Showing 90001 words to 93000 words out of 95753 words
Chapter 31 - BABBAN YARO Part 2 By Binta Umar Abbale .pdf
addu'ar ya mike a nutse ya dauki daddumar sa da glass d'insa dake aje a gefe ya nufi mazaunin
sa, ko da ya isa ba zauna ba toilet ya nufa cikin kuzari yati wanka ya fito fes dashi kasamcewar
ana zafi bai shafa mai ba, sai ya shafe jikinsa da turare ya sanya wasu ubansu parkinsan ash
coulor hade da wata hula mai kamar net fara tasa da ita, takalmi mai gidan yatsa yayi amfani
dashi ya d'aura tsaddan a gogon shi, kana ya manna farin tabarau din shi a fuskarshi, sai ya
kara wani uban kyau, kasancewar ya Tara kasumba bai yi aski ba, sai abin ya bada sha'awa
Amjadu ya saje da larabawan saudia domun duk kwakwar mutum bazai tab'a cewa ba balarabe
bane ga yanayin fatarsa lufluf domin har tafi ta wani balaraben goge wa fuskarsa babu walwala
a dauki wayoyin shi hade da wata k'aramar haka irin ta matafiya, kulle dakin yayi da key ya
sauka k'asa. Amjad ya nufin koma wa gida Cikin iyalinsa bayan yaje dakin Allah yayi addu'a ga
iyayen sa dashi kansa da sauran alumar musulmi.
Yana jirgi ya kira su Rambo ya Sanar musu gashinan kan hanya take suka wuce airport domin
tarar sa, Granny ya kira a waya ya fada mata, tace"Amma kayi mana bazata! Mai kake so a
girka ma." ? Murmushi yayi yace." Granny kuyi min Dambu da zogale." Dariya tasa tana fadin
"Kasamu k'ato Allah ya kawo ka Lafiya." Kashe wayar tayi tana kiran Iyami. Tace" maza a shirya
dambu mai kyau ga k'ato nan kam hanya." Iyami tace"Wallahi baby ce take kuka har yanzu taki
hak'ura kawai tana wasa sai ta fashe da kuka." Dariya granny tasa tace"Tana tuno uwarta ne,
jeki dauko min ita kije kiyi aikin ki." Da sauri Iyami ta dauko baby dake kuka har da majina.
Granny ta mik'a hannu tana son ta karbe ta ta make kafad'a wai baza ta zo ba, dariya tayi tana
fadin"Kaga ja'ira dole kuwa komai kukan ki kiyi shiru Ubanki na kan hanya. Tace iyami aje ta kije
kiyi aikin ki." Iyami ta ajeta a kasan gurin ta nufi kicin da sauri. Lokacin baby ta tsandare da
kuka, babu shiri granny ta dauke ta ta Goya Tana zagaye parlor da ita, Tunda ya doso kofar
parlor yake jin kukan sweetheart dinshi yaji ranshi ya sosu da sauri ya shiga ciki hade da
sallama k'asa_kasa granny ta amsa tana masa barka da zuwa, mamaki yake yi ganin baby a
bayan granny a goye amma taba kuka, wayoyinsa ya zube kan teble din gaban shi ya fara
kokarin daukar babyn da Granny take kokarin kwance ta, yace." Wai mai akayi mata ne take
kuka tun kafin na shigo nake jiyo ihun ta." Granny tace"Sheganta ka ce kawai wallahi tun da taje
gurun uwarta tayi kwana biyu Shikkenan ta dawo mana da rigima Don da kyar ma ta yarda da
iyami, nu kuwa sai nayi da gaske nake daukar ta." Ya gane inda maganar Granny ta dosa,
zama yayi cikin kujera yana goge mata fuska da hakincin sa, yace"Granny nifa bana ganin laifin
kowa sai naki ke da kika dauke ta kika basu." Cike da jin haushi yayi maganar. Granny tace"To
ka dawo ko zaka fara iyayin naka to me kake nufi iyayenta sunzo su dauke ta sai in hanasu ni
kam ban iya wannan k'ek'e da k'ek'en ba irin naka." Baice komai ba ya sanye leb'anshi na k'asa
bakin ta, kamar yanda yake mata tana jin jira, aikuwa ta kama tsotsa yarinyar bata manta ba.
Kallon ta yake yana jin wani irin tausayin ta cikin zuciyarsa duk sanda zai kalleta sai ya tuna
masa da Wife dinshi Mimi ko da yaje Saudia duk Rabin addu'ar shi tata ce. Baby Aysha ta fara
lumshe ido kalaman bacco still leb'anshi take tsotsa kad'an kad'an har bacci ya rinjayeta ta saki.
Ajiyar zuciya ya sauke ya rungume ta tsam a jikinsa tare da fad'in"Iyami ta gyara mata gurin
kwanciya tayi bacci."! Granny ta bude baki zata kwalawa Iyami kira kamar yanda ta saba. Da
sauri ya d'aga mata hannu yana yamutse fuska da ido ya nuna mata baby wai kar ta tashe ta.
Tsaki granny yaja ta mike daga gurin. Da kanta taje ta gyara mata gurin kwanciya ta dawo zata
karb'i ta kamar kurma haka ya zama Mik'ewa yayi ba tare da ya bata babyn ba ya nufi bedroom
d'insa da Yarinyar granny tayi sakaro da baki, tana fad'in"On ni naga iyayi da feleke a ka dawo
din zaka fara nuna mana iyakarmu ni da Iyami komai mukayi bamu iya ba hummm! Allah ya
sawak'e maka." Ni da Munnu ne zaune a Uwar dakin aunty Hauwa ta sanya muku tsuguna
cikin wani dogon bokitin na k'arfe inda ta sanya wata k'aramar tukunyar k'asa da garwashin
wuta had'e da wani mugun turare da wasu saiwowi masu wani irin kamshi, kullemu tayi a dakin
har da Dan mukkuli, tsaki babu irin wannan banyi ba, a ganina ni budurwa CE ba bazawara ba,
mai zasa aunty Hauwa ta dinga azabtar damu da turaran matsi kawai garin Neman gira a rasa
ido, tunda akace saura kwana goma sha hudu d'aurin auranmu aunty hauwa ta sanya mu a
gaba, domin har munnu ma da take surukar ta tace ita bata dauke ta a matsayin suruka ba,
k'anwar tace duk abunda zata min zata yi mata, kuma bayan haka Si Dan uwanta take gyarawa
Munnu tun tana jin kunya ta daina ji domin yau kwananmu uku a gidan aunt Hauwa tana yi
mana izaya iri-iri, magani kullum ta dama da nono mai Dan iskan bauri da wani irin k'amshi kai
hawa ka taje sai mun shanye tasa, wallahi ina daga tsigar jikina na Mik'ewa saboda yanayin
dandanon sa a bakina babu dad'i bauri yaji zak'i d'aci duka, ranar dai da taba ni zubarwa nayi
Munnu kuwa saboda kunya sai ta shanye tasa ta aje kofin ni kuwa kullum rigima muke da ita
kan hakan. Yanzu ma Mik'ewa nayi da sauri jin wani Abu na zuba daga k'asa na, zani na nasaki
na mai da pant dina. Munnu tace"Ya kika tashi ne." Cikin b'acin rai nace"Munnu ke in zaki
zauna zauna ki cigaba da azabtar da kanki kina budurwa ace wani Dole sai kin matse mtssss to
wace irin katsewa kuma ake buk'ata. " munnu tace "Don Allah ki koma ki zauna Wallahi tunda
kikaga ta dage akanmu hakan yana da amfani." Tsaki naja nace"Sai kiyi ke ni dai na gaji." Kofa
na nufa ina bugawa hade da kiran sunan aunt hauwa nace"kizo ki bude min zan shiga band'aki.
" bude min tayi taba fadin kiyi sauri ki fito kar maganin ya sane so nske ya bi jikin Ku sosai."
Hararata nayi ganin ta juya baya zumb'ura baki nayi na shiga band'akin ta dake parlor. Ina
tsungawa naga ni bu mai yauki na dilala daga gabana, dama tun da aunt ta sanyamu a gaba
nake jin wani azabbaban feelings na taso min. Ruwan zafi cikin wata butar.k'arfe na dauka na
daureye gurin sosai sannan na fito raina duk babu dad'i
*30/11/2019*
*BABAN YARO*
*MALLAKAR BINTA UMAR
*69*
Shirye-shirye ta kowa wane fanni ya kammala Ya Aminu ya had'a lefe na gani na fad'a sosai
Umma da aunt hauwa sukayi kokari a kansa, yanzu nawa lefan ake jira sai a fara Rabin goro
kullum muna tare da Jahid a waya muna shirya tsarin buki da yanda zai kasance.
Momyn Mujahid ce take kai kawo a parlor ta takasa tsaye ta kasa zaune wato Mujahid ya
yaudare ta ya rufe ta sun hada baki da ubanshi ya bujerawa bukatar ta, lallai ne ka haifi da a
cikin ka ya wulakanta ka lallai zata nuna masa iyakarsa, yanzu ta sakko daga sama dalili shi
mijin NATA ya kira ta tazo taga kayan lefa kuma saboda sun raina mata hankali wai itace zata
nemi masu kaiwa don haka baram!_baram suka rabu da mijin nata ta sauko a fusace jiran
zuwan Jahid din take domin tayi masa magana ta k'arshe kan auran.
Tunda ya shigo yaga tana kai kawo hankalinsa ya tashi yasan dole duk abunda yake b'oye wa
ta sani, ko k'araso wa bata bari yayi ba ta karasa gurinsa a zafafe ta zabga masa mari Tana
huci! Kamar zakanya tace"Ni zaka yaudara Jahid wato kun hada haki da ubanka kun rufe ni
saboda baka dauke ni a bakin komai ba ko? Jahid yayi shiru hade da yin kasa da kansa. Ta
cigaba da cewa "Wallahi in har nice na haifeka baza ka auri yarinyar da ta zageni ba, idan kuma
kayi ganganinci auranta to babu shakka a ranar zaka sake ta ko kuma in d'aga maka nono don
tsine maka zanyi wallahi tallahi kaji domin bazan yi kaffara ba."!!! Ta k'arashe maganar tata a
zafafe! Ya wani irin huci!
Jahid ya shiga cikin wani irin mugun yanayi a lokacin gumi ya dinga tsiyayar a jikinsa duk
yanda yaso ya fahimtar da mahaifiyar sa al'amarin ta kasa fahimta. Wasu mazan sukan fuskanci
matsala daga gurin matayen su a sanda zasu kara aure, shi daga gurin mahaifiyar shi ya
fuskanci matsala. Mik'ewa yayi baya ko kallon gabansa, ya fita daga parlor. Wani irin kallo ta
bishi dashi ta ta tabka wani irin tsaki, ta zauna kan kujera tana fadin" da in hada jini da talaka
gwara duk abunda zai faru ya faru.
Jahid kuwa kai tsaye b'angaran Amjad ya nufa a lokacin hankalin sa a tashe! Granny na
ganinsa cikin wannan halin ta tabbatar babu lafiya, zama yayi kan kujera hade da dafe kansa,
granny Tace "Tabbas komai yayi tsanani maganin sa Allah, Mujahudu akwai damuwa a tattare
da kai. Ya d'ago kansa yana kallonta, kawai sai taga hawaye a fuskar sa yana zubah, cikin
mamaki tace" kafadamun damuwar ka Insha Allah zan taya ka da addu'a. " Cikin karkarwar jiki
ya warware mata dukanin abunda yake faruwa. Granny ta jima tana mamakin al'amarin daga
bisani tace"Tabbas Hajiya Sa'a ta tabka babban kuskure, waye ya fada mata ana jayayya da
al'amarin aure duk yanda bakason hada zuri'a da mutum idan Allah ya kaddara faruwan haka
babu makawa sai ya faru idan tana tsananta kamar Yanzu Allah sai ya dauke ta ayi babu ita,
tashi muje gurin ta." Jahid ya mike da sauri ita kuma dauki hijab dinta ta zura, suna fita motar
Amjad na shigowa gidan, yana kwance a bayan mota ya hango Jahid din da granny sun nufi
motar sa, duk da cewa Jahud ya fahimce shine bai tsaya ba, da gudu ya fafari motar sumar bar
gidan.. Shi kuma Amjad sai dinga tunanin ko wanine babu lafiya cikin iyalin Jahid din, ya dauki
granny domin taje ta dubasu. Sam bai kawo komai cikin ranshi ba, ya shiga gida yanayin tozali
da sweetheart dinshi ya manta da koma.
"Sosai granny take fahimtar da Momy amma ta gagara ganewa da k'arshe ma so tayi tai mata
rashin kunya inda take fadin" Kinga Hajiya d'anki ko nawa da zaki dame ni lallai sai na yarda,
shin kin Sam irin rashin mutumcin da yarinyar tayi min kuwa, tsinanniyar yarinya mummuna 'yar
gidan malam shehu irin wannan har ta kalle mu ni da aminyata tace muna warin dauka da
bleecing a i wallahi Jahid ya sake ya auri yarinyar nan sai na tsinke masa."
Granny tace"Ki daiyi hakuri Asma'u yarinyar arziki ce Wallahi akasi aka samu kuma hada
zuria dasu akwai albarka Hajiya baki San ko akwai rabo tsakininsu ba, sai ki mutu saboda
wannan abunda kikayi ubangji baya so." Jin abunda granny tace ne yasa Many zuburowa!
Tace"kaji ni da tsohuwar najadu tsohuwar kawai! To wallahi sai dai idan kece zaki mutu,au!!
Fatan mutuwa kike mun, aikin banza to wallahi ba yanzu zan mutu ba." Jahid ya Dora hannunsa
aka cikin tsantsar tashin hankali da nadamar dauko granny inda yasan wannan cin mutumcin
za'ayi mata da bai dauko ta ba, ya zama dole duk son da yake wa Asma'u ya hak'ura da ita,
domin yana hango mugun rikici a gaba idan ya aure ta Hausawa suka ce idan so cuta ne hakuri
magani ne, nan ya mike ya futa daga parlor a karo na biyu, granny ta mike cike da taikacin da
b'acin rai tace"Duk yanda naso nussashe dake kin kasa ganewa har kina Neman kiyiwa danki
baki, ni zagin da kikayi min bai dame ni ba, tunda kin kwatanta hali irin na Asma'u da kike cewa
bata da tarbiyya Shikkenan na barki lafiya." Momy yaja tsaki da k'arfi tana fadin "Allah ya
rakataki gona, nace Umma ta gaida Ayshaaaaas."! Granny ko juyowa batayi ba cike da takaici
da damuwa ta samu Mujahid tsaye a gurin yana kiranta, mota ya bude mata ta shiga da sauri
suka bar gidan. A hanyarsu ne granny take rarrashin sa da kalamai masu sanyi kana tace "
Tunda mahaifiyar ka ta nuna bata so tom shawarar da zan baka ka hak'ura ka kwantar da
hankalin guri guda rashin Asma'u ba zai hanaka rayuwa ba insha Allah zaka cigaba da rayuwa
Cikin amincin Allah da yardar sa, idan Aure kake so ka sake samun mace wacce zucuyarka ta
kwanta maka sai is aura mutukar ta amunce din, wannan shine shawara kayi wa uwarka
biyayya." Amjad yace." Granny ban taba nadama akan al'amarin auran nan ba sai yau, da
Momy ta ci miki mutumci kawai domin kina so ki fahimtar da ita, insha Allahu na hak'ura da
Asmau amma INA Neman wata alfarma agurun ki." Tace" kafad'a komeye insha Allah mutukar
INA da iko dashi zanyi maka." Yace." Inaso al'amarin auran nan ya koma kan Amjad ba tare da
sani ba inaso ne ranar d'aurin aure yaji bazata !."
Granny tace'' hak'ika ka cika Aboki na gari Mujahid kuma idan kayi haka babu shakka ka
kyauta min, domin ni kaina ina tunanin matar da zai je ya auro wacce zata kula da baby Aysha
tsakani da Allah,Dole sai ita Asma'u da take a matsayin Uwa a gare ta, mungode mutuka da
alkairi ka." Jahud yace." Granny Amjad yafi k'arfin komai a gurina wallahi." Tace"Yanzu abun
damuwar shine ita Asma'u kana ganin ba'a shiga hakkinta ba."? Murmushi yayi yace." Nasan
inda zanyi da ita itama baza tasan abunda yake faruwa ba har a d'aura aure zanje cigaba da
zuwa gurun ta babu abunda zan FASA, gefe guda kuma zan je na nemi Kawun ta mu kashe
magana." Granny tace"Kayi nufin alkairi Allah yayi maka jagora Kai kuma ubangiji Allah ya
sanja maka mafi alkairi. " murmushi yayi ya cigaba da driving har ya sauke ta gida ya wuce ofis
din mahaifinsa domin ya Sanar dashi abunda ya yanke, to shima bai Wani jayyaya ba tunda dai
Shi Jahid din yace ya hak'ura to shi meye bashi sai fatan alkairi yayi yace inda Allah zamu
cigaba da shirye-shiryen d'aurin aure kamar yanda muka tsara, Cike da kwaran gwiwa Jahid ya
nufi gurin Kawu Yunusa, duk abunda yaje faruwa ya Sanar dashi a bazata Kawu yaji al'amarin
dad'i kamar ya kashe shi sai ya dinga shiwa Jahid albarka kamar me."take ya shaidawa 'yan
uwansa suka soma shiri amma ya gargadesu da cewar bayaso maganar ta futa har Asma'u taji.
Suka ja bakinsu suka yi shiru.
Duk wasu shirye-shiryen Jahid ya kammala su dai-dai da kayan da zasu sanya ranar d'aurin
aure suna hannunsa hakanan kayan lefe na kece raini da ya yahadawa Asmay an kai kwanaki
uku da suka wuce, shi ta b'angaran sa komai ya dai-dai ta. A zahiri ya nunawa Momy nsa ya
janye maganar shiyasa ta saki ranta, kuma Mijin ta bai kara tayar mata da maganar ba sai ta
yadda da maganar.
Saura kwanaki uku d'aurin aure aunt hauwa ta bude mans wuta kullum cikin durkar magani
kullum INA kwana da ciwon ciki da wata muguwar Sha'awa Mara fasali sai in sanja pant sau
uku a rana, maganar gyaran jiki ba'a cewa komai aunt Hauwa na da abokai iri-iri wata kawarta
ce ta tsaya a kanmu ni da Munnu ta hado mana kayan gyara jiki kullum sai munyi dake aunt
Hauwa ta iya hadawa sosai take samu a daki muna murje jikinmu bayan mun kama wani irin
turare ne mai k'amshin tsiya shima zata sanya mun mulke sako da loko na jikinsu dashi sai
munyi a wa daya tukkuna zamu wanke jikinmu tuni wani sihirtaccan kamshi ya kama fatar jikin
mu, duk inda muka zauna sai kamshi ni kaina bala'in son k'amshin jikina, kullum muna tare da
Jahid a waya, duk wasu k'awayenmu na nesa da na kusa mun gayyace d'aurin auramu, Alina
sai wani shishshige min take Sam ban Wani saki jiki da ita ba duk sabgar buki da ita akeyi taki
yin zuciya.
*Ranar d'aurin aure*
Amjad Jahid Khalid Ma'aruf suka futo cikin shiga iri daya shadda CE fara tas dinki babbar Riga
da 'yar ciki fad'ar tsadar shaddar bata lokaci ne, takalman su iri daya hulunsu irin daya
agogonsu iri daya komai iri daya sukayi amfani dashi kamar yanda suka yi ranar d'aurin auran
Amjad da Mimi mota suka shiga guda Khalid ne take draving har suka isa gurin d'aurin auran
dake cike makil da jama'a take wani maroki ya saki wata shegiyar gangarsa ya fara wasa Amjad
da fadin"Ango Na Asma'u sarauniyar mata gwarozo a cikin maza! Sai Amjadu! Hak'ika Wannan
yarinya tayi dace da miji na nunawa sa'a fari mai farar aniya yaro mai halin manya gugan k'arfe
sha kwarafniya gaba salamin baya salamun.!!!!!!!!! Jama'ar dake gurin suka dinga mamaki yaya
ga ango kuma maroka na wasa abokin ango wai meye yake faruwa ne."! Shi kuwa Amjad Sam!
Bai Kawo komai cikin ransa ba, kawai dai yafi tunanin ko don yanayin sunansu daya sa Jahid
din yasa marok'an suka kasa ganewa wanene angon a cikinsu.
Kawu Yunusa sai kaiwa yake yana kawo wa ya sha babbar rigar