashi kanshi Amjadu din, domin da har ta
dauki mayafi zata futa Ya Aminu ya hanata da sauri yaje ya kulle kofar waje da kwado domin
rigima muke da ita wai sai ta futa taje gurin su Mimi.



*****
Yana zaune a gurin shi kadai sai gilmawar nurses da d'aid'aikun marasa lafiya da suke shigowa
asibitin.
A gogon hannunsa ya kalla K'arfe goma shaura, cikin tararrabi da tsinkewar zuciya ya mik'e
tsaye yana kallon room din da aka shiga da Mimi ciki.
Kai tsaye ya durfafi d'akin baya ko kallon gabansa.
Karo suka buga da Jahid ya futo daga dakin hannunsa sanye sa safa, duk ta b'aci da jini.!! Wani
kallo yayi masa yana bin hannunsa da kallo cikin fad'uwar gaba.!
Jahid ya gyara yanayin fuskar sa, cikin rashin kuzari yace.''tana bukatar jini cikin gaggawa."!!
Amjad kokari yake ya bangaje Jahid ya shiga dakin.
Jahid ya tare hanya cikin sigar rarrashi yace." Colm down Aboki tsaya ka saurare ni tukkuna."
Cikin damuwa da fargaba yace." Muje ka sanya mata nawa jinin kar Ku kashe min matana."!!!
Muryar shi na kyarma ya k'arashe maganar tasa."

Jahid ya rike hannunsa ba tare da ya damu da jini da. Yake hannun nasa ba ya damk'e sosai
yace." A halin yanzu bani da masoyi sama da ita bani da kowa sai ita da abunda yake Cikin ta
sai granny su kadai suka rage min a duniya my friend bana so in rasa Momyna."!!!!! Tsabar
tausayi ta hana Jahid cewa komai ya ja hannunsa suka shiga wani d'aki.

A gigice Ya Aminu ya shigo gidan Hannunsa rike da wayar Garba abokisa.
Kamar dai d'azu da ya shigo mana da ita, duk ya rasa inda zai tsoma ransa, ya mik'o min wayar
bakinsa na kyarma yakasa cewa komai
Hannu na rawa na fara dubawa
Farko abunda na gani ya sani kurma wani ihu na jefar da wayar hanna hannu na d'ora aka ina
fad'in "Innalila wa'ina ilahi raji'un, shikkenan sun kashe mana Mimi mu."!!!!!!
Umma ta dauki wayar da sauri tana dubawa, Mimi ce rungume a hannun Amjadu lokacin da
suka shiga asibitin nasarawa abunka da mutumin da yayi suna a duniya aka samu wasu suka
dauke su vedio a wayoyin su, a lokacin suka fara turawa Media hade da sharhi cewa jama'ar
gari sun shiga har gidan *Young millionaire* sun Sassari matar shi mai dauke da ciki Dan wata
shida gashinan tana halin rai da rayuwa.!
Abunda ya k'ara tayar mana da hankali shine yanda mu ga jikin Mimi dashi kansa Amjadu din
duk ya b'aci da jini duk da cewar dare ne amma akwai hasken fitulu a ko ina na asibitin.
Umma ta mik'e tsaye cikin tawakkali ta kalli Ya Aminu da yayi tsaye a gurin duk ya rasa me zai
yi tace" Muje mu gani Aminu Mimi tata kaddarar kenan, bawa baya wucewa kaddarar sa, muje
idan ta mutu ne sai mu karbo gawar ta."

Hawaye Ya Aminu ya share ya futa daga gidan da sauri domin samo abun hawa.
Ni da Umma muka futa daga gidan kamar wasu zautattu! Shi kanshi hijab din dana sa a baibai
na sanya shi, hawaye ne kawai yake zura ra a idona shikkenan Mimi sai ta Allah a yanda na
ganta ina gani kamar kafin mu Isa a sibitin za'ace ta mutu.







*24/11/2019*
[11/25, 8:46 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*


*MALLAKAR_ BINTA UMAR*



*LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA
CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO
MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA
SAI TA CI SHI*

*62*


Lokacin da muka Isa asibitin goma da rabi ta wuce, Dan dai ma daran azimi ne akwai jama'a a
bakin asibitin suna siye da siyarwa, har ciki mai a dai-dai ta sahun ya shiga damu, Ya Aminu ya
biyashi kud'in sa, ni kam tuni na Dade da futowa daga a dai-dai sahun sai kyarma jikina yake yi.

Ko da muka shiga ciki babu mutane sosai wasu kujera muka samu muka zauna. Ya Aminu ya
nufi wani d'aki da sauri.
Waya ta dake hannuna na kunna na fara Neman numbar Jahid, sai da na kira sau biyar a
kashe, cikin mutuwar jiki na aje wayar a cinya ta, Ya Aminu ya futo daga dakin da ya shiga ya
nufo mu, fuskar sa babu walwala
Gaban Umma ya tsaya yace. "Yanzu wata nurse take min bayani cewar Mimi tana ciki har
yanzu ba'a futo da ita ba, kuma abun mamaki na dauka zamu samu mijin nata anan gurin
bab........ Kafin Ya Aminu ya rufe bakin sa, Jahid da Amjadu sun futo daga wani d'aki. Da sauri
Jahid ya k'araso gurin mu. Shi kam Amjad yana tsaye a gurin da yake. Jahid ya kalli Umma tare da fadin" Ashe har kun samu labari."
Umma tace"Ba dole ba wannan tashin hankali dai Allah ya sawwake, mana shi, yanzu ya jikin
Mimi yake. "!!?
Jahid yace." Jikinta Alhmdullahi Umma ku kwantar da hankalin Ku, jini ake bukata sosai za'a
kara mata saboda ta zubar da jini sakomakon fad'uwar da tayi."

Mik'ewa nayi zumbur nace"Muje ka sa mata nawa jinin kaji Don Allah ka cece rayuwar ta."
Murya ta na rawa na k'arashe maganar.

Jahid yace." Dole haka za'ayi muje a dauka a auna mu gani, idan yayi dai-dai sai a d'aura mata
yanzu ma an d'ibi na Amjadu ne."

Kallon shi nayi dake tsaye kamar wani maraya sai ya bani tausayi mutuka wata zuciyar tace ba
abun tausayi bane mutumin nan.

Wani daki muka shiga da Jahid ya dauki jinina ya duba yayi dai-dai Dana Mimi take ya umarce
ni na kwanta kan wani gado domin ya dauki jinin.


Amjad kuwa jingina yayi jikin bango hade da lumshe idonsa Sam ya kasa zuwa ma ya gaishe
da Umma saboda halin masifar da yake ciki.....Muryar Granny yaji ta shigo gurin cikin kuka take
fadin"Sai da tace kar ka futa kar ka futa ka futa gashi da ka futa ka dawo sumul k'alau! Da kai ita
kuma saboda tsananin son da take maka, ta fadi kan cikin ta."! Komai a kunne magangan da granny take yi domin dakin da nake ciki a bude yake, Jahid na

kalla Ina daga kwance nace "Nasan kasan dukanin abunda ya faru don Allah ka fad'a min
komai."?

Ba tare da tunanin komai ba Jahid yace." Wallahi Asma'u tsautsayi ne ya afka kan Mimi lokacin
da abun ya afku, tana hana Amjad din futa saboda jama'ar garin da suka kawo masa hari har
gida, garin kokarin rik'o rigar sa, kawai santsi ya kwashe ta ta fad'i kan cikin ta to shine fa take
ta zubda jini, amma insha Allahu zata dawo normal. Murya ta a cunkushe nace"Kana nufin ya sane ya futa bayan tace masa kar ya futa yanzu me
futar tashi ta jawo mana, ai dai gashinan da kunnen ka kaji Abunda kakar shi take fad'a ko." ?
Jahid ya sauke ajiyar zuciya tare da fadin "Tsautsayi fa baya wuce ranar sa, don Allah mu bar
maganar bana so Ku Dora alhakin abun kan shi." Shiru nayi ganin ranshi ya b'aci Jahid yana da
saukin kai da dad'in mu'amula amma baya son musu da taurin kai shiyasa nayi shiru kawai
amma cikin zuciya ta nayi alk'awari sai na fad'awa guy nan magana a kan Mimi komai daran
dad'ewa kawai don yaga tana da hakuri sai ya dunga gara ta kamar gare-gare kullum cikin
damuwar sa, da bata mata rai.

Jini Leda biyu a kauda a jikina nan Jahid din yace min na kwanta kan gadon na huta mintuna
talatin, INA kallon shi ya futa daga d'akin. Granny ce ta fad'o dakin tana kuka tana k'ara tisa
maganar da abunda ya faru. Fad'i take "wannan yarinya Ubangiji Allah ya tashi kafad'unta
amma babu shakka tana shan wahalar rayuwa. " Shiru nayi mata kawai ina bin ta da kallo. Amjadu masjid ya nufa domin yin sallah istigufari kawai yake a fili da Cikin zuciyarsa. Ta shi nayi
jikina babu kuzari na futo daga dakin, har yanzu su Umma na zaune cikin sauraron hukuncin
Ubangiji, kusan awa guda da shigar Jahid dakin da Mimi take ya futo, kallon mu yayi ya kalli a
gogon hannunsa sha biyu na dare saura minti ashirin, futa yayi ya nufi gurin Amjad dake cikin
mota
Amjad yace." Ta farko ko."? Daga kai Jahid yayi a hankali yace "Alhmdullahi ta farko kuma
munyi nasarar tsayar da jinin insha Allahu an sanya mata, shi gobe dole za'ayi scanning din
cikin domin ganin wane hali yake ciki.
Sunkuyar da kansa yayi cikin tawakalli yace." Allah ya kaimu lafiya Jahid ina cikin halin damuwa
ina bukatar rarrashin." Kafadunsa ya dafa yana rarrashin sa da kalamai masu sanyi.
Amjadu Rambo ya sanya ya je can *Mai takobi* ya karb'o nau'i kan abunci da abun sha, duk ya
sanya ya shiga dasu gurin mu, tsabar damuwa da fargaba bata bari munci komai ba, ko da
asubah ruwa kawai muka sha fafur abunci yak'i samun shiga a gurin mu, Ya Aminu dama ya tafi
gida ni da Umma ne kawai sai granny
Ko da muka yi sallahr asubah bamu koma ba, muna zaune daki daya muna jiran hukuncin
ubangji, granny na zaune kan dadduma da carbi a hannu Umma na kwance gefan ta. Itama dai
carbin ne a hannunta tana ja, cikin damuwa, ni kam ai fad'ar halin damuwar da nake ciki sai a
hankali, a Dan baccin da ya kwashe ni ne nayi mafarkin gani ga Mimi a tsaye a wani gurin tana
sanye da wasu fararan kaya duk jikinta fuskar ta dauke da wani irin annuri ta kara haske
mutuka, hannu nake mik'a mata tana mik'o min NATA hannun tana min murmushi, so nake in
kamo hannunta na kasa gani dai a kusa da ita amma na kasa kamo hannunta, gani nayi ta juya
da sauri ba tare da tace min komai ba ta fara d'ago min hannunta kafin in Ankara na nema ta na

rasa. Ni da kaina na fassarawa kaina wannan mafarkin tabbas Mimi zata yi nisa da rayuwar mu
Mimi zata yi nisa damu. Shine fa tunda na tashi na kasa sukuni ina kwance kan wani k'aramin
gado nayi lamo wasu irin hawaye masu zafi suna zubo min.

*****

K'arfe bakwai dai-dai Jahid ya shigo a sibitin cikin mota ya tadda Amjad yana bacci a zaune ya
bashi tausayi mutuka ya kalli su Rambo dake tsaye jikin motar yace."Kar Wanda ya tashe shi
Ku k'yale shi ya samu bacci shima Hutu ne. A gurin shi."
Gyada kai suka yi alamun sun amsa.

Kai tsaye dakin da Mimi take ya nufa, lokacin mu bamu futo ba, shiyasa bamu ga zuwan shi ba,
abun mamaki yana shiga dakin yaga nurses tsaye a kanta d'aya na goge mata baki daya na
kokarin gyara gadon, yaji dadin yanda ya same ta, gaisawa yayi dasu, suka futa da sauri, shi
kuma ya kalli Mimi fuskarsa a sake yace." Madam ya jikin ki."? A hankali tace"Da sauki." Yace."
Me kike ji yana miki ciwo a jikin ki."
Cikin ta ta nuna da hannunta." Yace." Kiyi hakuri zaji sauki insha Allahu." Mimi ta gyda kanta,
gurin yayi shiru na minti biyu dago kanta tayi, cikin sanyin murya tace"Sun kashe shi ko."!!!?
Jahid ya girgiza kansa alamar a'a saboda ya San ko wa take nufi.... Bude baki tayi zata yi
magana yace." Ko in kira miki shi ne."? Gyada kanta tayi, ya mike da sauri ya futa, lokacin mun
futo, muna zaune a wasu kujeru, granny ce ta tare shi tare da fadin"Kai Mujahid ka futo
zigwi-zigwi ko kallon mu naka yi ba kun barmu cikin alhini da tashin hankali ko."
Jahid shiru yayi mata kawai ya futa.

Mik'ewa tayi tana gyara d'aurin zanin ta tace"Ku tashi mu shiga ciki muna da kafafunmu sai
anyi mana iso Ku muje muga halin da take ciki baiwar Allah."
Aikuwa bayan ta muka bi, ni da Umma. Mimi na zaune kan bed kanta a kasa hawaye na
zurarowa a kuncin ta kuka take sosai, muka shiga, da sauri naje na rungume ta, tare da
fashewa da kuka INA fadin "Mimi ALLAH ya saka miki dukanin Wanda ya cuce ki." Rungume ni
tayi tana kuka sosai. Umma da granny suka k'araso gurin suna rarrashin mu, mussaman ita Mimi din. Zama nayi
kusa da ita hannuna cikin NATA, Yanzu zuciya ta tayi sanyi sosai na yarda mafarki karya ne tun
daga Mimi zaune a gaba muna magana da ita..... Dakin suka shigo hade da sallama. Tunda
nayi masa kallo guda na dauke kaina ina mamakin yanda hallintun sa suka jurkita mutum Dan
gaye Dan kwalisa mai kudi mai kyau mai jiji da kansa amma lokaci guda kamanin sa duk sun
sauya ya fyade lokaci guda, fuskarsa Tayi fururu, shi kanshi takalimin dake k'afafun shi na
wanka ne, kayan jikinsa ne kawai masu kyau.
Kai tsaye gurin Mimi ya nufa ya zauna kusa da ita inda bayana da nashi ya kusa haduwa sai
nayi saurin mik'ewa daga gurin, na koma kusa da Umma na tsaya, shi da Mimi kallon juna suke
yi sun kasa magana shine ma yayi k'arfin halin fadin "Momy ya jikin ki hope yanzu ba kyajin ko
wane irin ciwo ko."? Gyada kanta tayi har yanzu hawaye bai daina zuba mata ba. Sosai yake rarrashin ta da kalamai masu dad'i ko kunyar Umma baya ji har sai da yaga ta saki
tana dariya sannan ya daina shima ya saki jikinsa sosai ana hira dashi sama-sama shi da

Umma granny na sanya musu baki.
Kimanin Rabin a wa yayi ya mike tare da fadin zai je gida yayi wanka zai dawo bayan sallahr
azahar. Sallama yayi wa su Umma ni bishi da wani mugun kallo na tsana da kyama ji nake bani
da babban makiyi a duniya karma shi saboda guy a fiye son kanshi a duniya.


*****
Takardar scanning ta futa Dr Jahid ya shiga damuwa sosai da yaga abunda yake faruwa wato
baby girl dake cikin Mimi ta juya ma'ana kwanciyar ta ta sauya daga inda ake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login