Showing 66001 words to 69000 words out of 95753 words
Chapter 23 - BABBAN YARO Part 2 By Binta Umar Abbale .pdf
sai asibitin mu
muna da likitoci k'wararru so kar ka damu."
Gyada kansa yayi yace." Yaushe za'ayi aikin." ? Jahid yace." Insha Allah ranar Monday za'ayi."
Saura kwana uku kenan."? Jahid yace." Eh saura kwana uku. " OK Allah ya kaimu nagode
K'warai. "
Nan granny ta futo daga kicin ta same su, suka gaisa da Mujahid cikin barkwanci sannan ya bar
gidan
Amjad din ta kalla a nutse tace" Aishatu ta tashi ne."? Girgiza kansa yayi kamar wani maraya.
Granny tace"Sai hakuri ka kwantar da hankalin ka naga kamar ka tada hankalin ka, insha Allah
komai me wuce wa ne." Shiru yayi mata kawai. Ita kuma ta wuce daining domin shirya kayan
breakfast.
*******
A gajiye na dawo daga makaranta na zube rumfar Umma cikin gajiya da ishirwa nace"Wallahi
Umma da nasan zan sha wahala haka da ban dauki azimin nan ba, kinga yau juma'a anyi rana
mutuka ."
Tace"Hakane ai zaki samu lada sosai. " lumshe idona nayi kawai ishirwa Duk ta dame ni, so
nake a idar da sallahr la'asar nayi wanka ko zanji dadin jikina.
*********
Tunda motar shi ta shiga prison din, masu gadi da ma'aikatan gurin suke murna da zuwansa
dama duk karshen wata yake ziyartar su, irin wannan ranar ta juma'a bayan sakkowa daga
sallahr juma'a.
Daurarru dake kulle suna hangoshi ta tagogin dakunan su. Murna da farin ciki ya ishe su. Bayan
motar shi wasu manya manyan motoci ne na company *Dangote* suka dinga shigowa cikin
prison din, dukaninsu suna dauke da kayayyakin abunci na'ui ka daban-daban.
Ba tare da b'ata lokaci ba, 'yan jarida dake gefe guda suka mike domin fara'a aikunsu, dama
duk wannan ranar sukan kasance a gurin da suka San yana zuwa kai ziyara, matasa majiya
k'arfi ne suka fara sauke kaya suna ajewa inda aka tana da
Yana cikin mota Duk yana kallon abunda yake faruwa da irin hayaniyar da ake a gurin. Sai da
suka gama kwashe kayan tsaf, sannan ya futo daga motar Aikuwa 'yan jarida suka yi caaaa! A
kansa basu nemi suyi magana dashi ba, amma sun baibaye shi suna d'aukar hotonsa hade da
vidio duk wani motsi NASA sai sun dauka duk inda ya sanya kafa sai sun bishi.
Ofis din shugaban gurin ya nufa.
Suka bishi a baya sai da suka ga ya shiga ofis din sannan suka dakata, Rambo da doh-doh
suka tsaye bakin kofar suna zare ido.
Hamshakin mutum ne zaune kan kujerar sa sai juyi yake, kana kallonsa zaka San bashi da
imani fuskarsa a murtuke take leb'anshi baki kirin kana gani kasan yana shan taba da abunda
ba'a rasa ba, yana da manya manyan idanu,hanci sa yana da fad'i amma ba sosai ba, sannan
yana da kiba dai-dai misali. Duk wani Abu da yake faruwa ya na gani ta CCTV Duk ta hasko
masa komai da zuwan Amjadu gurin da yanda mutane suke ihu da yanda 'yan jarida suke
turereniya akan sa, duk ya ga komai.
Wani irin b'acin rai da kyashi duk suka dame shi, mugun haushin yaron yake ji saboda ya zame
su kadangaran bakin tulu.
Abun mamaki suna hada ido da Amjadu din yaji gabansa ya fad'i, Yaron yana da kwarjini da
haiba, take ya gyara zama yana masa barka da zuwa
Kafin ya zauna hannu ya fara mik'a masa suka gaisa a muntunce.
Sannan Amjadu yace." Fatan duk na same Ku lafiya."?
Alhaji Gali yace." Lafiya lou Alhmdullahi Ashe ka dawo gari. "
Babu walwala a fuskarsa yace." K'warai kuwa jiya na dawo insha Allah."
Kamar gaske Alhaji Gali yace." Ka cika Dan halak me son talakawa abunda gomnati ya dace
tayi bata yi kai gashi kayi mungode K'warai ubangiji Allah ya kara k'arfin a arziki. "
Amjadu ya bashi hannu suka gaisa, yace." Naga muna daf da shiga wata me albarka ga kayan
abunci nan insha Allah daf da sallah zan turo musu kayan sawa." Alhaji Godiya yake kamar
gaske.
Amjadu ya Mike hade da yi masa sallama ya futa.
Yana futa Aljani Gali ya dauki wayarsa ya fara kiran me girma governor, sai da ya kira sau
kusan uku sannan aka dauka, da sauri Alhaji Gali yace." Allah ya tai make ka?" Governor ya
gyara zama kan kujrrarsa Cikin ginshera yace." Tare da kai mutumin." Gali yace." Yaron nan fa
ya dawo wane shiri zamu yi a kanshi."? Governor yace." Na sani ai duk wani Abu da ya faru a gidan yarin gashi a gabana ina gani,
akwai shirin da muke masa ni da su Alhaji Hashimu insha Allahu sai mun rusa shi.
Alhaji Gali yace." Yana da kyau hakan , gaya nan ya kawo uban kayan abunci ." dariya governor
yayi yace."ka d'ibi iya yanda kake so ka bawa Wanda kake so sauran a zubah a store na gidan,
kar ka sake ka sakar mu, ka cuzguna musu abunci sau d'aya nake so a dunga basu haka ruwa
ma sau d'aya zasu sha a rana." Alhaji Gali ya saki dariya tare da fadin"Yallab'ai ai ba sai ka fad'a ba, haka ce zata kasance
insha Allah. "
Dariya suka kyalkyale da ita sannan suka kashe wayoyin su, dukanin su suna cike da farin ciki
da annushuwa.
Amjadu kuwa bayan futar sa daga gidan prison din kai tsaye gidan marayu suka nufa. Nan ma
duk wani Abu da ya sauke gudin prison din haka ya sauke musu, marayu da marasa galihu
ranar murna da dad'i duk ya ishe su, sosai kuma yayi Rabon kudi, musaman mata masu raino
rainon yara k'anano sosai suka samu kud'in a gurun shi.
Sai daf da magariba ya koma gida. Granny da Mimi na zaune a parlor duk suna kallon abunda
ya faru a TV.
Granny ta hau share hawaye tana tuno iyayen sa , addu'a take masa Allah ya kare shi daga
sharrin magauta tabbas idan ya zama shugaba a garin kano za'a huta dashi.
Amma Sam bata yi masa sha'awar mulki.
*********
K'arfe bakwai ta ranar lititin dai-dai tayi mana a babban hospital din Nasarawa dake jahar kano.
Ranar ina da makaranta amma haka Na kashe ta saboda nasan ko naje babu abunda zan iya yi
tun jiya nake Cikin halin damuwa INA wa Mimi addu'a Allah yasa ayi lafiya,
Umma kuwa kwanan zaune tayi da carbi a hannu, a subar fari aunt hauwa ta iso gida saboda
haka gari na waye wa muka nufi asibiti kowanne bakin shi da dauke da addu'a.
Muna zaune suka shigo a sibitin Amjadu da granny sai Mimi dake rungume a jikinsa, ta kara yin
haske sosai. Tana ganin Umma ta rugu da gudu ta rungume ta hade da fashewa da kuka,
Umma ta fara rarrashin ta tana fadin"Mimi kina dauke da da lalura kina gudu, ki daina kuka kinji
ko." Cikin kuka Mimi tace"Umma ki YAFE min ko da Zan mutu." Naji gabana ya fad'i jin abunda tace
Kallonta nayi nace"Don Allah ki daina mana wannan maganar Mimi."
Shiru tayi min ta k'araso gurin aunt Hauwa dake share hawaye rungume ta tayi tana kuka, aunt
rarrashin ta take da kalamai masu sanyi.
Hada ido muka yi dashi yana yana tsaye jikin kofa Yana kallonmu jikin sa sanye da shadda fara
tas! K'afafun shi sanye da takalman me gidan ya tsaya baki , yayi kyau sosai da sosai,
Idan ba idona ne yayi kin gizo ba sai naga ya fad'a idanunsa sun zurma ciki, a hankali ya
k'araso kusa da Umma hade da Dan risanawa yana gaishe ta.
Granny ma k'araso wa tayi tana tsokan Mimi alhalin itama Cikin zuciyar ta daurewa kawai take,
tun kafin Suzo take share hawaye: Cikin k'arfin hali aunt Hauwa take rarrashin Mimi hade da
karfafa mata gwiwa, shi kam Amjadu suna gama gaisawa da Umma bar gurin.
Motar sa ya nufa, ya zauna bayan ya kunna karatun alk'urani, me girma yana saurara
Muna zaune aka zo a tafi da Mimi.
Duk muka bita da addu'ar samun nasara.
K'arfe Biyu da kwata Dr ya futo ya same mu inda muke zaune.
Umma ya kalle ta da ta zuba masa ido,Sam ta manta da wata surukutaka dake tsakanin su,
tsugunawa yayi suka gaisa a mutum CE.
Tace"Ina fatan anyi Lafiya Dr."?
Cikin kwantar da hankali yace." Alhmdullahi anyi nasara insha Allahu an samu damar Ciro
k'wayar hallitar da izinin ubangiji d'ayan zai cigaba da rayuwa cikin hukuncin Allah kuma zata
haife shi lafiya."
Ajiyar zuciya Umma ta sauke tana tayi ma Dr godiya duk ta rasa yanda zata yi
Sauri kawai nake na idar da sallah ta tun a sujjadar k'arshe nake godewa Allah.
Granny da aunt Hauwa baki har kunne sai addu'a suke masa.
Ciki ya koma ya futo da wani Abu cikin kwali. Kai tsaye hanyar futa ya nufa.
Motar Amjad ya nufa domin yasan yana nan.
Yana ganin zuwan Jahid din gurin shi ya futo daga motar yana bin hannunshi da kallo cikin
fad'uwar gaba.
Bakinsa na rawa yace." Meye wannan."?
Jahid yace." Alhmdullahi wannan hallitar ce da aka ciro dole zaka gani sannan ka binne domin
ubangji ya soma fidda masa hallita ."
Zuciyarsa babu dad'i yace." Jahid Dole sai na gani hummm? Kawai a binne ubangji Allah ya
bani wani."
Cikin sanyin murya ya fad'i maganar.
Ajiye kwalin Jahid yayi ya dafa ka fad'ar Amjad d'in yana fad'in"Colm down Aboki na, ba dole
sai ka gani ba, hakkin kane Dole a nuna maka, amma insha Allah ni anan zan sanya a binne
shi, ka kwantar da hankalin ka."
A tausashe ya k'arasa maganar.
Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke yace." Ya jikin Momyna. " ? Dr jahid yace." Alhmdullahi jikinta
da sauki hakama babynta insha Allahu zata samu kulawa ka kwantar fa hankalin ka."
Hamdala yayi a fili yana godewa Allah yace." Muje in ganta OK." Ganin yanda ya daga hankalin
sa yasa Jahid din kasa yi masa musu, domin babu halin yace. Masa ba'a futo da ita ba tukkuna,
dole ya jagoran CE shi har dakin da Mimi take kwance.
*22/11/2019*
[11/23, 10:28 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*
*MALLAKAR_ BINTA UMAR*
*LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA
CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO
MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA
SAI TA CI SHI*
*60*
Lokacin da zasu shiga dakin da Mimi take ji nayi kamar in biso domin na k'agara na ganta,
Ashe bani kad'ai ba har su Umma, nauyi ya hanata magana granny tace"Muma zamu iya shiga
gurin ta ne."? Mujahid yace." A'a granny Ku bari a futo da ita shima Dan dai mijinta ne, kuma in
na hanashi zai iya shak'eni ga yadda yake muzurai."! Dariya suka yi ni kam yak'e kurrum nake yi nasan da babu shi tsaf! Mujahid zai shiga dani gurin
Mimi.
Kusan Mintuna ashir yayi a ciki sannan ya futo domin shi Mujahid din tunda ya raka shi ya futo
ya koma bakin aiki. Kallonsa muka yi dukaninmu,
Tsayuwar sa ya gyara kusa da kakarshi ya futo da wani farin hankici daga aljihun sa, yana goge
fuskar sa.
Granny tace"Ya jikin nata ta farko amma."?
Girgiza kansa yayi kamar ba yaso yace." Bata farko ba amma dai Jahid yace." Zuwa magariba
zata farko insha Allah."
Hamdala tayi tana kallon mu cike da farin ciki tace"Kunji abunda Mujahid yace ko. ? Muna
sauraren ikon Allah."
Umma tace"Shine abun dubawa kuma shine abun godiya." Shiru ne ya ratsa gurin na minti biyu
kana yace." Zan wuce ina sa meeting da ma'aikatana bayan sallahr isha'i." Umma tace"Ubangji
Allah yayi maja jagora mun gode kwarai."
Da "Ameen yake amsawa ya futa daga reception din cikin tafiyar shi ta zaratan maza. Yanzu ya
samu kwamciyar hankali kuma jakinsa na bashi cewar akwai nasara kan aikin da a kaiwa Mimi
fatan shi ta farfado lafiya domin yanzu a zuciyarsa yaji yana yi mata wani sahihin so na gaskiya
ga wani mugun tausayin ta da yake ji mussaman idan ya tuno rayuwar ta, ubanta ya gudu ta
taso bata San mahaifiyar ta ba, shiyasa kullum yake jinjinawa Ummansu Asma'u uwace ita me
baiwa D'a mama a yanda ya fuskanta yanda ta rike Mimi tamkar ita ta haifeta tana kula da ita
sosai kular da bata yiwa 'yar cikin ta Asma'u.
Aikuwa kamar yanda Dr ya fada bayan sallahr magariba Mimi ta farko kuma sa sunana a bakin
ta, take Jahidi ya zo ya kira ni.
Ina shiga dakin muka hada ido da ita. Idanunta duk sun kode sunyi ja sosai.
Kallona take yi har na karasa kusa da ita gefan bed din na zauna hade da kamo hannunta na
rike tamau.
Nace"Mimi ya jikin naki."?
A hankali tace"Da sauki Habibty kice wa Jahid ya bani ruwa nasha yak'i ya bani. "
Mujahid na kalla cikin tuhuma yace." Ba yanzu za'a bata ruwa ba."
Hannuna ta rike lebanta duk ya bushe, Mimi tayi mutukar bani tausayi. Nan na zauna ina
rarrashin ta, su Umma suka shigo dakin. Tunda ta ganta hankalin ta ya kwanta.
Granny kuwa fad'i take"Sannu kinji ko kishiya ta ko wace haihuwa da irin ta sai dai fatan Allah
yasa Ku gama lafiya."
Dr Jahid futa yayi daga dakin ya barmu da Mimi. Hannuna na nata bacci ya kara dauke ta.
Kin tashi nayi daga gurin bare in cire hannuna daga nata har wajan k'arfe goma na dare,
Amjadu ya shigo lokacin granny har ta soma gyangyadi.
Sallamar sa naji dakin gabana ya fad'i , ciki-ciki na amsa masa, domin Lokacin Umma na toilet
aunt Hauwa kuma ta tafi, muryar baban su Munnu na ji sun shigo tare.
Amsawa nayi da sauri na juya INA masa barka da zuwa.
Kan Mimi ya tsaya cike da tausayi da al'ajabi yake fadin"Ashe Abunda ya faru dake kenan
Mimi."
Umma dake futowa daga band'aki tace"Sannu da Zuwa."
Baban su Munnu ya juya suna gaisawa da Umma.
Nan yake jajan ta mata abunda ya faru yana kara addu'a ga Mimi tare da fadin"Sam shi bashi
da labarin abunda yake faruwa in banda shi Amjad din ya fada masa a waya.
Umma tace"Alkairi shi ake fada bata tashin hankali ba, duk da dai nasan hakkin Ku ne a fada
muku munyi laifi."
Baban su Munnu yace." Ya wuce yanzu babu Lokacin yin k'orafi ta lafiyar ta Muke ubamgji Allah
ya bata lafiya ."
Duk wannan abun da ake gogon yana tsaye kusa da kan Mimi ya rutsawa fuskar ta kallo kamar
wani maye gani a zaune bayan haka kuma ko kunyar su Umma baya ji.
Sallama Baban su Munnu yayi mana ya kama hanya ya futa Amjad din ya bishi a baya Umma
kuwa zama tayi kan wata kujera tana fadin"Ni na manta shaf ban sanya kin kira Munnu a waya
kin fada mata halin da ake ciki ba, in yaso ita sai ta fadawa Baban nasu."
Nace"Wallahi nima na manta shafa."!
Granny ce ta bude ido da sauri tana kallanmu ni da Umma tace"Kaddai bacci nayi a gurin
nan."? Umma tayi murmushi tare da fadin"Bacci kika yi amma bai yi tsayi ba." Mayafin ta ta
gyara tana fadin"Haba shiyasa kamar a mafar ki naji muryar k'ato ya shigo ko."
Nida Umma ka kalli juna wanene k'ato kuma."? Kafin muga tunani mu ya shigo dakin hannunsa
rike da wasu manya manyan ledoji.
Kusa da Umma ya aje ledojin cikin nutsuwa yace." Umma zamu tafi gida. Ga abun bukata nan
insha Allahu babu matsala."
Umma tace"Godiya muke Ubangiji Allah yayi albarka a rayuwa. "
Granny mik'ewa tayi tana wa Umma sallama, shikam tuni ya futa ko kallon inda nake zaune bai
yi ba, Kai sai ince tun d'azu da safe da muka hada ido dashi ban kara ganin ya kalleni ba ko da
wasa
Shige da fucen sa kawai yake.
Naji dadin Wannan sauyin da aka samu ta b'angaran shi.
Ya daina samun ido zan sake sosai dama idanunsa mugun dafi ne a tattare dani.
****
Alhmdullahi Mimi kullum samun sauki take yi yau kwannmu goma a sibiti kuma Alhmdullahi
jikinta yayi sauki sosai tunda tana cin abunci Mara nauyi kuma tana zuwa ko INA, kwakwaran
motsine dai Dr ya hanata
Amjadu kuwa kullum sai yazo shi da granny tare da kayan ciye-ciye hummm mu dake muke
jinya maimakon muyi rama muka yi kiba ta sati biyu sosai na ware ganin baya shiga harkata ko
yazo gaisuwace take hadani dashi, to shima tunda yaga jikin Mimi yayi sauki baya wani dadewa
yake tafiya sabgoginsa, Kullum ina cikin Ac fatata tayi luwai gashi kullum muna tare da Mujahid
muna shan soyayarmu ko Amjadu yazo ya tadda mu baya nuna damuwar komai karkari su
gaisa ya wuce ciki.ko a fuska baya nuna Alamun wani Abu wai don ya fanni tare da jahid ni ni
kaina yanzu tunani sauayrwa shi nace tafarar daya duk wannan rawar kan da yake akaina ya
daina yi, ta lafiyar matar shi yake.
To nima hakan yayi mun dad'i yanzu zuciyata ta Riga ta tsayar min da Mujahid a matsayin miji
maganar mu har gaban su Kawu Yunusa domun da suka zo duba Mimi sun gaisa da Mujahid
din a matsayin sa na me Neman aure na.
*****
Kwanan Mimi goma sha takwas ta warware sosai ni kuma dama tuni na koma gida saboda
makaranta, take Mujahid ya sanya ranar sallamar Mimi tare da tsauraran matakai babu yawan
motsa jiki da cin abun mai nauyi babu kar zurga zurga tayi yawa, shima Amjad din banda
tsawwala gurin yin sex wannan sune sharadan da Dr ya shimfid'a wa Mimi.
Granny itace ta dauki nauyi komai na gidan tunda anyi anyi dani kan na dawo gidan da zama
har Mimi ta haihu naki ya Umma ma babu yanda bata yi